Skip to content
Part 23 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ga dukkan alamu kuma nasan canzawar da nayi ne yafi komai ba shi mamaki, gashi kuma nayi kwalliya ta daukar hankali, ban wani ja zance yayi nisa ba, saboda ganin irin karbar da suka yi min na mike na fita. Ban tambayi su Habiba ba don kuwa nasan dukkansu suna jin shigowata suka yi kamar basu ji ni ba.

A kusa da kofar dakin Gambo na ci karo da wani lafiyayyen injin din wanki mai matukar kyau sai da na kare mishi kallo sannan na shigo cikin dakin nata tana zaune kan kujera, gaskiya ne da Hajiyar Giyade ta ce min ta fara murmurewa. Ina murmushi na mika hannu na dauki Adam karo na farko da na ji ina son shi tare da sunan da aka sanya mishin.

Na sake kallonta cikin murmushi na ce “Gambo rowar yaron nan take yi sai in yi ta aiken a kawo shi kina hanawa, bata kula zancen ba, ta mike taje ta kawo min yugurt mai sanyi mara sugar ta ajiye min, nayi murmushin farin ciki saboda ganin canjin da ta samu, na ce Gambo ashe injin din wanki kika samu shi ne nake ta aiken ki ba da kayan wanki in yi miki kina cewa babu, ba ki gaya min ba. Wa ya saya miki?

Ahmad ne ko Salisusu? Ta waiwayo a hankali ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min shi mijinki fa? Ba ki yi tunanin shi ya saya min ba, sai ki ce Ahmad ko Salisusu? Shiru nayi ban ce mata komai ba, itama ta dan yi shiru sai jimawa kadan ta kalle ni ta ce min to, wanda ba kya zaton ne ai na dauka ya gaya miki ne shi yasa ban ce Sa’adatu taje ta gaya miki ba.

Amarya ce yau a gidan tayi maganar cikin murmushi nima na dan yi mata murmushin kadan ta shigo har cikin falon Gambo ta zauna muka gaisa, ta mike zata fita tana fadin kai amma dinkin nan naki yayi min kyau a ina aka yi miki? Na ce a’a ban sani ba, haka naga an kawo su a dinke ta sake cewa kai ai auren wayayyen miji mai son matar shi dadi ne dashi.

Shiru nayi ban tanka mata ba, ta fita na kalli Gambo cikin mamaki na ce har cikin dakin nan yanzu Zubaida take shigowa? Bata tanka ba ta ce min sha nonon mana, na ce uh’uh Gambo ina dashi a gida ta ce haka ne ai daga wurin naku aka kawo to me za ki ci? Na ce ban son komai Gambo sai dai ina so kiyi min kullin kunu tayi maza ta kalle ni tana tambayata yau kuma kullin kunu kike so? Naga kuma aike ba mai san kunu ba ne shiru nayi ban ce mata komai ba, itama sai kallona take yi na kuma san kyau taga nayi.

A’a auren naku fa ya dan kwana biyu kai tafiyar lokaci bai da wuya, na ce me kika gani Gambo? Ta ce, to ko wannan canzawa da kika yi ai ya isa a san ba shekaranjiya bane ban ce mata komai ba, ta dan sake yin murmushi ta ce ai dama tunda naga maigidan yana maida jikinshi na ce to an zauna lafiya kenan.

Shi dai aure ai kin san ba komai ba ne illa yi nayi bari na bari in zaka zauna da mutane kuma to ka zauna da su akan gaskiya nace to Gambo.

Ado yayi sallama ya shigo Gambo tana yi mishi sannu da zuwa ga dukkan alamu dai ya zama da sosai wurinta cikin zuciyata nace kai Ado ma dai da kokari yake ko da dai shi da bakinshi ya sha kiran kanshi da ‘namiji’.

Gambo su Sa’a ba su taso ba ne? Ta ce mishi eh in ma sun tashin ba su riga sun iso ba, ya zauna suna hira da jin hirar tasu kasan sun riga sun zama abokan hirar juna sosai, a hirar da suke yi na fahimci Ado ne ya sanya Sa’adatu da Baba karami a Makarantar Islamiyar unguwarmu ban dai tsoma musu baki cikin maganganun su ba.

