Skip to content
Part 46 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ina zaune a falona ina karatun littafin (Riyadus-salihin) babin godiya kan ni’imomi nake karantawa, Baba Yahya ya shigo da gudu, can bayana ya tsallaka ya wuce ya buya.

Sai ga Umamatu ta biyo shi a fusace, ga dukkan alamu tsokanarta yayi, ta bude baki da nufin yin magana fushin nata yayi tsanani, na daga ido na kalle ta cikin natsuwa na ce mata.

“Umamatu sau nawa zan gaya miki cewar Ubangiji yana son masu hadiye fushinsu, nan da nan ta ‘sauka, ta kalle ni cikin ladabi ta ce na hadiye Goggo, na ce to ai kin san kuma yana son masu yafiya, ta ce na yafe mishi.

Na ce to kuma har ila yau yana son masu kyautatawa na kasa da su, tayi murmushi ta ce to Goggo ya biyo ni yazo ya karba.

Tana barin dakin na kamo Baba Yahya na jawo shi gabana, kumnenshi na kama na rike da hannuna ina ja yana bin hannun nawa yana fadin kiyi hakuri Goggo, na zaro ido ina kallon shi sau nawa nake gaya maka ba sa’o’inka ba ne?

Sau nawa nake gaya maka da Hindu da Umamatu da Nusaiba shekaru uku-ukı suka baka? Don haka ka daina tsokanarsu, ka daina yi musu rashin kunya.”

Jin da ya yi na ce da jan kunnen nashi ya Sanya shi tunanin da dokar da yasan an kafa min, cikin natsuwa ya ce Goggo Babana ya hana ki kama min kunne saboda yana min ciwo.

Na saki kunnen nashi cikin sauri na ce, to amma ba zai hana in in saka tsallen kwado ba ai, tunda kai baka son a tsokane ka amma ka iya tsokana. Sun ce maka superdi ka gaya mishi ya ce kar a sake.

Sannan sun ce maka Tanko ka sake gaya mishi ya hana, to zan gaya mishi ni da kaina ba ka da aiki in ka zauna a gida sai tsokanar yayunka kawai kake yi, don haka ya zabi abinda za’a rinka yi maka cikin biyu, ko dai ya bari in rinka sa Yaya Bala yana tafiya da kai gona ko kuma a gida Yaya Usman ya rinka horar da kai yana saka tsallen kwado.

Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, kiyi hakuri wahala zan sha in an sani tsallen kwado, nayi nauyi da yawa, na ce to bi bayan ‘yar uwarka kaje ka bata hakuri, ya ce min to. Ya tashi ya fita.

Yana fita ya bar dakin, na amsa wayar Yaya Ibrahim daga Kaduna, Anti Humaira ina kwana? Nayi murushi na ce lafiya Yaya Ibrahim, ya ya gida? Ya ya yaran?

Ya ce, lafiyarsu kalau, na ce to Mamansu fa? Ya ce ga ta nan tana jin ki, wai tana gaishe ki, na ce to na gode ina amsawa.

Yaya Ibrahim ya ki ya. daina kirana Anti Humaira, duk da a yau shi din wani irin kammalallen mutum ne natsattse, mai addini, mai mutunci da ganin girman na gaba dashi, don haka ba kirana Anti Humaira akan yanayin shirme irin na baya ba ne yana dai kiran nawa ne kawai saboda sunan da ya zabi kirana da shi kenan.

Yayi aurenshi tun a lokacin da ya gama karatunshi na (N.C.E) saboda sanin da nayi cewar shi din ba yaro ba ne karami, yana bukatar aure ya sani tsayawa wajen ganin yayi auren yana koyarwa yana kuma taimakon Ado kan al’amuranshi.

Da haka ya soma rike iyalinshi daga baya na bashi shawarar janyewa daga harkokin Adon don ya tafi yayi nashi na kanshi saboda lura da jaruntakar shi da nayi.

Kan haka na tasa Ado a gaba sai da ya ware dukiya mai dan nauyi ya bashi nima na tattara abinda na iya tattarawa na hada na mika mishi ya soma harkokinshi na kasuwanci.

