Shi kuwa Ado sai ya ce nin, in ya kama sana’a ko? Ko kuwa haka kabwai za su zubo mi shi? Ban kula shi ba, iyaka dai ban daina ba.
Rannan mun tafi Makaranta da safe shi kuma ya wuce gonarshi kan hanyar tafiyar ta mu dai ya bani tabbbacin a satin nan zai fara dibar masararshi ya sayar ko da bata gama karasawa ba, tunda ba zai sake zuwa wurin wani neman wani rancen ba.
Na ce mishi, to in dai ba ya zama dole ba kar ya yi hakan, ya kara hakuri kawai.
Na shiga aji ya wuce ya tati, ina aji ina tunanin Ado, irin wahalar da ya yi wa gonarshi ya soma diban masararshi a yanzu ba karamin asara ba ne tunda ba duka ne tayi ba wacce tayin ma bata yi wani kwari ba.
Ana tashinmu na fito ban ganshi a inda yake jirana ba, na dan tsaya kadan ko zai karaso ban ganshi ba naga za’a watse a bar ni ni kadai sai na biyo hanya na dawo.
Ina bullowa lungun gidan mu naga wata lafiyayyar mota a tsaye a kusa da Masallaci mai lambar Abuja, ban sake kallonta ba, na wuce na nufi cikin zauren gidanmu muka yi kaci6is da shi. Na daga ido na kalle shi har ya dawo yayi wanka yasa T-shirt da wandon shi masu kyau wadanda ma ba kasafai yake sanya su ba, yana kuma kamshin turarenshi.
Ban san dalili ba sai naji haushinshi ya kama ni nan take na soma yi mishi kuka, shi ne baka biyo min ba ka dawo gida?
Ina kukan ina tambayarshi, to kiyi hakuri mana Humaira, ki tsaya mana kiji abinda yasa nayi hakan in ban da uzuri ba ki gamsu ba sai kiyi hakan ki.
Daga cikin dakin zauren nan na jiwo wata murya tana tambayar Ado to kai tsoron kukan nata kake yi ne?
Da gudu na fada dakin jikin mai babban allo na kwanta shi da Baba Yahaya ne a ciki.
Mai babban allo ya ture ni yana fadin “Ke matsa can ja’ira, shagwababbiyar wofi, kar ya baro ki a makaranta ya dawo shi kadai akan me?
Duk tsiyarki da wayonki mata hudiu zai yi ba da ke kadai zai zauna ba, nayi murmusha na ce oho, ni dai nayi gaba, Baba Yahya ya taya ni murmushin tare da fadin gaskiyarki Aishatu.
Na gyara zama na gaida Baba Yahya cikin ladabi da girmamawa, yana kallona sai murmushi yake yi alamar dadi ya kama shi.
“Karatu kike yi?” Na ce mishi “Eh Baba.” Ya sake wani murmushin ya kalli Ado Ubangiji ya yi muku albarka ya rufa muku asiri ko ina ya kara don ya riga ya rufa sai neman kari. Ado ya ce amin Baba.
Na kalli mai babban allo ina murrmushi “Ina su Hajiyoyinka?” Ya taya ni murmushin tare da fadin kalau din su, ba su ma san zamu zo ba.”
Na sake kallon Baba Yahya na ce “Baba ba ku gaya wa kowa ba ne? Baba Yahya ya ce, ai babu wanda ya sani jiya da daddare ma da Yayanku yazo nan gidan shi da Atika nayi kamar in gaya musu sai kawai na fasa.
Nayi murmushi na ce dukansu lafiyarsu kalua Baba? Ya ce kalau dinsu Aliya dai zata tai aikin Hajji ita kuma Atika cikin dake gare ta yasa ba a yi maganar tafiyar tata ba. Dadi ya kama ni jin alherin da ‘yan uwana suke ciki.
Na sake kallon Baba Yahya cikin natsuwa na ce mishi oh Baba, ashe zaku zo dubani da sauri ya ce zamu zo mana Humairah, zamu zo mana mu gan ki.
Na kuma ji dadin zuwan da nayin ba kadan ba nazo na same ki kina karatu, mijinki ya maida ke makaranta don kiyi ilimi shi kuma naje gonarshi na gani wannan noma da wannan yaro yayi ya wuce abin mamaki sai abin tsoro.
Zuciya dai ita ce mutum, shi yasa Manzon Rahma (S.A.W) ya ce, in ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, in kuma ta Baci to dukkan jikin ne ya baci.
Na dan yi murmushi saboda jin dadin gamsuwwar da ya ce sunyi na ganinmu cikin natsuwa na ce mishi Baba har kun je gonar ne?.
Mai babban allo ya ce ai mu ta can muka fara don da muka yi tambaya gonar tashi aka kaimu, ai mijinki ya zama sarkin noma.
Na sake wani murmushin daidai Ado ya sake shigowa da wani kwanon a hannunshi.
Baba Yahya ya kalle shi cikin natsuwa daidai yana ajiye kwanon ya ce mishi kai mu fa mun riga mun koshi, wannan gaudan da ka kawo mana ba cin wasa muka yi mishi ba.
