Skip to content
Part 8 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ihun da Mama ta kurma mai tsananin karfi shi ne watakila yayi matukar firgita ni, har ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganni tsaye a tsakar gida ina huci cikin tsananin firgita don tsoro, ganewan da nayi na kubuta ba kuma a girma da arziki na kubutan ba, wani mummunan abin nima nayi mata ya sani kartawa da gudu na nufi gidan Mallam mai babban allo.

Ina tsugune gaban Mallam sai zare ido nake yi bayan na gama mayar musu da bayani, Hajiya ‘yardubu ta ce kai wannan zalunci da rashin tausayi da yawa yake, amma babu komai wata rana ba za ta yi ba.”

Mallam ya dan yi murmushi ya ce, “Itama yarinyar ai da nata laifin, haka kawai za a kama ta da duka ne bata yi komai ba? Ai ba ita kadai ba ce.”

Hajiya ‘yar dubu tayi maza ta ce, uh’uh Mallam, babu wanda bai san lamarin gidan nan ba, kai dai ayi sha’ani kawai.” Mallam ya ce, “To Allah ya kyauta, ta ce amin.

Abinci kawai Mallam ya bari naci yasa Hajiya ‘Yar dubu ta taso ni a gaba ta dawo dani gidanmu, gabana sai faduwa yake yi, yayin da ta tasa ni muka shiga wurin Mama.

Maman tana kwance tana ganin Hajiya ta mike ta zauna tana yi mata sannu da zuwa, suka gaisa ni kuma ina durkushe. ‘Yarki ce tazo mana gida da wani bayani na rashin hankali, shi ne na ce to bari dai in dawo miki da ita in ji gaskiyar lamarin, tunda dai ai banza bata kai zomo kasuwa, sannan sha’anin nan na ‘ya’yan yau maganarsu ba abin kamawa ba ne, in dai ba zahiri aka gani ba.”

Mama tayi ta bayani na kame-kame har tana gayawa Hajiya wai na cije ta a mazaunai, ta ce a’a shi ne abin mamaki cizo a mazauni kuma? Tayi maza ta bar maganar ta shiga tambayarta Mallam da sauran mutanen gida, watakila ta gane abinda  bayanin nata yake nufi.

Na shiga wani hali na tsoron kar Mama ta ce zata kama ni akan cizon da nayi mata, bata yi hakan ba watakila don maganar ta yayatu da yawa har gidan Baba Yahaya an ji, ya kuma yi wa Babana magana kan irin dukan da ake yawan yi min alhalin na riga na fara girma.

To sai dai Habiba duk inda muka gamu sai ta buge min baki wai ladan cizon Mama da nayi.

Rannan na dawo daga gidan ‘yar Inna Balki da aka gama bikinta wacce kuma take matukar sona Ruwaila.

Ina rungume da jakar ledar da ta bani kayanta kala biyu masu kyau da kayan kwalliya dangin su janbaki da hoda da gazal da man shafawa, gami da turare na zuba a ciki ina ta murna nazo zan wuce Habiba dake tsaye da kawarta a waje sai kawai tayi maza ta tare ni ta kaiwa bakina duka.

Na ce ban yafe ba, ta sake kai mishi wani dukan na sake cewa ban yafe ba, zata sake sai kawar tata ta ce mata “Haba Habiba, wane irin cin zali ne wannan? Don kawai kin ga tana yi miki shiru-shiru?”

Da sauri Habiba ta ce, kar tayi shiru ta rama mana taga irin yanda zan yi fici-fici da ita, kwanannan ma zamu yi maganinku don Mama tasa Babanmu yayi aure har ma ta samo mishi budurwar har an kai sadaki zaku sani.

Sum-sum na wuce na shiga gida, gabana sai faduwa yake yi jikina  kuma yayi matukar yin sanyi don kuwa ko ban san komai ba ban kuma isa komai ba rayuwar gidanmu ta riga ta karantar dani cewar kishiyar uwa ba karamar aba ba ce, sannan ganin  Habiba tana murna ya isa ya fahimtar dani cewar don mahaifiya ta za’ayi auren.

