Ke tafi da yarinyar nan Babana yayi maza ya daka min tsawar da ta sani nayi maza na juya na bar dakin na fito tsakar gida ina rarrashinta daga baya mana goyata na nufi zaure naja na tsaya ni kadai jikina sai faman bari yake yi saboda tsoron abinda zai faru tsakaninsu, tunda na fara jin Baba yana cewa ai tunda kin ce ba kya jin rarrashi to kuma wannan abin da ya shafe ki ne kin san dai baki isa…
Ban yarda na ji karshen maganar ba saboda tsananin tsorarta da nayi na kar in ji ya nufe ta da duka.
Lokaci mai tsawo Baba ya dauka bai fito daga dakin ba tun ina tsorace har dai na hakura na shiga sabgogina tunda itama Sa’adatun ta hakura tayi barci.
Sai zuwa can naga ya fito ya shiga wurin ya dan dade kafin ya sake fitowa yazo zai wuce mu a zaure ya kalle ni ya ce min, kai mata ita ta shimfide ta nayi maza na ce mishi to.
Ina shiga dakin Inna gabana ya sake faduwa, saboda kukan da na same ta tana yi, gashi kuma gaba daya kwalliyarta dama gyaran gashinta sun lalace.
Tasa hannu ta karbi Sa’adatu suka kwanta tare tana bata nono, ni kuma na fito na shiga kicin don bin umarnin da ta ba ni na dora mata sanwan abincin dare.
Kullum ka’idar Babana kenan Mama tana barin gida zai dawo ya samu Inna ko da kuwa dawowar nashi zai zama dalilin fadansu, ya tafi ya barta tana ta kuka ya gwammace yin hakan.
Har a wurin dangin Baba Innata ba wani farin jini ne da ita ba saboda Mama ta riga ta saye su da ‘yan kyaututtuka gashi kuma ita Innan a cikin kulle mai tsanani take, don ko nan da can Babana bai barinta taje.
Koda kuwa abinda ya shafi danginta ne sai dai in dolen ta kai dole, ‘yan uwan Babana da suke son Inna sune wadanda suka hada uwa da uba da shi wadanda Mama take mu’amalla da su ta koma bangaren ‘ya’yan da yake uba daya dasu.
Don a cewarta na uwa daya uba dayan su da uwarsu ma’ana kakarmu kenan basa nufinta da komai sai sharri don su suka fi kowa son ganin Baba yana aure. Tsiyar mutum ba zai sihirce mata yaya ya mallake mata su ba.
Duk da halin da zaman Inna ke ciki a gidanmu na rashin ‘yanci da rashin walwala ga rashin damar yin mu’amalla da miji a bayyane sai dai komai a darare koma a tsorace, hakan bai hana kishin Mama tsananta a kanta ba.
Kullum kawayenta suka zo ko wasu ‘yan uwanta da take yarda ta tattauna sirrinta dasu to hirarsu bata wuce hirar Inna. Idon su a kanta yake, hankalinta da tunaninsu gaba daya wurinta yake tafiya.
Rannan ina jin ta ita da aminiyarta Hajiya Anwamu, kai wannan ja’irar yarinya da an barta ta samu sakewa a gidan ita da mijinta da ban san yadda ta zama ba.
Mama ta kalli inda Inna take shanyar kayan ‘ya’yanta da ta wanke a daidai lokacin da Anwamu ke cewa, ni fa ba kyanta ne yafi komai kona min rai ba, game da ita uh’uh, tsabtarta tafi komai bata min rai.
Mace mai tsabta majadan ke ko da mummuna ce jan hankalin miji ne da ita, to balle wannan shi yasa na ke gaya miki daina barin yaran nan suna tara miki kayan dattinsu a dakinki kowacce ta tube to ta wanke kawai.
Ta dan ja tsaki kadan kafin ta ce uhun, ai mazan nan suna kwararmu. Sai da suka ga mun fara kaiwa inda muka kai sannan suka debo tsala-tsalan ‘yanmata ‘ya’yan cikinsu suka kawo mana, yanzu wannan in ka ce zaka sa wa miji ido a kanta ai sai ranka ya baci.
