Skip to content
Part 30 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ban iya cewa Ado komai ba saboda kukan da soma yi ban taba hira na gane matsananciyar ramar da yayi ba sai a yau, na dai san dai Goggo Ayalle tana yawan fadin yaron nan Adamu ya zube. Amma ban lura na gane irin zubewar ba, sai a yanzu.

Tashi yayi yaje ya dauko cokalin ya dawo ya zauna ya soma cin tuwon, ni in don ni ki ke kuka to ki share hawayenki, in kina so in san kina tausayina to in ina tare da ke ki bar ni in samu kwanciyar hankalin da nake bukata.

Yana gamawa ya tashi ya sake fita, nima na share hawayena na tashi naje sasan Baba Halliru wurin Goggo Jaku na gaisheta, na ce mata Goggo yau zan karbi furar da kullum ki ke cewa bana zuwa ina karba, tayi murmushi ta ce, kai ai kuwa dai kin kyauta yar nan, gata kuwa an gama mulmulata.

Ta miko min tayi shar gwanin sha’awa, sai Kamshi take yi, gata nan debi maza yanda zai ishe ki nasa hannu na debi guda hudu ta ce ke tafi can da kwauro, za ki yi wa kanki, ta sake watso min guda shida a cikin kwaryar da ke hannuna nayi mata godiya na tafi.

Nura na kira ko Zulai yayan Yaya Ruwaila ne gaba daya suka taho na ce to ke Zulai je ki ki huta kai Nura yi sauri kaje bakin kasuwa ka sayo min nono, ya ce to.

Ina zaune ina dama furar ina tunanin kai! Dabai akwai fura, amma babu nono. Nono ruwa-ruwa? Na jawo robar yougort din da ke dakin na bude shi na juye a cikin damammiyar furar na gaurayata na rufe.

Ana yin Azahar Ado ya sake shigowa nayi mishi sannu da zuwa, ya amsa. Na jawo kwanon  fura na mika mishi ya kalle ni da walwala a fuskarshi ya ce to ke fa? Na ce ai na sha, ya ce eh, amma ba zai taya ni musha tare ba ai.

Na zauna muna shan furar tare har muka gama, muka dan yi hira kadan sai na kalle shi na ce mishi, “To ka dan kwanta mana ka huta.” Ya ce in kwanta Humaira? Nayi maza na ce mishi eh, ya ce to za ki yi min tausa ne? Na gyda mishi kaina nuna alamar eh.

Yayi maza ya mike akan katifar nima na bi bayan shi na soma yi mishi tausa ina yi mishi danna ina bin gabobin jikinshi ina matsawa cikin hikima, shi kuma yayi lamo ya lumshe idanunshi nuna alamar jin dadi.

A hankali kuma yana furta wasu kalmomi da ni kadai ke iya jin su, bacci mai nauyi Ado yayi bai farka ba har sai da na tashe shi, wajen karfe hudu da rabi na yamma abin da bai taba yi ba tunda muka zo, ya kwanta da rana yayi bacci.

Da daddare rannan muna hira ni dashi ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min ni kuwa Aisha in ban da kar in yi ta takura miki har in yi ta kai ki bango ban sani ba da na roke ki kiyi min wata alfarma, na ce ta menene? Ya ce dakin nan da muke zaune a ciki ne bana son shi, duk da nawa ne.

Na ce, ni na gane saboda gininsu ma ya banbanta da na sauran dakunan gidan shi da na Baba da na Goggo Ayalle.

Bai bani amsa ba sai ya ce min nan din a takure nake, ba zan iya sakewa nayi kusa da Baba da yawa ba zan iya zama dashi duk wani motsina yana ji ba, shi ne nace da za ki yarda da mun fita daga ciki mun koma wasu tsofaffin dakuna da ke ta can baya, babu kowa a wurin sa muyi zamanmu zuwa lokacin da zan samu halin samar miki wurin da zai dace da ke.”