Duk da kashedin da Inna tayi min na jin magana in zo in gaya mata da na shiga dakinta kasa yin shiru nayi, durkusawa nayi gabanta da gwiwoyina duka biyu na ce mata Inna Habiba ta gaya min wata magana ki bar ni in gaya miki.

Ta ce, to gaya min, na kwashe bayanin duka nayi mata ta dan yi shiru zuwa na wani lokaci kafin ta ce min babu komai kar ki damu kanki kin ji ko? Na ce mata to, ina ce kina yin addu’o’in da na koya miki?

Na ce mata eh, ta ce to ai shi kenan. Da daddare Babana ya shigo wurinta saboda ranar ma girkinta ne, bata wani canza mishi ba, wai don ta ji labarin yana neman aure ina jin shi yana tambayarta wai ni menene amfanin gadon jariran can da aka sai miki ne?

Yasa hannu ya dauki yaron da muke kira Baba karami ya maida shi ciki ya kwantar, ban san yanda suka yi da Inna ba iyaka dai da safe bayan mun kammala komai muna zaune a daki ni da ita sai ta ce min.

“Da gaske ne Babanku zai yi aure har ma wai bikin ya matso, Mama ce ta hana shi gaya min wai don kar in hana auren ni da Babana.” Na zubawa Inna ido ina kallonta, ban ma san abinda zan ce mata ba, sai ta sake ce min babu komai kar ki wani damu ranki na ce mata to.

Kwana biyu da yin haka na ji Babana yana cewa Innata ga wannan kiyi hakuri, ki sayi wani abu ko bna ita Mama ta ce bata bukatar komai nawa, ita auren kawai da zan yi ya ishe ta farin ciki.”

Inna ta ce, haka ne tayi shiru, to amma dai ai kin san babu wata mata da…” Inna tayi maza ta ce, mishi uh’uh mu bar wannan zancen kawai, na gode, Allah ya kara budi, ya ce to amin ya fita. Bayan fitar tashi ne ta aike ni in kaiwa Hajiya Kubra kudin daga nan kuma in ce mata in ta samu lokaci ta tambayi izini tazo tana son ganinta.

Zaman lafiya sosai aka shiga yi tsakanin Inna da Babana, maimakon tayi mishi borin jin zafin  auren da zai yi sai kawai tayi kamar bata ji ba, tunda Mama bata maganar ba ta kuma taso ta ji, shima Baba a wannan lokacin hidima sosai ya yi wa Innar saboda jin dadin hakurin da tayi.

Tunda bai saba ganin hakan ba wurin uwargidan da za’ayi wa amarya, don haka sai yayi ta kokarin ya nuna mata cewar bata da matsala a auren nashi, ko da yake dai ni nasan can cikin zuciyar Inna akwai damuwa ta dai hakura ne kawai ta danne don kar ta tonawa kanta asiri, tunda tasan bata da ikon hana auren.

Sati biyu ne kawai bayan wannan lokacin sai muka wayi gari ana yin buki a gidanmu, Mama sai kawai da kawowa take yi cikin murna da farin cikin Babana ya sake auren budurwa.

Sai murmushi take yi tana fadin wannan ai ni ba kishiya ba ce a wurina ya ce, nima zan yi mata irin adalcin da uwar Fatima take cewa tana yiwa kishiyoyinta tunda ita ba za ta yi min irin cin zarafin da Fatima tayi min ba tunda iyayenta ba su yi mata irin tarbiyar da na Fatima suka yi mata ba.

An sha biki a gidanmu ba kadan ba, Inna dai bata wani yi gayyata ba a dalilin wai bata dade da yin hidimar suna ba, amma dai duk da hakan ‘yan uwanta sun taru suna kuma bata shawarwari iri-iri.

Ana kammala biki sai manufofin Mama nasa Babana yayi aure suka fara baiyana, cewar ita ta sa shi kuma ba zargi ba ne da kanshi ya fada cewar Mama ta ce kara auren nashi ne kawai zai kawo zaman lafiya kuma in ya duba da kyau ma ai zai ga gaba daya abokan shi ma mata uku-uku ke gare su ba biyu ba.

Tun daga ranar da aka yi budan kai ya hada su gaba daya a dakin Mama don yi musu nasiha kan zaman lafiya da muhimmancin karami yabi babba Mama ta ce in shi babban ya bi nashi na gaban ko?

