A gaban Zainab da na samu falon Mama nadire dan kwandon na ce “Ga shi nan ki ci.”
Ta buɗe ta gani sai ta rufe ta ce sai anjima ta rage murya “To ya kin yi min aikin da na faɗa miki?
Na girgiza kai ina ɓata fuska ta ce “Ya dai? Na taɓa cikina “Ciwo yake min.”
Ta ce “Mu je Khadijah ce mai magani ki sha.”
Muka haura sama, tana nemar min maganin na faɗa toilet sai da na gama murɗe murɗe na na gyara jikina, don a farkon yi yana min roshing sosai. Ganin ban gamsu ba na tara ruwa mai ɗumi na ƙara yin wanka na janyo tawul na daura daga kirji zuwa cinyoyi, na wanke bra dina da na ajiye tun safe guda uku sai na fito na samu Zainab ta miƙo min maganin na ce ta bari in fara yin shanyar, wata yar ƙofa na fita wani ɗan corridor nan muke shanya kaya irin waɗannan na fara kenan na ji motsi ban damu da waiwayawa ba don tunanina Zainab ce sai da na gama na juyo Najib ne tsaye ya naɗe hannu idanuwansa kawai za ka kalla ka gane irin rikicin da ya faɗa.
Gaba ɗaya na diririce kirjina ya shiga harbawa ba tare da na ɗauki bokitin da na zubo kayan shanyar ba na bi ta gaban shi don ba yadda zan yi in wuce ya tare ko’ina.
Ina shiga ɗakin hijab na zura na haye gadon Zainab ta zo ta tsaya “Tashi ki sha maganin.” Kamar in yi banza da ita ai ta ga a yadda nake ta tura min dan’uwanta mara kamun kai da na rasa uwar da yake nema a wurina.
Na dai tashi ta bani na sha na kora da ruwa na koma na kwanta na dunƙule wuri ɗaya don wani sabon murɗawa da cikin ke min tare da mamakin matsawar da ciwon cikin ya yi min a wannan karon ko da yake min kaɗan yake yi.
Sai sannu take min a haka ya fito ya same mu ganin shi yasa na rufe idona ruf “Me ya same ta? Ya tambayi Zainab”Cikinta ke ciwo.” Ta ba shi amsa tambayoyi ya ci gaba da yi mata tana nuƙu nuƙun amsa mishi ƙarshe da kanshi ya ɗauko kwalin maganin da ta ajiye bisa mirror ya duba, “Tana fama da wannan lalurar za ki tsaya ba ta magani tayar da ita mu je hospital.” Ta taɓa ni na kauce “Ko za ka ɗan jira mu ya Najib ta shirya.” Ya juya ba dan ranshi ya so ba.
Ta ce “Tashi ki shirya ya fita.”
Na ce “Ba sai na je ko’ina ba, wannan ciwon shi za a tafi ma asibiti? A waya ta kira shi ta faɗa mishi abin da kenan, bai ce komai ba ta katse kiran.
Zaune na tashi sai na miƙe na isa wurin kayana wata doguwar riga milk color mai guntun hannu na sanya saboda ba ta da nauyi na rufe kaina da siririn gyale sai na dubi Zainab “Tashi mu je kitchen mu yi girki.”
Saurin ɗagowa ta yi daga kan wayarta “Kin ji sauki ne? Na ɗaga mata kai ta miƙe muka sauko zuwa kitchen, akwai komai don haka ni na fara aikin tana gefena tana mita “Matar can fa don baƙin hali hatta magin da take amfani da su ɓare su take don ma kar a gane waɗanne iri ne, haka ma spices, ki gano mana kalolin magin Bilkisu, ina son sanin sirrin girkinta mai shegen daɗi.” Kafin in yi magana Najib ya shigo da ledoji biyu a hannu, kusa da inda Zainab ke tsaye tana yanka cabbeji ya tsaya ya ajiye ledojin”Ga magani nan ta sha.”
Ta wanke hannunta sai ta fara buɗe ta farkon magunguna ne sai ta biyun da ita ce babba dangin fruit ne sai drinks sai chocolate masu tsada.
Ko suɓutar baki ta yi ta ce “Kai ya Najib mutum na fama da wannan ciwon ka kawo mishi kayan zaƙi.”