Suka yi hirar su suka gama da ya ce mata zamu tafi sai ta ce mishi da jira nake yi Sa’adatu ta shigo don ta raka ku da kai da kafan nan, ko sai da safe a kawo muku? Ya ajiye dan makullen da ya kulle kofar gidan ya ce mata gashi in ta dawo ta kai mana ta rufe gidan ta kawo makullin nan sai mun dawo zan zo in karba ta ce mishi to muka fito.

Ba mu dawo ba sai wajen goma da rabi na dare saboda unguwanni masu yawa muka je har gidan Mai Babban Allo da gidan Alhaji Mai Kudi da gidan Musa abokin Ado wanda shima bai dade da zama ango ba, a hanya muna dawowa tun daga nesa Ado ya hangi Mama a tsaye a kofar gida cikin damuwa yake ta nana ta fadin me kuma ya fito da Mama waje tare da wadannan sakarkarun yaran?

Dama dai ayi sa a ba wata fitina suka dauko mana ba na ce to amin muna isowa yayi maza ya fito daga cikin taxi in ban da ma na tsaya na dauko mana ledar sayayyar da yayi mana da mai taxi ya tafi dashi.

Lafiya kike tsaye a waje a cikin sanyin nan Mama? Ina fa lafiya tana fadi tana kara tafa hannu tare da salati, me ya faru Mama? Ya kara tambaya don ya san abinda ya farun, “uhum daukar wa kaina abinda yafi karfina nayi na dauko fitina na saka cikin al’amarina yana nema kuma ya buwaye ni ya buwayi duk wani nawa.

Cikin natsuwa Ado ya tambaye ta fitinar sai kawai ta nuna mishi ni, yayi kasake yana sauraronta tana gaya mishi nema take sai ta raba ka da zumuncinka, ba kuma zai yiwu ba, ba zan barta tayi nasara ba, don babu inda na ji an ce don mutum bai yi aure ba, ba zai shiga aljanna ba.

Bukata dai kawai mutum ya kama kanshi ne ba a ki aure kuma a rinka leke-leke ba, to amma zumunci fa? Sau nawa ka ji ana cewa wanda bai yi shi ba ko yaje zai wuce saboda ayyukan shi sun kai sai makaran zumuncin ya kamo shi ya hana shi wucewa? Tana rufe baki don hutawa Ado yayi maza ya tambaye ta me aka yi ne Mama?

Ta ce, ai dama nasan ba za ta yi akan sanin ka ba, to dubi kofar gidan yadda ta kama shi ta kulle ta bar su suna tsaye a waje don su ce kai ne ku samu matsala a tsakaninku.

Ado yayi mata rantsuwa ya ce mata ba ita ce ta rufe gidan ba, ni ne Mama, ya kuma gaya mata yadda aka yi duk har ya bar key din a cikin gida nan da nan kuma ya tura ni na shiga na karbo na samu tana cewa haba Ado, yau kuke tare da su in ba ita ta saka ba yay a za a yi haka? Ni kam cikin zuciyata na ce Mama kenan, wanda take so ya more baya laifi a wurinta, komai yayi sai ta ce ba shi ba ne in ma shi da kanshi ya ce shi ne taga zai dorawa kanshi laifin da bata so ya dauka sai ta ce to sa shi aka yi. Ado yayi ta bata hakuri har dai ya samu ya lallabata ta shiga gida.

Muna shiga dakinmu ya kalle ni cikin natsuwa ya tambaye ni “Humaira za ki iya zaman kauye kuwa? Da sauri na bugi kirjina na ce kauye? Ya amsa eh, na ce hu’un su kauye manya, to ni me ma zai kai ni wani kauye? To ko Giyade abinda yasa take yi min dadi ai saboda Hajiya tana can ne.

