Skip to content
Part 43 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Gambo ta kalle ni so yake ki koma gobe? Na bata rai saboda ran nawa ya baci, na ce ban sani ba tunda ya kashe, to kira shi mana kiji, ya baro ki kin zo lafiya cikin farin ciki da alhairori iri-iri ai ba za ayi sanadin bacin ranshi ba.

Na sake kiranshi, nayi zaton ba zai dauka ba, sai naga ya dauka. A hankali na ce mishi kayi hakuri in ranka ne ya baci, ko da bana kusa dashi nasan murmushi yayi.

Gambo tana nan kenan? Na ce mishi eh, ya ce nasan ita ce zata ce ki bani hakuri tunda ke ba dabi’arki ba ce, Ban yi magana ba shiru nayi ina sauraronshi.

Ki dawo gida kawai Humairah, kin san tunda muka yi aure bamu taba yin nesa da juna haka ba, abin yayi min tsanani da yawa, nafi sabawa da in tafi in barki a gida ina jin marmarinki sai in juya, amma ba ke ki tafi ki bar ni ba.

Da kyar Ado ya yarda ya janye maganar tafiyar daga kwana bakwai, ya maida ita kwana tara.

Shi kenan sai kawai na soma shiry-shiryen komawa gida, ciki har da karasa zuwa wuraren ‘yan uwan da, ban je ba. Gambo kuma a gida tana tashi zan koma dakina.

Duk da naje gidan Mai Babban Allo, tun washegarin zuwana gida na sake komawa wajen shi don ba zai yiwu in zo in tafi ban gaya mishi halin da na baro gidan mijina dà ‘yan uwanshi ba, don ya ba ni shawara ko kuma addu’a.

A gidan mai babban allo ina zaune gabanshi shi da uwargidanshi Hajiya ‘Yar Dubu, matarshi ta sakun lalle, matar da ya yi sa’a ta zame mishi uwargida ta gaskiya, wacce ta danne al’amarin kishi tsakaninta da kowa ta tsaida adalcin da yayi sanadin da gidan ya zama dunkulallen gidan da babu bambanci tsakanin ya’yan nan da na can.

Ta sauko da Umamatu daga bayanta ta karbi ruwa zam-zam wurin mai babban allo, ta kwankwada mata kafin ta mika mishi ita, ta sake neman wuri ta zauna cikin natsuwa ta ce min aure suke so yayi ba kuma zasu barku ku zauna lafiya ba, sai sun ga sun sa shi yayi.

Ba su kadai ba ne mafi yawancin ‘yan uwan miji ai zuwa suke in dai zasu ji ka shiru da dan uwansu sai suce fin Karfinshi aka yi ko da kuwa hakuri ka ke yi.

Nayi maza na ce mata, haka ne Hajiya, ta ce to ke ni ganau ce ba jiyau ba, kar ki yarda ki shiga layin da ba na gaskiya ba ne, don ka mallake miji ka hanashi tsaida adalci tsakanin iyalinshi, ka hana shi yiwa kowa adalci.

In dai ba ka mallaki ‘ya’yanka ka hana su lalacewa ba, ba ka kuma mallaki hikima da dabarar hana alhaki kama ka ba, ai ka yi shirme.

Na ce haka ne Hajiya, ta ce to ladabi da biyayya tsakaninki da mijinki, yi nayi bari na bari, in yana fada a bashi hakuri ba yana fada ana fada ba.

Su kuwa ‘yan uwan miji nan da ki ke kallon su fita harkarsu kawai za ki yi, da wuya kwarai ki ga wata mata da za ta ce miki bata da tabonsu, sai dai aniyarsu kawai ta bi su.

Mai babban allo ya yi murmushi alamar yasan wani abu ko in da addu’ar ta Hajiya ta dosa, bai ce komai ba sai da ya ji hirar tamu tazo karshe sai ya ce min ke Aishatu.

Nayi maza na ce mishi na’am Mallam, ya ce to gyara zama da kyau sai kiji abin da zan gaya miki, na sake cewa to tare da yin abin da ya ce min din.

Cikin natsuwa ya soma yi min magana, kin ga wadannan mutane da ki ke tare da su? Na ce mishi eh, ya ce to je ki maza ki gyara abinda ke tsakaninku.