A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to mu koma mana. Ya zuba min ido yana kallona, babu damuwa? Na ce to ai ba daki na biyo ba, ba kuma shi nazo nema ba, ni a wurina kai ne muhimmin abu, kai na biyo kai ne mijina a yanzu kuma zan iya zama da kai a duk in da ya kama.

Kwana uku kawai da yin wannan maganar tamu Ado ya gama gyaran dakunan da da shara ake zubarwa a wurin ya kwasheta fes ya gyara wurin ya tsabtace shi ya gyara dakunan gyara na musamman ya sai buhun siminti ya toshe duk in da yake bukatar a toshe shi.

Ina jin Baba Tanimu yana yabon kyan aikin da Adon yayi, amma ban san kyan wurin ya kai haka ba sai da Adon ya kira ni naje na gani, dakuna uku ne a wurin gaba daya yayi musu gyara na sosai, kowane daki ya maida shi abin da yake son ganin ya zama guda daya, ya gyara shi a matsayin dakin kwana daya dakin dahuwa, wato kicin daya kuma bayan gida na sosai da za’ayi amfani da shi akan komai sannan ya killace wurin da wata yar katanga.

Yayi mata kofar shiga dan karamin tsakar gidan kafin ka shiga ‘yan kananan dakunan ni dai wurin ya ban sha’awa, yayi murmushi ya ce to yaushe za ki dawo ciki? Na ce ko yanzu, ya yi murmushi ya ce, to shi kenan.

Baba ne yasa Ado daukan katuwar katifar da ke dakin da muke din, don haka ya sayo mishi ‘yar karama.

Randa na tare a sabon dakin namu tsaf na same shi ya malale shi da leda yasa katifar yayi mata shimfida ga akwatinshi a gefe sai Jakar da yazo da ita da ‘yan tarkace kadan, dakin dahuwa kuwa yasa risho har da tukwane guda biyu da yan tarkacen kayan aiki kadan, food flask da dinner set da kuma wasu kwanuka.

Ga bokitaye da randa da dai wasu tarkace, ga kuma kayan abinci dan daidai gwargwado ko a ina yaké samun kudin da yake kashewa? oho! Tambayar da na yiwa kaina kenan, a zuciyata dai nasan babu abin da yafi min bandakin nan dadi, don na samu kebabben wuri har da bayan gidan hadakan da ban saba da shi ba yake sani jin kwiyan yin wanka.

Nayi maza na kammala abubuwan da zan yi nayi wanka saboda jin dadin ganin bandakin na zauna na shafa mai nayi gyara irin yanda na saba yi a gida, gabadaya dakin ya gauraye da kamshin kayan shafan da nayi amfani da su.

Ado bai shigo ba sai da yayi sallár Isha’i shima yana shigowa bandakin naji ya shiga yana wankan, Cikin zuciyata na ce ashe shima da kwiyan wankan yake ji, don tunda muka zo ban ganshi yana wankan dare ba, yana shigowa dakin ya Sanya hannayenshi duka biyu ya sure ni.

“Kina lissafin kwanakin aiko? Kina lissafin kwanakin da nayi ina hakuri ina fama da shan jar kanwa da lemon tsami? Tuni na langabe mishi na saka shi ya mance duk wata damuwa in har yana da ita da kuma wahalar da yake wuni cikinta, wanda nasan ya manta rabon da yayi irinta, duk wani abin da nasan zan yi wa Ado rannan da zai sa shi jin dadi ko farin ciki nayi mishi.

Na kuma yi matukar yin hakuri da shi, ban nuna mishi gajiyawata ko korafi kan al’amuranshi ba, ba don komai ba sai don zuciyata ta riga ta yarda ta amince da cewar Ado mijina da na kuduri aniyar zama dashi a kowane hali yake ciki in taimake shi, in ba shi hadin kan da da yake nema a tare da ni, in jiyar da shi dadi gwargwadon abin da zan iya yi.

