Skip to content
Part 21 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Rannan cikin dare ruwan sama mai karfi ne yake sauka kamar da bakin kwarya, ina kwance can cikin daki akan katifata bayan na shafe jikina da mayuka masu kamshi da kara laushin jiki sai da na feshe jikina sosai da turare mai sansanyar kanshi, sannan na shige cikin bargona na ruhu.

Ina jin yanda ruwa ke sauka da kuma sauraron tsawar da aka yi ina mai karanto addu’o’in da ake yi lokacin saukan ruwa, ko kuma tsawa. Ni kin kawar min da kofin da kanwar nan ke ciki ne? a hankali na ce mishi eh, ai ban san kana so ba ne ya ce ina so mana Humarai, ai kema kin san ina da bukatarta, gashi yanzu ruwan sama yayi karfi yaya zanyi in je kicin in samo wata? Na ce to ko in zo in kawo maka wata, ya ce bar ta kawai zan yi hakuri tunda ga ruwa yayi karfi.

Kwanaki kusan tara a jere babu abinda ban yi ba, wanda zan sa Ado ya tanka min na jan hankali da hila don dai in samu in sallama mishi kaina tunda na gane abinda nayi mishin ne ya sanya Gambo har yanzu bata daukan wayata, amma ya ki. Yana ganina a kusa dashi da lalatacciyar shiga sai yayi maza ya kawar da kanshi ko ya haye kan doguwar kujerarshi ya ja abin ruhuwa ya lulluba ya ce, wai bacci yake ji. Da rana kuma yana Azumi.

Cikin zuciyata na ce to ko dai ya tsorata da abinda nayi mishi ne yake ganin kamar a yanzu ma in ya matso kusa dani zan sake maimaita mishi? Gashi Mama ta tasa shi a gaba kullum sai ta shigo gida ta tasa shi a gaba kan sai lalle ya sallame ni, ita auren nawa ya riga ya ishe ta gara kawai a yanzu don in ance sai an kai kwana casa’in to bata san me zamu sake yi mishi ba cikin wadannan kwanakin.

Yana fadin kiyi hakuri Mama, ba yau ba sai ka ji ta soma rattabo mishi maganganu tana tuna mishi sanda ta dauko shi daga kauye da irin wahalar da yake ciki a wancan lokacin da kawo shi gidanmu da tayi ta maida shi abin da ya zama a yau amma yake nema ya butulce mata saboda aurena.

Shi kuwa sai ya ce mata ai ban manta ba, Mama na gode miki da wannan taimako da ki ka yi min ina kuma yi miki addu’ar sakaiya ta gari, ban da haka ma tun kafin kiyi min hakan ke din uwa ce don haka ne ma a yau bani da wata uwar da ta fiki, to in har hakanne me yasa nake cewa ka sake ta kana ki? Sai ya ce ai shi aure ajali ne dashi in wa’adinshi ya cika sai kaga kamar a mafarki.

A wannan lokacin tausayin Ado nake ji, don na tabbatar da dadin komai yake ji ba don gaba daya al’amuranshi sun sauya, yin su kawai yake yi amma can cikin zuciyarshi ina ganin kamar akwai wani abin da yayi matukar takura mishi gashi kuma yana dawowa gida daga kasuwa zan ganshi yana wasu abubuwa wadanda shi kadai yasan me yake yi.

A wannan lokacin al’amuranshi da yawa sun sauya, mafi yawancin lokaci a yanzu ya koma shigowa gida ne wajen sha daya da rabi ko sha biyu duk da ba wata jituwa mai yawa ba ne tsakanina dashi, wannan sabuwar dabi’ar tashi ba dadi take yi min ba, amma nayi kamar ban san me yake yi ba, don kar ya dauka na wani damu dashi.

Rannan tun bayan Sallar Magriba ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya, amma Ado bai shigo gida ba da ya idar da Sallar Isha’i, har wajen sha biyu saura kwata na dare, kamar in kulle mishi kofa don in hana shi shigowa dakin in ya dawo, sai naga to na menene yin hakan? Ai kulawama yabawa ne.

