Ana yin sallar asuba da na ga Zainab ta yi sallar ta kwanta Khadijah ma barcinta take don ita ma tana fashin sallar, take na canza rigar jikina na sauka ƙasa zuwa kitchen.
Na kunna gas har na sanya ruwa Mama ta fito ta ce “Ba ki gaji ba Bilkisu har kin fito? Na yi murmushi na soma gaishe ta ta amsa cikin fara’a. Indomie ta dafa wa yaran ni kuma na soya Irish da na samu an riga an fere.
Muna cikin aikin take gaya min ba yara kaɗai suka yi santin girkina ba har Baba ya ji dadin abincin.
Ban yi magana ba sai murmushi da na yi ta yi.
A maimakon Tea da ake sha kullum kunun gyaɗa na dama na zuzzuba a flasks wanda tunda na zo ban ga sun dama ba tun kuma da na ga waccan matar mai ƙonannen wayo ta dama ma Baba na san yana so ne.
Ina gyara wake zan markaɗa ta tambaye ni me zan yi da shi na ce ƙosai,ta kama baki
“Shi kenan kin gama gano abin da Alh ke so.”
Yaran suka soma shigowa suna karɓar abin karyawar su cikin shirin makaranta suna juyawa, Najib ya shigo a ƙarshe lokacin na fara soya ƙosan ya ce,
“Wow! Mama ƙosai kike mana? Ta yi murmushi tana nuna ni “Ka ga mai yi nan.”
Ya ce “Sai dai ba ta yi wa mutane magana yar taki.”
Ta yi ɗan murmushi “Tana yi mana.”
Na ce “Ina kwana? Ba tare da na waiwayo ba, kusa da ni ya ƙaraso har jikinmu na gogar na juna wai zai karɓi ƙosan, na dan matsa sai na ɗauki plate na zuba mishi, wurin karɓa idanuwanmu suka shiga na juna, ya yi kyau ƙwarai cikin wani lallausan yadi fari ga hula ta zauna a kanshi ya fita kitchen ɗin, Mama ma ta fita kai wa Baba.
Da na gama na ɗauki namu san da na shiga ɗaki na samu Zainab ta fito daga wanka Khadijah kuma na shiryawa.
Da na gabatar musu da abin karin Khadijah ta ce “Anya zan tsaya na kusa latti.”
Sai dai da ta ga Zainab ta tsiyaya kunun gyaɗar da ya yi fari tas don fulawar da na ɗaure shi da ita ta ce “Kunu har da ƙosai? A’a zan sha.”
A tsaitsaye ta karya tana yi tana duba agogo.
Da ta gama ta dire kofin ta fice.
Zainab ta ce “Na sha barci har ya Najib ya fice ban samu na yi masa ma muganar karatun naki ba ta janyo wayarta ta kira shi tana gama mishi bayanin ya ce ba damuwa.
Mu ma da muka gama wanka na yi Zainab ta ce in shirya mu tafi Sallon ɗin.
Ba mu fita ba sai sha biyu doguwar riga na sanya na kuma yane kaina da gyalen ta takalmi da jaka sababbi ne, zuwan mu Abuja da Hassan wanda muka dawo na yi ɓari suna cikin sayayyar da ya yi min.
Zainab ta ce sun yi mata kyau.
Bedroom ɗin Mama muka je da ba mu same ta a falo ba Zainab ta ce key din motarta za ta ara mata ta ce babu mai a motar, cikin jin haushi ta ce mu fita mu tari keke nafef.
Muna zuwa daidai kitchen na sheƙa a guje na shige Zainab tana me kuma za ki yi ban saurare ta ba na jiƙa shinkafar tuwo sai na fito muka jera zuwa waje, tunda na zo sai yau na fito sai da muka fita layin da yake shiru duk da akwai titi sai muka hau babban titi muka samu abin hawa,ta faɗi inda za a kai mu.
Sai kallon hanya nake ina tuna rayuwata a garin duk da ba a irin wannan Area na rayu ba, koyaushe zan ga Amir? Ban san ta inda zan soma zancen shi ba don bana tunanin a gidan akwai wanda Baba ya fadi ma na taɓa aure ma ballantana aje ga batun haihuwa.
Muka isa wurin wuri ne babba da sai matan da suka amsa sunan suke shiga wurin.
Ma’aikata biyu suka tare mu ta fadi abin da za a yi mana suka shiga aikin su.
Ana wanke min kai sai kallon gashina Zainab take ta ce “Kina da gashi mai yawa da tsawo Billy, da ace kina ziyartar Sallon ba ƙaramin kyau zai yi ba.”
Na ce “Ban zuwa ina dai iyakar nawa gyaran a gida.”
Ta ce “Yanzu za mu dinga zuwa koyaushe ana gyara mana.”
Na ce “Shi kenan.”
Sun wanke mana ƙafa bayan gyaran kan mun yi kyau sosai, ta biya za mu bar wurin wayarta ta shiga ƙara ba ta amsa ba sai da muka fita harabar wurin ta amsa “Ya Najib.” Ta fara faɗi
“Na dawo gida yanzu in ci abinci na samu kun fita.” Muryarsa da ta sa hands free ta kwararo daga cikin wayar.