Ya ce “Me kika ce? Ta kama baki “Ba komai. Yau ba za ka Company ba? Ya girgiza kai “Jiya fa na dawo, hutawa zan yi.” Ta riƙe baki cikin nuna mamaki “Kai ɗin ya Najib kake wani hutawa yanzu dai za ka fara koyon zaman gida.” Bai amsa maganarta ba ya ce “Wai ita ƙawar ta ki ba ta magana ne? Ta ce “Tana yi lafiya ce da ba ta da ita.” Ta matso da ledojin “Ga shi Billy ya Najib ya sawo miki na ce “An gode.”
Suna hirar su ina aikin ina sauraren su can ya ce “Bari in je ɗaki,idan kun kammala mai girkin ta kawo min.” Zainab ta dube ni tana dariya “Kin ji Billy ya Najib ya ce in kin ƙare yana jira.” Shiru na mata ta matsa min sai na sha maganin na ce “Ni cikina ya daina ciwo.”
Har muka kammala girkin muka rarraba yadda na ga ana yi Zainab ta tafi kai ma Najib na ɗauki na Mama.
Sama muka fara hawa ta yi sallah ni kuma na gyara jikina muka sauko muka ci abinci sai santi take wai da ma haka na iya girki har na fi baba Talatu iyawa, don duk a waɗanda suka yi musu aiki ta fi su iya abinci mai daɗi, shi ya sa suka riƙe ta ta daɗe a tare da su.
Ni dai murmushi na yi jin zancen ta.
Ana yin la’asar na ce wa Zainab ta zo mu shiga kitchen musamman da yau Mama ke da Baba.
Maman ta ce “Haba ki huta Bilkisu kin yi na rana.” Na ce “A’a za mu yi.”
Sai da Zainab ta yi sallah ta same ni kitchen ɗin, tuwon Semo miyar kuɓewa ɗanya na yi niyyar yi sai na tuna a labarin Zainab na taɓa ji ta ce Baban su na son amala don haka da na yi musu tuwon sai na yi mishi amalar da na ga garin ta na leda.
Ina juya miyar wayata ta ɗauki ƙara,na ɗauko ta baƙuwar lamba ce na yi picking muryar Aunty amarya da na ji yasa na tuna ban yi saving din nombarta ba na fara gaishe ta ta ce in zo tana son ganina. Na ce “To.”
Da na sauke miyar na dubi Zainab cikin yar damuwa ta ce “Ya aka yi? Na ce “Maman su Ahmad ce wai in je tana son ganina.”
Ta ce “Ki je bari in sauke miyar.”
Na tafi a hanya na wuce Najib da ke tsaye ya zuba min ido, na taɓe baki.
A zaune na same ta a falonta wai girki ta kira ni mu yi na ce mai girki ba ta nan mu ke yi ni da Zainab.
Ta ce Ok.
Na koma na samu Zainab, sai da na shirya abincin Baba, Maman ta shigo ta ɗauka, muka dauki na mu zuwa falon Maman.
Rabi’ah da Ihsan muka samu zaune suna ƙusƙus Zainab ta ce “To iyayen gulma ga abincin ku can sai ku je ku ɗauko idan kun ƙare gulmar.”
Ihsan ta yi narai-narai da fuska “Kai Aunty Zainab ba gulma muke ba, Rabi’ah ce ke cewa ya Najib saboda Aunty Bilkisu ya ƙi fita yau duk inda kuka yi sai ya bi ku.”
Wani iri na ji jin zancen ta ga Mama na tahowa na yi maza na haye sama na bar su da Zainab, ko abincin ban sauko na ci ba sai dai ta same ni a sama da muka gama kuma na hau gado ta ce “Ba za ki sauka ƙasa a yi hira ba? Yau dai har Khadijah ta bar karatun ta zauna ana hira da ita.”
Na ce “Barci zan yi.”
Wata riga mara nauyi tsawonta iyaka gwiwa na sanya na hau gadon, tana zaune tana zaune a ƙasa riƙe da wayarta.
Idona na rufe na fara tunanin Babana wanda tunanin ya zame min jiki da na samu kaɗaicewa aikina kenan. Ƙamshin turaren da daga jiya zuwa yau na gane mamallakin shi ya shiga hancina,na ƙara rufe idona don jin takaicin wannan ɗabi’a ta shi ta shigowa ɗakin balagaggu a san da yaso, ko da ƙannen na shi su kaɗai ne a ɗakin.
