Skip to content
Part 2 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Hamza na daya daga cikin mutanen da ba karamin sha zaiwa giya kafin ta bugar dashi, yasan ba ita bace ta saka shi bacci, duk da ya kwankwada daren jiya saboda yanda ranshi yake a bace, dan haka da wani irin ciwon kai ya tashi, kan na shi ya kara sarawa saboda aman da yayi na giyar. Shisa baya so yasha ta da wannan yawan, ran shi a bala’in bace yake jin shi har lokacin. Dan bayan ciwon kan da yake har wani dumi yaji ya dauka na bacin rai, dan karamin kitchen din da turawa sukafi yiwa lakabi da kitchenette ya shiga, dan wajen girkine da zaka iya dafa abin kari ko wani abu dai marar nauyi.

Jikin shi sanye da gajeran wando, amman ya saka riga mai dogon hannu hadi da hula ya saki hular a bayan shi, ya riga yayi wani irin sabo da riguna masu dogon hannu, komin zafin da akeyi kuwa, sai yaji iska na shigar mishi hannuwa duk idan ya saka riga mai gajeran hannu, ko a gida baya zama da ita, da daddare ma ba kullum yake kwanciya da singlet ba, dan ma zai lullube jikin shi tunda da AC. Coffee ya hada ya zuba a kofin tangaran da yake rubuce da Arc Hamzy a jiki, da yake bayason zaki ko da can, ballantana da yasan illar da yake da ita a jikin dan adam idan yayi yawa, haka ya fito da Mug din a hannun shi.

Kurba yayi yana hadiye shi dakyar saboda zafi,

“Oh shit!”

Ya furta yana furzo iska ta bakin shi, babu shiri ya koma kitchenette din ya dauko cokali ya saka a ciki yana jujjuyawa cikin son yadan sha iska ko yayane, kan mudubin dakin baccin ya ajiye kofin yana duba agogon dakin yaga karfe takwas da kusan kwata, yana da dan sauran lokaci, dan karfe tara zai fita, kuma yayi wanka. Wajen drawer din gado ya karasa yana zama tukunna ya janyo, paracetamol ya dauko ya balli guda biyu yana daukar robar ruwa da take ajiye a gefe ya jefa maganin a bakin shi tukunna yabi da ruwa. Ya sake mikewa ya dauko Mug din ya kurba yaji zafin ya mishi dai-dai. Bai dauki wani lokaci ba ya shanye yana zuwa ya wanke kofin tukunna ya mayar da shi inda ya dauka.

Gyara gadon yayi tsaf, dan a rayuwar shi bayason ganin waje a hargitse, bakuma ya son kazanta koya take. Ko wajen ajiye kayan shi ka bude a tsare yake sai abin ya burgeka, kowanne kalar kaya wajen su daban, boxers din shi da singlet kan su a tsari suke. Shisa ya tsani wani ya shigar mishi daki, idan akwai abinda yafi saurin bata mishi rai shine wani ya shigo mishi daki ya taba wani abin, dan koya akai kokarin mayar dashi yanda aka gani yana shigowa saiya gane. Saida ya gama tukunna ya taka wajen wardrobe din da take cike da bango daya na dakin saboda girmanta. Wani farin yadi ya dauko da babu aiki a jiki, sai maballan ne kawai da aka saka mishi blue, links ya dauko kalar maballan, sai agogo, hula da takalmi duka blue.

Lokacin da ya gama shiryawa da wahala ko namiji dan uwan shi yai mishi kallo daya bai sake kallon shi ba, ya hadu kamar ba daga jinsin bil’adama ya fito ba. Saida ya feshe jikin shi da turarukan Oud dan yafi son su, tukunna ya dauki mukullin motar shi yana takawa ya fita daga dakin ya sauko daga bene zuwa kasa. Yana zuwa bakin kofa yaja kyauren yana gyara labulen sosai yanda zai datse, bai damu da yasa mukulli ba tunda yana da maigadi kuma yasan babu wanda zai bari ya shigo mishi gida, zai kara mishi kashedi idan zai fita.

