Skip to content
Part 41 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Zan sha baƙin Tea.” Miƙewa kawai ya yi ya bar dakin.

Shigowar shi ta sa na buɗe ido ya zauna kusa da ni “Tashi ki sha.”

Na yunƙura na tashi zaune ya miƙo min na karɓa ina kurɓa a hankali har na shanye, na gyara na kwanta zufa na keto min, ya miƙe ya ƙara gudun fanka sai ya shiga bathroom “Tashi ki yi wanka.”

Umarnin da ya ba ni kenan bayan ya fito.
Duk da nauyin shi da na yi ta ji dole a gaban shi na yi wankan don ya kasa ya tsare ya kuma ƙi fita.

Na fito ɗaure da tawul da taimakon shi na shirya cikin wasu riga da skirt na shan iska ya ja ni muka fita.

Wunin ranar tare muka yi shi bai fita ba Aunty Farha kuma na fahimci ba ta gidan, har dare ban ji motsin motsin ta ba dakin shi ya ja ni muka kwana da safe da na fito na tabbatar Aunty Farha barin gidan ta yi, sai na ji ba daɗi ta gayyato ni gidanta kuma ta tafi don wani saɓani idan jama’a suka ji wane kalar zagi za su yi min?

Da na koma ɗakina na yi wanka ina ta saƙa maganar da zan gaya mishi.

Na fita dakin zuwa na shi cikin wata yar riga mara hannu tsawon ta iyaka gwiwa ina tura kofar dakin na hango shi tsaye gaban mirror yana murza hula cikin shigar da ya yi matuƙar yi min kyau, hannu ya miƙo min alamar in zo.
Na isa gaban shi ya riƙe ni da hannu daya dayan yana shafa cikina da ya turo rigar ya ranƙwafo kanshi daidai kunnena yana raɗa min maganganun da suka sa na rufe idona, kafin ya isa bakin gado riƙe da ni “Zan fita.” Na ce “Zan shiga Sch.”

Ya girgiza kai “Ban yarda ba sai kin ƙara warkewa.”

Na zare hannuna da ya riƙe cikin na shi yana murzawa jin na fara shiga wani yanayi “Aunty Farha ba ta dawo ba ya Sadauki.”

Na faɗi cikin rage murya, bai tanka ba sanin hali sai na kuma maimaitawa nan ma ƙin amsa ni ya yi, sai na zare jikina cikin na shi na matsa ɗan nesa da shi ina mishi kuka “Ni ma zan tafi gidan Mami idan Aunty Farha ba ta dawo ba.” Kallona kawai ya yi sai ya miƙe ya gyara zaman rigar shi ya bar min ɗakin.

Na daɗe zaune shiru cikin tunani kafin ni ma na miƙe na kama gyara ɗakin zuwa bathroom da na kammala na fita, kitchen na shiga muka gaisa da Iya Larai na faɗi mata abin da za a dafa sai na fita ban shiga kitchen ɗin ba sai yamma don ya Safwan bai shigo gidan ba sai ana kiraye-kirayen sallar magrib yana kuma shigowa alwalla ya yi ya fita zuwa masallaci, ganin yap dawo shi kaɗai na tabbatar da gaske yake ba za shi bikon Aunty Farha ba.

Ban ƙara mishi maganar ba har muka ci abinci ya gama kallon labaran shi muka yi shirin kwanciya, ya yi ɗaiɗai bisa gadon shi yana jira na na kwanta jikinsa cikin shagwaɓa na faɗi ya dawo da Aunty Farha ganin yanzu ma ba zai kula ni ba na sa mishi kuka ƙanƙame ni kawai ya yi ya shiga ba ni wasu manyan darussa masu wuyar mancewa.

Da ya dawo sallar asuba duk yadda na so in shiga kitchen in yi mana abin karyawa riƙe ni ya yi ya shiga barcin shi , ni ma dole na shiga barcin.

San da na farka takwas ta wuce brush na fara yi sai na fita na samu Iya Larai har ta kusa kammala abin karyawan na sanya mata hannu muka ƙarasa na bar ta tana wanke kayan da muka yi amfani da su shiryawa na yi na koma wurin shi , wanka na samu yana yi na zauna har ya fito ya shirya sai da muka fara karyawa na ce za ni makaranta ya ce sai kin warke na ce ni na warke yau kuma da ƙyar idan ba mu yi test ba.”

Bai ƙara magana ba sanin hali na san ya amince kenan.

Da muka kammala ɗaki na koma na idasa shiri muka fita tare zai sauke ni.

A inda ya kan tsaya idan shi ya kai ni ya tsaida motar.

