Hamza na daya daga cikin mutanen da ba karamin sha zaiwa giya kafin ta bugar dashi, yasan ba ita bace ta saka shi bacci, duk da ya kwankwada daren jiya saboda yanda ranshi yake a bace, dan haka da wani irin ciwon kai ya tashi, kan na shi ya kara sarawa saboda aman da yayi na giyar. Shisa baya so yasha ta da wannan yawan, ran shi a bala'in bace yake jin shi har lokacin. Dan bayan ciwon kan da yake har wani dumi yaji ya dauka na bacin rai, dan karamin kitchen din da turawa sukafi yiwa lakabi. . .