Yana karasawa wajen motar shi kirar Toyota corolla CE 2010 ya saka mukulli a jiki ya murza yana budewa, shiga ciki yayi ya kunna yana fitowa daga ita daga jerin motocin shi hudu in har da wadda yake ciki cikon ta biyar, tukunna yai kwana cikin tanqamemiyar harabar gidan na shi yana shirin fita da motar yaga shigowar wata, hakan yasa shi fasa fitar da tashi yayi zaune a ciki yana son ganin kowaye. Parking akayi daga gefe daya kara bata mishi rai saboda ba wajen da aka ware dan yin hakan bane. Yana kallon Huzaifa ya fito daga cikin 406 din shi da duk taji duniya, Muhsin na bude dayan bangaren ya fito shima. Ganin su biyun a tare yasa Hamza kashe motar shi ya bude ya fito shima.

Ganin su na kara harzuqa shi,

“Lafiya?”

Ya tambaya cikin yanayin da yasa Huzaifa kallon shi da mamaki bayyane a fuskar shi, Muhsin ne ya iya cewa,

“Kaya zamu kwashe.”

Tunda ya kula babu alamar mutunci a fuskar Hamzan,

“Zan duba in saka muku rana.”

Cewar Hamza din yana shirin juyawa,

“Bangane zaka duba kasa mana rana ba.”

Huzaifa ya fadi yanayin fuskar Hamzan na saka shi son dauke shi da mari, a duniya baya kaunar wulakanci ko ya yake, bama shida hakuri ne gabaki daya, shisa ba sosai yake shiga mutane ba, ballantana wani ya harzuka shi. Cikin idanuwa Hamza ya kalle shi yana amsa shi da

“Hausa nai maka bawani yare ba, meye baka fahimta daga ciki ba….”

Wata yar dariya Huzaifa yayi yana cewa Muhsin,

“Kayi magana da shi.”

Ya juya yana takawa wajen motarsu ya jingina bayan shi, dan idan ya tsaya bazai san lokacin da zai kaiwa Hamza naushi ba.

“Mun zo da masu mota da mutanen da zasu kwashi kayan, suna waje suna jira.”

Muhsin yayi kokarin yima Hamza bayani dan su fahimci juna, su ba rashin mutunci bane ya kawosu, duk da abinda yaima kanwar tasu, tarbiyar da suka samu wadatacciya ce, kai Hamza yake girgizawa tunda Muhsin din ya fara magana.

“Fita zanyi, ba kuma zan barku ku kadai a cikin gidana ba gaskiya, gobe ma ina da abinda zanyi. Idan na saka rana zan fada ma Hindun sai ta sanar muku.”

Sosai Muhsin yake kallon shi, akwai dalilin da yasa tun ranar daya fara ganin shi tsaye da Hindatu yaji bai mishi ba, a lokacin ya nema bai samu ba, sai jiya daya kwana yana juyi, yana fada ma kan shi yanda bazai kara bata rai idan yaji wata mace tayi wa maza kudin goron zagi ba. Da matar shi rike a kirjin shi tana bacci, darajarta na karuwa a idanuwan shi, baiga riba a wulakanta mace ba, balle wadda ta kasance a karkashin kulawar ka. Tun jiyan ya rasa kalar zuciyar da take kirjin Hamza da har zai iya korar mace tsakiyar dare batare da tunanin halin da zata shiga ba, macen ma da tsohon ciki.

“Kaga ba tashin hankali ya kawo mu ba, kaya kawai zamu kwashe mu tafi.”

Inda Muhsin din yasan yanda Hamza yake kokarin ganin ba suyi tashin hankali ba, daya wuce ya sami Huzaifa sun shiga motar su sun bar mishi gida. Tsayuwar da suke, lokacin shi da suke batawa da maganar kwashe kayan da take dawo da Hindu tunanin shi kara harzuqa shi sukeyi ba kadan ba.

“Idan baka da abu mai muhimmanci ni ina da shi.”

