Skip to content
Part 19 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Yana rungume da ita yana jin yadda ake dukan kofar kamar za a karya.

A fusace ya mike ya bude kofar. Sakina ya gani ta rike kugu tana jijjiga. Ta watsa masa mugun kallo tare da jan tsaki. Ta bude baki za ta yi magana kenan, ta ji saukan mari ta ko ina. Ganin zai iya yi mata illa yasa ta kwasa da gudu tana ihu. Dakinta ta shiga hannunta yana rawa ta kira mahaifinta, har ta mance fushi take yi da shi.

“Abba ka zo ka taimakeni. Abba zan mutu. Zayyad ya yi mani duka kamar zai kasheni.”

Alhaji Bako jikinsa har rawa yake yi, dama kuma yana cike da jin haushinsa saboda ya lalata masa aiki.

Cikin mintuna ashirin ya bayyana a gidan. Shi kuwa Zayyad zamansa ya yi a falon bai koma ba, ya rike kansa da karfi. Alhaji Bako ya shigo babu ko sallama.

“Kai dan iskan ina ne? Iyye! Uban wa ya ce ka dakar mani ‘ya? Ko baiwa na kawo maka?”

Zayyad ya mike yana wani irin huci. Ji yake ya tsane shi, baya kaunar ya buda idanu ya gan shi.

Bai san lokacin da ya damki wuyar rigar Alhaji Bako ba, ya ware jajayen idanunsa akansa.

“Kai! Kai shedani ne! Tunda nake jin labarin shaidanin mutum ban taba jin labari irin naka ba. Ka za ci zaka kashe Shugaban kasa ko? Ka zaci makircinka zai sa ya mutu ko? To ka yi kuskure! Insha Allahu, sai kun riga shi mutuwa. ‘Yarka kuma da kake magana akai, tunda ta zama matarka, dadironka sai ka kwashi kayanka ku fice mani daga gida. Idan ka sake shigo mini gida, zan baka mamaki Wallahi! Ni nasan wani irin mataki zan dauka akanka, don sai kare ya fika daraja!”

Bai sake shi ba, sai da ya jawo shi kamar tsumma ya watso shi waje sannan ya kwalawa mai gadi kira.

“Kai mai gadi. Idan ka sake barin wannan sakaran! Ya shigo mini gida, ka tabbata sai na hada da kai da shi na saka an rufe mini ku a dakin duhu, sai arzikinsa ya fito da shi.”

Alhaji Bako dai sai zazzare idanu yake yi. Tunda yake ba’a taba muzanta shi ba, irin na yau. Gaba daya Zayyad ya karya duk wani jijji da kansa, da kuma barazanarsa.

Zayyad yana gama maganarsa ya koma ciki ya rufe kofarsa. Samha kuwa da ta ji hayaniya, ta fito bata ga kowa ba, sai ta wuce dakin Zayyad. A lokacin ta kwaso hotunan da ta ajiye masa a drower ta dawo da su falo tana sake kallo. Ta barbaza hotunan, hakan yasa Zayyad yana shigowa, ya ci karo da fuskar Shugaban kasa da Abbansa, da kuma Alhaji Bako, dukkansu suna dariya, rike da jariri a hannu.

Da sauri ya karaso ya dauki hoton jikinsa yana wani irin rawa.

“Abba yasan Alhaji Mamman?”

Zama ya yi yana sake kallon hoton

“Ina kika samo hotunan nan?”

Ta dube shi sosai sannan ta ce,

“Tun ranar da na shiga dakin karatun Abba, anan na kwaso.”

Ya jinjina kai, tare da saka hoton a aljihu. Yana sauri zai fice, ta riko hannunsa. Idanunta cike da hawaye take girgiza masa kai,

“Tunda ka dawo baka huta ba, kake haduwa da abubuwan rudani da tashin hankali. Don Allah ka da ka fita yanzu, ka yi hakuri ka bari sai gobe. Babu abin da ya fi karfin Allah. Kayi addu’a.

Bai yi musu ba, ya dawo ya zauna kawai yana wani nazari.

Haka suka kwana hankali a tashe, don ma Samha ta matsa masa ya tashi sun yi Sallar dare, suka yi ta karatun Alqur’ani. Tabbas ya sami natsuwa, ya sami sanyin zuciya. Sai sai labarin da shugaban kasa yake bashi labari ne akan mutane ukun cikin hoton da ke hannunsa. Yana bukatar tambayar mahaifinsa kafin ya karasa wurin shugaban kasa.