Bai sake yin maganar ba, iyaka dai rannan nasan Ado bai wani yi bacci sosai ba duk da ya saba yin bacci mai nauyi dake baiyanar da alamar gajiyarshi a duk lokacin da al’amura suka faru a tsakaninmu, amma a yau har cikin dare da na farka idon shi biyu na ganshi. “Lafiya ba ka yi bacci ba?” Ya ce, min lafiya, tunaninki ne ya hana ni yin bacci, ya kamata in samar mana wani wuri da zamu zauna cikin ‘yanci da kwanciyar hankali Humaira, bai kamata ace kowane lokaci kina cikin fitina da fargaba ba, musamman a wannan lokacin da kike da juna biyu.” Juyawa nayi naci gaba da baccina na ki kula zancen nashi saboda ba na son kirana mai juna biyu da yake yi.

Tun washegarin ranar dai na lura Ado yana yin wasu abubuwa da suka fi kama da lissafe-lissafe da kuma kintse-kintse sai dai da yake gabadaya al’amarin ya tafi ne kan takardu sai ban maida hankalina wajen neman sanin abin da yake ciki ba tunda dai bai ce min ba sai nima ban tambaya ba.

Kwana biyu da tafiyar Hajiyar Giyade ina zaune a falonmu ni da Ado, in har da wata rana da na soma tunanin lalle juna biyu yana nufin wani abu mai girma da muhimmanci da wahalarwa kamar yanda kullum Ado ke gaya min, to ranar ne don kuwa wuni nayi a galabaice saboda amai, ko abincin rana ban iya girkawa ba balle na dare. Ado ya dawo daga kasuwa da yamma ya same ni a kwance nayi mishi bayanin abinda ake ciki ya ce to abin da nake fadin zai tabbata kenan?

Ya sake kallona ya ce min to sannu kin ji Humaira? Na ce mishi to ya sake kallona ya ce min amma in na roke ki ai zaki iya yi min wani alheri guda daya ko? Na ce mishi eh, ya ce to wanka nake so kiyi ki sanya min wannan rigar a jikinki in ganta, dazu naje na karbo ta daga wurin dinki in kin iya yi min haka shi kenan don ta rashin girki babu komai, sai in fita in je in nemo mana abinda zamu ci na ce mishi to.

Muna zaune da Ado bayan nasha kwalliya cikin sabuwar rigar da ya karbo min daga wurin tela ta dinkin kanfala ‘yar asali, sai kallona yake yi yana murmushi ke kin ganki kuwa? Ban ce mishi komai ba iyaka dai kawai nima nasan nayi kyau, to me dame kike so in je in kawo miki? Na dan rage fara’a kadan na ce mishi ni dama ka bar ni haka kawai tunda lalurar ciki take ai ba a biye mata, zai ci gaba da yi min magana sai ga Suwaiba ta shigo da gudu, murna take yi farin ciki mai yawa ne ya bayyana a fuskarta wai in ji Baba wai ku zo yanzu-yanzun nan kai da ita.

Tana fadin hakan ta juya da gudu ta tafi tamkar dai wata yarinya ‘yar karama, Ado ya waiwayo ya kalle ni, nima kallon nashi nayi ko lafiya? Na ce ba zan iya sani ba sai mun je mun ji. Nasa hannu na dauki gyalena, ya kalle ni cikin sanyin jiki ya ce ko dai za ki bari ne in je in ji tukuna? Na ce to ai cewa tayi muje tare kar ka je kai kadai din kuma ya zama maka laifi, ya ce haka ne to muje.

Muna shigowa gida Babana muka fara gani a tsakar gida sai Mama da kuma Gambota da ke can wajen bakin kofarta ga dukkan alama kuma kiranta aka yi ta fito. Muna shiga gidan muka tafi kasa don gaida Baba, amma maimakon ya amsa gaisuwar da Ado ke yi mishi sai ya kalle ni ya ce min, ke ga dakin uwarki can tafi ki shiga, kaima ga taka uwar nan jeka wurinta shi kenan kowa ya rike nashi, magana kuma ta kare dama ita ta ce a baka ita na baka yanzu kuma ta ce ta gano munafurci da raba zumunci in raba na raba magana ta kare kar in sake jin wani ya ce wani abu zan saba mishi.