Ai rabon ma da in ci gauda mai dadin na yau har na manta matanmu na can ba su iya irin wannan girke-girken ba.
Ina jin sun tsunduma hira da Ado akan maganar gonar tashi nayi maza na nemi izininsu na shiga gida naje na tube uniform dina na daura sabuwar atamfata.
Na gyara nayi tsaf, na yafa sabon gyalena na dauko abincin da na tanadan mana muci, in mun dawo. Na hada da abin shan da nayi na ajiye cikin randar kasa na dora a tire na hada dasu plate cokali da kofuna, na dawo nayi sallama a bakin kofar suka amsa.
Na shiga na tsuguna na ajiye tiren mai babban allo yana kallona yana cewa, amma ai kina jin Babanki yana cewa sarkin noma mun koshi ko?
Ban asa mishi ba, na kalli Baba Yahya cikin yanayin da zai tausaya min, na ce mishi Baba wannan abincina ne da nayi da hannuna, kuci ko ba yawa.
Nan da nan ya ce, zuba mana muci Aisha, nayi maza na jawo plate-plate zan fara zubawa, mai babban allo yana fadin “Ka ji wai tana jaddada da hannunta tayi kamar hannun nata ya wani iya ko kuma dabanne.
Ado yana murmushi yana fadin, kai dai bari ka ji kawai Mallam.
Ina zuba musu abincin, Baba Yahya yana kallona. Burabuskon gero ne da miyar taushen da taji busasshen kifi da tantakwashi, sai kamshi suke yi daga shi har miyar.
Na zuba musu a plate na zuba musu miyar sosai na mika musu, Baba Yahya ya kai lomar farko ya tsaya ya sosa kunnenshi da dan makullin motarshi kafin yaci gaba da kai loma bakin shi.
Jimawa can, sai naji yana tambayata Ke da ki ke sammakon zuwa makaranta Aishatu, da wanne lokaci ki ke wannan girkin?”
Kan in yi magana Ado ya soma yi mishi bayani har yana ce mishi ban cika gane ina wahala mai yawa ba Baba, saboda Humairah wata irin yarinya ce mai hakuri da juriya.
Duk abin da zata ji ta taimaki abokin zamanta shi take yi, babu yanda za’ayi in dawo gida bata gamsar de i ba, tana kuma tausayin wahalata.
Matsalarta daya ce, Baba kullum a kanta muke fada da ita, Baba Yahya yayi murmushi saboda ganin rin kallon da Adon yayi min yasan zolayata yake so yayi.
Ya ce, kishi ne da ita Baba kishin ma na rashin hankali, in ba haka ba…. Mai babban Allo ya karbe maganar, don haka Adon yayi shiru shi yana sauraron shi.
Yayin da Baba Yahya yake ta faman murmushi, ni kam tsuke fuska nayi na sunkuyar da kaina kasa, ai duk tsiyarta sai kayi hudun nan don kayi biyu ma’ai ba wani kokari kayi ba.
Kana girbe amfanin nan naka, ka samu wata santaleliyar fara ka hada, kaga sai ya zama kana da baka ga kuma fara ka kawo.
Baba Yahya yayi dariya ya ce rabu da su kin ji Humairah ke dai ki kara kokari akan wanda mijinki yake bada labari kin ji ko? Na ce, to Baba.
Na kwashe kwanuka na fita dasu na dawo don yin sallama da su, ina durkushe Baba Yahya sai faman sanya mana albarka yake yi, zan je in baiwa uwarki labarinku.
Na sake wani murmushin, kudi ya miko bandir din Naira hamsin-bamsin guda biyu sababbi, “Rike wannan ki rinka zuwa makaranta da su.”
Nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya, suka fita suka tafi ina leke ina ganinsu tsaye tare da su Baba Tanimu da sauran mutanen unguwa.
Na koma na shiga gida ina ta murnar kudin da Baba Yahya ya bani cikin zuciyata, ina fadin shi kenan ajiye su zan yi in girkin ya zo kaina Ado ya samu abin da zai yi cefane dashi.
Jimawa can sai ga Ado ya shigo murmushi yake tayi, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi sun tafi?
Ya sake wani murmushin ya ce sun tafi Humairah, ni a rayuwata ko me zan cewa Baba Yahya? Oho! Nayi murmushi na ce mutumin kirki ne amma Baba Yahya kadai mai babban allo fa?
Yayi murmushi ya ce, dukansu Humairah, amma Mallam ai kin san ganinki yazo yi, na ce ai haka kace? To bari sai na gaya mishi.
Yayi dariya ya ce, “Yi hakuri.” Na mika mishi kudin da Baba Yahya ya bani, ina murmushi “”Gashi nan ka samu kudin cefane in girkin ya zo kaina.
Wani irin lallausan murmushi ya sake kafin ya daga gefen katifa ya rinka fiddo min bandir din dari bibiyu sai da ya ajiye guda biyar, zubawa kudin ido sosai nayi ina kallonsu, a ina ka same su? Ya ce a ina na samne su kuma? Ban da wurin Baba Yahya. Sannan ko mai babban allo bai ga lokacin da ya bani ba.