Da safe bayan ya shirya ya karya, yana fitowa falon ya sami Sakina. Tana ganin shi ta zube kasa tana kuka tana bashi hakuri. Bai ce komai ba, ya wuce abinsa. Samha kuma ta zauna tana canza tasha tana satar kallonta.

Ta taso a fusace ta rike kugu.

“Uban wa kike harara?”

Samha ba ta tanka mata ba, ta ci gaba da latsa remot. Ta fizge ta kwada shi da kasa.

A nan ma sai ta tashi kawai ta shige ciki. Gaba daya tausayi ta ba ta shiyasa ba ta tanka mata ba.

Shi kuwa Alhaji Bako ya kasa barci, maganganun da Zayyad ya gaya masa ya tashi hankalinsa. A hankali kalaman boka suka dawo masa rai,

“Zai haifi yaron da zai gagareku, zai haifi makashinku. Duk runtsi kada ku bari ya gano waye mahaifinsa, shi ne kadai rufin asirinku.”

Gabansa ya sake faduwa. Yana tuhumar kansa meya sa don ransa ya ba ci, zai rubuta abin da zai iya dawo da shi hayyacinsa, kuma ya aika masa har ofis? Yanzu da ya gani fa? Ko da yake ba zancen mahaifinsa ya yi masa ba.

Ya zama dole ya je wurin Alhaji Salisu.

Kai tsaye Zayyad ya nufi gidan Alhaji Salisu.

A lokacin Alhaji Bako ya riga shi isowa, don haka yana jin yadda ake daga murya kamar ana fada, a babban falon bakin gidan.

Da sassarfa ya shiga.

“Abba!”

Ya kira sunansa. Hakan yasa duk suka juyo a rude. Ya karaso ko kallon Alhaji Bako bai yi ba. Ya zaro hoton ya mika masa.

“Abba mene ne alakarka da Alhaji Mamman? Meya sa ko da wasa baka taba gaya mana kana da wata alaka da shi ba? Meya sa a baya da aka zabeni a matsayin wanda zai duba lafiyarsa, ka nuna mini kai sam! Baka amince ba? Meya sa? Akwai tarin tambayoyin da ya kamata ka warware mini su. Meya sa na taba auren Sakina a baya, a yanzu ma kuka sake barina na aureta? Kuna nufin mance rayuwata ta baya shiyasa kuka sami damar da zaku yi wasa da ita a yanzu? Dole akwai wani abu da kuke boye mani. Babu wani uba na gari da zai amince ya hada jini da mutum irin Alhaji Bako. Yanzu wani abu ya dawo mini cikin zuciyata. Yadda kake takatsantsar da Nura da Sharifat baka yi da ni. Ko dai ba kaine ka haifeni ba?”

Alhaji Salisu ya wanke Zayyad da mari jikinsa yana kyarma.

“Ya isheka haka Zayyad! Ban yi lalacewar da Dan da na haifa zai dinga zuwa yana gaya mini duk maganganun da suka fito daga bakinsa ba. Idan bani na haifeka ba, me zai sa ka rayu da ni? Me zai sa in soma in fifitaka fiye da kowa? Don ka ga hotona da Alhaji Mamman sai me? Akwai abokaina dubu da na dauki hoto da su, meya sa baka taba tambayana akansu ba? Sai Alhaji Mamman? Saboda ya fini arziki? Da talaucina na rikeka na reneka har ka zama abin da ka zama a yanzu. Kuma na hanaka kusantar Alhaji Mamman ne, saboda bana son kana shigewa masu kudin nan ‘yan siyasa saboda na fika sanin illarsu.”

Zayyad ya kalle shi cike da rashin yarda.

“Idan wannan ne dalilinka, meya sa wancan shugaban kasan da ya sauka, baka hanani shiga jikinsa ba? Idan kudi ne da arziki wanda ya sauka ya fi Alhaji Mamman. Meya sa a lokacin kokari ma kake yi ka ga na shige jikinsa?

Alhaji Salisu duk sai ya rude ya gigice. A lokacin kiran waya ya shigo wayar Zayyad. Ya zaro wayar bai daina kallon mahaifinsa ba. Ya daga.

“Dokto Zayyad ka yi sauri ka zo, jikin mai girma shugaban kasa ya tashi, kuma sunanka kawai yake kira.”

Shi kansa bai san lokacin da ya fice ba, ya shige motarsa a gigice.

Alhaji Salisu ya dawo da dubansa kan Alhaji Bako.

“Ka gani ko? Shikenan asirin mu ya tonu. Sai mu jira hukuncinmu tun a duniya.”