Cikin kaduwa mai yawa Ado ya ce ka raba min aure Baba me nayi maka? Baba bai tanka mishi ba ya wuce ya shiga wurin Zubaida, ga alama a wurinta yake. Gambo ta biyo bayana zuwa cikin daki don ni kam ma ban wani tsaya jin komai ba, tuni na haye kan gadonta na kwanta sai Ado da Mama ne a tsakar gida, “kin sa Baba ya kwace min mata Mama? Ta ce ka kwantar da hankalinka ai dama ni nasa shi ya baka ita yanzu kuma ba ka san wacce zan sa a baka ba nan da kwana tara ma za’ayi komai tunda na riga na gama komai ai ba zan barka ka zauna haka ba, tunda nasan ka riga ka dandani dadin mace.

Ba ke kika ba ni Humaira ba Mama kaddara ce ta bani ita ba kuma zan rabu da ita ba, ba kuma na son kowace iri za ki sake bani in gidan da kike cewa zan bari ne akan zama da ita zan bar shi zan fita daga harkokin da kike cewa zan fitan miki, zan fita daga dukiyar tashi abinda ba a tsammani na zan mayar dashi zan rike Humaira ne kawai Mama don ita kadai din nake bukata a yanzu.

Kai Ado, tayi mishi tsawa mai karfi zaka zage ni ne? Ya yi maza ya ce ba zan zage ki ba don ke uwata ce amma kuma ba zan yarda ki raba ni da matata ba, Mama ban ga abinda tayi miki ba ina kuma sonta.

Ni kuwa ina shiga bandakin Gambo na kama aman tun daga falonta har bayan gida da sauri Gambo ta biyo bayana tana kokarin taimakona. Ado kuwa ya juya ya fita ya bar gidan ban san inda ya tafi ba sai dai bai dauki lokaci mai tsawo ba sai gashi ya dawo, kayayyakin ciye-ciye yaje ya sayo min har cikin dakin da nake kwance ya shigo bai saurari maganar da Mama ke yi mishi na kar ya shiga dakin nan ba hakuri yake ta bani wai in kwantar da hankalina kar in ce zan daga hankalina.

Nayi murmushi na ce babu komai ni kam ai dama a nan nake su suka dauke ni suka baka ni in sun ce in sake dawowa ba zan zarge su ba don haka kaima kayi hakuri, ya ce min to me kike so in kawo miki yanzu? Na ce babu komai kar ka damu ai ga Gambo in ina son wani abu zata yi min, ya ce to sai da safe.

Tunda Ado yasa kai ya bar gida cikin dare a cewar sai da safe bai sake dawowa ba, babu ma wanda ya ce ya ganshi a unguwar don ina jin Mama tana tambayar ‘ya’yanta sun ga Kawunsu kuwa? Su ce mata a’a Gambo ma tayi ta neman shi a waya amma babu layinshi, ya rufe. Ina jin ta tana fadin ni Binta wannan yaro ko ina ya shiga haka oho. Ban dai ce mata komai ba amma ni kaina a cikin damuwar nake don kuwa nasan yana cikin bacin rai mai yawa.

Cikin zuciyata dai addu’a sosai nake yi mishi don kuwa ina matukar tausayin halin da ya samu kanshi a ciki wanda kuma a dalilin aurena ne ko da dai na sani a farkon al’amarin ni suka yi nufin cutarwa, amma hakan ba zai rage min komai a tausayinshi da nake ji ba tunda nima a yanzu ba zan iya cewa ba na son shi ko kuma ban damu dashi ba.

Rannan da safe muna karyawa ni da Gambo na kalle ta cikin natsuwa na ce mata “Yau kam in Ado bai zo gida ba Gambo zan fita in neme shi a irin gidajen abokanshi da muka jejje, ta ce to ya yi kyau kam hakan duk dai ke ma ba lafiya ke gare ki ba, amma abin ai yayi tsanani daga sai da safe abu ya tafi har kwana uku? Muna cikin wannan maganar sai muka jiwo Babana a tsakar gida yana cewa Mama, yaron nan fa Ado ko kasuwa ba ya zuwa, ta ce rabu dashi ja’iri mara kunya da butulci wai shi nan yayi fushi ne a dole ga mai zafin rai ya bar gida, aje a nemo shi in yaso ya samu hanyar cewa sai an mayar mishi da ita sannan zai dawo to yaje duk inda za shi an hana shi itan yafi ruwa tafiya.

<< Mijin Ta Ce 22Mijin Ta Ce 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.