A karo na farko a rayuwarta da taji bata dokin hidimar biki, yan gidan kansu mamakin rashin kazarniyarta da rawar kan da ta saba duk idan taji maganar bikin yan uwa, balle kuma wannan da akeyi a cikin gidan su, abinda basu sani ba shine littafi hausa ta samu daya dauke mata hankali daga kan komai. Tun da ta kunna waya tayi mamaki sosai da bataga sakkonin Elias ba, da hannunta ta goge 2go din daya gama fita daga ranta. Banda kallo babu abinda tafi yi da wayar, tunda bata da wanda zatayi hira dashi sosai a whatsapp sai kawayenta da kusan kullum suna tare a makaranta, hirar da zasuyi a gida bata da wani yawa. Sai yanzun data samu littafin Hausar da Dimples ta tura mata.
‘Tana Tare Da Ni’ na Miemiebee. Gabaki daya littafin ya gama tafiya da ita, Anas yayi dai-dai da kalar mijin mafarkin ta, bata tsammani ko a cikin fina-finan da take kallo, daga na Indiya harna kasar Korea ta taba cin karo da jarumin da taga yayi dai-dai da tsarinta irin shi. Duk da ba ganin wannan tayi ba, amman an haska mata shi ta yanda zuciyarta ta zayyana mata mutum sak, fari, dogo, mai faffadan kirjin da ba zata taba gajiya da kwanciya luf a cikin shi ba, gashin kanshi bakine wuluk, a kwance luf-luf kamar na mutanen kasashen ketare, ga fatar shi nada wani irin haske kamar gilashi saboda rashin wani kurji ko tabo a jikin shi, labban Anas ruwan hodane da zaka iya rantsewa yana shafa musu janbaki.
Babu abinda yafi tafiya da imaninta a tare dashi irin idanuwan shi,blue ne masu hasken da zata iya misaltawa da sararin samaniya. Gashi miskili ajin gaske, magana ma sai kayi da gaske zakaji ya furtata, ajin shi wani irin ajine da yake wahalar samu, sai da Fannah ta shigo rayuwar shi. Ta hargitsa komai tana canza shi, kalar son da yake mata, yanda ta sake shi, kuma ita kadai take ganin canjin yayi dai-dai da ra’ayin Hindu. Anas ne duk ajin shi da jiji da kai yake kuka wiwi tamkar yaro dan wata biyu a gaban Fannah. Duk idan yace
‘Flower’
Sunan da yake kiranta dashi sai Hindu taji wani abu ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta zuwa dan yatsar kafarta saboda shauqi. Da ace Anas zai fito daga littafin ya tsaya a gabanta ya furta mata kalmar so, zata amsa shi batare da wata gargada ba, ko baice yana sonta bama in dai zai aureta bata da wata matsala, dan in suka zauna zasuyi ta fada daga farko, amman tasan zasu shirya daga baya, zai fara son ta, wahalar abin ta fito daga wanka ayi dai-daito ya shigo dakin daga ita sai towel, ba zata jira tsautsayi ya kwance towel din ba, da kanta zata san yanda zatayi ya subuce. Sanda zai hargitse ta manne a zuciyar shi babu wanda zaiji labari.
Zuwa yanzun Hindu tayi wani irin zurfi cikin tunani, sam bataji maganar da Anty take tayi mata ba, sai da ta fisge wayar hannunta tana dorawa da
“Dan ubanki baki da wani aiki yanzun a rayuwar ki saina waya? Kinsan Allah na kusa haramta miki wannan shegiyar wayar tunda naga alama ke baki da hankali…”
Da hanzari cikin wata irin faduwar gaba Hindu take kallon Anty.
“Dan Allah Anty kiyi hakuri, banji bane Wallahi.”
Harara Anty ta watsa mata.
