Skip to content
Part 9 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Suna fita Zayyad ya dago ya watsawa Sakina kallon tsana. Jikinta babu inda baya kyarma.

Suna fita wayar Zayyad ta fara neman agaji. Dr. Ramatu ce, dan haka ya dauka suka gaisa.

“Ina kanwata bani ita mu gaisa.”

Ya dubi Samha ya mika mata waya,

“Antinki ce.”

Ta karba da sauri ta saka a kunne tare da yin waje da wayar suna gaisawa. Umma tabi ta da kallo ta ce,

“Ga dakuna nan dole sai ta fita waje ne? Daka nuna mata dakin Sharifat ai.”

Ya girgiza kai,

“Umma kyaleta kawai.”

Samha suka yi ta hira da Dr. Ramatu. Take tambayarta ko akwai matsala? Ta girgiza kai kamar tana ganinta,

“Anti babu matsalar komai. Ya wurinsu Baba?”

Dr. Ramatu tayi murmushin jin dadi,

“Duk suna lafiya. Amm… Samha kashe wayar ana kirana zan sake kiranki anjima.”

Suka ajiye wayar a tare. Sai a lokacin kunnuwanta suke jiyo mata kalaman Alhaji Bako.

“Kasanni kasan halina ko? Kasan babu abinda bazan iya ba, tunda nayi sanadin loosing memory din Zayyad babu abinda bazan iya aikatawa ba. A cikin mintuna kalilan zan iya zama sanadin da zai dawo ya tuna rayuwarsa ta baya, ta yadda wasan zai tashi da mu dukka. Kai kasan da ba dan rasa tunaninsa na baya da yayi ba, da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Domin kuwa maganganun da ya nada akansa da tuni ya gayawa duniya. Ka bini a hankali Walh.”

Alhaji Salisu ya kama hannunsa,

“Kayi magana a hankali mana. Nace kayi hakuri mu bar zancen nan. Na amsa laifina kuma a shirye nake da na gyara. Dan Allah kabar maganar ba tar da Zayyad Wallahi banason wani abu ya sameshi. Yaron da ya mance duk wata rayuwarsa ta baya me zai baka tsoro da shi kuma a yanzu?”

Alhaji Bako yayi masa mugun kallo, kasancewarsa kafaffe, ga mita.

“Ka mance likita ya gaya mana zai iya tuna komai, musamman idan ya tuna abubuwan karshe da ya ji kafin gushewar tunaninsa?”

Alhaji Salisu ya gyada kai,

“Na tuna. Amma tayaya zai iya ganewa? Ba zai taba iya tuna komai ba.”

Alhaji Bako ya shafi kansa yana sosa tsakiyar sankonsa bayan ya cire hular.

“Kai dai Allah ya kyauta. Na dauko files dinnan na shi waye, na kuma rubuta kalaman da muka yi ya ji, na karshe kafin gushewar tunaninsa. Duk na hada na aika masa asibiti. Ina tabba tar maka daga lokacin da ya gani, duk abubuwan da suka shige masa za su dawo. Kana ganin aikinsa na likitanci ne kadai bai mance ba. Tun ana tsoron barinsa akan aikin har aka kyale shi. Wallahi lokacin zuciya ce ta jawo mini aikata kuskuren nan.”

Alhaji Salisu ya dan yi shiru, daga bisani ya ce,

“Ya gaya mini maganar files din, amma kuma ai sun bace. Wata yarinya ta sace kuma har yau dinnan ba asan inda suke ba.”

Samha dai ba ta tsaya ta ji zancen files ba, amma ta ji daidai inda yake cewa akwai files da aka rubuta rayuwarsa da zai iya dawo da tunaninsa.

Ta rude kwakwalwarta ta kasa tuna mata cewa da wannan files din na wurinta ake magana.

Da sauri ta koma ciki jikinta yana rawa.

Zayyad kadai ya kula da yanayinta, bai ce mata komai ba, suka cigaba da ‘yar magana sama-sama da Umma.

Umma ta dubeta ta ce,

“Kiyi hakuri da abunda Abbanku yayi maki kinji?”

Ta kasa magana sai sunkuyar da kai kawai take yi. Sakina dai tunda mahaifinta ya fice aka daina yi mata kallon arziki. Duk ta muzanta a falon. Yadda Sharifat take yiwa Samha rawar kai, abin ya kona mata rai, saidai babu halin magana.

Kowanne ya tashi ya nufi inda zai yi Sallar isha’i. Zayyad kuma ya fice ya sami mahaifinsa yana shirin shigowa. A tare suka wuce masallaci.