A yanzu yana zaune a Kaduña a gidanshi na kanshi da ya gina da matarshi Rumana da ‘ya’ yanshi maza guda uku.

Dama na ce bari in tambaye ki yaya jikin na Mama? Na ce da sauki sosai, ya ce to ki rinka hakuri fa, ko kuma in ce kiyi ta karawa tunda nasan kina yi.

Nayi murmushi na kawar da zancen ta hanyar tambayarshi an samu sakon nawa kuwa? Ya ce eh an samu, na ce to in Rumana zata zo sai tazo min dashi, zata zone? Nayi murmushi na ce ba za ta zo duba mu ba ga Mama ta dawo?

Ya dan yi murmushin ya ce, to’ to shi kenan sai ta zo din na ajiye wayar can cikin zuciyata nasan tsanar da Mama ke nunawa Rumana ke damunshi, ita kuma Mama tana tsanar Rumaia dama Ibrahim din baki daya ne har da ma ‘ya’yan da suka haifan saboda ni.

Saboda tayi juyin duniya Ibrahim ya dauke ni kamar yanda ita da sauran ya’yanta suka dauke ni ya ki, don haka taki shi ta hakura dashi akan idona akan idonshi. Ado yayi dariya ya ce ai ta kware ki Mama daina barin Humnairah tana kara kwararki.

Daina bar mata abin da ki ke so, ki rinka yarda kawai ke da ita kuna haduwa kan abin da ki ke son tunda kaddara ta riga ta hada ki ke da ita.

Gaskiyar Ado ne kaddara ce ta hada ni da Mama kaddarar kuma ta kaddara min mallakar mutanen da take matukar so a rayuwarta don haka kiyayyata da ita maimakon raguwa kullum karuwa take yi ban kara sani da fahintar hakan ba sai a shekarun baya-bayan nan shekarun da Ado ya sake komawa cikin al’amuranta saboda yawan rashin lafiyar ta da kuma wulakanci mai tsanani da ta ke fuskanta a wurin Babana ga shigar ya’yanta cikin matsalolin aure da ma rayuwa.

Ganin da yayi zata tozarta, ya sanya shi yin tattaki zuwa har gidanmu tafiyarshi gidan na farko kenan tun bayan barin gidan da yayi yaje ya daukota ya kawo ta yayi jinyarta sai da ta warke tayi garau ta samu lafiya ta murmure tayi kiba tayi kyan gani.

Sannan ya maida ita dakinta bayan’ ya gyara mata shi yasa mata duk wani abin da ta bukaci a Sanya mata, ya daurawa Anti Sha’awa aure ya kwashe ya’ yanta ya maida su gidan ubansu, ya baiwa Habiba jari mai karfi don yin sana’a, tunda a gidan su kullum fada ake yi akan abinci sannan ya dawo.

Amma duk da haka bai sa Mama ta samu zaman lafiya a dakinta ba gatan da ta ga ta samu wurin Ado da kulawar da taga yana yi mata ta hanyar yi mata aiken kudi akai-akai saboda maganinta da ma wasu al’amuran rayuwarta.

Sai ya sa ta yunkurin sake tasa mutane a gaba da fitina, shi kuwa Babana ya ce ina? Ai wannan zamanin ya wuce, bai zai yiwu ba, ba zan lamunci hayaniya da fitina ba, ba kuma zai yarda a tasa mishi wata mata a gaba ba tunda a yanzu kam a zahiri ai Zubaida ce ta damu Mama.

Sai dai idan nayi nazari naga ta kasa hakura da kiyayyar da-take yi min yadda take kina kuma haka take kin Umamatu, sai in gane ta hakura da Gambon ne kawai saboda ta gane tafi karfinta bata kuma Kallon inda take.

A wannan lokacin kullum wurin Ado Mama ke kawo karar Babana, kullum kuma karar ba ta wuce ba ya shiga dakina ya dade kamar nasa, ba ya saurarona ba ya bani hakkina.

