Skip to content
Part 14 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ni da Gambo hankalinmu yayi matukar tashi, in ban da kuka babu abin da nake yi, Gambo kuwa ta shiga tattara kayanta tana kintsa abinda yake bukatar kintsi alamar kenan in har Baba Yahaya bai yin nasarar hana Babana hada aurena da Ado ba, to zata tasa ni a gaba mu tafi mu bar mishi gidan.

Da yamma bayan Sallar La’asar na shirya na fita gidan Mallam mai babban allo, na tafi na gama rattaba mishi komai yana sauraro yana kuma shan furarshi bai fasa ba, babu alamar damuwa ko wani bacin rai a tare dashi.

Bai kuma ce min komai ba sia da na gaji na ce mishi to Mallam kana jina ba ka ce min komai ba.

Lokacin ne ya dago kan shi ya kalle ni wani irin lalataccen kallo ya yi min sai da ya gama share furar da ta taba labban bakinshi sannan ne ya ce min ba kun zartar da abin da zaku yi ba ne ke da uwarki, ga kuma Yahaya yana taimakonku shi ne kuka zo ku ka gaya min.

To ni meye nawa a ciki? Ba sai ku je kuyi abinda zaku yi ba? Na soma yiwa Mallam mai babban allo kuka yayin da shi kuma ya shiga yi min fada abinda ya yi dalilin da kukan nawa ya karu.

“Kin taba ganin in da mai Doki ya koma kuturi? Ya ce zai ba da ke ga Ado ace bai isa ba to sai waye ya isa? Sai ku da Yahaya? Haka kawai don kun samu mutum mai hakuri sai kuma ace iya shegen da za’ayi mishin har da na wulakanci da rainin hankali?

Ita uwarki ita ta ce miki ta zabi mijin da zata aura? Ko shi Yayanta bai kawo nashi gwanin ba? Na ce mishi a’a ni ga nawa gwanin da nake so a ba, ya kuma bada ita a dole duk da a lokacin auren tsinken zabori ban bada ba, amma na gwada iko na cewar ni ne uba mahaifi.

Shi kuwa Alhaji Surajo ke da uwarki kun ce bai da irin wannan ikon a gidan shi saboda shi ba uba ba ne ko? Tashi ki bani wuri, ya yi min umarnin ta hanyar tsawa.

Ina mikewa yana magana zata zo nan uwar taki ta same ni, sakarya kawai sha-sha-sha, in ban da sakaryar uwa wa ke taimakon ‘ya bijerewa uba ana karo ne tsakanin kwai da dutse? To in ma cutarku ake son yi sai me? Don an cuce ku, kuma sai me?

Kafin ayi muku ba a yi wa mutanen kirkin da suka fiku ba? Bai wuce ba? Abin mamaki itama Hajiya ‘Yar dubu rannan taya shi yi mana fadan tayi, har tana fadin shi lamarin aure ma ai ya wuce duk yanda ake zaton shi, sai dai addu’a kawai, in ban da a gidan ku a ina ake yin haka?

Uba ya ce ga yanda zai yi ace wai bai isa ba? Ko da yake ba laifinku ba ne ku kadai, na shi yafi yawa don shi yayi sakacin da mace tasha gabanshi sai abinda taso yake yi.” Mai babban allo ya shiga yi mata fada kan hakan da ta fada, ni kuwa nayi gaba na bar su tunda dai na gane ba goyon baya zan samu ba.

Kin yi mishi bayanin kuwa? Gambo tayi min tambayar a sanyaye saboda ganin yanda nima jikina yayi sanyi, na ce mata eh, amma dai kar kije. Tayi shiru tana kallona, zuwa can ta ce min shi Baba ba zai fahimci yanda abin yake ba, na ce mata eh.

Ilai kuwa rannan dare nayi sai ga Suwaiba ta daga labulen dakinmu babu sallama babu komai ba tare da ta gaida kowa ba ta ce min, wai in ji Kawu Ado wai kije yana kiranki.”

Muka yi shiru ni da Gambo, ta juya ta tafi na kalli Gambo na ce mata, bari in je in ji abin da zai ce min, ta ce min to.