Saboda na yarda na amince sona yake yi da zuciyarshi guda daya dawo da ni kauyensu da yayi kuma ba laifi ba ne gurinshi na asali yazo da ni mafi yawancin wahalar da yake yi kuma na yarda mafi yawancinta tawa ce.

Sallar Asuba ya fita yayi ya dawo ya same ni

nima ina sallar, nayi zaton komawa zai yi ya dan kwanta kafin ya fita tunda ni dai nasan kashi uku bisa hudun daren idonshi biyu ne, amma sai naji ya ce min ni na tafi bai ma jira amsawata ba.

Na idar da sallata na koma na kwanta, sai da na dan yi bacci kafin na tashi na duba abin da muke da shi na abinci na gama gyaran wuri da tsabtace shi, nayi wanka nazo na shirya abin karyawa, na karya na gyara jikina na jawo kofar wurina na rufe don kar kaji su shiga suyi mana ta’adi.

Na fita naje na gaida manyan gidan duka kafin na wuce can tsakar gida wurin haduwar matan gidan. inda ake da babban fili sosai da ke dauke da wurin girki a can nesa ga runbuna a can wani gefen ga in da ake aikace-aikacen wanki ko wanke-wanke, wani gefen can kuma daka ake yi da nika ga kuma wata katuwar rumfa da ke tsakanin wasu manyan bishiyoyi in da ake zama ana yin hira.

Zaman tsakar gidan nan yafi komai dadi, don wuni ake yi ana raha ana barkwanci ana kwashewa da dariya, shagala nayi a cikinsu ana tayi ina kallo har ina taimakon masu daka da yin tankade, ban ankara ba sai naji ana kiran sallar azahar.

Gabadaya aka watse kowa ya nufi wurinshi don yin sallah, kofata tana rufe kamar yadda na barta a zuciyata na ce yau ma Ado bai dawo ba kenan, na idar da sallah naje na karbo fura nazo na dama na ajiye mishi na koma wurin matan gida, na ce ba zan iya zaman kadaici ba, in ya dawo ya kira ni ko kuma ya sha furarshi ya tafi.

Ado bai shigo ba sai bayan ‘sallar magariba, ban taba ganin tashin hankali da bacin ranshi irin na rannan ba, kina nufin ba za ki iya zaman wurinki ba? To me yasa ki ka yarda ki ka dawo? Kina nufin ai ba zan dawo gida in same ki a wannan dan tsukakken dakin namu kina zaman jiran dawowana ba?

Sai in ina son ganinki in biki cikin mata ina kwala miki kira? Ke ba ki san hakkina ba? Ba ki san abin da za ki taimake ni da shi ba? Fura ce zan rayu a kanta Humaira? Ba ki ga kamar dandanon abincinki a bakina zai yi matukar yin amfani a gare ni ba?

To bari in gaya miki dama kin bi a hankali wannan taron nasu da ki ke gani-randa suka tashi tambayar junansu gulma suka sa dake a ciki abin zai baki mamaki, ke baki taba zaman gidan yawa ba duk fitinar da ki ka sani a gidanku wasan yara ne.

Gabana ya yanke ya fadi, jin da nayi Ado ya kira fitinar gidanmu wasan yara na ce to ai gara ka maida ni gidan namu, abin da kawai na fada kenan. Ado yasa hannu ya make ni, kina hauka ne? Na ce kina hauka ne da kullum za ki rinka kallona kina cewa in maida ke gidan naku ke kina da gidan zuwa ne?

Ko ba ki ji abin da maigidan ya fada ba sanda ki ka zabi biyo ni? Ya ce kar ki sake taka gidanshi saboda ya yafe min ke bai da sauran bukatarki.”

Dukan da Ado ya yi min bai bata min rai ya daga min hankali irin wannan maganar da ya soka min ba saboda gaskiyar abin da Babana ya gaya min ya gaya min. Nayi kukan bakin ciki har na gaji a kasa da kwanaki talatin na barin iyayena da nayi na biyo shi har ya fara goranta min abin da ya farun.

