Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Mu Gani A Kasa by Fatima Sunusi Rabi'u

Abuja Nigeria.

Sanyayyiyar iskar damina ce ke kaɗawa a daidai lokacin, gari ya yi luf da ni’ima yayin da sararin samaniya ya yi fayau dashi gwanin burgewa da ban sha’awa. Tuƙi yake cike da ƙwarewa yana sharara gudu saman lafiyayyar kwaltar da ke birnin tarayya Abuja.

Ya yi tafiya me nisa kafin ya iso babbar unguwar tasu ta Asokoro. Wani katafaren gate ya dosa inda ya buga horn, da sauri Maigadi yazo tare da wangale mishi ƙaton gate ɗin ya kutsa hancin motar shi ciki. Sannu da zuwa Officer ke masa hannun shi kawai ya iya ɗaga mishi.

A cikin babban harabar gidan ne ya samu guri ya yi parking, kusan minti biyu kafin ya iya zuro ƙafarshi daga motar, ƙafar tashi mai sanye da ƙayatattun baƙaƙen takalmi sau ciki ce ya zuro a hankali kamar mai tsoran fitowa. A hankali kuma sassan jikin ya fito da shi, “Ma sha Allah” Ƙyaƙƙyawa ne ajin farko.

A hankali yake tafiya kamar mai tsoran takawa hannun shi ɗauke da ƙatuwar wayar shi yana duba saƙon da yaji shugowar sa tun yana tuƙi. Dan tsaki yaja ganin mai saƙon kafin ya zura wayar cikin aljihu ya doshi hanyar da zata sada shi da parlourn gidan. Da gudu ta taso tare da nufarshi da niyyar faɗawa jikin shi “oyoyo Yaya Aliyu!” Ta furta da tsantsar farin ciki. Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, chak ta tsaya jiki a matuƙar sanyaye. Ƙarasawa Yayi gaban Amminsa dake tsaye tana kallon abin da ke faruwa. Zaunawa yayi saman Cushin yana me duban Ammin tashi. “Barka da hutawa Ammi!” Ya furta cikin sanyi bazaka taɓa cewa shine yayi maganar ba, sakamakon laɓɓansa ne kawai suka motsa idan ma ba kusa dashi kake ba, ba lallai ne kaji me ya furta ba.

Wani kallo ta ma shi ba tare da ta amsa ba, ta mayar da kallonta ga yarinyar da ya nunawa ko in kula wacce ke tsaye kamar gunki har zuwa lokacin. “Sareenah tsayuwar ta isa haka, ko baki gaji da kallon nashi ba ne?” Cike da kunya tayi wani far! Sai ta juyo a sanyaye tare da zama gefen shi. “Abuturrab har yanzu halinka na nan ko? Ko ka mance wacece Sareenah a gareka ne?” Wuci ya fesar me zafi kafin ya ce”Ammi yunwa nake ji” Ya faɗa da nufin ɓangarar da wancen zan cen. Kallonsa take ko ƙittawa babu, wani murmushi ta saki wanda ita ce kawai tasan ma anarsa kafin ta kalli Sareenah “Ki kai mishi abinci part ɗin shi” “No Ammi!” Ya furta kamar zai yi kuka. “Ki kawo mishi anan” Girgiza kai yake amma ya kasa cewa komi sakamakon kallon da Ammi tayi mishi.

Tashi tayi a gurin yabi bayanta da kallo har ta ƙarashe hawa saman benen, sanyayyar ajiyar zuciya ya saki ƙirjin shi na wani irin bugu. Bai san time ya ɗan ja yana gurin zaune ba sai da Sareenah ta ƙara so tare da ajiye tray ɗin dake hannunta. “Yaya Aliyu ga abincin!” Ta faɗa tana ƙoƙarin zama gefensa. Da sauri ya miƙe yana jifanta da wani mugun kallo, ƙala bai iya ce mata ba ya miƙe tare da nufar ƙofar parlour. “Abincin fa? Ko na biyoka da shi part ɗinka?” Ta jero mishi tambayoyin a lokaci guda, juyowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata. Yana fita kai tsaye part ɗin sa ya dosa, komi fes-fes kamar yadda ya zata.

Kai tsaye bedroom ya wuce yana zuwa komi na jikinsa ya cire tare da faɗawa toilet, wanka ya yi ya ɗauro alwala sannan ya fito ɗaure da towul ɗaya a hannunsa yana goge sumar kan shi. Mirror ya nufa inda ya shafa maya-mayansa tare da feshe jikinsa da turaren sa mai daɗin ƙamshi, Ƙananun kaya ya saka dogon wando tare da riga t-shirt sai ya ɗora wata me kauri ta sanyi me haɗe da hula, sakamakon yanayin garin na sanyi.

Ya so ya huta amma kiran sallar ta Azahar da ake ƙwala kira a masallacin ƙofar gidansu ne ya sashi nufar hanyar fita daga badroom ɗin. Yana fita kai tsaye masallaci ya nufa.

Sareenah bayan fitarsa da gudu ta hau sama bedroom ɗin Ammi, tana shiga ta sami Ammin na waya da gudu ta ƙarasa tare da faɗawa jikinta ta saki wani kuka. Ba shiri Ammi tayi sallama da wacce suke wayar tare da sanar da ita anjima zata kirata. “Sareenah lafiya kuwa?” Ammi ta tambayeta bayan ta ajiye wayarta saman ƙaramar durowar dake kusa da ita. Cikin kuka wanda zallarsa shagwaɓa ne da sangarta ta ce “Ammi Yaya Aliyu ne! Mene ne na masa ya tsane ni haka?” Da sauri Ammi ta katseta ta hanyar ɗaura ɗanuatsanta saman laɓɓan Sareenah “Kar in kuma ji” Ammi ta faɗa tare da kawar da ɗan yatsanta kafin tacigaba da cewa”Shi har ya isa? Bai kai matsayin tsanarki ba Sareenah ki cigaba da shige masa kamar yadda na nuna miki a juri zuwa rafi dai, nasan dole wata rana tulu zai fashe.”