Alhaji Bako ya yi ajiyar zuciya,

“Asirinka dai ya tonu ba nawa ba. Ni bana sarewa! Zan je innemo dukkan mafitar da zan nema. Ko da kuwa na raba Zayyad da numfashinsa ne.”

Alhaji Salisu ya girgiza kai,

“Ni bana son ka kashe shi gaskiya. Ina son yaron. A dai yi wani abu amma ban da kisa.”

Alhaji Bako ya zazzaro ido,

“Ko ‘yata da na haifa idan na ga zata bani matsala zan rabata da duniyar, bare kuma wanda babu abin da na hada da shi. Ina da tabbacin idan ya je ya zakulo komai, mahaifiyarsa zai koma nema. Ni kuwa duk wanda zai tunkari wannan dole ya bakunci lahira.”

Shi kuwa Zayyad ikon Allah ne kadai ya kai shi gaban shugaban kasa. Ya same shi yana ta barcinsa. Ya jawo likitan da ya bari a wurin yana tambayarsa.

“Meya faru ne?”

Ya girgiza kai,

“Ka bari kawai yallabai. Mun ga tashin hankali. Jijjiga ya dinga yi yana kiran sunanka. Ina ganin a shawara ka daina yin nesa da shi, har Allah ya bashi lafiya. Muna murna aiki ya yi kyau, kuma sai ga tashin hankali.”

Ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba.

A bangaren Samha kuwa, yana fita itama ta fice. Sakina tana ta mamakin irin wannan zaryar da Samha take yi.

Kai tsaye tsohon kangon da suka yi rayuwa ta nufa. Haka kawai take jin kewar mahaifiyarta. Ta kwantar da kai tana kuka. Ta dinga shure File din ba tare da ta kula ba. Babu wani abu da aka taba masu. Komai yana nan yadda suka barshi. Abin har mamaki ya dinga ba ta.

Sai can tabar wurin ta dawo gida. Sakina ta samu a falon tare da wani yaro kamar za ta shige jikinsa. A firgice ta waiwayo tana duban Samha.

Samha ta karaso falon tana zare idanu,

“Me zan gani haka?”

“Abin da idanunki suka nuna maki.”

Sakina ta ba ta amsa tare da mikewa tana jijjiga.

“Kai tashi ka fice a gidan nan tun kafin in sauke maka haukan da ke kaina.”

Sakina ta zabura,

“Na fi ki zama mahaukaciya. Ba zai fita din ba, idan kuma kin isa ki zo ki fitar da shi.”

Samha ta dubi Sakina,

“Ki kyale shi ya fita! Wallahi idan bai fita ba, sai na baki mamaki yau dinnan.”

Sakina ta ware idanu,

“Ubanki ma ya yi kadan bare kuma..”

Ji ta yi an wanke fuskarta da wani irin mari, kafin ta dawo hayyacinta ta sake jin saukar wani marin. Kafin tasan abin yi, Samha ta yi kukan kura ta fizgota ta watsar a kasa. Kafin ta damko yaron, har ya ruga da gudun gaske ya yi waje.

Samha ta wuce daki ta bar Sakina a wurin tana kuka rike da kugunta.

Ta dauki waya ta kira Babanta. Bayan ta gama kora masa bayani ya ce,

“Ke dalla kin dameni da tsinannan korafi. Kin isheni Sakina. Wannan ‘yar tatsitsiyar yarinyar ce za ta tsaya tana dukanki ke kuma kina kuka? Mtsww..”

Ya katse wayar. Sakina ta bi wayar da kallo, kafin daga bisani ta rushe da kuka.

*** ***

‘Yan sandan da suke kula da shugaban kasa, suka zo wurin Zayyad.

“Ga ‘ya’yan shugaban kasa suna son ganinsa.”

Zayyad ya mike fuska a daure ya fito. Mufida ce da Walid suna tsaye cikin wata shiga irin ta marasa kirki. Ya harde hannayensa a kirji yana dubansu a wulakance. Duk rawar kai irin na Walid sai da Zayyad ya yi masa kwarjini.

“Ina ji.”

“Mun zo duba Daddy ne.”

Walid ya bashi amsa. Sai da ya dan jima yana dubansu sannan ya ce,

“Ba zaku samu damar ganinsa yanzu ba. Idan ma za a iya ganinsa kila sai nan da kwanaki uku insha Allahu.”

Mufida ta ware idanu ta ce,

“Har da Mommy?”

Ya sake tamke fuska ya ce,

“Koma waye.”