Na dubi inda yake dafe da sitiyari “Allah ya tsare ya ba da sa’a.”

Sai na kama kokarin buɗe ƙofar in fita a rufe take bai buɗe ba na san yana son magana da ni ne, don haka komawa na yi na gyara zama cikin sauraro, hannu ya sa a gefen aljihunsa ya ciro kuɗi sai ya miƙo min “Lacture nawa za ku yi? Na ce “Biyu.” “Idan kun fito ta farko ki nemi abin da za ki ci don ba wani abinci kika ci ba.”

Na karɓa da godiya na fita ya ja motar

Lacture daya muka yi ba kuma a yi test ɗin da muka yi zato ba zuwa sha biyu mun fito ban nemi ya Sadauki ba don shaida mishi yadda aka yi ba ko jiran direban da ya kan turo mota na ɗauka ta kaini gidan Mami.

Ita kadai na samu zaune a kamar yadda dama na yi zaton ita kadai ɗin zan samu a irin wannan lokacin, Daddy ya fita.

Na zauna muka gaisa ta ce daga ina ni kaɗai?
Na ce makaranta muna ta hirar mu har lokacin sallah ya yi aka kuma dawo da Afnan daga makaranta Mami ta fara miƙewa ni kuma na riƙe hannun Afnan zuwa dakin da mai renon ta take na cire mata unifoam na sauya mata wasu kayan muka fito zuwa bed room din Mami na samu har ta fara sallah key din ɗakina na ɗauka muka fita mai renon Afnan muka haɗu da ita tana so ta ba ta abinci na bar ta da ita na wuce dakin na bude na shiga na yi haramar sallah da na idar hijab mara nauyi na ciro cikin kayana na cire wanda na zo da shi na hau gado don ba abin da nake so irin in yi barci, ban kuma dauki dogon lokaci ba ya ɗauke ni.

Sama-sama na riƙa jin kukan wayata na miƙa hannu na ɗauka na kai ta kunnena ba tare da na buɗe ido ba muryar direba na ji yana cewa ya shigo bai gan ni ba. Na ce mun tashi na wuce gida. Ya min sallama na ajiye wayar na ci-gaba da barcina.

Wani lokaci mai tsawo na ɗauka ina barcin da na kasa tashi har sai da na ji muryar Mami a kaina “Wane irin barci kike haka Bilkisu? Sau biyu ina shigowa ba alamar za ki tashi.”

Na tashi zaune ina ƙara jan hijab ɗi na tare da addu’ar Allah ya sa da ina barci bai yaye ba ta ga cikin da nake ɓoyo.

Na yi hamma ina girgiza kai “Fito ki ci abinci.”

Ta ba ni umarni na ce “To Mami ta juya na miƙe alwala na ɗauro na zo na yi sallah sai na fita ba tare da na cire hijab ɗin ba.

Tun kafin in gama saukowa daga step biyar ɗin da za su sa da ka da falon na hango shi zaune tare da Mamin ina kakkare cikin da hijab na isa wani kallo ya cillo min da ya sa tsoron shi ya kama ni kafin ya koma kallon Mami na zauna mai aikin Mami ta iso dauke da tray ta soma jera min kan wani ɗan tebur na ce Ayya iya da kin bari na shigo kitchen ɗin da kaina.”

Kai ta girgiza “Ba a yi haka ba. Ta gama ajiyewa ta koma kitchen ta dawo ɗauke da wani jug ta gama shirya min abincin na yi mata sannu, ina cin abincina a hankali suna hirar su da Mami lokaci lokaci yana ɗaga kai yana kallona amma miskilancin shi ya hana ya yi min magana na gama na miƙe Mami ta ce,

“Ina za ki? Na ce ” Wanka zan yi.” Na wuce ina ji a jikina kallona yake wankan na yi na yi alwala sai da na yi sallah na yi shafe-shafe cikin kayana na ɗauko wata riga mai girma na sanya tana da wadataccen mayafi na rufe jikina na fito yana cin abinci tare da Mami da Daddy na karasa na gaishe da Daddy ya tambaye ni karatuna Mami ta ce in zo in zauna a ci abinci, na ce “Na ƙoshi Mami ai ban daɗe da cin abinci ba.

Ya Safwan dai ko ɗagowa bai yi ba na zauna a daya daga cikin kujerun falon na maida hankalina kan TV, da suka gama Daddy ya yi baki ya fita falon da yake ganawa da baki Mami ta zo ta zauna kusa da kujerar da nake zaune ya Safwan ya taso Mami ta ce “Akwai biki na yaran yaya A’isha a Safana karshen watan nan, zan tafi da Bilkisu ta ga dangi.”

