Skip to content
Part 4 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Zatai karya idan tace gabanta baya faduwa. Asali tunda suka fito daga gida wata zufa take tsatssafo mata a saman goshi har zuwa tafikan hannunta, da sukaje gidan su Ummi sam kasa samun sukuni tayi. Biebee na kula da ita, batai mata magana ba saboda ta fada mata daga farko bataji ba, sau daya take gaya maka gaskiya ta koma gefe ta saka maka ido, yanda zataji dadin cewa ta fada maka baka dauka ba idan komai ya kwabe. Bata sake shiga tashin hankali ba sai da Elias ya kira wayarta, jikinta har bari yake

“Bie muje…Anty ta fara kirana.”

Hindu ta furta muryarta na rawa, kai Biebee ta jinjina mata, Ummi ce ta ce,

“Wai tun yanzun zaku tafi? Kai dan Allah…. Hindu ba Anty tasan nan kuka zo ba.”

Murmushin karfin hali Hindu ta yi.

“Zata fitane zan dora girki, yamma nayi shisa.”

Kai Ummi ta jinjina tana fadin,

“Bari in dauko Hijab dina in rakaku.”

Wannan karin Biebee ce ta girgiza mata kai.

“Dan wahalar da kai? Mu biyune fa, kiyi zamanki dan Allah.”

Duk da haka saida Ummi ta rakasu har bakin kofar gida, sannan sukayi sallama, da sauri Hindu ta daga kiran Elias daya shigo a karo na ukku.

“Haba Hinduna, inata kira sai an mun sarautar za’a daga?”

Dan murmushi Hindu ta yi.

“Kana ta ina?”

Sai da yayi jim tukunna ya ce,

“Bakin wani saloon Umtaz…”

Kai Hindu ta jinjina dan ta gane wajen.

“Gani nan karasowa to.”

Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta batare data jira amsar shi ba, ta kalli Biebee.

“Wai yana wajen Saloon din Umtaz.”

Biebee ta jita, bata dai ce komai bane, suka dan kara sauri kowa da abinda yake sakawa cikin zuciyar shi. Suna karasawa kwanar da zata kaisu titin da Elias yace yana tsaye Biebee ta riko hannun Hindu.

“Zuwa zakiyi, ki kira shi kice yana cikin wacce motar, ki fara hango shi tukunna.”

Shawarar Biebeen ta zauna mata, wayarta ta danna tana kiran Elias da ya daga a bugun farko

“Ban ganka bafa… Kana cikin wacce mota?”

Hindu ta fadi kafin ya numfasa.

“Cikin wata jar golf.”

Elias ya amsata ta dayan bangaren.

“Golf?”

Hindu ta maimaita cike da mamaki, daga ita har Biebee suna zira kansu suka hanga wajen saloon din, akwai motoci jefe a wajen, amman jar golf din da suke hangowa tayi kama da motar da ake dibar jogon kaji ana cin kasuwar kauyuka da ita, ga wata irin kura da ba zasuce ta kasa bace ko qoqewar da fentin motar yayi bane ba, kallon juna sukayi, Biebee na kokarin ganin bata kwashe da dariya ba, a hankali ta ce,

“Kice bari mu duba.”

Hakan Hindu tace tana sauke wayar da wani irin yanayi da yake fassara ‘akwai matsala’ bayyane a fuskarta, dariya Biebee takeyi harda rike ciki.

“Wanne irin iskanci ne wannan Bie? Ya zanyi ni yanzun… Jar golf yace, ni kuma waccen motar kadai ce ma golf a duk motocin titin nan, anya shine? Ko dai wasa yake mun? Aike kinga motocin gidan su.”

Kai Biebee take girgiza mata.

“A gidan ubanwa naga motocin gidan nasu?”

Tsaki Hindu taja.

“Ban nuna miki hotunan shi ba?”

Wani kallo Biebee tayi mata.

“Da kika nuna mun hotunan bance miki ni ban yarda dashi ba?”

Numfashi Hindu taja ranta a bala’in bace.