Ba mijinki ne zai gyara miki ba, ba kuma shi ne zai rinka tare miki fada tsakaninki da su ba, in dai ba shima nema ki ke ki maida shi ya zama abin da ya zama ba.

Ai ke mace ce suma mata ne, halinku daya, dabi’arku daya, rashin kirkinku daya. Dangin miji ba mutanen kirki ba ne, amma matar da bata yiwa kanta adalci ba. Ama in zata yi wa kanta adalci to zata gane su din “yan uwane na gaskiya, abokan zama na amana.

Tasan yadda za ta yi ta zäuna da su lafiya bisa girmamawa da mutuntawa da adalci, ba don komai ba sai don tasan ita din zata wani  wata rana dangin mijin wata ne ko kuma üwar mijin wata, to me zai hana ka yi wa wasu adalci don kai ma naka in sun zo suyi maka?

Yanzu dan karamin misali zan yi miki, Hadiza ni na haife ta? Na daga ido na kalle shi don jin ya kira Hajiya Kubra Hadiza, ya ce ba sunanta kenan ba?

Na yi maza na ce sunanta ne, ya sake tambayata ni ne na haife ta? Na ce a’a, ya gyada kai ya ce ai kinsan gidan ubanta, kin san iyayenta, tunda kuna zuwa.

Na ce mishi eh, ya zuba min ido yana kallona, kafin ya ce min to da wata yar da ta fi ta a nan gidan? Nayi maza na ce mishi a’a, ya ce to da ta dauke mu a yanda mafi yawancinku ku ke daukan dangin miji zamu zama haka mu da ita?  Na ce a’a, ya ce to dubi tsakaninta da uwarki ita tafi kowa kusa da ita, ba haihuwa uwarki tayi ba, ba daga gidansu tazo da ita ba, kanwar mijinta ne ta maida ita yarta, ta hada damu duka ta rike mu da gaskiya don ta yarda mu ne ‘yan uwan da tafi bukatar zaman lafiya da su.

Ranta ba ya baci ne? Yana baci, tunda mijinta shima shi ne amma bata taba tsallake ni taje takai kararshi wurin mahaifinta ba, duk da ni ban taba zaunar da shi a gabanta nayi mishi fada kan laifinshi da ta kawo in ba.

Sai in ta tafi in yi mishi nasiha, in gaya mishi ya yi hankali da gidanshi, kuma ko da mijinta ya soma yi mata kishiyoyi bata canza ba, ta kuma san daga san gidan ne aka sa shi ya yi mata amaryarta ta farko.

To yau me gari ya waya? Da tayi hakuri ta yiwa kowa adalci ta zauna da kowa da amana har kishiyoyinta yau waye gidan?

Shiru nayi ina kallonshi, da kanshi ya ce, ita ce don kuwa ita ce uwar Alhaji Abba, ko shi kadai ta haifa kuwa kin san tayi haihuwa mai albarka, balle ga su Ahmad ga su nan da yawa don ita kadai mutum takwas yanzu take da su.

Ko ba ka sónta zaka je gaishe ta don tasa baki danta ya yi maka alfarmar da ka ke nema a wurinshi, tunda babu abin da ya ke so da girmamawa irinta.

Don haka je ki ki gyara tsakaninki da kowa ki zauna da kowa lafiya ki yiwa kowa adalci.

Na ce to, ai ba na gane abinda zan yi musu Mallam, ni a ganina muna iyakacin kokarinmu ni da mijina a kansu, tsanata kawai suka yi.

Wani murmushin ya sake kafin ya ce, to bari dai in dan sa ki a hanya, kin ga dan uwa na Musulunci kawai? Ina nufin ba dan uwan da hakki biyu ya hada ku ba, hakkin  Musulunci da hakkin makwabtaka.

Na ce mishi eh, ya ce to yana da wasu hakkukuwa guda biyar da suka zama wajibi akan ka kai Musulmi. Hakkukuwan kuwa su ne, na farko in ya yi sallama ka amsa, idan yayi atishawa ya yi hamdala ka yi mishi addu’a ta nemar mishi gafarar Ubangiji, in ya yi rashin lafiya kaje har in da yake kwance ka gaishe shi. In ya rasu ka halarci jana’izar shi, in ya gayyace ka cin abincinshi kar ka ki uwa, kin ji su su biyar?

