Motarmu na tsayuwa a harabar gidan da ta fara cika da mutane da motoci ban fara sauka ba sai da Mami ta fita, na bi ta da hand Bag ɗinta da na karɓa na riƙe mata
duk da zumuɗin da nake cike da shi na son haɗuwa da Zainab wadda ko da muna hanya mun yi waya ta ce suna gida ita da Khadija.
Bayan Mama da yaranta akwai wasu mata zaune, gabaɗaya yaran suka miƙe suna wa Mami sannu da zuwa, sai suka fara ihu oyoyo Aunty Billy.
Zainab ta fara isowa gaba na, cikinta da ya turo riga shi ya hana mu rungume juna.
Sai Asma’u da ta iso da gudu na rungume, Zainab ta kama hannuna muka isa gaban Mama na zauna ina gaishe ta ta amsa da dariya tana faɗin
“Bilkisu ce ta koma haka? Lallai an gaida Daddy da Mami.”
Na yi murmushi na miƙe muka gaisa da Khadija wadda na ga kamar ba ta da lafiya.
Sai da muka haura sama. Zainab ta ce min laulayi take.
Na ce “Ita sai yanzu, ku ko yan zafin love tun daren farko kuka cinye komai.”
Duka ta kawo min na kauce ina dariya, ta cire glass din da na manna a idona ta sanya a idonta ta ce
“Kin sauya Billy kin zama babbar yarinya, in zan ce kin haɗu ina nufin haɗuwa ta ƙarshe.
Na dubi jikina ina murmushi “Wannan kuma faɗar ki ce.”
Riga da wando ne jikina da lulluɓinsu, a wata boutique da muka shiga da Mami ta saya min su kala-kala, sai na manna glass na tsari kawai takalmina ma mai tsini ne ga kitso da na je shagon gwanaye aka yarfa min sai ƙunshi da na sha ƙafa da hannu.
Hure idon Zainab na yi da ta ishe ni da kallo
“Ina Oga Najib.”
“Anjima nan za ki gan shi zai zo mu tafi gida.”
Na gyaɗa kai. Mun nutsa cikin hirar mu kiran Najib ya shigo wayata na ɗaga ya ce an ce mun iso in same shi yanzu wurin lilon nan.
Na miƙe ina ce wa Zainab “Ya Najib ne zo mu je.”
Glass ɗina ta mayar min muka sauko,
Mama ta kama baki da ta gan mu
“Komai ba ki ci ba Bilkisu kun haye sama.”
Na yi murmushi “Zan ci Mama bari in dawo.”
Zainab ba ta bi ni ba zaman ta ta yi.
Tunda ya hango ni ya kafa min ido har na isa gaban shi “Congratulations ango.”
Na fadi da murmushina, ya langaɓe kai
“Baba ya hana ni zuwa Abuja, ban san me ya sa bai son ba ni ke ba, na ga wanda zai ba ina zaune.”
Na zauna kusa da shi. “Aikin kenan mutumina, kullum ƙorafi kai da kake ango.”
Ko da nake ango sai in ƙi faɗin abin da aka yi min.”
Shiru na mishi don in da sabo na saba da wannan ƙorafin kodayaushe muka yi waya sai ya yi.
Nan ya tsare ni har sai da Mami ta kira ni a waya, na ce mishi ina zuwa
Abinci ta sanya ni na zauna gaban ta na ci da na gama na ciro tsarabar da na yi ma kowa na basu.
Zainab ta ce “Ba fa ki je ki gaishe da Mamanki ba.”
A lalace na dube ta “Wai Aunty?
Ta harare ni na ce “To zo mu je ki raka ni.”
Sai da muka je ƙofar part ɗin ta rage murya
“Kin san na manta ban tsegunta miki ba, bayan tafiyar ki ya Najib ya ji ta tana waya tana faɗin yadda ta so haɗin ki da shi don ta mallake shi ya zama na ta ita kaɗai, da nasarar da ta samu na tatsar shi da take.
Sai kuma yayanta da ta fara karɓar abin hannunsa da sunan za ta riƙa miki sayayya, ga shi an ɗauke ki.”
Na gwalo ido “Duk kuma Auntyn?
Ta ce “Ita fa.”
Na ce “Allah ya kyauta, amma duk wayarmu da shi bai taɓa faɗa min ba.”
Ai ya bala’in tsanar ta ko hanyar part ɗinta bai zuwa.”