Shi yasa ni a gidana har sayar mishi da girkina nake yi, ko in bashi kyauta ta cikin hikima kuma in san yanda nayi na fanshe ta wata hanyar, tunda in ya kwana wurin nawa ma menene? In ban da kayan bacin rai.
Mama tayi maza ta kyalkyale mata da dariya, ta ce tafdijan ai ba zan iya irin wannan sakarcin naki ba. Ta kwashe bayani tsab na sabon tsarin da ta kawo a gidan na cewar mai goyo bata da miji bata kuma da girki saboda dawainiyar goyonta.
Hajiya Anwamu ta ce, anya Majadan a hakan kuwa ake har yanzu? Kwarai kuwa, in ji Mama, ai tunda ta haifi ‘yar nan har yanzu ban bata girki ba, shi kuma kin san ba ma mai irin wannan fitinar ba ne, da dai an yi.
Amma yanzu ko harkokin cudewar kasuwar nan da ake ciki ai ta isa ta hana mazannan namu kuzari.
Anwamu ta ce haka ne jimawa kadan ta sake waiwayawa ta kalli inda Inna take zaune tana taje gashin kanta data gama tsefewa ta ce uhun, ni kam da za’a bar ni da na ce yarinyar nan ciki ne da ita.
Mama ta zabura da sauri alamar kaduwa ta ce ciki? Kai haba wane irin ciki to a ina ma ta gan shi? Ita ba fita take yi ba balle in ce suna haduwa a wani wuri shi kuma ba dawowa gida yake yi ba in bana nan tunda ai ko da nake fita unguwa da yaran don bana barin su balle ace sune zasu yi girkin dana bari ai kullum ina tambayar Ado da bana nan kun zo gida ne?
Sai ya ce min ni dai nazo na kawo cefane Inna ce Alhaji fa? Sai ya ce a’a shi bai lura ba.
Cikin zuciyata nayi mamakin jin yadda duk da baiyananniyar kiyayyar da Ado ke yiwa Innata ya ki yarda ya gayawa yarshi gaskiyar abinda yake faruwa tsakanin Innan da mijin su in bata nan.
Mama ta sake kallon Aminiyar tata ta ce, mata ai kin san ita din bata rabo da shafe-shafe kullum a cikin shi take shi yasa nake cewa ita din ba wata fara ba ce mai ne kawai ya maida ita haka.
Hajiya Anwamu ta ce, to ba zan yi miki musu ba, amma ni dai nasan matar da aka hana miji ya kama hannu tsabtarta da ban take da irin ta wannan yarinyar.
Kalli kyan kitson da ta tsefe ke da kike da mijin kalli kitson da yake kanki. Cikin zuciyata na amince da cewar ita Hajiya Anwamu mata ce mai auna komai a mizanin hankali, don kuwa ni da kunnena nasha jin Babana a irin ranakun da yake dawowa wurin Inna in Mama bata nan yana cewa Inna.
Nafa gaji da ganin wannan kitson a canza min shi a kuma zizara min lalle in gani in dan ji dadi, wani lokaci ma zan gan shi yana bata kudi masu dan auki yana cewa ki sayi sabbin under wears ki kuma bada sabbin dinkuna tunda nasan kina da zannuwan da ba a dinka ba.
A duk lokacin da yayi irin wadannan maganganun kuwa to ko da bata tanka mishi ba, to zaka ga tayi abinda yace din, za kuma ta nuna mishi in an kawo.
Don haka nima na yarda yawan kwalliyar Innata har da yawan kulawar Babana na boye.
To sai dai ita Mama duk da wannan hannunka mai sanda da aminiyar tata tayi mata don ta lura tasa ido ko zata yi sa’a ta gano abinda ke gudana ta ki yarda, ta na ce to taja ta tsaya kan cewar ai shi Babana ba ma zai kwatanta wani abu makamancin abinda ake zaton ba, don yasan karonsu da ita.