Ban so su fahimci idona ban da haka da na janyo abin rufa na suturta jikina.
Zainab ta ce “Ya Najib wannan kwalliyar fa? Ya ce “Fita zan yi.” Ta ce “Ba ka ga kyan da ka yi ba.” Bai amsa mata maganar ba sai cewa ya yi “Ƙawarki har ta yi me, ba dai ciwon cikin ba ne? Ta ce “Ta ji sauƙi ta kwanta ne. Billy Billy ta shiga kiran sunana tana taɓa ni.
Na ƙara damƙe idona na ƙi motsi “Ta yi barci ya Najib.” Ina ji a jikina idonsa a kaina yake kamar in ta ƙwala ihu, “Kuke kwana a gadon nan bai muku kaɗan ba? Na ji ya tambaye ta ta ce “Bai mana ba haka muke kwana.” Ya ce “Ba sai ku yi wa Baba magana ba.”
Ta ce “Wai yi wa
ganin fa maganar yaran can fa gaskiya ce, yar gida za a yi ke da ya Najib.” Ta ƙarasa faɗi tana wata dariyar shegantaka gabana na ji ya buga wace ni mai aure huɗu reras da auren yaro ɗanye sharaf da bai wuce tsara ta.
Harara na galla mata ta ƙara kecewa da wata dariyar Allah kin ga ko yaya zai girme miki, don ba za ki wuce tsara ta ba shi kuwa kin gan shi ma sha Allah Baba ya iya kiwo in kin gan shi sai ki ce ya yi 30, ɗan lelen Baba ne shi kaɗai mishi ɗa namiji in ban da su Ahmad yan ƙanana, za ki ji daɗin ki abin ki sai a haɗa da namu kawai.”
Sai kuma ta dubi inda Khadijah ke karatu ta harari wurin sai ta rage murya “Duk waccan alhuda- budar ta ja min, ita kullum ina za ta karatu ina ta fito karatu, har tana tana gama digiri masters za ta jona.
Tsakanina da Allah ni aure nake so in ita ba ta yi a kyale ta ni a yi min, shi ya sa ban zaɓar wa kaina karatun da zan ta yi kamar cin ƙwan makauniya.”
Zaune na tashi jin zancen ta na jingina bayana da bango “Ikon Allah ke karatun ne ba ki so ni kuma a rayuwata ba abin da nake so irin karatun sai dai ban samu gatan yin shi ba.”
Ta jinjina kai “Lallai ma kina son karatun shi ne tun zuwan ki ba ki yi magana ba? Gobe za mu yi maganar da Mama ta yi wa Baba magana. A wane matakin karatu kike?
Na ce “To anan fa ake yin ta don iyakata Ss 2 ta ce “Ba damuwa ki zana jamb kawai da WAEC ki ci gaba da karatu.
Na ce “A’a dai da zan samu makaranta ta koyar da harshen turanci in kuma samu maimaita karatu ko na shekara guda ne saboda daɗewa ta rabona da karatun.
Ta ce “Ba damuwa nan kusa da mu akwai ta koyon turancin, idan kika gama sai ki samu lesson Class ki yi shi ma ko na shekara ne sai ki zana jamb din da WAEC.
Amma ita wannan makarantar Najib zan ma magana zai sanya ki in yaso sai ya faɗa wa Baba.”
Murmushi sosai na yi na shiga mata godiya har ta ishe ta ta kwanta ta juya min baya.
Shigowar saƙo a wayarta yasa ta kai hannu ta dauka sai kuma ta tashi zaune tana bubbuga ni “Kuɗi sun zo Billy, gobe za mu ziyarci Sallon a gyara mana kai da jiki da ma kaina sai ƙaiƙayi yake.”
Ba tare da na tashi ba na ce “Kuɗi daga ina?
“Sweetyna ya turo min, da ma wannan month ɗin Baba bai bamu kuɗaɗen da yake bamu ba.” Ni da ban san baban na ba su kudi ba na dai ce “An gode ma Sweety Najib.” Ta yi yar dariya sai ta gyara ta kwanta da haka muka yi barci.