Ya fadi yana bude motar shi, kafin ya shiga ya juyo ya kalli Muhsin din,

“Wallahi kuka shigar mun gida karar ku zan kai wajen yan sanda, saboda ina da dukiya a cikin gidana….”

Tukunna ya shiga motar shi, ya tayar yana fisgarta da akwai tsautsayi saiya takama Muhsin da mamaki yagama cikawa kafa. Jikin shi da wani irin sanyi ya karasa wajen Huzaifa yana fadin,

“Wallahi mutumin nan bashida mutunci, ko kadan bashida mutunci bansan ya akayi bamu kula da hakan ba kafin mu bashi Hindu, kaji abinda yake gayamun? Wai zai kira yan sanda idan muka shigar mishi gida.”

Jinjina kai Huzaifa yayi cike da bacin rai, yana kasa furta wata kalma,

“Muje kawai mu sallami mutanen nan, sai mu biya ta gida, kar muyi wani abu ko da sauran zama a tsakanin su.”

Sai lokacin Huzaifa yace,

“Da wa? Ai kasan Allah ko zata mutu ba zata dawo gidan wannan mutumin ba, daman shegiyar kafiyarta ce, da Baba daya goya mata baya.”

Dan murmushi Muhsin yayi yana bude motar ya shiga ya zauna. Huzaifa ya bude dayan bangaren mazaunin direba yaja suka fice daga gidan, masu manyan motocin har biyu suka sallama tare da karbar lambar wayar su da cewar zasu sake neman su azo a kwashe kayan. Tukunna suka kama hanyar gida, Huzaifa har lokacin zuciyar shi a makoshi yake jinta.

“Inda na mari yaron nan da zuciyata tadan yi sanyi.”

Dariya Muhsin yayi dan baka raba fuskar shi da fara’a ko da yaushe.

“Allah dai ya rufa asiri, idan ka biye halin mutane abinda yafi mari ma sai kayi musu. Ni yanzun Baba ma nake tunani wallahi, ran shi ya baci jiya tunda kaji yace a kwashe kayan a daren. Me zamu ce mishi?”

Dan kallon shi Huzaifa yayi kafin ya mayar da hankalin shi kan tukin da yake.

“Me zamu ce mishi daya wuce mu fada mishi gaskiya? Yace ba zamu shigar mishi gida baya nan ba, idan kiran shi Baban zaiyi sai yayi.”

Numfashi kawai Muhsin yaja yana fitarwa batare da ya sake cewa komai ba. Duk da shine sama da Huzaifa din, bai ja maganar ba saboda bayason ya kara tunzura shi. Yafi so yaga anbi komai a hankali, duk yanda zasu kai da kin Hamza idan zaman su bai kare da Hindu ba yasan haka zasu hakura suna gani ta koma. Sam ba zai so su biye mishi ya kara zubar da mutuncin shi a idanuwan su ba, ko babu rabon komawa akwai ciki a jikin Hindu. Haka suka karasa gida babu wanda ya sake cewa dan uwan shi komai.

***** *****

Baba da kanshi daya dawo sallar Asuba ya shiga bangaren Anty yana fada mata abinda ya faru. Da yake uwa daban ce tun a daren jiyan taji a jikinta, dan haka kawai bacci ya kaurace ma idanuwanta, sai tunanin Hindun daya cika mata zuciya. Kuma ta kasa tashi tayi sallah ko da raka’a biyu ce, jin Mama na tare da Hindun yasa tayi alkunya tana kasa shiga duk yanda zuciyarta take son ganin halin da take ciki. Da yake ita bafullatana ce, lokaci zuwa lokacin fillon na motsa mata. Tana zaune a daki, ta saka wannan ta kwance har karfe bakwai na safe.