Da safe ma haka daga sallar Asuba bai sake shigowa ba sai da ya shigo don yin shiri ya fita kasuwa ban ce mishi komai ba, zai kawo cefane in yi girki amma ba zai tambayi nashi abincin ba, in na ajiye ma ba zai taba ba, a zuciyata na ce shima dai zaman namu ya ishe shi hanyoyin rabuwa yake bi watakila jira yake yi Mama ta sake bashi wani umarni mai karfi kafin yayi sakin don tasan dai saboda ita yayi.

Muna cikin wannan zaman da Ado na kowa ta kanshi yake yi, duk rashin mutuncin da yake tatawa kuma kallonshi kawai nake yi, iyaka dai ina yi ina lissafin kwanakin da suka saura casa’in din su cika.

Ina zaune a tsakar gida bayan fitarshi kasuwa sai ga wayar Gambo ta shigo, ina bare-bare cikin yanayin rawar jiki na dauki wayar a dalilin na kirata yafi sau talatin bata amsa ba, Hello Gambo salamu alaikum.” Duka gaba daya na hada mata saboda zumudi, bata tsaya amsa gaisuwata ba sai ta soma tambayata ni wane irin zama ku ke yi ne ke da wannan yaron?

Da sauri na tambaye ta, wane yaron Gambo? Ta ce, mijinki mana, cikin zuciyata nace to itama Gambo mijina take kiran Adon? Kafin in soma yi mata bayani kan munanan dabi’unshi da nake shirin gaya mata don in roke ta ta kara tsaya min da addu’a akan rabuwarmu don ta zo cikin sauki ba tare da ya cutar dani ba, sai na ji ta soma cewa “kin ga ki shiga hankalinki da ni fa.” Cikin hanzari na tambaye ta me nayi Gambo?”

Maimakon ta bani amsa fada ta soma yi mu ma fa da ki ke ganinmu ba ma wulakanta aure mutuntashi muke yi in miji ya zalince mu, kuma mu zuba mishi ido saboda mun san watarana ba zai yi ba, mu wulakanci ne kawai ba ma yarda da shi ba kuma mayi wa wani, to amma ke na menene yana iyakar kokarinshi a kanki kullum sai kin wulakanta shi, kin ci mutuncinshi, da sauri na tambaye ta, me nayi mishi Gambo? Tun bayan wannan abinda ya faru na sake yin wani abu ne? ko shi ya kawo karata wurinki don ya hada ni dake, kiyi ta fushi da ni? Tunda ai dama can Gambo kin sani ba, son mu yake yi ba babu kuma abinda bai yi ba wajen ganin ya taimaka an kuntata mana sai kawai nayi ta soma fadin kinci gidan ku na ce miki kinci gidanku da wannan bayanin da kika tsaya kina yi min Gambo sake ji an ce min anga mijinki a waje bayan karfe tara na dare yana zaune to ni dake ne sakarya kawai mara hankali zaku hankatashi ne?

Tuni na soma yiwa Gambo kuka sosai ita kuwa bata kula da kukan nawa ba fada kawai take yi, nan da gobe kamar yanzu in ban ji kin dauki matakin gyara al’amari a tsakaninku ba to zaki yi mamakin abinda zan yi akanki ta ajiye wayarta.

Kuka sosai na zauna nayi saboda na gane itama Gambo a yanzu so take in mikawa Ado kaina bata damu da abinda zai biyo bayan hakan ba bata tsaya nayi mata bayanin da zai fahimtar da ita gane shima adon bai da wani kwadayi mai karfi a kaina ba tunda ai nayi mishi tayi na saki shi ne bai kula ba, to sai kuma yanzu da zaman namu yayi matukar yin daci bama tsami ba sai ta ce ta bani daga nan zuwa gobe da safe to me take so in yi mishi?