Ta yi shiru tana kallon Walid. Kafin daga bisani suka juya suna kananan maganganu. Har suka bace bai daina kallonsu ba. Shi mamakin ma da abin ya bashi, yadda ko keyar matarsa Hajiya Ramatu bai taba gani a wurin ba. Ya yi ajiyar zuciya ya koma ciki.

Yana nan zaune a gabansa ya kafe shi da idanu, yana jin wani abu akansa. Bai san meya sa ba, da ya kalli Walid ya ji karin faduwar gabansa. Domin Walid yana dan dibar kamanni da shi. Shugaban kasa yana farkawa ya zubawa Zayyad idanu. Bai ma san ya farka ba, saboda dogon tunanin da ya afka.

“Zayyad…”

Da sauri ya waiwayo sai kuma ya nufe shi yana masa sannu.

“Zayyad Sallah zan yi.”

Cikin natsuwa yake kare masa kallo. Akwai wani tabon Allah a bayan kunnensa, wanda shi ma Zayyad yana da irinsa. Jikinsa ya yi sanyi. Sai dai ya kasa gano ta yadda hakan zai yiwu.

“Ok. Bari in kawo maka roba sai in yi maka alwalar.”

Ban daki ya nufa ya kawo masa komai. Anan ya yi masa alwalar sannan ya jingina shi da filo yana kallon alkibla.

Bayan ya idar da Sallar ne ya kafe Zayyad da idanu. Zayyad ya dukar da kai kawai yana wani tunani.

“Zayyad..”

“Na’am Daddy.”

“Hajiya Ramatu ba ta zo ba ko?”

Ya jinjina kai.

“Amma Mufida da Walid sun zo dazu.”

Ya yi shiru.

“Allah ya jikan Hajiya Farida, da ita ce da sai dai ta kwana a bakin kofar nan.”

Ya dan dube shi. Kamar zai tambaye shi wace ce ita, sai kuma ya yi shiru.

“Zayyad ranar ina baka labarina da aminaina bamu gama ba ka dakatar da ni.”

“Hakane Daddy.”

“Na fada maka mu uku muka taso. Muna son junanmu sosai. Sai wata kaddara ta gifta. Na kamu da son wata yarinya mai suna Farida. Ban taba fada mata ba, sai watarana na daure na aiki wani yaro ya sanar mata. Da ni da abokaina bamu boyewa juna komai, amma ni sai na zabi in boye soyayyata da Farida. A ganina zan yi masu bazata. Ashe ban sani ba, Daya daga cikin abokaina shima yana sonta. Bako shi ne mafi soyuwa a cikin abokaina, sai na ukun mu Salisu. Tashin farko Bako ya aika iyayensa, wanda ni ban aika kowa ba. Anan aka tsayar da lokaci. Aminina Bako yana son Farida fiye da zaton mai zato, haka nima ina son Farida.

A lokacin da Farida ta fito ta gayawa Bako ga wanda take so, ta kuma gayawa iyayenta, sai matsaloli suka yi yawa. Daga nan abotarmu ta fara samun tangarda.

Ina kwance a dakina Bako da Salisu suka shigo babu ko sallama. Babu irin zagin da basu yi mani ba, suka kirani maci amana, nasan Bako yana son yarinya na zagaya. Zan ga abin da zai faru muddin bako bai mallaki yarinyar nan ba.”

Shugaban kasa ya dan yi, shiru idanunsa suka cika da kwalla. Jikin Zayyad yana rawa ya ce,

“A’a Daddy ka bar maganar nan har ka warke sosai, ka ga aikin da muka yi maka baya bukatar damuwa.”

Shugaban kasa ya girgiza kai,

“Idan ban fada maka ba Zayyad aikinku zai iya tashi a banza. Gwara in gaya maka ko zan sami sassaucin abin da ke damuna shekara da shekaru.”

Zayyad ya lumshe idanu yana jin karin tsanar Alhaji Bako.

“Da kaina naje na gayawa Farida na hakura da ita. Amma hakan bai yiwu ba, domin Farida kwanciya ciwo ta yi, kamar za ta mutu. Iyayenta da kansu suka zo suna rokona akan kada su rasa diyarsu. Ni kuma na yi gudun lalacewar abotarmu, don haka na ki amincewa, har sai da aka danganta da mahaifina. Mahaifina ya kirawo Bako da Salisu da ni, ya yi mana nasiha akan kada mu yarda mace ta raba mana zumuncinmu. A yadda na ga sun fita, na gane sam! Nasihar mahaifina bai ratsa su ba.

Haka aka yi bikina da Farida babu yabo babu fallasa.

<< Miskilin Namiji 18Miskilin Namiji 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×