Kafin ta fito daga dakin tana shiga kitchen, kowa girkin shi yakeyi tun suna da kuruciyar su. Sai dai yaran duk abinda sukaji suna marmari da aka dafa a gidan shi suke ci, cikin ikon Allah da yake Baba tsaye yake akan gidan nashi, kishin dake tsakanin matan da ba’a iya kauce mishi baisa kan yaran ya rarrabu ba, duk da zaka gane yan daki daya daga yanayin shakuwar su, amman suna kamanta zaman lafiya dai-dai iyawar su, kuma suna kokarin ganin ko da sun sami sabani basu saka yaran a ciki ba.

Asma’u da suke kira da Asma ta samu harta tashi tana soya dankalin turawa.

“Ina kwana Anty.”

Ta fadi tana daukar soyayyen dankalin guda biyu ta saka a bakinta.

“Lafiya kalau… Harkin tashi.”

Kai Asma ta jinjina wa Mama tana dorawa da,

“Ina da Test da safen nan.”

Ta sake saka hannu cikin dankalin ta dauki guda daya.

“To ko kibari in karasa kije ki shirya karki makara.”

Murmushin jin dadi Asma tayi dan inta tsaya karasa suyar dankalin zata iya makara, tunda karfe takwas da rabi malamin yace. Bata tsaya jan magana ba ta fice daga kitchen din tana wucewa dakinta. Tsaye Mama tayi a kitchen din komai baya mata dadi, kafin taji sallamar Hindun da ta sakata juyawa cikin hanzari tana fadin,

“Hindu…”

Itama da ta samu tayi sallar Asuba, bacci ne ya dauketa sai yanzun nan ta tashi, wanka kawai tayi tana zira doguwar rigar da Mama ta ajiye mata kan gado, son ganin Anty taji tanayi ta kuma son halinta, sam ba zuwa zatayi inda take ba, shisa ita ta lallaba ta taho. Ganin Antyn da yanda ta kira sunanta suka hadu suna kara karya mata zuciya, batasan lokacin da wani irin kuka ya kwace mata ba tana karasawa ta fada jikin Anty da duk damuwar da take ciki bai hanata fadin,

“Karki kayar dani Hindu, kinga ga mai a wuta. Kiyi hakuri kinji ko.”

Ai kamar hakurin Antyn take jira wani sabon kuka ya sake kwace mata, duk yanda taso ta boye halin da aurenta yake ciki saida Hamza ya kure duk wani zabi da take da shi,a hankali Anty ta dagota daga jikinta tana fadin,

“Kinci abinci?”

Kai Hindu ta girgiza, ko kadan ta manta da wani abinci, da gaske yunwa ma sai kana cikin kwanciyar hankali kake jinta. Sai yanzun da Anty tayi mata maganar abincin ne ma taji yaron cikinta ya juya mata da alamun yunwa, shisa dazun data mike taji jiri na shirin dibarta, bayan hannuwanta tayi amfani dasu wajen goge fuskarta.

“Kije ki zauna in zubo miki.”

Kai Hindu ta iya dagawa Anty, tana wucewa falon ta samu kujera ta zauna, dan inta zauna kasa wajen tashi wahala take sha saboda cikin da yake jikinta. Tana zama Asma na fitowa daga daki ta shirya tsaf cikin kayan da Hindu bata gani saboda Abaya da Asma ta dora a kansu, kanta sanye da bakar hula mai duwatse, tayi kyau cikin kwalliyarta mai sauki, da sauri cike da farin ciki ta karaso inda Hindun take tana fadin,

“Yaa Hindu”

Kafin tadan dakuna fuska cike da tunanin da yazo mata na me Hindun takeyi a gida da sanyin safiya haka, tukunna ta kula da idanuwan ta da dukkan fuskarta da suke a kumbure da alamun kuka, walwalar fuskar Asma ce ta dishe, damuwa na maye gurbinta.

“Asma…”

Hindu ta kira sunan kanwar tata cike da duk wani karfin gwiwa da zata iya tattarowa wajen ganin bata fashe da kuka ba. Gefenta Asma ta zauna tana jin gabaki daya komai yai mata tsaye, kafin tace wani abu Anty ta fito daga kitchen hannunta rike da faranti da dankali a ciki, dayan hannunta da ruwan shayin da ta hada.