“Har zuwa yaushe ne tulun zai fashe Ammi? Kin san dai yarda Yaya Aliyu ke zuciyata!” “Ke dai Sareenah albasa ba ta yi halin ruwa ba, da tayi tabbas ba za ta yi yaji ba tun da har na ce miki haka to ki ɗauka mana, kin san ba na san ɓacin ranki” Ammi ta faɗa tana sharewa Sareenah hawayen dake zuba a fuskarta. Numfashi ta sauke tare da lafewa jikin Ammin tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, sannan tasan wacece Ammi bata faɗin ƙarya sai abin da ke ƙasan zuciyarta.

Fitowarsa daga masallaci ba ɓata lokaci ya ɗauke key ɗin motarsa, cikin tafiyarsa ta alfarma ya doshi harabar gidan, tun daga nesa ya dannawa motar key ta buɗe yana zuwa ya faɗa ciki tare da kunnawa. A ɗari ya fita gate ɗin gidan daman tuni Maigadi ya buɗe masa tun lokacin da yaga ya doshi motar.

Wani gidan abinci ya nufa na manya sai wanda ya amsa sunansa ke cin abinci a gurin. “Barka da zuwa ƴallaɓai” Wata murya siririya ce tayi maganar. Bai ɗago kan shi ba, tun bayan zamansa saman kujerar haka jin maganarta bai sa shi jin zai ɗago ba, duk kuwa da jin bugun zuciyarsa da ya tsananta. “Me kake buƙata?” Maganar ɗazu ta ƙara ratsa masarrafar sautinsa, bai ce ko ci kanki ba wata farar talarda ya ga an ajiye mishi, sai lokacin ya kai idanuwansa kan takardar, abinci ne da nasha da dangin na ƙwalama kala-kala rubuce a jikin takardar. Pen ya ciro gaban rigar shi tare da making abin da ke buƙata tare da ture takardar da baya jin zai iya magana miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi.

Ta ɓangarenta kuwa tun bayan parking ɗinsa Madam (Shugabar gurin abincin) Ta ce”Ke Tataah ga kostoma nan jeki gurinsa” Cikin sanyinta ta miƙe tana tafiya slow kamar yadda take, daidai zamansa ta ƙarasa tare da tambayarsa abin da yake buƙata. Jin shuru ta ɗago idanuwanta ta dubesa, gabanta taji ya bada dammm! Haka ta daure ta kuma tambayarsa cikin sanyi amma bai bata amsa ba sai ta saka mishi takardar tana mai jin haushi a zuciyarta sakamakon ko in kula da ya nuna mata. Ganin abin da ya yi a ranta ta ce”Uhmm! Masu abu da abin su, tabbas a rashin kira karen bebe ya ɓata” Tana duba irin wannan izza da girman kai na wannan mutumin.

Lokacin da Madam ta ce taje tsoro ne ya fara ɗarsar mata sakamakon yadda ƙadangarun bariki ke kai mata haushi a gurin, tana tsananin tsoron zuwa tambayar abin da masu sayen abinki ke buƙata saboda wasunsu maganar banza suke mata, a kallon farko ta ɗauka shima hakanne musamman da ta ganshi matashi sai ta fuskanci maganar nan ta kowa da halinsa amma wannan kuma girman kai ke damunsa, da wannan tunanin ta ɗauki takardar tare da nufar gurin Madam ta miƙa mata. Kome da ya buƙata aka haɗa masa tare da ba Tataah ta kai mishi, tsaye tayi a gurin tana kallon yarda yake danna wayarsa bai damu da kallon kowa dake gurin ba.

Jin tsayuwar mutum kuma ba a ce komi ba ya saka shi ɗagowa a hankali, idanuwansu ne suka gauraya da na juna, sauran kaɗan tiren hannun Tataah ya sunɓule saboda tsorata da tayi da yadda da tsinci gabanta na dukan tara-tara. Da sauri ya saka hannun ya amshi Tray yana jan dogon tsaki duk da shima yaji shock a haɗa idanuwansu amma ba zaka taɓa gane hakan ba.

Wani banzan kallo ya aika mata da faɗin “Nonsense ba ki da hankali ne za ki ɓata ni?” Da sauri ta juya tare da barin gurin.

Duk bayan saƙon ɗaya sai yaja tsaki jin zuciyarsa ya yi sam babu daɗi, yunwar da yake ji ne yasa shi buɗe abincin ya fara ci, amma da ya tuno fuskarta sai yaja tsaki da haka ya cika cikinsa, Drink ya ɗauka yana sha a hankali yana amsa wayar da ake ta kiransa tun ɗazu. “Aliyu ka shigo ne?” Abinda aka faɗa daga can ɓangaren kenan, sai da ya kurɓi lemunsa ya haɗiye sannan ya furta “I, akwai wani abu ne?” “Ɗan renin wayau, mu muna nan muna jiranka kana shanya mu!” Robar lemun ya ajiye tare da cewa “Faruuk bacci zan yi” Ƙit! Ya katse kiran daidai miƙewarsa.

Gurin biyan kuɗi ya dosa tare da barin gurin cikin sauri.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.