Zaman lafiya kuwa ai a wurinka yake tunda kaine mai gida in ka tsaya kan hana zalunci da kuma tsoma yara cikin zaman kishi, amma fa sai kaso hakan tunda ni kam ina ruwana? Ai ni ‘yar kallo ce, menene ban gani ba cikin sha’anin kishiya da sanabenta? Ai babu wani dare da jemage bai gani ba sai na ranar mutuwarsa.

Baba ya ce, haka ne to yanzu tunda ku uku ne yaya ku ke gani zaku ci gaba da kwana bibbiyun ne ko kuwa zaku canza? Ta ce, to sai suyi magana amma ni kam ai ba zamu raba ka da wannan yarinyar ba tayi min  kuruciya da yawa, kaje can kawai kayi sha’aninka ni na bata nawa girkin in ka yi kwana biyu a wani wuri sai kayi hudu a wurinta.

In gari ya waye dai kazo mu mu mu gaisa mu tattauna al’amura tunda kasan duk cikin su babu wacce takai ni sonka tunda su duk Alhaji suka aura ni kadai ni ce nan matar Surajo.”

Babana yayi murmushi alamar jin dadi ya ce, to kuma kin san haka kya ce kin yafe musu ni? Ta ce oh’oh ai ba komai, ka saki jiki kayi hidimar ka Alhaji, ai mun riga mun zama daya.

Ya gyada kai alamar yarda, ya ce haka ne, haka ne Majadan, ta ce to menene? Ai na riga na ci dubu sai ceto.

To hakan aka yi, Innata a matsayinta na wacce aka yi wa Amarya ita ce ta dauki nauyin yiwa Amarya girki na kwanaki bakwan da ango ke yiwa Amarya, ta sake yi mata girkin kwana biyun da Mama ta bata kyauta. Sai nan ta yi wa kanta nata girkin bayan Baba ya yi wa Amarya kwana tara ya dawo wurinta.

Ya sake komawa wurin amarya ta sake jerawa amaryar girkin kwana hudu a jere nata dana kyautar da aka yi mata, sannan ta sake yiwa kanta da ya zo wurinta daya fita zai koma wurin amarya ne ta ce to yau kam a baiwa amarya cefanenta, ta fito ta yiwa kanta girki itama zata huta saboda goyo ke gare ta.

Babana ya ce, ai kin yi kokari kwana goma sha bakwai fa kika jera kina yi ke kadai sau daya kuma ban kama ki da laifin yin girkin magudi ba, Allah ya saka miki da alheri, ta ce amin.

Ya fita ya tafi, ba mu san yanda aka yi ba sai gashi ya dawo wai ba zai yiwu ace tun yau an baiwa amarya girki ba wannan wane irin kishi ne? ‘Yar yarinya ‘yar kankanuwa ace ba za ayi mata girki ko na wata biyu ba.

Inna ta ce, ai fa kana ta juya ta gyara ta yi kwanciyarta ya yi fadanshi har ya gama ya fita bata tanka mishi ba. Mama ta fito ta karbi girkin tana fadin ai ba zai yiwu ba ace wannan ‘yar yarinyar ta shiga kicin don  ana jin haushinta a dora mata dawainiyar da bata isa yi ba, tunda dai ni ce babba a gidan ai dole in shiga hidimar girkin nata.

Inna tana daga kwance ta ce, babbar banza ba, nayi maza na kalle ta don ba dabi’arta ba ce fadin irin wadannan maganganun. Nan take cinta a zuciyarta.

Mama kullum takan yi wa amarya girki nata da na kyautar da tayi mata sai dai kuma kwandala bata mika mata cikin canjin cefanen da ke raguwa, mu kuma ta koma min dira mana abinci kamar yanda dama ta faro a baya.

To na da ma da sauki don zata yi kwana biyu ne Innan ma ta kwana biyu to yanzu ita kadai kwana hudu take yi, ga amarya fitsararriya babu alamar kunya ko tsoro a tare da ita ga alama kuma ta riga taji labarin Inna kafin zuwanta.

Don haka da shirinta sosai ta shigo cikin gidan, ba kuma yarinya karama ba ce kamar yanda ake fada, don kuwa ba za ta rasa shekaru ashirin ba, zuwa da biyu ba kuma wani karatu ta yi ba, mijinne dai bai samu ba sai a lokacin.