Na ce eh Mallam, ya ce to yan uwantakan Musulunci ne yake da wadanran hakkokin.

To ina ga ‘yan uwantakar da ta zama bayan na Musulunci akwai na makwabtaka? Kin taba sanin hakkin makwabci akan makwabci? Ban kai ga ba shi amsa ba sai ya ci gaba.

Ya ce, to ga kuma uwa uba na zumunci, babu abin da ke ruguza bawa irin shi, akwai kuma alhairori da yawa ga wanda yayi hakuri ya yi shi ya bada hakkin shi.

Wasu Malaman sai suka ce tun a duniya ake amfana da tukucin shi, ayi ta jan kwanakin mai yin shi don ya dade yana yi, wasu suka ce a’a ba kara mishi kwanaki ake yi ba ayukanshi na lada ake nunnunka mishi.

Wasu kuma suka ce zuriyarshi ce bata tabewa, sai ayi tayi mata albarka, to wanne ne a ciki in anyi mana ba a so? Na ce babu, ya ce to kiyi hankali da su, don hakki uku suke da shi a kanku.

Hakkin Musulunci, hakkin makwabtaka da kuma hakkin zumunci, na ce mishi to Mallam.

Na sake kallonshi cikin natsuwa na ce mishi, to ba ni addu’a Mallam. Ya yi murmushi ya ce wadancan da na baki kin raina su?

Shiru nayi ban ba shi amsa ba, sai na ji ya ce je ki ki rike su sun ishe ki istigafari. Hailala, Salatin Manzon Rahama, kiyi tayin su gwargwadon ikon sa ki cikata da la’hau’la 100.

Na sha gaya miki ita kadai in ki ka rike ta ta isa, magani dari babu daya take yi wa mai karantata, karami daga cikin maganin nata kuma shi ne bakin ciki.

Nayi wa Mallam godiya nayi mishi fatan alheri, nayi sallama da shi da iyalanshi na fito daga gidanshi cikin zuciyata ina tunanin babu abin da ya dace damu illa mu tashi kawai mu bar gidannan muyi nesa da kowa balle hakkin wani yaje yana hawa kan mu, kuma wai komai mugun halin mutum sai ace wai sai ka ba shi hakkinshi.

To in kayi nesa da shi ba ka huta ba? Sai da na biyo gidan Anti Ramlah na shaida mata tafiyar tawa kafin na isa gida.

A gida Gambo sai shiri take yi gaba daya ‘ya’yan da aka haifa da Umamatu mata biyu Nusaiba da Hindu ya’yan Ruwaila da Ade da kuma da namiji daya na amaryar gidan Usman.

Sayayya mai kyau Gambo tayi musu iri kuma daya, tsofaffin gida kuma duka atamfofi dattawan gidan shaddodi yadi biyar-biyar matan gidan da a hira ne kawai na gaya wa Gambo yawan su na kuma ce mata cikinsu mata biyu ne kawai ba su haihu ba.

Tayi dariya ta ce, lalle gidan naku gidan yawa ne, gaba daya dakunan sai da ta baiwa yaro daya riga ai kyau na kalli irin lodin tsarabar da ta tara wai duka na mutanen gida ne, na ce mata aa Gambo, to ni da zan zo me suka ba ni suka ce in kawo miki?

Nan da nan fuskarta ta yamutsse alamar maganarta bata yi mata dadi ba, nayi maza na ce mata to kiyi hakuri.

Ana gobe zan tafi gidanmu ya cika makil da ‘yanuwa wai an zo min wunin sallama wasu kuwa sun zo ne yi wa Gambo taimakon aikin abin tsarabar da zan tafi da shi.

Muna gefe ni dà Anti Ramlah wacce tazo min da mai kitso da kuma lalle su suna ta aikinsu mu kuma hirarmu muke yi. Ai naso in zo miki da kaza mai nonon rakumi ban samu nonon ba ne. Na ce ar na ci, da sauri ta ce min a ina ki ka samu? Na ce, Aliya ce ta kawo, Anti Ramlah ta ce, kai Hajiya Aliya fa ta kile ko da yake dai ai sirikar Hajiya Kubra ce.