“Daman ya za ayi kiji, kin saka kanwar uwarki a gaba… Mutane na can kinzo nan kin lafe kina danna waya sai tambayarki akeyi”
Anty ta karasa maganar tana dorawa da
“Ki tashi kibar mun daki ni…”
Mikewa Hindu tayi tana kokarin bata nuna bacin ran da take ciki a fuskarta ba, wayarta Anty ta miko mata
“Saura in shigo inga kina danna waya, idan na karba sai an gama hidimar bikin nan tas zan baki”
Karba Hindu tayi tana wucewa dakinsu ta saka wayar a caji dan tayi kasa sosai, mukulli ta dauka ta kulle dakin, shisa bata ganin laifin kawarta Aina’u da suke kira da Dimples da take cewa bata son mutane, saboda suna da bala’in sa ido da takurama yan uwan su mutane. In ba takura ba me zatayi musu, kamu ne an riga anyi, sunje sunyi kunshi da kitso, gobe Asabar daurin aure za’ayi tare da walima sai akai amarya tunda anan garin Kaduna zasu zauna. Bata ga me zataje tayi musu ba da suke faman tambayarta, inba salon son su shiga rayuwar ta ba.
Da sallama ta shiga bangaren Mama tana wucewa dakin su Halima da take jiyo hayaniyar hirar su, ta leka da sallama, Halima ce da kawayenta, sai wasu cikin yan uwansu da kusan sa’annin Halima din ne, wasu kuma duk da auren su ma harda yara daya zuwa biyu. Murmushi ta dora saman fuskarta tana gaishe dasu, kafin ta juya dan ba wajen zamanta bane, su Khadee ta nemo, suna zaune da yan uwan su, yaran kannen Baba da kuma na Mama da Yayyenta, sun kacame sunata hira.
“Ke banza ina kika shiga tun dazun anayi babu ke?”
Mimi ta fadi tana matsama Hindu ta zauna a kusa da ita, hadi da leqa wayarta tana ganin hoton Halima da Yaa Ahmadi, ya leko wajen kamun na yan mintoci akai musu hotuna
“Wallahi sunyi kyau ba kadan ba”
Mimi ta fadi tana mikawa Hindu wayar dan taga hoton sosai, zata iya rantsewa Halima har wani kyalli-kyalli takeyi da batasan ya akayi ba, wani irin kyau take mata tun satin bikin naban mamaki, ita batayi haske kamar su ba, ta biyo duhun Mama, amman tana jerin masu kyawun gidan
“Shisa auren namiji me kyau ma girma ne”
Hindun ta fadi batare da tasan maganar ta fito fili ba
“Kibari kawai yar uwa, namiji me kyau fa duniya ne, ba ka auri mummuna ya bata maka hotunan biki ba”
Saddika ta amshe zancen, dariya sukayi su dukansu, Khadee ta kalle da murmushi a fuskarta
“Allah ya shiryaku Wallahi.”
Hannu Hamida ta daga mata
“Amin. Amman ki rantse har kasan ranki bakya son auren me kyau? Mijin da ba zaki boyema kawayenki ba”
Wannan karin Hindu ce take dariya sosai, dan an tabo mata inda take so, shisa wani lokacin tana son yan uwanta na bangaren Baba saboda wayewar su, ta dauka zasuce wani abu da tayi maganar Miji me kyau, ashe duk sun gane kan al’amarin. A wannan zamanin me akeyi da namiji mummuna. Khadee kai kawai ta girgiza musu, tana sa Hamida juya idanuwanta
“Kinji zancen ko? Hajiyata Allah ya bamu masu kyau.”
Kai Mimi ta jinjina
“Masu kudi kuma.”
Hindu na saurin amsawa da
“Amin thumma amin.”
Fati da take gefe sai lokacin ta tsoma musu baki
“Banji kunce mafi alkhairi ba.”
Tana sa Hindu amsa ta da
“Wannan ai itace karshe, in dai yana da kudi, yana da kyau… Ai da alkhairin shi yazo”
Sosai suka cigaba da hirarsu akan maza masu kyau da irin yanda zasu zaba su darje. Hindu ta jima tana mamakin dalilin da zaisa ka daga hannu wajen rokon Allah miji ka tsaya a iya ‘mafi alkhairi’. A ganinta hakan babbar wauta ce, ka bude bakinka ka zayyana kalar shi tun daga sama har kasa, kai a zuciyarka kasan kalar mai alkhairin da kake so. Tun da ta fara hankali, ta fara fahimtar akwai wani abu soyayya da kuma aure take addu’ar namiji me kyau mai kudi, ita shine mafi alkhairi a duniyarta. Indai yana da abubuwan nan biyu babu wani abu da zata nema. Yanzun ne ma addu’ar kan canza lokaci zuwa lokaci.