“Kai ya Najib yaushe ka fara dawowa cin abinci?
Abincin da na ci na ƙawarki jiya sun yi matuƙar yi min daɗi har na yi oder abinci na kasa ci, kawai na taho kuma ba ku nan.”
Muka haɗa ido na gwalo ido ita kuma tana danne dariyarta.
“Kuna ina?
“Sallon muka je ya Najib.”
Ku jira ni, zan zo yanzu in mayar da ku gida.”
“Ka bari ya Najib,gidan ƙawata Zahra Isah za mu yanzu sai 4 za mu koma gida.”
“To ku jira ni zan zo in mayar da ku.”
Ta ce “To ” ta mayar da wayar jaka ta dube ni tana murmushin shaƙiyanci “Ya Najib ya kamu, ni kuma zan dama kununa yadda nake so.”
Na yi gaba na bar ta tana maganganun ta ta ce “To jira ni mana.”
Ban tsaya ba ta ɗaga ƙafa ta kamo ni “Keke napep ta ƙara tare mana zuwa malali lowcoust cikin jerin tamfatsa tamfatsan gine-ginen da ke wajen ta ba mai keken umarnin tsayawa gaban daya, muka fita ta ba shi kuɗin shi.
Tana buga get maigadi ya leƙo ta tambaye shi Zahra na ciki ya ce eh ya buɗe mana.
Babban gida ne da Zainab ta ce min tare ƙawar ta ta take da surukanta, zamana da Inna na ji ya dawo min a ƙwaƙwalwata.
Sai dai akwai tazara mai nisa tsakanin su ita tana can karshen gidan.
Ta yi ta yin knocking kafin a zo a buɗe Namiji ne ya buɗe wanda ya kama baki alamar mamaki da ganin Zainab yana faɗin yau suna da manyan baƙi.
Ya ba mu hanya muka shiga ciki muka zauna kan kujerun falon, ya shiga kiran sunan Zahra, farar mace mai ciki ta fito sanye cikin baƙar doguwar riga.
Tana ganin Zainab ta fara balla mata harara kamar idonta zai faɗo Zainab ta kama dariya “In zo gidanki ki kama harara ta sai in tashi in yi tafiyata.”
Ta ƙaraso ta zauna kusa da Zainab “Ƙawata mara mutunci daga kun kawo ni kun watsar ziyarar ma ta gagara, ba ki da kirki Zainab.”
Mijin nata da ke tsaye a can kusurwar falon ya ce “Amma ki yi baƙi ba ki ba su ko ruwa ba ana wannan ranar, kina ta suturu ta miƙe tana murmushi “Na yi missing ɗin aminiyata.” Ta shiga wata ƙofa ta dawo da ruwa da lemo sai da Zainab ta zuba min sannan ta zuba ma kanta Zahran ta dube ta “Sabuwar ƙawa kika yi?
Sai da ta dubi inda nake “Yar’uwata ce.” Ta ce “Allah sarki sannu da zuwa.” Sai kuma ta rage murya “Kin san bana son idanun Sunusi na kiciɓis da irin waɗannan dirarrun matan.”
Zainab ta yi saurin kallona sai na yi kamar ban ji su ba ta hanyar kauda kaina.
Sai Sunusin ya ce me za ta ba mu ba ta yi girki ba? Bai kuma ba ta damar magana ba ya ce bari ya yo ma bakin take away Zainab ta ce ya bari ba za mu dade ba ya ki key din motarsa ya dauko ya fita falon Zahran ta ce lallai Sunusi ya taya ni murnar ganin ki.
Ta ja mu bedroom ɗinta Zainab ta yi sallah na zauna ina duba wayata da dabara na ɗauki wayarta na kashe ta na jefa jakata don ban so Najib ya zo ɗaukar mu gabaɗaya takura min yake idan yana wuri.
Har ya kawo abincin muka ci suka yi ta hirar su ina sauraren su har aka kira La’asar ta yi sallar ta ce “Kin ga ya Najib bai kira ba, kuma yasan gidan nan don ƙanen Sunusi abokin shi ne.” Allah kuma bai bata ikon neman wayarta ba ta kira shi.
Na ce “To ko za mu tafi?
Ta ce “Gaskiya, don ban so magrib ta yi mana a hanya Mama faɗa za ta yi.”
Muka yi make up muka fito ta rako mu har get mijin kuma ya ce mu gaida gida
Muna takawa don fita inda za mu samu abin hawa jin horn a bayan mu yasa gabana faɗuwa don tunanina Najib ne muka juya a tare sai dai Sunusi ne ya tsaya daidai inda muke ya ce “Ku shigo in sauke ku Zainab.
Ta ce “Zo mu je Bilkisu.
Ta buɗe min baya ta shiga gaba yana hawa titi ya ce “Ina kika samo kyakkyawar mace haka?
Dan shiru ta yi sai kuma ta ce “Yar’uwata ce.”