Ahmad da ya fito daga ciki ya sa na wuce ya bi ni a baya yana min sannu da zuwa, a falon na zauna ya shiga ya kira ta da ta fito sai na ga duk ta canza min ta yi wata iri ko me ye matsalar ta allahu a’alam.
Na gaishe ta na ba yaran chocolate da na ruƙo musu na ɗauki yarinyarta da ta yi wayo tana yawon ta na yi mata wasa sai na sauke ta na yi mata sallama na fito.
Wannan karon ma Gwoggo Maryama ta zo har da Bilkisun ta.
Godiya sosai ta yi wa Mami saboda ina ba ta labarin duk irin kyautatawar da suke yi mini, da muka haɗu ta ce ta ga zahiri.
Na faɗi mata ina son in je in gano Mamana.
Ta ce in bi a hankali.
Ranar ɗaurin aure da karfe uku na rana muna zaune da Zainab Rabi’ah ta kutso cikin mutane ta same mu.
Zahra matar Sunusi ta yo ma rakiya ita da wata, tana bata rai ta dubi Zainab
“Da ƙyar na gan ku Aunty Zee, ga wayarku kun ƙi ɗagawa.”
Muka ba su wurin zama aka kawo musu abincin da ake rabo.
Muna ta hira wadda suka zo tare da Zahran ta ce wa Zahran “Ni kam Zahra wannan ta yi min ina son ta.”
Zahra ta yi yar dariya “To kin ji Billy kin burge ta tana son ki “
Na yi murmushi “Ni ma ina son ta.”
Mamanta yayar Mamana ce, a Kano suke zaune ta zo sunan yayata da ta haihu ne.”
Zahra ta yi ƙarin bayani Zainab da tun da aka fara ba ta tofa ba ta ce “Allah sarki.”
Ta ciro wayarta “Ki bani phone number ɗinki.”
Na faɗa mata ta sanya sai ta kira ta ce in yi saving. Sai da na yi ta ce a ina nake zaune? Na ce Abuja, ta ce ita a Kano take mijinta ne ke zaune Abuja, amma ta kusa komawa Abujan, sunanta Ummu hani, ta ce “Idan na koma can za mu yi zumunci sosai Billy.”
Na ce “In sha Allah.”
Da za su tafi muka raka su ni na amso musu abin da ake rabawa ga mahalarta bikin, wata rantsattsar mota suka zo ita kuma ke jan motar, ko da yake shigar ta kawai ka duba ka san matar wani wanda ya ci ya tada kai ce, za ta ba ni a ƙalla shekara uku ko biyu.
Da muka dawo rakiyar su na ce ma Zainab tunda na ga Ummu hanin nan nake mata kallon sani, sai dai na rasa da wa take min kama sai da suka tafi.”
Ta ce “Da wa take miki kama?
Na ce “Inna Maman Hassan.”
Ta ke ce da dariya “Nana kundashira, indai haka Innar take, amma ta haifi Hassan zankaɗeɗe?
Na riƙe baki “Kin ji ki sai ta ƙi haihuwar kyakkyawa abu na Allah. Har kin tuna min da Rahina idan muka haɗu gidan Gwoggo ta ga ina kukan baƙin cikin da Inna ta kuntuka min sai ta ce ka ga Innar nan da hancinta kamar maggi dunƙule.”
Zainab ta ke ce da dariya
Na ce “Allah daga gajartar har yar ƙibar da baƙin ba su da maraba don dai wannan yar gayu ce.
Ta taɓe baki “Ƙila yar’uwar su ce.”
Da za a tafi kai amarya wanda aka ce sai an kai ta za a tafi wurin Dinner.
Ni da Khadija da Zainab muka tafi a motar gidan su, ba mu wani zauna ba da muka shiga muka fito lokacin Najib ya iso da abokansa an sha farar malum malum sai abin ma ni ya ba ni dariya daga ban taɓa ganin ya sa ta ba.
Za mu shiga mota ya hango mu sai ga shi suka tafa da Khadija ta ce Congratulations bro. Zainab ma ta matso suka tafa ta yi mishi murna ya miƙo min hannu na yi baya ya ƙanƙance min ido.
“Me kuke shirin yi? Na ce “Gida za mu.”
Ya dubi Khadija ta ce “Ƙyale ta bro za mu koma gida daga can za mu tafi.
Ya ce “Bari in ajiye ku.”
Baya suka shiga na zauna gaban sai da ya tsaya a hanya ya yi mana sayayyar kayan ƙwalam muka ƙarasa su suka yi shirin zuwa Dinner ni kam ƙin zuwa na yi na zauna muka yi hira da Gwoggo Maryama.