A zauren gidanmu na same shi tsaye cikin kwalliya, sai wani kamshi yake yi tanfar wani wanda ya zo tadin gaske, sai dai ba don tadin yayi kwalliyar ba, dabi’arshi ce yin hakan don a yanzu ko Babana bai kai Ado sanya yadi mai tsada ba, muka dan yi shiru kadan na dan wani lokaci kafin na kawar da shirun ta hanyar tambayarshi.

“An ce kana kirana?” ya ce min “Eh” na ce to lafiya? Ya ce, kalau, tadi zamu yi. Na sake kallon shi a sakarce na ce tadi wane iri? Ya ce tadin aure, na ce to muyi in ji, ya ce ai gashi nan muna yi.”

Na gane shima irin zuwan da nayi shima shi yayi, don haka sai na ce mishi Ado, ya ce Humaira, na kawar da duk bacin ran da nake ciki don in samu gaya mishi abinda zan gaya mishi, na ce mishi yanzu nan kai idan aka baka ni aka ce ka aura sai ka aura? Cikin natsuwa ya ce min kwarai kuwa, na sake zuba mishi ido ina kallonshi na ce mishi saboda me zaka yi hakan? Saboda baka jin kunya? Saboda baka jin tausayi? Saboda ba ka damu ba kai kayi ta taimako ana yin cuta? Ko kuwa saboda me?

Cikin natsuwar shi ya sake cewa, saboda ni namiji ne, na sake tambayarshi saboda kai namiji? Ya ce min eh, na ce mishi to babu laifi to amma zan aike ka wurin wadanda suke saka kana yi, wadanda suka turo ka kazo ka aureni, don ku kara cutarmu saboda duk abinda ku ka hadu kuka yi mana ni da uwata bai ishe ku ba. Ka gaya musu ni na ce wannan karon ba za ku yi nasara ba, don ba zan kyale ku ku sake sanya uwata cikin wani bacin ran ba.

Don haka in har zaka ji shawarar da zan baka to kayi maza ka ce musu ka fasa ba kaso, don kar suyi dalilin fadawar ka cikin wawakeken ramin da ba za su iya fiddo ka ba.

A hankali ya ce min, babu komai don an yi hakan na ce to shi kenan, na juya zan shiga gida, ya ce to tsaya ai da sauran bayani, na ja na tsaya ina kallon shi menene bayanin? Kudi ya ciro ya miko min dunbus a hannunshi ya miko min tare da fadin kudin tadi zan baki.

Sai da na kalle shi na kalli kudin sannan na sake kallonshi na ce mishi ai baka da su, baka da ko kwabon da zaka bani in karba, don duk wani abin da kake dashi kake barazana ka ke wani menene? Na ubana ne, sannan ina so in sanar da kai don nasan komai hatta asara-asarar da kake cewa an yi da kudin kujerar Gambota da aka baka kaje ka biya mata kujerar Hajji kaje ka dawo ka ce kayi sujada an dauke kudin sai daga baya kai da Mama kuka ce kun je kauye kun sayar da gonakinku na gado ku ka sai gida. Nasan komai.”

Ya ce to ai yayi kyau gara da ki ka san komai, ungo kawai ki karba in baso kike kiyi ma kanki ba, na ce ai babu komai tunda yanzu dai ka mako na karbi kudin hannun ka wanke kifi aka yi da ruwan jikinshi cikin dukiyar ubana ka ke fantamawa don haka rike ka kara ci, na wuce shi nayi tafiyata.

Tunda Ado ya kira ni na amsa kiranshi sau daya ban sake ba, ko a hanya muka gamu wucewa kawai yake yi nima in wuce.

