Skip to content
Part 45 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Mami dai tunda muka dawo ta fara shirin bikin tarewa ta, wanda na ga biki sosai take niyyar yi.

Kullum ba ka rasa manyan ƙawayenta da suke shirin tare.

Ginin gida ya kammala, Daddy ya ce zai shirya min wuri Baba kuma ya dage shi ma sai ya yi na shi karshe dai Baba ya shirya min two bedroom flat Daddy ma ya shirya min dayan shi kuma ogan ya shirya Main palour da na shi two two bedroom ɗin.

Mama da matan ƙannen Baba sun zo sun shirya kitchen.

Na Daddy kuma kawayen Mami ne suka jagoranci komai.

Ranar da aka kawo Invitation card Mami ta kira ni ina daki na fito na same ta tare da ya Safwan, da ban san sa’adda ya shigo ba.
Kusa da ita na zauna a Tree Sitter na kai hannu na ɗauko card ɗin daya da ban san ko na mene ne ba, sai dai dubawar farko na yi saurin mayarwa na aje.

“Ki ɗi ba, ki rabawa ƙawayenki.”

Mami ta ce Maimakon in yi yadda ta cen hawaye na kama ta zuba min ido cikin nazarin abin da zai sanya ni kuka.

Shi ya Safwan da ke danna wayarsa ko ɗagowa bai yi ba, har Mami ta karaci tambayarta ta mike don amsa kiran waya da aka yi mata, ya bi ta da kallo sai da ta shige ya taso ya tsaya kaina har ya miƙo hannu zai taɓa ni sai kuma ya mayar aljihu. “Kukan me kike?

Ya tambaye ni cikin kwanciyar hankali, kamar ina jira na ce “Ni mutanen da za su zo sai su gan ni da ƙaton ciki? Ni ba na son bikin tarewa.”

Bai ce min komai ba inda ya taso ya koma ya zauna har Mami ta dawo.

“Daga ba ta son taron bikin a bar shi kawai Mamina.”

Ta ce “Saboda me ba ta so?
Ya yi shiru kamar ba zai magana ba sai da ya ga ta tashi za ta yi tafiyarta ya ce “Pls Mamina.”
Kallon shi kawai ta yi ta juya ta yi tafiyarta.
Na san ba ta yarda ba kenan sai na ci-gaba da kukana, kafin na miƙe na koma daki .

Kwanciya na yi na rufe ido ban ji motsin shigowar shi ba sai ƙamshin turarensa na ji.
Ban buɗe ido ba sai da ya riƙe hannuna “Ki yi haƙuri.” Abin da ya ce min kenan “Kar ki ƙara kuka.”

Na ɗaga mishi kai.

Ya ɗan jima a dakin da ba gwanin doguwar magana ba ne shiru muka zauna har ya kara ba ni haƙuri ya tafi.

Na daɗe kwance ina juye-juye ina hango yadda bikin zai kasance ina ɗauke da ƙaton ciki.

Ranar ina kwance a daki cin abinci kawai ke fitar da ni.

Washegari kuma ina shirin makaranta kiran ya Safwan ya shigo wayata “In kin shirya ina jiran ki.”

Abin da ya ce kenan ya katse kiran. Na gyara zaman dogon hijab ɗin da na ɗora saman riga da zane na atamfa da ke jikina na fita.

A ɗakinta na samu Mami na yi mata sallama, na bar gidan ina tunanin ko ina ya Safwan ɗin yake sai na hango motarsa dan nesa kadan da gidan.

Na nufi wurin sai da na shiga na zauna na ce mishi ina kwana? Bai dubi inda nake ba ya ce “Ya kika kwana? Na ce “Lafiya lau.

Ya tashi motar ya harba titi.

Sai da ya tsaida motar zan sauka ya ciro waɗannan Invitation card ɗin masu yawa ya ajiye kan cinyata “Ki rabawa ƙawayenki da abokan karatunki, ki yi haƙuri kar ki sake kuka, ki yi yadda take so.”

Ɗaga mishi kai na yi, ya ɗora min kudi saman katunan na ce “Na gode.” Na buɗe ƙofar na fita.

Na yi rabon katin ne ta hannun abokiyar karatuna Ruƙayya Babangida.

Mami ta haɗa ni da manyan mata masu gyaran jiki, sun yi min irin gyaran da ya dace da yanayin da nake ciki.

Sun kuma yi min lacture ta zamantakewa da yadda zan gyara kaina.

Ɗunkuna na musamman Mami ta yi min tun saura kwanaki biyu yan Safana suka cika gidan, yan Kaduna ma haka, Mama da yaranta duka sun zo har Zainab me ciki., an ce Maman Ahmad ta dawo. Matan ƙannen Baba su biyu.

Gwoggo Maryama ana gobe suka iso ita da yaranta da aminanta har da dangin mijinta.

Cikin Zainab mai wata bakwai da nawa mai biyar girman su daya sai dai ni nawa ina ɓoye shi ta hanyar shigar da nake.
Ni kaina na san ba karamin kyau na ƙara ba bayan kyan ciki da na yi ga kuma uban gyaran da na sha.