Ita dai Samha jikinta bai daina rawa ba. Haka ba ta daina mamakin maganganun su Alhaji Bako ba. A lokaci daya tausayin uncle Zayyad ya dirar mata. Meyasa mutanan nan suke son mayar da gidan uncle Zayyad tamkar wani kufai? Yanzu dama wanda na aura baisan waye shi ba? Lallai idan hakane Zayyad yayi kyan kai, da yayi auren shekaru biyu. Da ace auren soyayya muka yi, da na shiga ukuna duk ranar da ya dawo tunaninsa ya ce bai sanni ba, baisan yadda akayi ya auri almajira kamana ba.

Kallon Sharifat ta yi ta ce,

“Dan bani Alqur’ani.”

Da sauri ta mika mata. Ta fara rera karatun Qur’aninta cike da kwarewa wajen fitar da hakkokin kowane harafi.

Baki suka bude suna kallonta. Sakina sai ta raina kanta, domin ki sallar ma da tayi cikin gaggawa ta dungara kai ta sallame.

Umma ce ta shigo domin ta gaya masu Zayyad yana kiransu. Jin karatun da Samha take rerawa sai ya burgeta.

“Idan kin kai karshe ku zo ku je gida yana jiranku.”

Ta juya tana mamakin a inda Zayyad ya samo yarinya mai kyau da tarin baiwar ilimi.

A falon ta kasa kallon Abba. Da yake ta riga Sakina fitowa, saboda ta shiga bandaki. Abba ya dubeta da fara’a ya ce

“Kiyi hakuri ‘yata. Dan uba yayiwa diyarsa fada ba wai baya sonta bane.”

Takaici ya kama Zayyad, ransa ya sake baci. Mahaifinsa gaba daya ya koma tsoron Alhaji Bako yake ji, a sabanin da can baya. Ya rasa dalilin irin wannan rawar jikin da kyarman da yake yi masa.

Haka suka yi masu sallama sannan suka wuce.

Sakina ta wuce sum-sum zata shiga gaban mota. Ya watsa mata mugun kallo kafin ya ce,

“A gaban motar kika zo? Ki koma baya ko kuma ki koma ciki Abban ya kawoki.”

Da sauri ta koma baya, a zuciyarta tana jin bakin cikin da ba ta taba jin irinsa ba. Yau ita ce wata can ta kwace mata gaban motar miji? Samha ta so ta qi shiga gaban, ganin ransa duk a bace yasa ta shiga kawai kanta a qasa.

A mota ya yi magana ba tare da ya dubi daya daga cikinsu ba.

“Akwai mai bukatan wani abu na ci?”

Da sauri Sakina ta ce,

“Fura nake so da gasassar kaza.”

Bai ce mata komai ba, sai hannunsa daya da ya saka ya kamo na Samha, ya kula tana cikin damuwa da tashin hankali. Ya dauka abinda Abbansa yayi mata ne yake damunta.

Sakina tana kallon yadda ya kamo hannun Samha yana murzawa, kasancewar ko a bayan ba ta zauna da kyau ba, gaba daya kanta yana gaban motar.

Tayi shiru tana nazarin tunda take da shi bai taba kama hannunta yana tuki ba, yau ga Samha ta zama ‘yar lelensa.

A gefen titi yayi parking ya fita yaje yayi siyayyansa sannan ya dawo da ledoji, kowacce ya mika mata nata. Suka amsa. Samha ta ce,

“Na gode.”

Ya jinjina kai. Ita kuwa Sakina buda ledojin ta shiga yi tana duddubawa.

Bayan sun isa gida Samha ta haura samanta. Wanka ta fara yi ta saka kayan barci masu kauri, sannan ta dawo falon tayi tagumi.

“Tayaya zata tunkari Zayyad da maganar nan?

“Assalamu alaikum.”

Firgigit tayi tana dubansa.

“Meyasa baki son cin abinci? Kina so ki rame ne ko?”

Ya dawo kusa da ita tare sa bude ledojin yana ciro kayan. Da kansa ya tafi kitchen ya dauko plate ya juye mata kajin.

Da kanshi ya dinga ba ta tana ci kadan kadan. Duk da bakinta babu dadi, amma cikinta yana bukatar wani abu.

Sai da ya tabba tar ta koshi ya ba ta sassanyar furar. Ta ji dadin shan furar kasancewar abu mai ruwa ne.

Shima ya dan ci kadan, sannan ya je ya wanke hannunsa ya ce mata,

“Zo mu je dakina.”

Babu musu tabi bayansa. Ji yake kamar ya rungumeta ko zai sami sasssauci a zuciyarsa.