“Ni yanzun ya zanyi? Juyawa zamuyi wallahi…”

Kai Biebee take girgiza mata.

“Zai yiwu wasa yake miki, ki sake kiran shi kice ya fito ko shi zai hango mu, kice kin saka hijabi ruwan toka.”

Duk da taso su juya din tunda Elias yai mata wannan rainin hankalin, amman kuma ita taga hotunan shi, ta kuma ga kalar motocin da yake hotunan a jikinsu, maganar Biebee zata iya zama gaskiya, kilan shima yaga golf dinne yake so ya gwadata, yaran masu kudi kanyi haka wani lokacin dan suga ko tsakani da Allah kake son su. Shisa ta sake kiran Elias ta fada mishi abinda Biebee din tace su duka biyun suna labe jikin katangar da zata hadasu da titin da Elias din yake. Sai dai ga mamakinta murfin motar aka bude ta mazaunin da bana dire ba bane, kafin taga an ziro kafa daya, ana kama murfin motar, sannan taga ya saka dayan hannun shi kamar zai tattaro wani abu ya fito dashi, a tare suka ware idanuwa ita da Biebee.

“Butar shayin buzaye…”

Hindatu ta fadi dan shine karshen zaginta idan abu yakaita makurar mamaki, Biebee na karbe zance da fadin.

“Inalillahi… Ke Hindatu mun shiga uku….La haula wala quwwata ila billah…. Kinga me nake ce miki ko?”

Cewar Biebee da take a tsorace ganin shanyayyar kaface Elias din ya tattaro ya fito daga ita daga motar yana jingina jikin shi da murfin motar, sannan yai amfani da dayan hannun shi yana fara kiran wayar Hindu da batasan lokacin ma data sauketa daga kunnenta ba, sai da taji ringing dinta, dagawa tayi batare data kara a kunnenta ba, tana hango Elias daya bude baki yana fadin abinda bataji ba ta cikin wayar. Tana godema Allah da duk yanda Elias yayi naci hotonta daya yagani wanda yake a dp dinta na WhatsApp, ca tayi shida zai ganta wata rana harya gaji.

Wayar ta kashe gabaki dayanta.

“Na shiga ukuna ni Hindatu.”

Ta fadi tana kallon Biebee da mamaki ya hanata dariya, hannun Hindun taja suna komawa baya.

“Mu zagaya ta baya mu wuce gida.”

Bata bari Biebee ta sake fada mata ba, da sauri suka nufi inda suka fito dan suyi zagaye zuwa gida. Sauri suke kamar zasu tashi sama, basu fara tsagaita tafiyarsu ba saida suka sha kwanar da zata kaisu gida, sannan Biebee ta ce,

“Elias…”

Tana jan sunan kamar yanda Hindu takan fada kar suyi mata iskanci cewar sunan shi Iliya, kafin ta kwashe da wata irin dariya tana dorawa da.

“Yar banza… Daman nabari kin karasa wallahi.”

Hade rai Hindu tayi tunda ita bataga abin dariya a cikin wannan al’amarin ba, tana da yakinin ita kam yarda da wani namiji da zasu kara haduwa a 2go zai mata wahala, daman Khadee ta fada mata itace taki ji. Tace mata babu kalar tarkacen da babu a 2go.

“Yanzun meye abin dariya?”

Ta bukata tana kallon Biebee din da taci gaba da dariya kamar haduwa da Hindun tayi da gurgu shine abu mafi nishadi da ta taba cin karo dashi a duniya. Dogon tsaki Hindu taja tanayin gaba, Biebeen nabin bayanta da fadin,

“Haba Kawata ta Eliass,”

Shiru Hindu tayi mata, duk tsokanar da Biebee take mata bata kulata ba, ko sallama batayi mata ba ta shige gida. Kai tsaye dakin su ta wuce ta cire Hijabinta tana ajiyewa akan gado, ta ajiye wayar da takejin duk yanda ta saba da ita zatayi kwana biyuma bata dauka ba, idan Elias ya kirata ya gaji zai hakura. Zatayi amfani da lokacin tayi karatun jarabawar da yake gabanta. Amman duk da haka bayan ta fito dan taya Anty hidimar girkin dare sai da taji zuciyarta na lugude kamar Antyn zata gane abinda ya faru, a tsorace take har suka gama aikin, duk surutunta ko magana bata son yi sosai.