Rannan ina jin kan Ado ya daure ne da al’amuran, bai fahimce su da kyau ba, yasa shi kallona cikin natsuwa ya ce min ni me Mama ke nufi da wadannan kalmomin, na sauraro da hakki ne? Ko tana nufin har yanzu itama bata daina ba ne? Nayi shiru nayi kamar ban ji shi ba, can cikin zuciyata na ce ai da ita ka kira ka tambaya.

Ba ki ji ina magana da ke ba ne? Tunda ba zai yiwu in gaya mishi abinda ke zuciyartawa ba tunda nasan yin hakan bacin rai zai zama, sai kawai na maida maganar wasa na ce mishi, towwwo! Wato in mutum ya girma sai ya hakura? Kenan nima in shirya, ya yi maza ya jawo ni jikinshi yana dariya tare da fadin a’a-a’a ai ke ban da ke a cikin Humairah tunda ke ai ke kece. Zuwa can yaja tsaki an jima ya sake jan wani tsakin ina dai jin shi ban tambayi dalili ba, can anjima abinda ke damun nashi ya kasa zama yayi shiru a cikinshi. Sai naji ya ce kwata-kwata Mama bata fahimci rayuwa ba.

Ba ta ma san yadda rayuwar take ba, ai baka cin zamaninka ka ce zaka ci na wani, ya sake jan wani mummunan tsaki sannan ya ci gaba, ke kuma kin ci naki kin hana wasu cin nasu.

Kin kama hakkokin mutane kin daddane kin yi sanadin da abubuwa da yawa suka caccabe, kin hana ‘ya’ya jin dadin rayuwarsu saboda baki yi musu tarbiyar da ta dace da su ba. Ga alhakin Jama’a da ki ka yi ta diba amma wai har yanzu ba ki fahimci komai ba? Wai lokacin saduda ma bai zo miki ba? Haka ake rayuwa Humaira? Nayi mishi murmushin yake naja bakina nai shiru.

Ya zuba min ido yana kalloma amma kin san bana so in yi magana ayi min shiru ko? Nayi murmushi na ce kayi hakuri Kawu mu bar wannan zancen kawai muyi wani tunda ni ai ba ni da bakin magana kan wannan batun. Saboda dai ka riga ka karantar da ni na gane wata gaskiyar ma fadarta rashin kunya ne.

Yayi murmushi saboda yasan nasha fadar gaskiya akan Mama in muna hira ya ce shi na zage ta, dan haka na daina.

Ya ce, to naji kawo mana wani zancen muyi tunda na kawo nawa kin ce a’a, na matsa jikinshi kawai na soma yi mishi abubuwan da na san sun fiye mishi hirar dadi da kuma muhimmanci.

Tun sanda Mama ta sake dawowa cikin al’amarin aurena ban samu wani cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali ba saboda har a yau bata hakura ba burinta bai wuce na taga, ta ga bayan auren nawa ba saboda haka kullum tana gidana.

Nata gidan da tsawon rayuwar kuruciyarta take kirarin nata ne, mijin ma nata ne wanda duk zai zauna da su kuma sai dai yayi hakuri, to zaman cikinshi ya gagare ta, a yanzu a shekarunta na girma, shekarun da a su ne ya kamata ace gidan ya zama nata don tafi bukatarshi.

Shi kuma Ado a baki ne kawai yake fadan halin Mama kaga kamar babu wanda ya kai shi sanin halin nata bale ya fishi fahimtarta, da  ta zaunar dashi ta gaya mishi abin da ta gaya mishi ta kulla abinda take son kullawa.

Sai ka ganshi yana huci yana zare ido, yana fadin maganganu da in ba ayi hankali ba ráyuka zasu yi matukar baci.

Haba Humaira! Haba wannan abin tausayi har ina? Zaman gidanku kuma ya gagareta da gimanta ta baro dakinta ta dawo nan, nan din ma zai gagare ta ne?

To in nan ya gagare ta taje ina? Rannan dai na danne ziciyata kawai amma kiris ya rage in ce mishi to ta shiga duniya mana.