Sakina tana labe ta windo tana kallonsu. Yadda yake yi mata kamar zai mayar da ita cikinsa. Har sun kusa shiga ya manneta a kirjinsa. Taso ta kwace kanta, idanunta suka hasko mata Sakina a window din falonta. Dan haka ta mayar da kanta ta kwantar tana sakin ajiyar zuciya. Ya sake manneta sosai, sannan suka shige. Ya rufe kofarsa da key.

Bandaki ya shiga ya sake wanke bakinsa, sannan ya dawo ya sameta tayi shimfida a qasa.

Ya girgiza kai,

“Akan gado zamu dinga kwana kuma a tare. Ni na gaya maki babu abinda zanyi maki.”

A zuciyarta ta ce,

‘A yanzu ne ma zan sake kama kaina, kada kayi mini wani abu ka dawo kace bakasan ka rabani da budurcina ba.’

Suna hawa gadon zata kwanta ya rikota suna kallon juna.

“Akwai abinda ke damunki. Fada mini menene.Yanzu dan Abba yayi maki fada sai ki daina walwala?”

Ta girgiza kai da sauri,

“Wallahi ba fadan Abba ne ya sakani hakan ba.”

Bakinta yana rawa hawaye kaca-kaca a idanunta ta ce,

“Wai… Wai ashe kayi loosing memory ne.”

Bai firgita ba, sai da ta labarta masa komai da ta ji. Ta boye masa wasu maganganun akan mahaifinsa, dan tana ganin kamar ba zai yarda ba.

Zayyad ya ware idanunsa. Cike da mamaki da al’ajabi.

Ya kasa zama takun tafiya kawai yake yi yana kaiwa da komowa.

“Tabbas nayi loosing memory. Amma kuma na gaza tuna ta yadda hakan ya faru. To amma meyasa Abba yake tsoronsa?”

Ta jinjina kai ta ce,

“Akwai wani sirri mai girma a tsakaninsu ne da yayi masa barazanar zai sanar da kai muddin bai yi masa biyayya ba.”

Hankalin Zayyad ya tashi kwarai. Dole ya koma ya zauna yana kokarin ganin ya matsawa kansa wajen tuna wani abu.

“Alhaji Bako shine wanda yayi sanadin da ka rasa tunaninka, sai dai bansan me yayi maka ba.”

“Na shiga uku! Wanene ni? Me yake faruwa da rayuwata?”

Sosai Samha take jin tausayinsa yana kwaranya a zuciyarsa.

Jawota sosai yayi jikinsa yana shafa bayanta. Yayi kamar yayi barci hakan yasa ta daina jin tsoron itama ta yi masu addua yana jin tana tofa masa, sannan ta rufe ido. Sassanyar kamshinta yana kara ratsa zuciyarsa. Ya rasa da wani irin humra Samha take amfani da har kamshinta ya zama na daban.

Duk da idanunsu a rufe suke hakan bai hana zuciyoyinsu shiga rudani da tashin hankali ba.  tunani ne iri-iri a cikin zuciyoyinsu.

Barci baro ya sace Samha. Dan haka ya raba ta da jikinsa ya koma ya zauna kawai rike da kansa. Tabbas sai yanzu ya tuna da lokacin da ya farka daga asibiti yake jin ana cewa ya rasa tunaninsa. Sai dai kuma a lokacin Abbansa yayi wani furuci, amaimakon shiga tashin hankali sai cewa yayi,

“Ahamdulillahi.”

Ya dade yana mamakin furucin mahaifin nasa.

Daga bayansa ya ji tayi magana,

“Uncle Zayyad inbaka wata shawara?”

Da sauri ya cira kai yana dubanta.

“Eh bani kanwata.”

Ta sakko da kafafunta, tana sake daure gashin kanta wanda tsantsinsa ya hana gashin zama a cikin ribom.

“Ka daina sakaci da Sallah. Ka dinga tashin dare kana salloli kana gayawa Allah damuwarka. Sannan ka dinga sadaka, kana azumtar litinin da Alhamis. Insha Allahu zaka samo mafita. Allah zai haskaka maka komai dan ka sani. Nayi alkawarin zan nemo takardun da suke dauke da abubuwan da za su dawo da kai tunaninka. Koda kuwa idan ka dawo hayyacinka zaka ce baka sanni ba.”

Ta karashe cikin damuwa. Sannan ta ce,

“Da sharadin idan na samo bazan baka ba, sai ka nuna mini inda mahaifiyata take kada itama kace ka mance wacece ita, bare har ka iya tuna inda take.”

Yarinyar tana bashi tsoro. Maganganun manya ne a bakinta. Hakan ya tabba tar masa da Samha tana tare da tsofaffi domin ta mori hikimar magana.

“Shekarunki nawa?

Ta daga kai kamar mai son tunawa sannan ta ce,

“Ina cikin na sha tara.”