Ganin lokacin sallar isha’i yayi yasa da yawansu tashi. Hindu bangaren su ta koma, duk da daga farko bataso fitowar ba, taji dadin hirar su, ta kuma ji dadi da Anty tasa ta ajiye waya taje. Tana idarwa ta daga hannuwanta sama, bayan tayiwa Baba addu’a da Anty da yan uwanta, tata addu’ar ta fara, neman lahira da mutuwa me sauki dan tana firgitata, tukunna ta fara fadin
‘Allah Kai Kace mu roke Ka zaka amsa mana, Allah kabani miji kyakkyawa, dogo, ko bakine ina so, Allah idanuwan shi su zama irin na Anas din Tana tare da ni. Mai kudin da zai kaini hajji da umra, ya sai mun mota ya bani kyautar gida. Miskili na gaske, mai aji, wanda zai so ni fiye da komai a rayuwar shi. Allah kabani yara masu kama dashi sak’
Maimaitawa tayi sau bakwai tukunna ta rufe da Salatin Annabi SAW dan addu’ar tayi saurin zuwa. Mikewa tayi tana komawa bangaren Mama san suci gaba da hirarsu, tasan in sun gama wasu zasu dawo nan bangaren Antyn su kwana, kamar yanda akayi jiya.
***** *****
Washegari da sukaje wajen kai amarya, Hindu taji dadin hirar novel din da suka dingayi ita da Mimi, dan ta saka ta bude facebook account, ta kuma shigar da ita groups da yawa da zata dinga samun litattafan hausar a saukake. Suka kuma yi musayar lamba da alkawarin Mimi zata dinga turo mata litattafai masu dadi. Gidan Halima yayi mata kyau duk da ba wani girma gare shi ba, daki biyune, amman filat ne yasha tiyal masu daukar ido. Ga Baba yayi kokari matuka wajen zuba mata kayan alfarma.
Kyawun da gida yayima Hindu bai hanata rokon wanda ya linkashi girma kamar sau goma ba, tafi son gidanta ya kasance da bene, yanda mijin inya daukota zai sauko bene da ita. Ba irin wannan dan gidan ba, tana kuma so ta shiga wannan falon yau, ta shiga wancen gobe. Burinta me girma ne, ta daina maganar ko da Khadija saboda yanda take mata kallon marar hankali wasu lokuttan, ita kuma bata so ko kadan, dan ra’ayin su ya banbanta baya nufin ta dinga kallonta kamar ba zata sami abinda take buri ba.
Ko babu komai, hausawa kance in da rai da rabo. Kusan Hindu zatace da duk ranar da take wucewa da yanda burinta yake kara girma, ta dauka da tagama sakandire ta samu damar da take bukata tayin zance da samari zata tara su kamar layin markade, sai ya zamana burinta ya katange hakan, gashi yanzun ita da kanta tanajin canjin da tayi a jikinta na bayyanar cikar yan matanci. Tunda Khadee da kanta kan yabata idan tayi kwalliya lokaci zuwa lokaci ta fara yarda da tana da kyau. Ta dibo hasken fatar Baba, a dakinsu kaf itace tayi dogon hanci irin na Mama. Ga bakinta dai-dai fuskarta, tana da matsakaicin tsayi, tana kuma da kyawun da zaka fahimta a kallo daya.
Jamb tayi mata rashin darajar da kan faru da dalibai masu burin zuwa jami’a. Sosai take hasaso kanta a KASU kafin jamb tayi mata yankan kauna. Gashi Baba baya bari ka zauna, ya tsani zaman shekara dayar da zakayi a gida baka wani abu, zaice ko FCE ce ka farayi, karatu karatune, duk ta inda dama ta baka ka fara, a hankali in kayi hakuri zaka kai inda kake so. Dari da saba’in da hudu taci, ya kai yanda Kaduna Polytechnic suke so, amman tayi sashin kimiya da fasaha da akafi sani da Science ne a sakandire. In ka tambayeta dalilin da yasa ta zabe shi ba zata fadi guda daya ba.