Khadija ce ta kwana Zainab da da ma Najib ɗinta ne ya zo suka je wurin daga can suka yi gida sai da safe karfe goma ta dawo.
Da biki ya ƙare Gwoggona za ta wuce na so bin ta, Mami ta ce in yi haƙuri sai mun samu wani hutun.
Na dai samu na je makarantar su Amir na gan shi ya ƙara girma da wayo.
Ranar monday muka koma Abuja washegari ban fito da wuri ba saboda gajiyar tafiya sai da na gama shan barcina da na tashi na amsa kiran Ummu hani da kullum sai mun yi waya, muna gamawa na fita zuwa dakin Mami ita ma wayar na samu tana yi zan juya ta yafuto ni, sai na shiga na fara mata gyare gyare ina sauraren hirar ta da tilon ɗanta wanda na lura tana kewar rashin shi kusa da ita.
Bayan ƙare wayar ta dube ni “Sannu ɗiyata, ni da mashiriricin yayanki ne wai next week za su dawo.”
Na taya ta farin ciki ganin yadda fuskarta ta toni asirin tsantsan farin cikin da take ciki, na yi addu’ar Allah ya kawo su lafiya.
Ranar da za su dawo girke girke na musamman aka yi a gidan har ni ma sai da na shiga na taimaka.
Bayan kammaluwar komai na ce ma Mami zan shiga in ɗan kwanta don tun tashi na da mura na tashi, ta ce in wuce in yi kwanciyata ina kuma kwanciya barci ya yi awon gaba da ni.
San da na farka na yi mamakin irin barcin da na yi wanka na yi da ruwa mai ɗumi kafin na fito na yi sallah, sama-sama na yi kwalliya na daura zane da riga na atamfa na ɗora hijab sai na fito zuwa falo, su biyu sun amsa sallamata Mami da surukarta Farha, cikin nuna kulawa Mami ta ce “Kin tashi ya murar? Na ce “Na tashi Mami Alhamdulillahi.”
Inda ya Safwan ke zaune ya ɗan kishingiɗa idanuwansa na kan wayarsa yana latsawa na ce “Ina wuni ya hanya?
Lafiya kawai ya ce ba tare da ya ɗago ba, na juya wurin matarsa da tun kafin ma in gaishe ta cikin fara’a ta ce “Ke ce Mamin ta mu kenan ɗiyar kuma Mami?
Mami ta ce “Ita ce Farha.”
Na gaishe ta ta amsa cikin sakin fuska da alamu tana da son jama’a, jin Mami ta ce ina mura sai ta shiga tsokana ta “In shiryo farfesu mai ɗan yaji kenan daga tsohuwa tana mura? Ni dai murmushi nake ta yi ban yi magana ba Mami da ta ga na kasa ramawa ta ce “In kina mata tsiya Farha ai sunan mu ɗaya.”
In ina son tsokanar ta zan tsaya wurin momyn Daddy na, idan kuma na dawo wurin ki Mami sak.”
Ta faɗi tana kallon mijinta da bai gwada ma ya san abin da ake ba.
Saukowar Daddy daga sama shi da yarinya da ba ta wuce shekaru uku ba sai dai da yake lukuta ce tana kuma da tsayi za ka yi tunanin ta fi haka sai dai akwai kyau kamar an tsaga kara da uwarta, don dai uwar siririya ce ƙwarai kamar za ta karye.
An gyara ta haka ma sumarta mai tsawo da cika ta sha gyara.
Tana gaba Daddy na biye da ita bai ƙarasa saukowa ba ya tsaya ya ce maza ki sauka a bare miki chocolate ɗinki, kwata-kwata ta hana ni aikin da nake.”
Mami ta yi dariya ita da Farha Mami ta ce “Haba Daddy daga saukar amarya ka koro ta kuma a gaba na.”
Farha ta tare wa yar ta “Ai dai ya ba ta chocolate Mami.”
Daddy ya juya “Haba ta cika haɗa kashi, ga labari.”
Mami ta kira ta “Kawo in ɓare miki.”
Noƙe kafaɗa ta yi uwar ta yi dariya “Afnan kuma da rowa. Ta miƙa hannu “Zo my Afnan in ɓare miki.”
Itan ma noƙe kafaɗa ta yi ina cewa “Zo baby in ɓare miki.” Sai ga ta har da saurin ta.
Maryam litee