Ban da haka ma ta riga tayi sa’a ba abinda yake gudu irin bacin ranta in ban da haka ai da zama da wadannan bai zamo mai sauki ba a wurin kullum fa sai tsohon nan ya zo gidannan wai yazo ganinta sai kace shi kadai ne ya haifi ya a duniya.
Ai kin san dai ba haka kawai yake yi mana wannan zaryar ba.
Hajiya Anwamu ta rike baki nuna alamar mamaki ta ce ai fa kam da walakin wai goro cikin miya, kin kuma san shi fa duk ‘ya’yanshi da jikokin shi da ake aurarwa inda duk suka je ai karbe gida suke yi in ban da nan din.
Mama ta gyada kai alamar jin dadin cewar da aka yi ita kadai ce ta gagara.
Mama da ‘ya’yanta sun ki sun kuma tsani ace wai ni din kama da Babana nake yi, balle ma ni yayi subutan baki yace ai duk gidan nan babu mai kama da Alhaji Surajo irin Humaira sai kaga ta taso da fadanta kuma da iyakacin gaskiyarta fadin zata yi rai a bace tana fadin wannan ai wulakanci ne.
A ce duk ‘ya’yan da aka haifa a gidan nan ba a samu mai kama da Alhaji ba sai akan wannan mummunan yarinyar, to ta ina kamannin nasu yake? Ku nuna min don in gani.
Duk da wannan balokoko da zare ido da Mama ke yi don hana fadin kamannin nawa da mahaifina su can wurin dangin Inna sun dage kan wai ban dauko komai na Mahaifiyata ba, har ma basa gajiya da bayar da labarin wani abinda ya faru sanda Innan take goyona suyi ta dariya.
Wai ana hidimar aure ne a gidan Alhaji Mai kudi sanda ya auri amaryar gidan ta yanzu Furera Jama’a sun cika sai aka shigo dani ana tambayar ina uwar wannan yarinyar take?
Mai tambayar kanwa take wurin mai babban allo, don haka Inna tayi shiru tana kallonta bata ce mata gata ba. Sai da Hajiya Kubra tazo wucewa taga abinda ke faruwa shi ne ta kalli Inna tayi mata dakuwa, ta ce shakiyancin banza kina kallo ana tambaya ina uwar yarinya ba za ki sa hannu ki karbe ta ba sai kiyi shiru kina kallo?
Sai a lokacin ne mai tambayar ta kalli Inna ta ce yau ga abin mamaki, Binta ce ta haifi wannan bakar yarinyar? Gabadaya aka kwashe da dariya tayi murmushi ta ce Ubangiji ya rayata ya kuma sa mai albarka ce aka ce amin.
Ko kadan ni din bana kama da mahaifiyata, don kuwa yayin da Inna take fara sol, ni din baka ce. Inna mai dogon gashi ce ni kuwa gashin kaina matsakaici ne sai dai akwai laushi da santsi da kuma cika kai.
Inna dara-daran idanuwa ke gare ta, ni kuwa nawa madaidaita ne, sannan ita siririya ce ni kuma ba ni da jiki bani kuma na ma darata tsayi kadan, to amma duk da haka su Mama sun ce Inna ba da ita nake kama ba, to a danginta na samo kamannin nawa.
Rannan muna kwance kan gado daya ni da Innata yayin da su Atika da su Aliya suke daya dakin nata donni kam duk in da Inna take ba na iya barin wurin ko da kuwa Babana yana nan sai in shi da kanshi ne ya kore ni.
Kan hakanne mutanen gidanmu suka kulla mata sharri har ya bazu mutanen waje ma suka ji wai duk cikin ‘ya’yanta tafi sona har ma wai bata hada son nawa da na kowa.
Ni kam cikin zuciyata cewa nake yi aniyar kowa zata bishi, in ma mai fadan yana fada ne don ya haddasa mata matsala cikin ‘ya’yan nata mun san duk daya muke a wurinta.
Inna kamar ki bani gashin ki tayi maza ta juyo ta kalle ni cikin yanayinn murmushi ta ce na ki fa? Na dan yi magana cikin natsuwa na ce ai nawa ba mai yawa ba ne irin naku ke da su Atika, su kam sun ji dadi kama dake suke yi.