Na zauna nan wurin zuciyata sai kake sake take yi ta saka wannan ta kwance ta saka wancan ko abincin rana rannan ban yi ba saboda zuciyata a kuntace take.

Wajen karfe shida na yamma ya dawo gida, alamar dai daga kasuwa yake don dama lokacin dawowarsu kenan. Ban iya daga ido na kalle shi ba, saboda raina yayi matukar baci da abinda yayi min na hada ni da Mahaifiyata da yayi, ban taba sanin Gambo tana iya fushi dani ba in ban da a ‘yan kwanakin nan a kuma sanadin aurenshi, auren da a farkonshi daga ni har ita kin shi muke yi muna neman tsari dashi har ma ni ce mai danne zuciyata in bata hakuri akai, to ko kuma menene yayi mata dadi da auren a yanzu oho?

Har bayan Sallar Isha’i ni da Ado babu wanda ya ce wa wani ci kanka, kowa sha’anin gabanshi kawai yake yi, ya fito daga wanka ya sanya kayanshi ya fesa turare kamar dai yanda ya saba yi kullum shirin fita yake yi kamar dai kar in ce mishi komai in bar shi yayi tafiyarshi sai kuma na tuna Gambo da kalaman kashedin da tayi min na in ta sake jin an ganshi a waje bayan taran dare zan gamu da ita.

A zuciyata na ce uhun in ban da Gambo mutumin da ya riga ya mallaki hakoranshi talatin da biyu wanda ba wani ganin juna da mutunci dama can muke yi ba dan gara ma a dan zaman wuri daya da muka yi shi ne ma aka dan yi wa juna dan alheri a ciki shi ne wai zata yi fushi da ni saboda shi na sani nima wani lokaci nakan dan ji tausayin shi, saboda matsin lambar da yake fuskanta a wurin Mama a kaina.

Wacce ita din kuma da gaske madadin uwa take a wurinshi suna kuma son juna yana girmamata babu wanda yayi zaton zai iya bijirewa umarninta a kaina, to amma duk da haka ina ganin ni an takwaran ace dole ni ce zan nemi shiri dashi ba a daidai kuma lokacin da yake fito min da halaye iri-iri.

Kirjina sia harbawa yake yi bal-bal-bal saboda tsananin kin yi mishi maganar da nake shirin yi, sakai yayi ya fita ya miko hannu zai ja kofar ya rufe a daidai lokacin da na bude baki na ce mishi ina magana, yaja ya tsaya nuna alamar wai ni yake sauraro.

Sai da ya ji ban sake cewa komai ba lokacinne ya sake dawo da kanshi cikin dakin, kin ce kina magana? Ban iya cewa komai ba in ban da hawayen da suka soma zubowa daga idona, shar-shar-shar tanfar dai ba kukan na wuni ina yi ba.

Maida kofar yayi a hankali ya rufe sannan ya juyo gare ni, me ya faru Humaira? Baki da lafiya ne? Ban iya ce mishi komai ba, babu abin da yake cin zuciyata irin tilasta nin da Gambo tayi sai na nemi shiri dashi bayan kuma tasan me hakan yake nufi, ta kuma diban min kankanin lokaci na na yin hakan, ganin da na yi ya nufe ni da shirin taba ni ya sani kai gwiwoyina kasa na durkusa ban daina kukan da nake yi ba.

Hannu biyu ya saka ya jawo ni jikinshi nayi maza na zame, me nayi miki Humaira? In wani laifi nayi miki yasa ki wannan kukan na roke ki kiyi hakuri, ki kuma gaya min shi don gobe kar in sake yi miki shi. Rarrashin da yayi min ne yasa ni gaya mishi cewar yana hada ni da Mahaifiyata.