***** *****

Duk da girkin Anty ne, bangaren Mama ta shiga tana idar da sallar Magriba, ta kasa hakuri, tunda Huzaifa ya karbi memory dinta yace zai turo mata fina-finai, tun safen bata kara ganin shi ba har yanzun. Halima tagani, batama san ta dawo ba, dan taje gidan Yayan Mama din da yake Unguwar rimi, akwai yar shi da suke KASU tare, suna karatun shirye-shiryen jarabawar su ta zangon karshe a shekararsu ta uku. Dan abokin Baban ne ya manne ma Halima, da Baba yaso sai ta kammala karatunta, Hindu batasan meya faru ya amince aka saka rana ba, gashi yanzun bikin sai kara matsowa yake, sauran watanni biyu, tana kammala jarabawarta da sati daya.

Sosai Hindu take fatan samun mijin da yafi Yaa Ahmadi kamar yanda suke kiran shi, zatayi karya idan tace sanda yake zuwa gidan baya burgeta, duk da bai karasa irin tsayin Mijin da take so ba, amman ya iya gayu, gashi yana shigowa zaka fara jin kamshin turarukan shi na tashi. Magana daya zuwa biyu Yaa Ahmadi kan jefa turanci cikin kwarewa. Amman taji dadin auren Halimar da zaiyi, ko ba komai basuyi asarar hadadden gaye ba, a nata tunanin ya zama nasu, ta kuma ji dadi ba kadan ba.

“Yaa Halima yaushe kika dawo?”

Numfashi Halima ta sauke, cikin sanyin muryarta ta amsa da.

“Da yammacin nan, Anty tace kunje duba kawarku ke da Biebee.”

Kai Hindu ta daga mata, tana jin yanda zuciyarta tayi tsalle data tuna fitar da ta saka Elias fadowa a ranta, duk saurin karbar memory din ma babu amfanin da zai mata yau, dan ba zata kunna wayar ba.

“Eh kam… Yaa Huzaifa ya shigo?”

Kai Halima ta girgiza mata, sallamar da sukaji na saka su juyawa su duka suna amsawa, Hindu na dorawa da.

“Ina wuni.”

A dakile ganin Musa ne dan Kanwar Mama, ta dauka tana son farin namiji, sai akan shi ta fara gane kalar namiji itace karshe cikin jerin abinda take so a tattare dashi, gajartar Musa ta sa ko kadan baya burgeta, ba ca yayi yana son ta ba, kwata-kwata a tunaninta data kwatanta idan yace yana sonta dinne baiyi mata ba. Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, babu wani dalili tana jin mutum baiyi mata ba, amman kiyayyar da takewa Musa dabance, kuma sai ya dinga abu kamar baisan gajere bane, yana daddaga kafadun da takeji kamar ta kwantara mishi wani abu akai dan takaici

“Hindun Baba….Ya kike?”

Ya fadi cike da iyayin da ita kadai take gani a tare da Musan, ta tsani yanda ta karfi da yaji yake nuna akwai wani kusanci a tsakanin su, sai yashe mata baki yakeyi. Mama tace Baban shi qwara ne, da Hindu ta dauka a bakaken fata kawai akafi samun guntaye, amman saiga Musa ya fito a qwaran shi sak, amman tana hango tsakiyar kan shi.

“Lafiya…”

Ta amsa can kasan makoshi, da Halima bata wajen ko inda yake ba zata kalla ba, amman tasan halin Halima, ta kwada mata mari ba abu bane mai wahala, ko Yayarsu Salma basa tsoro haka kafin tayi aure, Halima bata wasa dasu, a haka sai kaganta kamar tana da sanyi, sai kaji saukar mari akan kuncinta, dan bata son raini, bata kuma so taga kana wulakanta mutum, shisa ba sosai suke shiri da Hindu ba, sau daya ta taba cewa Musa gajere a gaban Halima ta kusan kwada mata mari.