Ya ce “Ma sha Allah, ina sunanta? Ta ce
“Bilkisu ce.”
“Mai gadon zinare kenan Bilkisu sarauniyar mata. Sunan ya dace da mai shi.
Ya ce “Ni fa na gani kuma na ƙyasa, wannan yar’uwar taki ina ciki ki shigar da ni.”
Ta dafe ƙirji “Zahran fa da wane ido zan dube ta?
Ya ce don Zahra sai ki ƙi taimaka min in samu abin da nake so?
Har muka kai suna ta musayar kalamai sam Zainab ta ƙi shi kuma ya ƙi hakura yana yin parking na ɓalle murfin na fita
Ita kam ya tsare ta.
Ina shiga daki na fara wucewa na tuɓe kayan jikina na shiga toilet na gyara jikina na fito na sauka ƙasa falon Mama na same ta zaune da ɗaya daga cikin ƙannen Baba na dayan gidan na gaishe su zan juya ta ce “Zo ki yi zaman ki Bilkisu.
Magana yake gaya mata wani abokin shi ya ga Khadijah yana so yana da mata guda da yara uku, gobe idan Allah ya kaimu zai zo su ga juna. Ta ce “Allah ya kaimu. Suka gama zancen su ya tashi ya tafi.
Ta ce min abinci na ce mun ci a can. Na mike zuwa kitchen sai da na haɗa markaden shinkafar na miƙa wa Dauda mai kula da ayyukan gidan sai na zo na fara miyar waina.
Ina yin miyar ina duba wa Mama girkinta da ta shigo ta ce “Me Bilkisu ke mana ko’ina ya ɗauka da ƙamshi? Na sunkuyar da kaina na ce
“Miya ce.”
Zainab ta shigo kitchen ɗin ta kama hannuna “Zo mu je ki ji Bilkisu.”
Na ce “Bari in karasa miyar.”
Ta ce “Don Allah zo mu je.
Na rage wutar gas din sai na bi bayanta sai da muka yi nisa da kitchen ɗin ta ce “Kin gan ni sai yanzu? Sunusi zai sa ni bakin duniya, ya hanani tafiya ya dage son ki yake, don Allah haka ake? Matarsa ƙawata ce ta ƙut, mu muka yi bikinta kawai sai in shige gaba a yi mata kishiya da yar’uwata?Duka-duka shekara guda kenan da auren nasu.”
Na ce Kawai ki share shi.”
Ta ce “Huum Allah yasa zai sharun.”
Muka shiga falon Mama Khadijah na zaune ita da Najib.
Zainab za ta yi mishi magana ta kula da hararar da yake balla mata ta haɗe hannayenta “Sorry bro na rantse gudun kar magrib ta yi yasa muka taho.
Ya ce “Wayarki da kika kashe kuma fa in yi miki bayanin Baba ne ya aike ni ku jira ni.”
Kusa da shi ta zauna ta ba shi haƙuri sai kuma ta fara ba Khadijah labarin Sunusi mijin Zahra daga zuwa ya ce yana so na.
Jin zancen sai na haye sama har na kwanta na tuna da miyata na sauko da sauri su biyu na samu Najib na yiɗin ya fita.
Sai bayan sallar magrib na gama miyar na samu Zainab falon Mama muka ci abinci na yi sa’a har na gama Najib ɗin bai shigo ba, ban zauna hira ba gudun kar ya shigo na hau sama na yi kwanciya ta.
Da gari ya waye kaya na canza na fita zuwa kitchen riga ce mai roba na sanya da ta kama jikina hannunta karami ne tsawon ta iya ciki sai na daura zane na rufe kaina da siririn jan gyale kamar yadda rigar take ja.
Ƙullun na fara haɗawa Baba Talatu ta dawo don haka ciki na same ta gas na kunna na sanya kujera na zauna na daura tanda don tuyar waina.
Mama ta shigo ta dibar wa Baba ta tafi kai mishi Najibyaur shigo yau ma cikin shiri yake har ya fi jiya yin kyau, da yake kofa nake kallo tun da ya doso kitchen ɗin na gan shi.
Na mayar da idona kan tandar gabana ya tsuguna “Ranki ya daɗe sarauniyar mata, yau kuma waina ake mana?
Baba Talatu da ke wanke kwanoni ta yi maza ta ɗauraye hannayenta “Ina kwana Yallaɓai? Ya juya inda take wanda na yi imanin bai ma san da ita ba. Ta fita da sauri sai ya matso kusa da ni yau ma jikinmu na gugar na juna “Zan ci wainar Gimbiya.” Ya fadi cikin wata murya da har ta so yi min tasiri.
Na ɗan matsar da kujerar sai na miƙe kula da yadda ya tsura wa ƙirjina ido yasa ƙirjina ya ƙara tsananta bugu ji nake kamar in fita da gudu.
Na dai yi ƙarfin halin juya baya flet na ɗauko na zuba mishi wainar hannuna na rawa sai da na rufe na zuba miyar a bowl na jera a babban tray na miƙa mishi,yana jifana da mayen kallon ya karɓa, shigowar Mama sai ya fice.
Maryam litee