Gyaran jiki sosai aka yi min kafin aka yi min adon lallen dan daidai mai kyan gani da sha’awa, sannan aka yarfa min kitso.

Azahar bata yi ba sai ga Bala da direban da ya kawo ni sun iso, Gambo tana ta dariya kai Bala har kun iso? Bala yana fara’a don sun riga sun saba da Gambo saboda jan shi a jiki da take yi.

Nan da nan ta shiga ina aka saka dashi da direban kafin yamma komai ya kammala, dubulan, nakiya, alkaki, tayota, tuwon madara, kwakumeti, babu abin da Gambo da masu taimakonta basu yi ba.

Da yamma kuma sai ga Hajiya Kubra an kawo ta a sabuwar motar da Alhaji Abba ya saya mata, sai da ta shiga suka gaisa da Mama kamar yanda ta saba sannan ta shigo wurin Gambo.

Kwalla guda tazo dashi shake da soyayyan naman rago, ga kuma danbun naman abokitin kwallan ga kuma man shanu da yaji ki kaiwa mijinki.

Wannan nashi ne, ki kuma gaya mishi na gode, Ubangiji ya yi wa zuriyarshi albarka, zan kuma zo da kaina in yi mishi godiya, na ce mata to.

Washegari tun safe aka gama shiri’ na shiga wurin Babana muka dan yi hira na bashi hakuri akan al amura na kawo abin da zan iya bashi na bashi duk da dai nasan ba komai zai yi mishi ba sái dai kuma ya ji dadi yayi tasa min albarka.

Itama Mama na shiga nayi mata sallama na ce mata ni zan tafi, kallona kawai take yi watakila kalmar da zata yi amfani da ita ne a kaina ta rasa, na mike muka yi sallama da su Habiba na mika wa ‘ya’yan Sha’awa dubu biyu na ce su raba.

Habiba ta biyo ni tana yi min rakiya zuwa kofar gida, in da ‘yan uwa duk suke tsaye suna jiran fitowata.

A cikin zaure na tsaya don yin magana da ita, saboda ta hakura ta sauke girmen kai ta sassauto har dakin Gambo ta biyo ni tana yi min sannu da zuwa, har ina jin Mama tana tambayar ta kema kin bi ne saboda yar wainar da take baki?

Na kalle ta cikin natsuwa na ce mata, in hali yayi kin koma dakinki kiyi hakuri, Habiba saboda kema kin san wannan zaman naku ba tsari ba ne, tayi maza ta ce min haka ne Humairah, na gode.

Na ciro dubu hudu na milka mata na ce kiyi hakuri godiya tayi tayi min, na juya zan tafi tana bina kice ina gaida Kawu, na ce zai ji, in kin samu mai zu a ki aiko min da zani don zannuwan nawa sun fara yin sanyi.

Na ce to ai kwauron baki ki ka yi Habiba da kin gaya min da wuri duba miki, to amma yanzu kinga kayana har an riga an daure su.

Adam da Baba Karami suna tsatsaye ga Sa’ adatu tana rungume da Umamatu ‘ya’yan makwabta ma duk suna tsaitsaye, na sake yin sallama da Baba na shiga mota muka kama hanya daidai karfe bakwai da rabi na safe.

A gida rannan muka yi sallar azahar a gidan kuma na samu Ado shima kuma a safiyar ya iso don haka tsaf na samu dakin yayi matukar farin cikin dawowan namu, ya kuma yi magana mai yawa kan irin hidimar da Gambo da ‘yan uwanta suka yi.

Nan da nan na shiga rabon tsaraba nan da nan aka shiga zirga-zirgan zuwa yi min sannu da zuwa, sai ka ce ba ni ce na tafi ana amsa sallamar tawa da kyar ba, na ce kai akwai hikima mai yawa a cikin al’adar bahaushe ta yin tsaraba.

Ni kuwa duk wanda yazo sai na mika mishi wani abu yara in sun shigo in debo tuwon madara ko kwakumeti in danka musu.

Dare nayi Ado ya tasa ni a gaba ya soma bari yana rawar jiki yana marairaita, tanfar dai wani lokaci mai tsawo muka yi ba mu hadu ba.

<< Mijin Ta Ce 41Mijin Ta Ce 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×