‘Ko gawayi ba zaki iya yiba, kina kushe halittar da Ubangiji yayi kamar bakije islamiyya ba, idan gajartar shi batai miki ba, sai a samo tsani kihau sama kiji dalili. Wallahi Hindu ki iya bakin ki, ba tun yau nake jin yanda kike kushe halittar mutane ba, idan baki haifa ba, zaki iya aura.’

Shine abinda Halimar ta fada mata, a ranta ta dinga zabga addu’a kar Allah ya amsa, dan taji haushi sosai. Tunda bakin cikine, ita ta sami me kyau tana mata fatan auren gajere. Ko maza sun kare sai ire-iren Musa gara ta hakura da auren, yanzun ma dakinsu Khadija ta wuce dan taga Musa naso ya karayi mata wata magana. Halima ce taje ta kawo mishi ruwa bayan ya zauna tana fadin,

“Bari in kira maka Mama.”

Kai Musa ya daga mata, ba wani dalili bane ya kawo shi gidan sai Hindu, tun randa ya fara dora idanuwa akan yarinyar ta kwanta mishi, yayiwa Mama magana akanta tace ya dakata ta kammala sakandire, amman sosai yaso ace ko sanar da ita Hindun Mama ta bashi dama yayi kar wani yazo yayi masa shigar sauri. Mace irin Hindu ba’a saka wasa a neman auren su, amman duka kasa da shekara daya ya rage musu. Har kasan ranshi yake jinta, lokutta irin haka yakan kasa hakuri sai yazo gidan yaganta sun gaisa, kullum kyau yake kara ganin tana yi mishi da yan matancinta da yake kara fitowa. Dan haka Mama na fitowa suka gaisa yace zai wuce.

Murmushi Mama tayi, ba tun yau ta kula yakan zo gidan bane da sunan gaisuwa dan kawai yaga Hindu.

“Ka gaishe su, dan Allah kace ma Hajiya ta shirya da wuri jibin zuwa sunan yar wajen Jummai… Nima da wuri zan fito in shaa Allah.”

Kai Musa ya jinjina mata sukayi sallama ya wuce. Zata so yaron da Hindu saboda hankalin shi, kuma duk a gidansu babu wadda ta shaku da ita sama da Hajiya, mahaifiyar Musa, ga Baban shi ma mutum ne na kirki dayake samun shaidar mutane a duk rana, tace ya bari tagama sakandire ne sanin tsarin Baban su Hindun, kuma yaran yanzun ba’a yanke musu hukunci, gara shi Musan ya fara neman soyayya a wajen Hindu kafin manya suce zasuyi katsalandan su sha kunya.

*****

Satin bikin Halima yayi dai-dai da satin da Hindu ta fara kallon film din korean da yayi tashe a shekarar 2010 mai suna Secret Garden da ita sam bata san yanda akayi sai yanzun take kallon shi bayan shekara uku dayin shi ba. Daga farko film din yaso yayi mata wani iri, dan ta saba ganin Lee Min Hoo da ya samu wajen zama a zuciyarta yayi kane-kane yana saka duk wasu sauran jaruman fina-finan korea sai take ganin su daban, tamkar kyawun su da soyayyar su bata kai tashi ba. Sai da ta rasa abin kallo, da yake yanzun a wayarta take yin kallon, sai ta saka earpiece ta dade kunnuwanta yanda babu wanda zai dameta.

Yanzun ma saida ta tabbatar har wanke-wanke tayi, tayi sallar isha’i, bata da wani assignment tukunna ta saka earpiece tana kwanciya kan kujera dan daren jiya har mafarkin film din ta dinga yai saboda yanda ta saka shi a ranta. Soyayya ce irin wadda take so, zuwa yanzun ta daina ganin fuskar jarumar, dan ta jima da daukar tata fuskar ta makala a jikin jarumar, ya zamana tanajin kamar da ita ake zuba madarar soyayyar da take faruwa cikin film din. Daman haka rayuwa take, sai kaga mijinka ya fado ta inda baka tunani. Tasan hakan na faruwa a Najeriya, kawai ba sosai ba. Yanda jarumin duk kudin shi, da ajin shi ya bada kai bori yahau wajen soyayya ya gama tafiya da Hindu.