Ba zaka kirata mai kokari ba, ba kuma zaka sakata a layin marassa kokari ba, ta kasance a tsaka-tsakiya, inka raba ajinsu gida uku, tana cikin kaso na tsakiya, sakamakonta baya wuce C ko da can, da wahalar gaske kaga B, tana cikin mutanen da turawa kan kira ‘average’ ta fannin karatu. Har ranta aikin likitanci bai taba burgeta ba, saboda shi Zaid yake karanta, kusan duka gidan daliban Science ne, asalima tana son karantar abu daban da wanda kowa a gidan yake karanta, karshen abinda take so shine a fara gwada kokarinta da wani a cikin gidan.
Ko kuma azo ana mata wani iyayi na daban, sai dai ta duba ta rasa kwas din daya kamata ta karanta, ta kasance tana matukar sha’awar zane-zane tun da karancin shekaru, duk litattafanta baka rabasu da zane, tayi shawara da Baba kan ko zata koma Art ne, saiya bata shawara mai zai hana ta koma fannin Technology saita karanci Architecture fannin zanen taswirar gidaje, amman kwas ne da yake matukar bukatar jajircewa dan ba sosai ake samun mata a fannin ba.
Ko da bata so ma zatayi tunda Baba ya nuna yana sha’awar kwas din, a yanayin fuskar shi taga alfahari a kwance data yanke shawarar yin kwas din. Baima saka kowa a gidan ba, da shi da ita suka dinga zuwa hidimar siyan form da sauran duk wani abu da ake bukata. Cikin ikon Allah ta sami gurbin karatu a Kadpoly, sai taji dadin kasancewar babu nisa da gida, in taso ma da kafarta zata iya takawa. A haka Hindu ta fara karatun ta a shekarar 2014. A lokacin ne komai ya fara canza mata.
Zatayi karya idan tace Architecture baizo mata da bazata ba, sam duk wahalar shi ta wuce yanda Baba yake fada mata. Amman kuma tana jin dadin yanda mutane kanyi mamaki in sukaji abinda take karanta, sukan kuma jinjina mata, hakan ba karamin dadi yake mata ba. Da gaskiyar Baba, ajin su bakwai ne kacal mata, sauran duk maza ne. Har zuwa yanzun da suke a zangon su na farko bakowa take magana dashi ba, asalima kullum da earpiece manne a kunnuwanta dan kar ayi mata magana, kawarta daya duk ajin itace Hauwa, a haduwa ta farko zaka dauka Hauwa nada bala’in girman kai, saboda kullum fuskarta a hade take, saika zauna da ita zaka gane saukin kan da take dashi.
Kusan duk inda zasuyi a cikin makaranta tare suke zuwa, hatta da cin abinci, kafin wani lokaci sunyi wata irin shakuwa da zata baka mamaki. A bakin Malamai Hindu ta fara jin Hamza Abu Abbas, dalibin da ya kafa tarihin da ba’a taba kafashi a makarantar ba tunda aka bude department din, haka kawai ta tsinci kanta da son sanin kowaye shi, sosai take jin son sanin Hamza Abu Abbas din da kowanne Malami yake musu kwatance dashi. Amman wanda zata tambaya a ajinsu duk bakine, yanda taji labarin shi a bakunan Malamai, haka suma sukaji.
Ta gwada yiwa Hauwa zancen a shekararsu ta farko, ta tabe baki tana dan daga mata kafadu cikin halinta idan bata dauki abu da muhimmanci ba
“Koma waye nikam harya gundure ni, bana so ana maimaita mun abu daya kullum, Hamzan nan sun mayar dashi kamar wani abin bauta”
Murmushi Hindu tayi, da tunanin Hamza lokaci zuwa lokaci ta kammala shekararta ta farko ta shiga NDII, tasan ko hasken Hamza ba zata kamo ba a wajen karatu balle ta kwatanta, inda take yanzun yayi mata, kawai tana son sanin ya yake, ko kadan ne taga kamannin shi, taso tambayar yan HNDII dinsu da suka fita, kawai batasan yanda zata fara kawance da wani a cikin su bane a lokacin, da ko mai hoton Hamza tagani. Har Khadee tasan labarin Hamza a bakin Hindun, tunda kaf abinda ya faru a makaranta inta dawo saita bata labari. Anty kanta takan ji zancen Hamza, Hindu na mita wata rana idan sunyi abu an kushe.