Tuni amarya ta gundure ni na rasa yanda zan yi da zuciyata in ji dadi, na tsane ta na tsani duk wani al’amarinta saboda tasa min uwa da tayi a gaba da rashin kunya iri-iri. Babu damar Inna tayi wani motsi sai kawai ka ji ta tana sake mata maganganu.

Mama kuma tana kara zugata tana fadin, a to ai karen bana shi ne maganin zomin bana, in ni anyi min na kyale dole don kar ace girmana ya zube yarinya kam ai ba za ta yarda ayi mata takun da ake yi min ba.

Wani irin kishi mai tsanani ya kama ni game da amarya saboda ganin yanda aka dauke ta aka fifitata akan Innata, take kuma ci wa Innar tawa tuwo a kwarya.

Babana kuma yake zumudin ta yake faman zirga-zirgan wurinta sai ko wurin Mama, dakin Innata bacci ke kawo shi a dole wataran ma ya ki zuwa wurin nata ya shige nashi wurin yayi kwanciyarshi.

Zuciyata ta kai matukar zafi game da abubuwan da nake gani, gashi kusan kullum sai naga idanuwan Inna a kunbure alamar buya tayi ta yi kuka.

Rannan na amsa iran Babana a falon Mama suna zaune dukansu na durkusa ina sauraron maganar da yake yi min. Wannan ba uwarki ba ce da kike kiranta da sunanta?

Na sunkuyar da kaina kasa nayi shiru can cikin zuciyata kuwa cewa nake yi, to ai nima tawa uwar da sunanta kowa yake kiranta, ban kuma taba ji an yi wani tsawa kan hakan ba.

Zuciyata ta tafi wajen tunanin lamurra iri-iri, don haka ba sosai nake fahimtar maganganun da ake ta yi min ba, na dai san kawai na ji kashedin da Baban yayi min na  in ya sake jin na ambaci sunan Zubaida da bakina to zan san bolko miya ne, ke Zubaida ko bana nan ta kira ki da sunanki kizo ki gayawa Mama in na dawo zata yi min bayanin komai.

Ta ce, to, cikin wani yanayi na shagwaba, ni kam a wannan lokacin in ban da Innata tana cikin gidan, watakila da gudu nayi na bar gidan saboda yawan bacin ran da nake samun kaina a ciki.

Na daina ambaton sunan Zubaida sai dai kuma bana kiranta wani Anti, in mu’amalla ta hada ni da ita magana kawai nake yi mata, ta yanayin da zata gane da ita nake yi ba sai na ambace ta ba.

Rashin jituwa mai tsanani ya shiga tsakanina da ita saboda gaba daya bata shakka ko shayin sakin bakinta ta gayawa Inna maganun banza na rashin mutunci.

Ko kuma ka ji ta tana yi wa Inna gori kan wasu abubuwan da zaka kasa sanin inda ta samo labarinsu. Haka kawai kuma sai tayi yaji in Babanmu ya dawo sai ace mishi wai Inna ce take yi mata wulakanci da barazana.

Sai ya tura Mama taje mishi biko in ta dawo ayi ta rattabo mishi bayanai. Wani lokaci ma bayanin yana karewa Babana zai kama ni ya nada min dukan tsiya ya kuma gaya min cewar in har ban daina biyewa Innata, ina taya ta bakin kishinta ba to ni da ita ne zamu bar mishi gidan don ba zan yarda da abinda zai kawo rai ba kan iyalinshi ba gara kawai ya kori mutum ya tafi ya bar mishi  gida a zauna lafiya.

Rannan Inna tana wanki tana matsewa tana ajiyewa a kasa, kusa da bahon din wankin nata saboda sai da ta wanke wurin da zabor yayi tas kafin ta fara wankin ni kuma ina gefenta ina wanke-wanken da Mama ta sani a ina kuma yi mata magana a hankali sai kawai ga Zubaida  ta fito daga dakin Mama tazo ta keta tsakaninmu ta taka wankin da Inna ke  tarawa da kafarta mai sanye da takalmi.

<< Mijin Ta Ce 7Mijin Ta Ce 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.