Zatai karya idan tace gabanta baya faduwa. Asali tunda suka fito daga gida wata zufa take tsatssafo mata a saman goshi har zuwa tafikan hannunta, da sukaje gidan su Ummi sam kasa samun sukuni tayi. Biebee na kula da ita, batai mata magana ba saboda ta fada mata daga farko bataji ba, sau daya take gaya maka gaskiya ta koma gefe ta saka maka ido, yanda zataji dadin cewa ta fada maka baka dauka ba idan komai ya kwabe. Bata sake shiga tashin hankali ba sai da Elias ya kira wayarta, jikinta har bari yake
"Bie muje...Anty ta fara. . .
Nice novel
Kina kokari a duk littattafan ki,akwai darasi,Allah ya qara basira
Great book