Da wani yace mata zata so Kadpoly har haka zata karyata, amman zuwa yanzun da project dinsu na kammala NDII yake ta matsowa sai take jin tana son taci gaba a makarantar. Maganar Samari kuwa babu kalar da bata haduwa dasu, na farko basuyi mata ba daga shigarsu zuwa abin hawansu ballantana harta saurare su, na biyu kuma ko kadan bata da cikakken lokaci, kallo ma saitayi wata bata gama film daya ba, gara dan karatun Hausan takanyi shi a manhajar Wattpad data gano yanzun, tunda tayi wayar hannu ta Android.
Zuciyarta da wani irin nauyi take takawa zuwa gida, duk gajiyar da tayi a yammacin ranar bai sa ta nemi abin hawa ba, kafin ta tashi daga makaranta sukayi hira da Dimples ta WhatsApp tana bata labarin saurayinta Faisal da ake ma inkiya da Fash, harta turo mata hoton shi, gaye ne na kwatance, duk da Hindu tayi mata murna, a can kasan zuciyarta taji wani iri, ga kawayenta duk sun sami Samari tsayayyu, dan Biebee har ana maganar kawo kudin gaisuwarta da Usman, sai itace har yanzun wanda zai kwanta mata a rai ma bata gani ba, ballantana ayi wata tsayayyar magana.
Zatayi karya idan tace abin baya damunta, zuwa yanzun sai take ganin kamar dole ta sassauta burinta, kamar da wahala ta sami mijin da take mafarki, tafiya take kan titin da zai kaita gidansu, amman hankalinta ma sam baya jikinta, koya ta rufe idanuwanta ta bude su sai taga zanukan Hamza na zangon karshe da yayi sun gilma mata, dan suna gama magana da Dimples ta tsinci kanta a hanyar Data room, ta nemi ganin zanukan shi, aka kuma dauko mata. Zuwa shekarar a cikin ajinsu, a ajin manyansu, a internet taga zanuka babu adadi, batasan me yasa nashi ya zamana daban ba.
Hannu tasa tana shafar rubutun shi na cursive daya rubuta sunan shi dasu, cikin salon da zaka iya rantsewa da Allah ba hannu ne ya rubuta ba, babu kala ko daya a zanen shi, bakine, banda wajen sunayen da yayi amfani da maka ja da baka wajen yin design. Zanen kan shi kamar da injin aka buga. Lallai dole Malamai suyita magana a kan shi. Daga zanen shi tagane banbancin da yake dashi da sauran mutane, taji wani Malamamin su yace Hamzan ya sami gurbin karatu a South Africa, duk da bai tsallaka kasashen ketare ba, South Africa a wajen Nigeria take, akwai maza irin Hamza a duniya, akwai Maza irin Fash din Dimples, akwai irin Murtalan Hauwa, batasan me yasa ita ta kasa samun kalar nata namijin ba.
Ranta a bace take jin shi, tana gab da gida taji wata mota a baya tana ta mata hon, bata juya ba duk da tasan da ita yake, abinda ya saba faruwa ne zai faru yau din ma, zata tsaya, shikuma zai fito daga motar, tun daga yanayin fuskar shi zai zamama bai mata ba, balle kuma ta tsaya ta karema yanayin shigar shi kallo, lokacinta zata bata kamar yanda ta saba, su kansu Samari zuwa yanzun ya kamata su gane ita din ba ajinsu bace ba, Hindu ba matar mummuna bace ba, matar me kyau ce, su daina binta, amman ba zasu tabayin wannan abin arziqin ba. Inda duk zata shiga sai an sami mutum daya ko biyu mummuna da zai bude bakin shi da sunan tayi mishi.
Wata zuciyar ta saqa mata, ta tsaya, ta saurare shi, dan tsayawa tayi, kamar hakan yake jira yayi parking, babu laifi motar shi za’aje da ita ko shopping ne in ba’a shiga taron biki ba, a tunanin Hindu. Cikin hanzari ya fito yana yi mata murmushin data runtsa idanuwanta tana sake bude su
“Guntu ne”
Wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata, duk da tsayin shi daga inda yake zaifi nata kadan, fuskar shi babu yabo babu fallasa, sai da ya ketaro yana karasowa kusa da ita taji yana warin ajiyayyen quli-quli. Sosai ranta ya kara baci, ta hade girar sama da ta kasa, ta rasa abinda yake damun wasu mazan da ba zasu saka turare ba, jibi irin motar daya fito daga ciki, da maza zasuji shawara da sun dinga karanta litaffafan Hausa, watakila idan sukaji yanda Mazan Novel suke tashin kamshi kamar waliyyai zasu fara neman turare. Haka mazan gidan su, basa wari, amman kuma batajin kamshin turaren su na kama waje bayan sun tashi.