Da sauri ya ce min ban taba yin hakan ba Humaira, ai nasan tana sonki ba zan bata ki a wurinta ba, ban da haka ma yaushe ne na soma mu’amalla da ita da har zan je ina kai sukarki wajenta? Me ya faru wanda yasa ki ka ce ina hada ki da ita? Ban kalle shi ba na ce mishi ta ce ni nake saka yawon da ka ke zuwa, ya dan yi murmushi kadan ya ce bana fita yawo Humaira, hira nake zuwa shagon Sani mai shayi, wurin taruwar samari ne mu dan yi hira in dan ji dan saukin zuciyata, kema in bar ki ki dan sake.

Ba zan iya zama dake shiru ba in yi ta zuba miki ido ban kula ki ba, gashi kuma a yanzu ina cikin wani hali na canka-cakare, ban san abinda nake ciki ba a yau, ban kuma san abinda zan fuskanta ba, iyaka dai kawai nasan ina cikin wani irin rudani da ban taba shiga ba, wanda kuma na shige shi ne a sanadin aurenki da nayi.

Hausawa suna fadin wai tsalle daya mai jefa mutum rijiya, ya kuma yi dubu bai fito ba. Wani lokaci naka yin tunani in ce da dai ace na sani to da naji kashedin da kika yi min na cewar kar in karbi aurenki in nayi wannan tunanin sai in ce da nayi hakan watakila da ban samu kaina cikin halin da nake ciki ba, watakila da rayuwata bata canza ba daga yanda take watakila da yanzu ina nan ina zamana lafiya ina tafiyar da harkokina cikin kwanciyar hankali da gamsuwa.

A duk lokacin da tunani ya tsananta gare ni na rasa yanda zanyi in warware wa kaina matsalolin da na samu kaina a ciki, sai in ce wa kaina to in sauwake miki auren mana in zauna lafiya tunda dama ba da wata kyakkyawar manufa aka karbi auren ba, to in kuma nayi wannan tunanin sai kuma in samu kaina da tambayar kaina, in na yi hakan zan koma kamar yanda da din nake? Zan iya fidda ke cikin raina, in koma walwala da nishadi kamar da?

In zan yaudari kowa ba zan yaudari kaina ba, ina son zama dake sai dai kuma abubuwan da nake ciki da barazanar da nake fuskanta za su bar mu mu zauna tare? To in ina cikin wannan barazanar me ya kamata in yi? Shine hakuri, hakurin kuma yana nufin dole sia na rinka yin nesa dake saboda kar in aikata miki abinda zai zamo rashin adalci in tilasta ki yin abinda bakya so duk da nayi kokarin yi miki hakan a baya dalilai biyu ne ko uku suka ingiza ni yin hakan.

Na farko dai tsananin matsuwar da nayi a ikanki na biyu jin hirar ku da nayi da Ramla sia na gane har da ita ke zuga ki na uku kuma shine ban hango abinda na hango ba a yanzu, ban ce mishi komai ba, ban kuma tsaya tambayar shi abinda ya hango ba, iyaka dai kawai na mike na shiga bandaki nayi wanka na fito daure da farin tawul a kirjina, har lokacin yana zaune a inda na bar shi can cikin daki na wuce na zauna a bakin katifa bayan na ajiye kayan shafana kusa da ni.

Ko ba ka ce kana sona ba ma ya riga ya zama min dole in baka kyautar kaina tunda abinda Gambo take so kenan, zuciyata ce tayi min wadannan kalaman.

Ina magana ne na dan daga murya kadan na gaya mishi bai bata lokaci ba ya shigo, kallo daya yayi min ya kawar da kanshi gefe me ki ke so in yi miki Humaira? Ban kalle shi ba na ce mishi mai zaka shafa min, ya sake kallona da dan guntun tawul din da ke jikina ya durkusa a gabana yana fadin ba shafa man ba ne matsalar Humaira, abinda nake tunani shine kanwa ko andre leber sold ba za su yi min wani amfani ba, na ce to shi kenan nasa hannu na lakato man zan shafawa kaina, sai kawai naga ya karbe man ya daga hannayen nawa ya sagala akan kafadar shi wai don ya ji dadin shafa min man sosai.

<< Mijin Ta Ce 20Mijin Ta Ce 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×