Muna cikin haka muka wayi gari Anti Sha’awa da ‘ya’yanta guda uku sun kwana a gida ga dukkan alamu kuma ba lafiya ba ne, yaji ta yiwo don ina jin Mama tana yiwa Babana bayanin dalilin yajin nata, tana fadin wai ka ji min dan iskan mutumin nan mara mutunci Alhaji, Zubaida tana daga kicin ta ce assha surukinne kuma dan iska? Ban kulata ba don har yanzu bana shiga harkarta, gaisuwar safe ce kawai take hada ni da ita daga nan babu kari, na dai lura kawai na gane ita da Mama sun dan yi tsami sai dai ban san dalilin tsamin nasu ba, kawar da kunnuwana nayi daga sauraron Zubaida na maida su wajen Mama da Babana.

Wai ashe aure yake nema ka ji dan iska, ko yaushe ya gama ciyar da na gidan? Oho!.

Babana ya dan yi maganar da ban ji ba sia na ji Mama ta soma cewa, ina Alhaji? Ai ma ba zai yiwu ba kar ma ka fara sai ka ce wata mara gata? Ai sai ya zo nan shi da kanshi sai mu ji dalilin kara auren nashi, menene ba a mishi ta ina aka gajiya mishi? Ko kuma dai neman fitina? Ba’a gama kada wata ba ana cewa wata ma ta tube, ai zamu gamu ni dashi zai gane karon babu dadi in don yaga ina yi mishi lako-lako ne.

Haka Babana ya hakura ya kyale Anti Sha’awa a cikin gidan nan yana kallonta ita da ‘ya’yanta har tsaraba yake kawo musu bai kawowa nashi ‘ya’yan ba, tana yiwa kowa kallon uku kwabo sai tayi ta habaici tana fadin maganganu kan aurena da Ado, wai daga rufa mana asiri da aka yi amma muna wani iya shege in ban da Mama ma ai Kawu Ado ba mijina ba ne, don yafi karfina kamar in ce to aba shi daidai dashi mana nima abar ni da daidai ni sai Gambo ta ce min kul, ja bakinki kiyi shiru na ce mata to.

Kwanan Anti Sha’awa uku a gida mijinta bai zo ba, bai yi aike ba, hankalinsu gaba daya ya soma tashi don sun saba in ta yiwo yaji ya yi ta zirga-zirga safe da yamma yana kawo hasafi ana wulakantawa ana tambayarshi baka bayar a gida ba sai da aka zo nan? Ai ya zama aikin banza.

Shi kuma ya yi ta bada hakuri yana rantsuwar babu ne amma in akwai ai babu wanda zai fi maigida son ya yi wa iyalinshi alheri. Mama tana fadin ba dai kai ba kam don kai kam ba mai alherin ba ne.

Rannan da yamma sai ga Baba Yahaya yazo gidan, sallama daya ya yi ya shigo cikin gidan bai jira sai an amsa mishi ba yana rike da wani kunshi na tsohon buhu a hannunshi na fito daga kicin da sauri don in karbi buhun a hannunshi, sai kawai naga Innar Giyade tana biye dashi tukuf-tukuf.

Tsalle na buga na kuma kurma ihu da karfina kafin na kankameta ina fadin “Kai ku firfito ga Hajiyar Giyade tazo.” Da gudu aka yi ta firfitowa yi mata oyoyo, ni kuma Baba Yahaya ya tsare ni da ido yana yi min dakuwa hannu bibiyu don Atika ta riga ta karbe buhun da ke hannun nashi. Kaga min ja’irar yarinya kina hauka ne ko kuwa kara sa mana ita za ki yi? Na sake ta cikin sauri a hankali cikinladabi na ce mishi Baba kayi hakuri.

Na kama tafin hannunta na rike tana kokarin kwacewa kyale ni ni kar ki matse ni, na ce haba Hajiyata ai tamu da ke bata baci, har dakin Mama na kaita don nasan can ne masaukin nata a can muka tattaru gaba dayanmu muna ta hargowar yi mata oyoyo rabonta da gidan anyi matukar dadewa.

Mama ta shiga hidimar yi mata hidima sai ina aka saka da ita take yi, itama dai nasan ta gane Baba Yahaya ne yaje ya daukota ba kuma kan komai ba sai kan maganar aurena da Ado. Rannan ni da Gambo muka kwana muna murna tunda ga Hajiyar Giyade tazo ai kuma zance ya kare ana baiyana mata komai zata hana auren.