Su masu kyau farare sol-sol ni kuma baka mumm….kan in karasa tayi maza ta daure fuskarta nima nayi maza nayi shiru waya ce miki baki muni ne?
Ta zuba min ido tana kallona, sannan ta dan saki fuska kadan ko kadan baki da muni ba kuma zaki yi ba, ko kin ji ana ce miki mummuna kar ki sake damuwa ki dai kudura ranki cewar za ki natsu ki zama mutuniyar kirki mai kamun kai da natsuwa.
Mai girmama na gaba da ita, mai jin maganar iyaye, mai maida hankali akan karatunta mai jin tausayin kannenta, kin ji ko?
Nayi maza na ce mata to Inna, ta juya ta ci gaba da kwanciyarta zuwa can sai naji ta ce min, kin fara girma yanzu kuma ke din mai manyan barage ne, amma duk da haka ina so kiyi karatu tunda ni ban samu damar yi ba, don haka kar ki yarda ki kula kowa kiyi karatunki kawai nace mata to.
Yawan maganar karatu da Inna kiyi min yasa na zamo ko a bani kudin Makaran ta ko kar a bani to zan taka da kafata in tafi Makarantar secondary ta kofar fada inda muke karatu.
In na tashi kuma sai in karasa gidan Malam mai babban allo in ci abinci in huta in na yi Sallah in zo gabanshi in biya karatuna na Alkur’ani da kuma littattafan sannan sai ya bani kudin mota in shiga in dawo gida.
Kan hakan ne Mama take cewa Babana wai ba ina zuwa makarantar don nafi kowa son karatun bane a’a ina zuwa ne saboda gidan mai babban allo, su kuwa su Habiba ba su da kowa a wurin shi yasa suke fashin zuwa.
Rannan na dawo gida daga Makaranta da yamma babu kowa cikin gidan sai Innata sai kuma Babana shi kuwa na san ya dawo ne a dalilin yasan Mama da ‘ya’yanta basa zuwa, nayi zan shiga falon Inna sai na ji Babana yana cewa kai kukan mata sai a barku.
Wato ashe duk ta sani a gaban nan da aka yi a kanki bin ta bai ishe ki ba? Ke kin fi so dai kiyi ta ganina cikin fitina? Ki boye ciki a jikinki wata bakwai ba za ki gaya min ba sai yau?
Alhalin kuma na tambaye ki yafi sau nawa in akwai shi ki fada don a san yanda aka yi dashi tunda ina amfanin fitina?
Inna ta ce babu, to yanzu yaya za’ayi kenan? Ta sake ce mishi ai ban sani ba kai nake sauraro. Ya ce to kin ga ni bana son abin da zai tayar min da hankali.
Ina ganin asibiti kawai zamu tunda kema gashi ko yaye yarki baki yi ba, bata ma tafiya, uhun, sannan ana ganewa sai ace ba ki da miji amma ga ki da ciki yaya kenan?
Inna ta ce, kana nufin kenan a cire? Ya ce eh to kin san wani abin dole kan saka kayi shi ba don kana so ba, ni fitina ce bana so.
Ta ce, to ai sai ka gaya mata kawai cewar ba naka ba ne, yayi maza ya daka mata tsawa ta hanyar tambayarta wane irin zancen banza ne wannan?
Nan take ta soma kuka tana fadin ita ya maida ita gidan su ya taimake ta ya mayar musu da ita tunda ita bata da halin zuwa da kanta su barta ta zauna.
Inna ta tubure da kuka gabadaya tana fadin ya mayarwa iyayenta da ita tunda akan tsoron kar matarshi tasan tana da ciki zai iya kaita wurin haluka hankalin Babana yayi matukar tashi.
Ya shiga fadin ni Binta? Ni da bakina na ce ki zubar da ciki? Na ce muje a san menene abin yi? Nayi sallama a bakin kofar sau biyu kafin ya amsa na shiga ina wucewa zuwa dakinmu shi ma yayi maza ya fita watakila dama zaman ya ishe shi.