Tabbas Ado namiji ne dama kuma nasha jin Mama tana cewa shi namijin ba dan goyo ba ne, a gabanshi kuma ma ta fada ta ce namijin ai ga ki nan gashi nan.

Rannan dai kam kwanan da muka yin ba mai dadi bane, don haka yana fita sallar Asuba na duba inda ‘yan kudina da nake tarawa suke, don yau kam nayi niyya ko ba za su kai ni gida ba in dai za su raba ni da garin Dabai, to zan tafi in yaso nasan yanda nayi na karasa gida. Ban ga komai a wiirin ba sai nera hamsin saura ya kwashe.

Kwana biyu muna cikin wani hali ni dashi, rannan ya dawo da yamma ya same ni, kin gani Humairah mu biyu ne ni da ke a nan, ya kamata in wani abu ya faru a tsakaninmu na rashin jin dadi in na ba ki hakuri ki hakura, ba zai yiwu ace kullum sai na kai wa Gambo maganar za ki hakura ba, in dai ba so ki ke mu rinka tayar mata da hankali ba.

Kuka na soma yi sosai da sosai, kiyi hakur na sani ban kyauta ba da nayi miki gori, to amma ke kin ga yayi miki daidai kan maganar da ba ta taka kara ta karya ba ki rinka cewa in maida ke gidanku? Ai ya kamata ace ni da ke mun fahimci wani abu a tsakaninmnu, shi ne zaman namu ba na rabuwa ba ne ba kuma na wulakanta juna ba.

Tsawon lokaci yana yi min maganarsu na rarrashi da ban baki har dai ya samu ya shawo kaina na hakura, muka shirya.

Tun daga wannan lokacin na rage shiga can cikin gida don yin hira da matan gidan sai dai kawai in gari ya waye in shiga in gaishe su dukan su in dawo wurina in gama aikina in gyara komai in yi wanka in gyara jikina, duk da ‘yan kayan nawa har yanzu guda uku ne sai lodin rigunan baccin da babu damar in sanya su da rana sai da daddare in yi mana abinci irin wanda naga ina, so don komai na abinci Ado kawowa yake yi, komai tsadarshi kuwa.

Agada, Doya, Dankali, Wake, Kuskus, Indomie, kwai, manja, Mangyada, Manshanu, Shinkafar tuwo saboda masa da kuma ta wara duk ina da su ina kuma da kayan tea zan kuma tashi da safe in je in karbo kunu da kosai, don ko ban je ba za a biyo ni da shi, don haka nake girmama su in je da kaina.

Shi kuwa Ado ka’ida ne kome nayi na karyawa to sai na karbo mishi dumame wurin Goggo Ayalle ya fara dashi kafin ya ci wani abin.

Kullum zai baro gonarshi sha daya ya dawo gida, yana dawowa zai tube kayan jikinshi ya shiga bandaki yayi wanka, ni kuma sai in tsoma su a ruwa in wanke su in shanya in wanke mishi ranbut din nashi na hannu da na kafan in jefa su kan rufin dakin namu su sha rana, sai da yamma in kwashe su.

Yana fitowa daga wankan zan sanya mishi tabarma a inuwan dakina ya hau kai ya zauna in gabatar mishi da abin da na tanadar mishi.

Yana ci muna hira yana bani labarin gonar tashi, mafi yawancin lokaci in muka zauna a wurin zai yi wuya mu tashi bai nanata gaya min maganar da ya saba gaya min ba, ina so in samu damar da zan nuna miki halarcina Humaira, ina so in samu damar da zan nuna miki cewar ni din da namiji ne.

In ya gama abin da zai yi ya kama hanya ya fita sai kuma in sake zama in shirya mana abinda zai dawo da azahar ya ci, hakan kuma bai hana ni tanadar mishi furar da zai sha bayan yaci abincin.”

<< Mijin Ta Ce 29Mijin Ta Ce 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.