Baba wani irin mutum ne mai iya martaba mutum ya sake kallona cikin murmushi mashin zan je in sayo mana don in hutar da ke tafiyar kafan da kike yi zuwa makaranta kullum da dawowa.
Asabar da Lahadi kuma in dan rinka daukanki muna fita kina ganin kauyuka da kasuwanni.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce, ni na yafe kaje ka biya bashin da ka karba in sun ragu ka rike don cefanen abincin gida.
In gonarka takai kayi girbi in ka gama biyan sadakin aurarrakin da zaka yi in wani abu ya ragu ka sayi mashin din.
Yayi dariya ya ce, wai wa ya ce miki zan yi aure ne? Na galla mishi harara na ce, uhun ba ina jin mai babban allo yana ce maka kar ka yarda in tsufar da kai ni kadai ba? Yayi dariya mai karfi ya ce, kai Humairah! Ke kam ban san iyakacin kishinki ba.
Don haka yau bari in yi miki wani alheri tukuicin zuwa mai babban allo gidana, in hutar da ke in kwantar miki da hankali, don ki sakata ki wala kiyi abin da ki ke so, aure ko?
Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa da walwala kafin ya ce a yanzu a wannan halin da muke ciki ba zan yi shi ba, ban ce miki kwata-kwata ne ba zan yi ba, a’a a wannan lokacin ne ba zan yi ba.
Don haka kar wata ta sake ce miki an ganni wani wuri bani ba ne, in kuma lokaci yayi na in yin to ni da kaina ne zan gaya miki.
Don ina fatan in yi ne a lokacin da ke da kanki za ki gamsu da cewar eh, ya dace in yi in ba, wannan halin na samu ba, ba zan yi miki kishiya ba Humairah to me zan yi da ita? Duk da cewar da nayi wa Ado kar ya sayi mashin sai daya saya don irin na matasa, yana kawo mashin din gida su Baba da su Goggo suka sa albarka ya shigo ya ce min ki shirya in rana tayi sanyi za ki raka ni Ruwan bago muje in kaiwa Mallam Haruna kudinshi.
Daga nan kuma tunda yau ranar Lahadi ne sai mu tsaya a kasuwar “Sundu’ muyi sayayyar abin da ba mu dashi na kayan abinci, na ce mishi to.
Da yamma na shirya nayi kwalliya da daya atamfar tawa itama Nicharm ce amma nayi kyau sosai, na yi wa mutanen gida sallama naje na dale bayan mashin din Ado, wanda tunda na gan shi nake ta faman murmushi.
“Ke ba ki san yanda tafiyar kafan nan da ki ke yi yake ci min rai ba ne.” Abin da yake gaya min kenan, lokacin da na sa hannu biyu na kankame shi kamar yadda ya yi min umarni.
Muka fara tafiya, sai da muka tsaya a Sundu muka yi sayaiya muka ajiye a wata runfa muka wuce zuwa Ruwan Bago.
Gidan Mallam Haruna, ni na shiga wurin iyalinshi na shiga wurin uwargidan Hannatu, don Ado ya ce min ita yafi sani, nan sauran matan suka same ni muka yi hira da su, sai da ya gama ya aika a kira ni.
A hanya muna dawowa Ado yana bani labari, kai biyan bashi da dadi Humaira, kai da ka biya ka ji dadi shima wanda ka baiwa ya ji dadi.
Balle shi Mallam Haruna ma bai dauka zan maida mishi da kudin ba. Nayi maza na ce don me? Ado ya ce mutanen yanzu fa ba wani damuwa da biyan bashi suka yi ba.
Na ce, hu’un, ai kuwa dai suna daukarwa kansu jidali.
“Kinga iyalin Haruna ko? Ga gidanshi ga ya’ yanshi gashi yana noman nan, yana kuma taba kasuwanci. Komai nashi gwanin sha’awa ko? Na ce ni ban sani ba, na dai san kawai bai fika komai ba.
In dai ba yawan matan nashi ba ne yake ba ka sha’awa, to, to shi kenan mu bar maganar, na ce eh gara mu bari.
Ana cikin haka rannan girki yazo kaina, kafin zuwan ranar kuwa babu abin da Ado bai tanada ba na kayan amfani, tunda ga bokitaye, robobi, kwanuka, kore, ludaya, cokala suna kammale.
Ina tashi da safe na kammala ayyukan wurina, nayi duk abin da zan yi na jira Ado ya dawo kamar yadda yayi min umarni, gabana sai faduwa yake yi, ina dai ta faman addu’a.
Kar fa ki ce za kije kiyi wahala mai yawa ga buhun shinkafa can na kawo, in kinga ba za su taimake ki ba sai ki juye ta kawai gaba daya, ki juye mata abin hadinta akai in ta nuna za’a ci.
Nayi murmushi na ce mishi to na fita. Ina fike da tsintsiyar zabori a hannuna don share wurin yin girkin, da kuzarina na fita sai dai ina dosar wurin na susuce.