Rannan kwananta biyu a gidan tasha farfesu ta kuma wastsake gajiyar girma, idanuwanta sun bude sosai ta soma gane kan gidan da kyau, ina cikin wanke-wanke na ji ta tana tambayar Babana ni wannan yarinyar Sha’awa me take yi ne a gidan nan? Ya dan yi ‘yan wasu maganganu da ita da kanta na ji tana cewa, ban fa ji ba to balle kuma ni da nake nesa. Sai ga Baba Yahaya yana sallama ta amsa mishi tare da yi mishi sannu da zuwa, sai albarka take ta sanya mishi tare da tambayarshi iyalin sun je gida lafiya ya ce mata lafiya kalau sun ce a gaishe ta, ta ce to tana amsawa, Allah dai yayi musu albarka ya kuma amfana su, Babana ya ce amin.

Sai da aka dan yi hira sosai sannan Baba Yahya ya gyara zama ya ce mata, to Gambo ko da naje na dauko ki akan ki zo kiyi mana bakunta saboda kin dade ba ki zo mana ba, to ba bakuntar kadai ba ce tasa na dauko kin, tayi maza ta gyada kai tare da mamula bakinta ta ce, nayi zaton hakan nayi zaton da wani abu watakila tsakaninka da dan uwan naka ko kuma tsakaninshi da iyalin shi.

Baba Yahaya ya sake gyara zama kafin ya ce mata kan maganar auren Humaira ne, Hajiyar giyade ta ce Humaira, Humaira ya ce mata Aisha, ta ce af to, tayi shiru tana sauraronshi ya gama rattaba mata ba yanin komai sai dai ya yi kokarin cire sunan Mama a ciki watakila don yasan ba wani son Mama take yi ba, watakila kuma bai son nuna mata gajiyawar danta kan rikon gidan shi.

Sai da ta gama sauraronshi tsaf yayin da ni da Gambo da su Atika muke dakinmu muna sauraro cikin murna da farin ciki zata zartar da hukunci na adalci a tsakaninmu suma su Mama da nata iyalin suna wurin su don daga ita sai Babana da kuma Baba Yahaya ne a tsakar gidan.

Muna cikin sauraronta sai muka ji ta ce mishi, kan wannan maganar ne kaje ka dauko ni Yahya? Cikin ladabi ya ce mata eh, Gambo sai kawai muka ji ta ce to ai kuwa dai baka kyauta min ba, ashe wadannan yara ba ‘ya’yanka ba ne ina dalilin da ba zaka zartar da hukunci a kansu ba? Ina dalilin da za ku zauna kuna kace-nace dashi akan wannan ja’irar yarinyar mai bakin ido? Ba ga sauran ‘yanmata a dakin uwarta ba?

Ko su me zaku yi da su? Su masu son auren nan ai duka sun cancanci a basu wa za’a ba wa za’a hana? Yanzu shi wannan yaron na gidan nan in an hana auren nan ba a ji kunya ba? Ai sai yaga kamar don ba ku ku ka haife shi ba gashi kuma a gabanku ya girma yana kuma hidimarku ai shi ne ma gidan tunda bini-bini za ka ji Ado dai, Ado dai, Ado dai.

To kuma sai ku hana shi aure Yahya? Ai bai yi ba ni da Gambo da su Atika muka zaro ido don jin ba zamu samu goyon baya ba, sai dai dole muka yi shiru muna ci gaba da sauraro, su wadannan ‘yanmata guda biyu da suka saura a dakin Fatsuma tunda su na majadan sun samu nasu mazan ko? Baba Yahya yayi maza ya ce eh, sun samu, ta ce to su sauran na dakin nata Atika da Aliya ko? Ya ce “Eh, sunan su kenan ta ce to ka baiwa Salisu su daya shima dan wan uwar tasu da ya zo nema ka bashi daya ai ina ganin ma gaba ta kai su sun zo neman baka an ba su farare.

<< Mijin Ta Ce 13Mijin Ta Ce 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×