Fuskar shi ta kalla da take ta naso, inda za’a tsaya a tatse man dake fuskar zai soya wainar kwai
“Hajiya…”
Ya fadi yana wani dashe mata bakin dayasa hancin shi bajewa kan fuskar shi yana dishe dan kyawun da taga yayi mata
“Sannun ka.”
Ta fadi a dakile tana karema kayan jikin shi kallo, wandone ya saka baki mai ratsin ja da fari, sai wata jar riga daga ciki, ya kawo kwat ruwan toka ya dora, sai irin hana sallah da take ganin tsofaffin inyamurai na sakawa a fina-finan kudu. Bai kara fita daga ranta ba sai da takai dubanta zuwa takalman kafar shi da sukayi mata kama da jirgin kwale-kwale. Sunyi budu-budu da kasa
“Sai yaushe ne zan sami kalar saurayin da zai kwanta mun?”
Tayi tambayar a zuciyarta, a fili tana jin kamar ta fashe da kukan bakin ciki, da ta sami saurayin har yaushe zata tsaya kula irin wannan.
“Na tsayar dake kan hanya ko? Kibani lambarki muyi Magana.”
Wani irin kallo Hindu take mishi da yasa shi fadin
“Nasan baki sanni ba, Sunana Badamasi, lakcara ne ni a KASU”
Lumshe idanuwanta Hindu tayi, tana budesu cikin godiyar Allah da bai kaita KASU ba, indai haka lakcarorin su suke, gara da bataje ba. So takeyi ma tabar wajen kar ace saurayin da take mafarki yazo giftawa yaganta tsaye da Badamasi. Wayarta ta dago tana fadin
“Ka gayamun taka lambar, ina sauri ne zan karasa gida”
Cike da fara’a Badamasi ya gaya mata lambar shi, Hindu tayi kamar tana sakawa, tukunna ta dago kai da dan guntun murmushi tana fadin
“Banda kati yanzun, ina karasawa gida zan kiraka….”
Dan jim Badamasi yayi da kokwanto shimfide a fuskar shi, amman murmushin da Hindu tayi saiya dan bashi hope akan cewar zata kira din, yana juyawa ta zabga mishi harara
“Allah kaci gaba da gina katangar karfe irin ta kurkukun kiri-kiri tsakanina da irin wannan bayin naka, Allah ka kawomun saurayi irin wanda nake so”
Hindu take fadi kasa-kasa tana kara baza sauri, tasha kwanar da zatayi zagaye sosai kafin ta karasa gida dan kar Badamasi yayi tunanin biyo bayanta, duk da haka tanayi tana wai-waye harta shiga gida.
***** *****
Godewa Allah takeyi da bata da assignment a ranar tunda satin jarabawarsu ta karshe ne zai kama, sun kuma yi presentation dinsu na karshe sai bayan jarabawa, a gajiye likis take jinta. Tunda sukaci abincin dare tana bangaren Mama ita da Khadee suna hira
“Kinsan yau naga zanen Hamza… Inalillahi… Wallahi ban taba ganin zanika masu kyan nashi ba… Kinga rubutun?”
Ta karashe tana cire wayarta daga key tana kokarin shiga gallery dan ta nuna ma Khadee hotunan zanen da ta dauka
“Ai tunda kikaji Malamanku na maganar shi, duk yanda kike fadar kushen su kan ayyuka, kinsan ba karamin kwaro bane”
Kai Hindu ta jinjina tana mikawa Khadee wayar
“Kalli fa.”