Haka take so ta kasance da ita, dukkan kudin shi ya zama nasu ne, store dinsu da ya kusan rabin barnawa jarumin ya dauki jarumar dan ta zabi dukkan kayan da take so, amman ta watsa mishi kasa a ido tana nuna bata so, ta juya tana fara tafiya, amman duk irin wulakancin da tayi mishi sai ca yayi.

‘Nal tteona jima (Karki barni)’

Cikin yanayin daya burge Hindu, bata san lokacin da ta mike ba, tana tsayar da film din, idanuwanta ta lumshe tana bude su, tana jinta tamkar a kasar Korea lokacin data maimaita kalaman da jarumin ya fada, tana watsa hannayenta, ji tayi kamar ba dai-dai tayi ba, haka ta shiga maimaitawa, sai ta girgiza kanta ta sake maimaitawa, ko kadan bata kula da Zaid daya shigo ba yanata magana dan ta tare mishi hanya, sai da taji ya dala mata wani duka a gadon baya hadi da tureta.

“Dalla matsa…wawiya kawai.”

Ya furta a kufule yana shigewa ciki, dan zai tambayi Anty aron wayane ya kira Baba, katin shi ya kare, kuma yana bukatar magana dashi kan lemukan daya aike shi siyowa da za’ayi amfani dasu wajen bikin Halima din. Sosai dukan ya shigi Hindu, saida ta cire earpiece din ta samu waje kan kujera ta zauna, tana tuna yanda ko kusa batayi hanyar Korea ba, da Zaid bai dala mata dukan da yayi mata ba yanzun, shisa komai na kasashen ketare yake burgeta, yanayin ‘yancin da suka samu na rashin kwaba kansa ta hasashen itace a wannan matsayin. Ka kwanta sanda kaga dama, ka fita lokacin daka ga dama, amman duk gidan Khadee ta dauka zata fahimci wannan fannin, data gwada mata magana tsaki taja tana fadin.

‘Sai a sakeka kamar tunkiya, shisa kike ganin ga rayuwar su nan, babu kan gado, musulunci ma Rahma ne wallahi.’

Shiru Hindu tayi ta kyaleta, dan ita ba maganar musulunci takeyi ba, maganar zamantakewar rayuwa takeyi. Wayaki irin wannan ‘yancin, ka kula duk kalar saurayin dakaga dama, kaje party babu wanda zai hanaka, har tsakar dare fita sukeyi. Amman sukam a gidansu, mazan ma akwai shekarun da zaka kai kafin ka fara fita bayan Magriba idan ba masallaci zakaje gabatar da sallar isha’i ba. Balle su kuma da in suka dawo daga islamiyya shikenan sun gama fita sai dai in su duka gidan zasuje wani waje. Ko aiken su ma ba’ayi tunda akwai maza a gidan.

Gajiya tayi da tunani kan abinda ba zata canza ba, hakan yasa ta mike tana nufar daki, da niyyar idan Allah ya bata aron rayuwa, ta sami kalar mijin da take mafarki, zasu gina rayuwar su kamar ba daga yankin Najeriya suka fito ba, har yaransu zasu zamana daban, zasu taso cikin yancin duk da ta rasa a yanzun. Shisa Baba yake da waje daban a zuciyarta, shi kadaine mutum daya a yanzun da yake da cikakken ikon da zai takurata amman baiyi hakan ba. Kwanciya tayi tana fasa yin kallon, gara tayi bacci kawai, dan bama lallai tunani yabarta ta nutsu kan kallon ba.

<< Mijin Novel 3Mijin Novel 5 >>

3 thoughts on “Mijin Novel 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×