Karatun nata fa Mami? Ya tambaye ta yana ƙarasowa “Za su samu hutu zuwa lokacin, na yi magana da ita.”

Bai ce komai ba sai dubana da ya yi “Tashi mu je.”

Ban ji nauyin zaman Mami a wurin ba na ce “Ni ba zan koma gidan nan ba.” Bai yi magana ba sai Mami ce ta ce “Saboda me? Na ce “Dama sati na ce zan yi a can.”

Mami ta yi ɗan murmushi “To kai ka ji ta gaji, ina labarin nata gidan ba a kammala ba? Ya kamata a sanya ranar tarewar ta ko bayan mun dawo biki ne.”

Yana daga tsayen ya ce “Akwai fa sauran aiki Mamina.” Ta jinjina kai “To dama ba ka shirya ma tarewar ta ta kenan ba shi kenan, amma daurin aure wata uku ba ka kammala gyaran gida ba? Ko sabon gini ka sa indai yin ake wata uku bai isa an gama ba? Don haka sai mu yi zaman mu, ranar duk da ka shirya ta taren.”
Ya ɗan matso inda take ki yi haƙuri Mami, ayyuka ne suka sha min kai na bar batun aikin gidan.”

Ta ce “Shi kenan, lokacin da ayyukan suka yi maka sauki sai ka ƙarasa, sai mu sa bikin tarewar.”

Kanshi ya dafe sanin hali na san doguwar maganar ce ta fara damun shi “Pls Mami ki yi haƙuri ki bari mu tafi, na yi miki alƙawari gyaran ba zai wuce one month ba.”

Cikin yanayin da za ka fahimci ta soma hasala ta ce “Ka wuce min anan Sadauki.”

Ya ce “Allah ya ba ki haƙuri Mamina.”

Ba ta yi magana ba har ya yi mata sai da safe ya fice.

Ina nan zaune Daddy ya shigo na yi musu sai da safe na yi daki, na riga na yi wanka don haka shirin barci na yi wasu riga da wando kalar su pink na sanya.

Ina kwanciya na janyo wayata missed call din ya Safwan na gani har uku sai Text message na karanta na kuma karantawa karshe na kwanta rigingine da fillow ina tuna ya Safwan da kewar shi da zan yi amma gara min in daure in ba haka ba ban san ranar da zan baro gidan Aunty Farha ba.

Na daɗe ina juyi saboda barci da ya kasa samun nasarar sace ni.

Washegari ya kama Lahadi ba Sch, da na yi sallah komawa na yi barci shi ma ban farka ba sai da Mami ta zo ta tashe ni, na tashi da sauri ina janyo hijab ɗin da ke gefena na ɗan rufe jikina.

“Ina kwana Mami?

Ta ɗan yi murmushi “Kin zama sarkin barci Bilkisu, za mu je mu gano ginin naku idan kika yi wanka kika karya.”

Na ce “To Mami.”

Ta juya ta fita ta ja min kofar.

Na miƙe na isa gaban mirror ina kallon fuskata da jikina yadda komai nawa ya fara sauyawa, ina shafa fuskata na ji karar wayata na isa gefen gado inda take ajiye na ɗauka ya Safwan ne.

Na yi picking sai na gaishe shi bai amsa ba sai tambaya ta da ya yi yadda na kwana ba ni da wata matsala na ce E ya ce good sai ya katse kiran.

Wanka na shiga na yi na fito na shirya cikin riga da zane na yi lulluɓi da wadataccen mayafi na zura takalmi na fita, ban cire mayafin ba na karya da na gama bedroom ɗin Mami na wuce shirin na samu ita ma tana yi na zauna bakin gadonta, sai da ta ajiye kwalbar turaren da ke hannunta ta juyo ta fuskance ni “Me ya faru Bilkisu da kika ce ba za ki koma ba? Na girgiza kai “Babu komai Mami.”

Ta ɗan ƙara min kallon nazari “Ban fa son ki ɓoye min komai.”

“Aunty Farha ta bar gidan, yau kwana biyu kenan.”

Meye dalilin tafiyar ta ta? “Ban sani ba Mami.
Ta gyada kai ta gama yane jikinta da lafaya ta ce “Mu je.”

Ta kama hanyar barin dakin na bi bayanta.

Sai da na je na gaida Daddy muka fita inda Direba ke jira har ya bar unguwar ni da ita ba wanda ya yi magana sai wayarta da ta ciro ya sadauki ta kira ta ce ya same ta a gidan na shi .

<< Mutum Da Kaddararsa 40Mutum Da Kaddararsa 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×