Ware idanuwa Khadee tayi cike da mamakin ganin wai hannu ne yayi wannan zanen
“Karki ce mun da hannu ne wannan”
Dan murmushi Hindu ta tsinci kanta yi, cike da alfahari kamar tasan Hamzan, ta dangwala screen din wayar tana nuna ma Khadee sauran hotunan da fadin
“Ai danma baki gansu a fili ba, rubutun kawai abin kallo ne.”
Kai Khadee ta jinjina tana mamaki matuka, sosai suke hirar Hamzan, kafin taje ta kwanta, haka kawai Hindu najin wani kusanci tare dashi da ba zata iya misaltawa ba, sai take tunanin ko yana wanne halin, ko zai taba dawowa Nigeria ma oho, ko sau daya zata so taga fuskar shi
“Zai iya yiwuwa mummuna ne.”
Zuciyarta ta ayyana mata, tana sakata yin murmushi. Shafin twitter ta shiga dan ganin diramar dake wakana ta ranar, babu wani abu a TL din nata na nishadi sai ta sauka tana komawa facebook, zuciyarta taji ta doka da tunanin ta duba Hamza ko a facebook ne, da sauri taje search tana rubuta.
‘Hamza Abu Abbas’
Jerin mutane wajen goma suka fito, na farkon da ta ga hoton profile din shi an rubuta ARC ta shiga. Tana kuwa bude ta ga description dinshi taqaitacce ne, inda yayi sakandire, Kadpoly, sai University of Johannesburg da take da tabbacin nan yake karatu yanzun. Zuciyarta na wata irin dokawa ta tura mishi da Friend request, kafin ta shiga wajen hotunan shi har wata zufa takeji tana karyo mata, hotuna ne sunfi 800+, gyara kwanciya tayi tana dubawa daya bayan daya, hotunan zanukane wanda akayi da hannu da kuma na kwamfuta, sai zanen da akafi kira da rough sketches a turance da su kansu suke a tsare.
Hoto daya taci karo dashi na Hamza, yana tsaye ya juya baya, da riga mai hade da hula a a jikin shi, rigar mai dogon hannu, da alama hannuwan shi na cikin aljihun rigar ta gaba daga yanayin tsayuwar shi, rigar fara ce kal da bakin rubutu daga kasa an saka HAMZY_ da manyan baki. Dogone sosai, irin tsayin da take so, ji takeyi kamar tace mishi ya juyo taga fuskar shi. Komawa tayi tana duba maganganun dake kasan kowanne hoto daya saka wato comments, mutane nata yabawa da zanen nashi, cikin harshen turanci, harshen hausa, sai kuma yaren da ta kasa karantawa, amman babu ko godiya daya da yayi musu, like yake dannawa shima ba’a kowanne comment ba.
Yanzun kam Hindu har a zuciyarta take jin ta fada abinda turawa kan kira da ‘Obsession’ akan Hamza. Sosai take son sanin komai da ya dangance shi, taje ta saka sunan shi a twitter bata ga ya fito ba, ta nema harta gaji, har yanda taga ya saka a bayan rigar shi ta saka, amman bata gani ba, ji take kamar kanta zai tarwatse saboda tunani, ta hasaso fuskoki sunfi kala hamsin tana dorawa a jikin hoton shi data hani a facebook, amman sai take ganin kamar bata dace dashi ba. Tunanin taje Instagram ta duba shine ya fado mata, ga wayarta da take nuna mata battery dinta saura biyu, generator dinsu ya sami matsala, kuma sunki kawo wutar dare yau. Data sani ta saka caji a makaranta.
‘Hamza Abu Abbas’
Ta saka, tana ganin wasu mutane sun fito da ta bubbude amman bata ganshi ba, bata tunanin yana cikin su, dan wasu ma larabawa ne. Sai ta sake duba
‘HAMZY_’
Shima bai fito ba, gyarawa tayi zuwa
‘Hamzy_’
Aikam sai gashi ya fito, da wannan hoton nashi na facebook a jikin profile din shi. Tana budewa taga tarin followers dinshi har dubu arba’in da yan kai, taga mintina biyu da suka wuce ya saka hoton da network ya hanashi ya bude mata da wuri, ga wayarta zata iya mutuwa gabaki daya. Budewa hoton yayi tana saka idanuwanta cikin na Hamza da yake kamar yana kallonta, zuciyarta nayo tsalle ta dawo makoshin ta, dai-dai lokacin da wayarta ta dauke!