Rannan ma da wata matsala ta sake samun Mama ta sake yanke jiki ta fadi, stroke dinta ya dawo, da sauri na yi wa Adon waya ya dawo. Amma abin mamaki wai da ya tambaye ta abinda ya faru da yake bakinta bai mutu ba, sai ta ce mishi ni ce nayi mata sanadin hakan.

Watakila tayi zaton daga fadin hakan zai ce min zo ki tafi gidanku, ba na auren yadda ta saba ganin ana yi wa ‘ya’yanta, sai kuma maganar ta kare ayi min fada ya kuma shirya ya tura ta gida tare da Suwaiba wacce har yanzu aure ya gagare ta, to sun je sun dawo gamu nan kuma muna zaune tare a gidan.

Wadannan dalilai da nake lissafawa sai suka sa auren nawa ya zamo auren da a daidai lokacin da mutancin waje suke yi min hangen  jin dadi da farin cikin da ke cikinshi saboda nasarorinshi na zahiri da suke baiyane.

Ni kuma da nake ni ce a cikinshi cikin zuciyata nasan yanzu ne nake zaman hakuri mai yawa, sai dai kuma ban taba yarda fitintinun da ke kewaye dani a cikin nashi sun sani na taba cewa da na sani ba, a kullum na gayawa mai babban allo matsalolina ko a waya ne.

Hakuri zai yi ta bani yana gaya min cewar shi dan Adam haka rayuwarsu take, yakan girma ne yana tare da matsalolinshi, don haka in yi ta hakuri. Dadin abin dai kawai a wurina shi ne duk kokarin Mama ta kasa shiga tsakanin Kawu Ado da Gambota ta bata.

Tayi-tayi abin ya gagara, tayi juyin duniya ta rasa yadda zata yi, bata ma kara tsinkewa da al’amarin ba ta kara tsorata dashi sai a lokacin da Adon ya zartarwa Sa’a hukuncin aurar da ita ga babban amininshi Barrister Tukur Usman.

Wanda yasan Sa adatu tana da saurayin da take so bai ma tsaya wajen yin shawara da kowa ba, izini kawai yaje ya nema a wurin Baba. Sai kawai ya fadi daurin auren kowa yaji, Mama tayi bakin ciki kamar zata mutu ta tasa shi a gaba tana kuka ga Suwaiba shekara da shekaru babu aure, ka samo mutumn mai muhimmanci irin wannan ka dauki wata Sa’a ka bashi don dai kai sun shanye ka ba ka ganin kowa ba ka son kowa sai su?

Ya ce ba samo shi nayi ba Mama, Aminina ne ya sha kuma yi min kukan matsalolin gidanshi ne ya roke ni in ina da wata “yar da na san me tarbiya ce in yi mishi hanyarta yana so.

Kin ga kuma yana cikin damuwa ba zan kara mishi damuwarshi ba, ban yi mishi adalci ba in nayi mishi hakan.

Yanzu ita Sa’a ba damuwa bace sai Suwaiba? Yarinyar da bata son auren ban ganta tana yin kuka a gabanka ba, yayi murmushi ya ce ai iyakar dai abinda zata yin kenan Mama.

Ba za a kai ta gidanshi ta ki bin umarninshi ba, ba za ta je tayi mishi rashin kunya ko wulakanci ba, ba za taje ya ce mata yi ta ki yi ko bari ta ki bari ba, saboda su a dakinsu uwarsu tana da tasiri mai karfi akan ‘ya’yanta.

Tana kuma da halin girma nayi wa suruki adalci, ni kadai nasan irin taimakon da tayi min akan aurena, su Suwaiba kuwa ba haka suke ba Mama, ina jin ta rannan tana gaya miki ko taje gida bata gaida Babansu ko kallonshi bata yi, saboda bata da lokacinshi.

Shiru kawai nayi muku, to yaushe zan dauke ta in baiwa wani? In dai ba so nake in taje tana wattsakewa daga halin rashin mijin da take ciki ba ta soma cin mutumcin mu ni dashi.

Shi yasa na barta ta kawo shi ita da kanta, kayan dakin dai zan bayar.

<< Mijin Ta Ce 45Mijin Ta Ce 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.