“Ke ba makaranta zaki tafi ba kika sami waje kika zauna.”

Kallon Anty tayi, da bata furta suna da test ba, ita kam batajin zata tafi tabar Hindun cikin wannan damuwar da take gani shimfide akan fuskarta, turo labbanta tayi tana sa Hindu fadin,

“Ki tashi karki makara Asma… Ina nan ai har ki dawo.”

Idanuwanta Asma ta dauke daga kan Anty tana dawo dasu kan Hindu cike da alamun tambayar dake fassara ‘Kinyi alkawari?’. Kai Hindu ta daga mata tana dorawa da,

“Da gaske?”

Tukunna Asma din ta mike, kitchen ta wuce tana dan dibar dankalin ta zuba a murfin kular da yake ciki dan ba zata iya tsayawa daukar wani kwano ba, tea ta hada tana shan shi a tsaye cikin sauri kafin Anty ta shigo taganta ta zageta tana cin abinci a tsaye. Tana gamawa ta mayar da kular ta rufe tana fitowa da gudu-gudu ta shiga dakinta tana dauko mayafin Abayar ta nada a saman kanta sai jakarta ta gefe, ta zira takalma tana fadin,

“Saina dawo.”

Fatan alkhairi Hindu da Anty sukayi mata, ko amsa basu samu ba saboda saurin da takeyi. Kofin shayin da Anty ta bata ta karba tana fara kurba, hadi da dibar dankalin tana ci, ko rabi batayi ba taji yaron cikinta ya harba tamkar abinda taci din harya isar mishi. Jin da tayi komai ya hargitse mata lokaci daya yasata ajiye kofin hannunta tana kiran sunan Allah kafin ta mike cikin hanzari tana nufar bandakin baki da yake cikin falon hadi da tsugunnawa kan gwiwoyinta tana fara kelaya amai tamkar zata amayar da hanjin cikinta, ko sannun da Anty take mata bayan ta shigo bandakin bata iya amsawa ba. Amai take babu kakkautawa har mamakin ta inda yake fitowa takeyi dan tana da tabbacin iya dan abinda taci yanzun nan ya gama fitowa.

Baba ne ya shigo dan yaje bangaren Mama baiga Hindun ba, hankali a tashe ya tsaya daga kofar bandakin yana fadin,

“Subhanallah… Me ya sameta?”

Dan rausayar mishi da kai Anty tayi, mai ciki ai ba’a rabata da laulayi kala-kala, mai dalili da akasin haka. Damuwa ce fal a ran Anty da take kokarin boyewa a fuskarta. Ita ta zubama Hindu ruwa tana kuskure bakinta ta kuma wanke fuskarta. Kafin ta dafa sink din tana mikewa dakyar

“Ki dauko mata hijabi mu tafi asibiti… Harda ruwan jiya daya daketa.”

Baba ya fadi yana karasa maganar da wani yanayi a fuskar shi, a kasan ran shi yanajin yanda bazai taba yafewa Hamza wannan rashin arziqin ba, murya cike da rauni Hindu tace,

“Baba ba sai munje asibiti ba, tunda daman gobe in shaa Allah zan koma awo…”

Kai Baba yake girgiza mata.

“Ki kalli yanda kike magana dakyar Hindatu, kice ba sai anje asibiti ba? Kina wasa da lafiyarki ko?”

Dan murmushi Hindu tayi, a fuskar Baba take ganin shine namiji daya a rayuwarta da ba zai taba karya mata zuciya ba, namijin da bai taba karya alkawurran da bai ma daukar mata ba amman yake cikawa a duk rana. Tana kuma jin yanda shi kadai ne dalilin da zai sa ba zataiwa mazan yanzun jimlar marassa mutunci, marassa adalci, marassa tausayi ba. Wata irin kaunar Baban taji cike fal da zuciyarta da take ciwo.

“Baba Allah ba sai munje ba, da nayi bacci shikenan.”