Ya ware idanu. Bai zaci ta kai hakan ba.

“Kin taba zama da tsofaffi ne hala?”

Ta gyada kai sannan ta ce,

“Wannan innar da na kawo asibiti ina zama da ita sosai. Rashin lafiyar mahaifiyata da ya tsananta ne yasa muka dan rabu. Kuma mun zauna a wani gidan aiki ni da mahaifiyata. Na kara wayo da gogewa ne asanadin gidan. Kasancewar aikin kwana muke yi a gidan aka bamu mazauni. A can aka sakani Makaranta. Da na girma sosai ne lokacin ina babban sakandire mijin matar ya nuna yana sona. Allah ya tsare da yayi mini fyade. Shine matarsa ta koremu. Dama kuma na addabesu kullum cikin dambe nake da yaranta ina dukansu. Hatta masu gadi ban barsu ba, shakkana suke yi. Ta gane mijinta yana kokarin yi min wani abu ne, a wani dare da ya lallaba yaje har dakin mahaifiyata kasancewar tana da nauyin barci, ya toshe mini baki ya daukoni. ya kaini falon baqi. Yana kokarin aikata abinda yakeso. Duk karfi irin nawa Alhaji Mansur ya fini. Allah ya taimakeni matarsa ta taso tana nemansa, dan tayi mamakin inda yaje a cikin daren nan. Anna ta ganshi da ni yana ta kokarin cire mini kaya. Salatin da ta sakane yasa ya dago a razane. A ranar akayi yaqi sosai, ta dinga tsine mana ni da mahaifiyata. Nayi mamakin yadda har take ganin laifinmu. Da sassafe ta koremu daga gidan. Har yau ban sake haduwa da daya daga cikinsu ba. Bayan mun bar gidan na cigaba da zuwa makaranta dama kudin gaba daya ya biya mini. Sai da na gama Sakandire dina sannan rayuwar tayi mana wuya, Mama kuma ta kwanta ciwo saboda tsananin damuwa.”

Zayyad ya furzar da wani irin huci,

“Ta kuma kamu da ciwon zuciya ko?”

Ta dan kalleshi. Ba tayi mamakin furucinsa ba, domin tasan yana tare da Mama.

“Kada ki damu. Mahaifiyarki tana cikin koshin lafiya. Sai dai nasha wuya kafin na iya karbota daga hannun yaran Alhaji Bako. Ko da yake nima yarana na tura suka taresu. Na gode da shawarwari. Koma ki kwanta zanyi nafilfili ne.”

Ta sakko a hankali ta ce,

“Mu je zan tayaka nima.”

Sosai take sake shiga zuciyarsa. Bai taba tunanin zai iya yi mata kallon rahama ba.

Bayan sunyi alwala ne, suka yi nafilfili har raka’a goma sha biyu. Dukkansu suka dauki Alqur’ani. Suratul Arrahaman yace su bude. Yadda yake karatu yaso ya shagaltar da ita. Tayi mamakin yana da irin dumbin ilimin nan amma yake wasa da kusantar kansa da Allah?

Sai karfe uku da rabi na dare suka kammala. Suka yi addu’o’i masu yawa sannan suka shafa.

A jikinsa ya kwantar da ita yana shafa gadon bayanta. A haka barci barawo yayi awan gaba da su. Barcin yayi masu dadi. Shi kansa rabon da ya sami barci mai tarin natsuwa har ya mance. Lallai shigowar Samha cikin rayuwarsa alkhairi ne.

Washegari da wuri ya shirya ya tafi masallaci, ita kuma ta gaba tar da sallarta a dakinsa. Ba ta koma barcin ba, ta sake tsaftace masa komai. Kaya marasa kyau ta fitar da su. Sannan ta wanke masa kananun kayansa ta shanya. Ta wanke bandakin, ta kwashe robobin shower gel din da suka kare duk ta fitar da su. Bayan ta share ko ina, ta koma samanta ta hado masa kalolin turarukan wuta irin wanda ‘yar Borno take hadawa da kanta take saidawa. Turaren nan da ta saka kadan sai da ya zagaye ko ina na gidan da kamshi. Ba ta yi wanka ba, ta wuce kitchen din da Samha ta hanata shiga, ta hada masa lafiyayyen abin karyawa. Kasancewar babu abinda babu a kitchen din. ta jere komai a saman dining, sai dai ta dauke kayan Break dinsa ta kai dakinta ta rufe da key. Domin bazata iya barin abunda za su ci a kasa ba. Wannan ta barwa Sakina ne da kuma duk mai bukatar ci.

<< Miskilin Namiji 8Miskilin Namiji 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×