Kabiru ya jinjina kai ya bar wurin yana jin wani abu a cikin zuciyarsa.
Husna tana zaune shiru kamar ba amarya ba, ta ga Gwaggo ta shigo da M.Y. bata ɗago ba, bata kuma tashi ta fice ba. Jin ankira Salma yasa ta gyara zama don ta ji abin da za a gaya mata.
Nasiha Gwaggo ta yi mata irin na amare, sannan ta ce ta tashi ta bi M.Y yau zai bar garin kasancewar ya sami kiran gaggawa.
Salma ta ƙanƙame Gwaggo tana kuka. Husna ta yi saurin miƙewa jikinta yana kyarma, sai dai kuma kukan Salma ya ratsata sosai. A sanyaye ta ce,
“Gwaggo kika ce anan za abar Yaya Salma, yanzu kuma ancanza ne?”
Gwaggo ta sharce hawayenta ta ce,
“Eh ancanza. Babban mutum muje akaita mota.”
Husna tana ji tana gani M.Y ya sanya Salma a cikin motarsa suka wuce. Anan tsakar gidan ta fashe da kuka mai cin rai. Tana jin shikenan Salma ta Shiga wata rayuwa mai wahalar fassara. Shi kenan daga yau baƙar ƙaddarar Salma zai fara… Ina ma zata iya aikata wani abu, da bata amince ta zuba idanu anɗauki Salma ankaita cikin mata marasa kirki kamar su Anti Salima ba.
A ranar daga ita har Gwaggo haka suka zauna sukuku kamar marasa lafiya.
*****
Sai ƙarfe ɗayan dare, M.Y ya sami shigowa cikin gidansa cike da gajiya. Abin mamaki duk sunyi cirko-cirko suna kallonsa. Shima idanun ya ware ya ce,
“Me ya hanaku barci?”
Bilki ta yi tsalam ta ce,
“Abin da ya hanaka shi ya hanamu.”
Murmushi ya sakar masu, wanda iyakarsa fuska. Ya wuce ɗakinsa yana zare kayan jikinsa cike da tunani kala-kala.
Salima ta biyo shi a fusace tana jin yau sai anyi wacce za ayi.
“Ina amaryar? Ta tambaye shi tana shirin fashewa da kuka.
“Baki da lambarta ne? Sai ki tambayeta inda take. Idan ƙorafi zaki yi min don Allah ki fita.”
A yadda ya yi maganar yasa dole ta shanye ɓacin ranta tana jin ba ta haka ya kamata ta biyo masa ba. Idanunsa cike da barci ya haye gadon. Saboda ƙwayoyi da Jamilu ya bashi yasha tuni sun fara aiki.
Salima ta fito a fusace tana duban sauran,
“Ance da Amaryar ya zo amma kinga shi kaɗai ya shigo nan. Ina ya kaita?”
Bilki ta yi carab ta amshe,
“Idan ya kawota gidan nan a ina zai ajiyeta? Kina ganin ko gyaran bangaren da amarya zata zauna bai yi ba. Kinsan Wallahi namiji munafuki ne, tunani nake yi ya kaita ɗayan gidansa na Unguwar rimi.”
Salima ta dafe ƙirji da ƙarfi,
“Danƙari! Wallahi bai isa ba. Bilki ke ce babba, ki je ki tada masa hankali ya tashi ayi duk yadda za ayi a daren nan.”
Bilki ta ɗan yi tunani, a wannan karon ta fahimci Salima tsaf! Zigata kawai take yi. Don haka ta ɗan karkace ta dubi Amina,
“Ke Amina kece har yanzu kike gaban goshi jeki ki jiyo mana ina amaryar take.”
Babu musu ta kama hanya ta shige ɗakinsa. Yana barci tasa hannu ta tashe shi. Ya buɗe idanu da ƙyar yana dubanta. Sai ta juye masa sak! Yarinyar da ya kasa manceta daidai da sakan ɗaya. Hannu yasa ya jawota gaba ɗaya ta sami makwanci a ƙirjinsa. Wasu abubuwa da yake yi mata shi ya ruɗata jikinta har rawa yake yi. A wannan dare Amina ta sami gamsuwa irin wanda bata taɓa samun irinsa ba. Da farko tsoron su Bilki yasa ta tafi inda suka turata, amma a yanzu tana gode masu da irin wannan dama da suka bata. A ƙalla sun kwashi awa guda, suna nunawa juna irin kewar da suka yi. Wanda shi baya cikin hayyacinsa sosai, harda ƙarfin ƙwaya ya taimaka masa.
Su Salima kuwa kowacce ta gaji da zaman jiran Amina har suka fara gyangyaɗi. Can Salima ta yi firgigit tana duban agogo. Ƙarfe biyu har da ‘yan mintuna. Ta ɗan taɓa Bilki ta ce,
“Ko dai Amina ta wuce ɗakinta ne?”
Duk suka yi shiru, zuwa can Salima ta nufi ɗakin M.Y Bilki ma ta rufa mata baya. Amina suka gani tana rungume a jikin M.Y
Da ƙarfi Salima tasa Salati. Firgicin Amina ya fito fili, domin bayan ta mayar da kayan jikinta sai ta ji tana da buƙatar kwanciya a gefen mijinta ta shaƙi ƙamshinsa tunda ta daɗe rabonta da hakan. Bilki ta yi kukan kura ta fizgota sai gata a ƙasa.
M.Y ya buɗe idanunsa da ƙyar ya dubesu. Gaba ɗaya gizo suke yi masa, dole ya mayar da kansa ya kwanta. Yana jin suna dukanta suna cewa ta yi satan kwana, amma bai da ƙarfin tashi bare ya ɗau mataki. Gaba ɗaya jikinsa ya ƙarasa mutuwa.
Duka sosai suka yi mata har sai da suka kumbura mata gefen baki.
Da asuba ya farka, sannu a hankali ya tuna duk abubuwan da suka faru a daren jiya, don haka ya yi saurin barin gidan gudun ma su ganshi su sake tada wata fitinar.
Duk inda Jamilu yake yana da buƙatar ganinsa domin ya ƙara masa ƙwayar. Jiya damuwa ce tasanya shi sha, a yanzu kuma damuwar ta sake dawowa.
Salima ta fara shigowa ɗakinsa sai taga babu kowa. Ta ƙara zabura. Anan suka yi ta masifa suna ƙarawa. Kiran duniyar nan sun yi masa a waya amma yaƙi ɗauka. Amina kuwa ta kasa fitowa, saboda tsoron abin da zai sake kaiwa ya dawo. Taso ta sanar da iyayenta, sai dai tasan fadan zai yi tsanani ne, ƙarshe M.Y ya ɗora mata laifi. Dole ta kama kanta, dan tasan dole su ji zafi. A can kasan zuciyarta kuwa farin ciki take yi mara misaltuwa.