Badon ran shi yaso ba, sai don bako yaushe yake iya matsama Hindun ba, ko da kuwa a yanayi ne irin wannan.

“Allah ya kyauta, ya kawo sauki…ki kwanta ki huta kinji ko? In dai kika karayin amai asibiti zamu je.”

Murmushin karfin hali Hindu tayi tana dan dagama Baba kai, Anty kuwa kallon su takeyi, kaunar dake tsakanin su ba sabon abu bane a wajen ta, lokutta da dama idanuwa take binsu dashi. Baban da kan shi ya taka ya raka Hindu har dakin Asma tukunna ya fito yana kallon Anty da fadin,

“In ta sake yin aman ki kirani mu tafi asibiti…zan karya in kira su Muhsin dan nace su kwaso kayanta.”

Kallon shi Anty tayi, cikin taushin murya tana fadin,

“Alhaji anyi saurin kwaso kaya? Da an bari an kira shi anji me ya hadasu tukunna.”

Wani irin kallo Baba yakewa Anty.

“Yazo aji me? Ya korar mun yarinya tsakiyar dare, da tsohon ciki tukunna in kira shi? Yace mun me? Ni ince mishi me? Bafa gajiya nayi da kulawa da ita ba, ba kuma kasa ciyar da ita nayi kafin yazo ya tsugunna ya nemi aurenta in dauka in bashi ba, ya wulakanta mun ita haka kice mun in saurari me ya hada su.”

Ganin yanda ran Baban yake a bace yasa Anty fadin,

“Ka yi hakuri.”

Dan tasan halin shi, idan ran shi ya baci babu abinda zai saurara, musamman kuma yanzun an taba yar gaban goshi Hindu. Ai tasan sai abinda Allah yayi, ita bataso a yanke hukunci ba’a duba duka bangare biyu ba, dan hakan ne adalci, dan kyautawa ko kadan Hamza bai kyauta ba, ko ita ranta yana kan sosuwa da abinda yayi din, amman zai iya yiwuwa tayi mishi wani abin ne, batajin namiji zaiyi irin wannan hukunci batare da kwakwwaran dalili ba.

“Kawai dai ina jinjina yanda zaiyi irin wannan hukuncin batare da wani dalili bane, shisa nake so aji nashi bangaren.”

Antyn ta sake fadi ganin kamar Baba zai saurare ta, karamin tsaki yaja yana ficewa daga dakin kawai, dan idan ya tsaya fada zasuyi da sanyin safiyar nan. Baisan me yasa Antyn take magana kamar ba mace ba, da ya kamata tayi kishin abinda akaiwa yarta, baice kar a kyautata ma dan adam zato ba, bai kuma ce abinda take so ayi din ba mai kyau bane ba, asalima hakan shine adalci. Amman baiga dalilin da zaisa a kowanne yanayi sai anma jinsin shi na da namiji uzuri ba, ko wanne irin abu namiji zaiyi sai an so juya abin ya koma kamar ita macen ce da laifi. Na rana daya ya kamata a kalli mace cikin kuncin da namiji ya kunsa mata a karbi korafinta batare da kokarin gano me tayi da ya ba namijin dalilin yin abinda yayi.

A ganin shi babu wani uzuri da zai karba akan abinda Hamza yayi, kowanne irine kuwa. Daya rufe idanuwan shi Hindu yake gani tsamo-tsamo cikin tsakiyar ruwa da tsakar dare, inda maigadi bai taimaka ta kira shi ba haka zata kwana cikin ruwa, a kofar gida. Ko da wani bai cutar da ita ba, sanyi kadai ya ishi yai mata illa mai girma, ga cikin da yake jikinta. Kirjin shi ma zafi yakeyi ba kadan ba, idan baiga an kwaso kayan Hindu daga gidan marar mutuncin nan ba hankalin shi bazai kwanta ba, indai harya isa yana kuma da cikakken iko akan yar shi ba zata taba komawa gidan Hamza ba.

<< Mijin Novel 1Mijin Novel 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×