Yan makarantarmu ba ma yan Department ɗinmu ba na sha mamakin yadda suke ta tururuwa kara suka yi min sosai.

Ana ta sha’ani ina tuna Mamana na rasa yadda zan yi ta mayar da al’amarina na ta, duk da gaya mata da na yi bai sa ta turo kowa na ta ba.

Ranar da ake yinin bikin manyan mata masu ɗinbin yawa suka taru suka kuma zubar da kuɗi kamar fahari.

Da Zainab da Khadijah da Rabi’ah da yaran Gwoggo Rahina da ta Kano tare muke da su a dakina.

Ranar da zan tare da hantsi muna zaune da su a ɗakina ni kadai na yi wanka su sannan suke ta yi wasu ma na kwance kiran ya Safwan ya shigo wayata na ɗaga ya ce in same shi a baya wurin part ɗin Daddy.

Zainab da ta fi kusa da ni ta ce “Ke da wa? Kallon ta kawai na yi na ce “Ina zuwa.”

Tsaye na same shi ya rungume hannaye a ƙirji ya bi ni da miskilallen kallon shi. Rabon da in gan shi tun kafin a fara hidimar nan.

Ya ce “Zo mu je.”

Na bi shi a baya a kafa muka taka har muka fice.

Daga ɗan nesa ya ajiye motar muka je muka shiga sai da muka kusa isa na gane inda za mu asibitin da ya kaini ne, ashe ranar ce zan koma awo, ba ɓata lokaci aka yi min muka koma gida sai da zai sauke ni ya ba ni wata jaka.

“Ƙungiyarmu sun shirya mana party na taya murna daga can za wuce da ke.”

Na daga mishi kai na rungume jakar na sauka na shiga ciki.

A bisa gado na ajiye jakar Zainab na shirya Samha ta ce “Kin daɗe ina kika je? A hankali na faɗa mata ta yi dariya “Amarya mai ciki.”

Masu kwalliyar amare na musamman da aka dauko suke yi min kwalliya yau ma su suka yi min kwalliyar zuwa Dinner wadda da an tashi za a wuce da ni ɗakina.Alkyabbar da aka ɗora min ta ɓoye cikina.

An yi taro na manya gogaggun yan boko da suka ci suka tada kai.

Sai dare taron ya tashi aka wuce da ni babu wadda ta zauna kowa da ya leka zai yi fatan alheri ya juya, na yi na yi su Zainab su kwana suka ce ba hauka ake yi ba suka juya gidan Mami.

Wucewar kowa na yaye alkyabbar da ma kayan jikina da suka hadu suka takura min yaushe rabon da in samu in sha iska ina faman ɓoyon ciki.

Wanka na shiga na yi na fito daure da tawul cak na tsaya ganin ya Safwan tsaye a filin ɗakin na dube shi ya dube ni sai ya tako zuwa inda nake ya riƙe hannuna zuwa bakin gado.

“Kin yi alwala mu yi sallah?

Na girgiza kai ya ba ni umarnin in je in yi na wuce na yo na same shi ya ja mu Sallah raka’a biyu ya yi mana addu’o’i sosai na neman albarkar aure da zuri’a masu albarka.

Bayan haka ya ja ni zuwa dakinsa can muka kwana.

Ko da na yi sallar asuba ban fita wurin ba, barci na yi sosai wanda na kwana biyu ban samu na yi kamar shi ba ya Safwan kuma bai tashe ni ba, da dai ya gama na shi barcin wanka ya yi ya fita da na tashi na ga sai ni kaɗai na miƙe na fita a Main palour na gan shi yana aiki a computer jin motsina ya waiwayo na langaɓe kai hannu ya miƙo min na ƙarasa inda yake ya kama ni na zauna kan cinyarsa ya dora hannunsa kan cikina “Ki yi wanka ki zo ki ci abinci. Wane irin barci kike haka ko gajiyar abin ne? La

Tashi na yi da sauri na jin abin da ya ce na nufi wurina ba ko waiwaye.

Wanka na yi na shirya kaina na naɗe gashina da ya sha gyara wata baƙar riga mai matuƙar kyau da ta yi matuƙar burge ni na sanya na rufe kaina da gyalenta na ƙara fesa turare sai na fita yana zaune a inda na bar shi hango kwanoni a dinning na nufi can na zauna na zuba ina tunanin daga inda aka samu abincin.

Sai da na kammala muka zagaya ko’ina na gidan a tare ya gabatar da ni ga mai gadi da shi kadai ne ƙwal a gidan, da muka dawo na kira su Zainab ina rokon su biyo kafin su wuce dariya ta fara yi min wai ai su yanzu sun ji ƙamshin Kaduna.

Tare muka wuni da ya Safwan har dare bai fita ba na je ɗakina na shirya na zo in kwanta na ji yana waya “Na riga na roƙe ki Farha ki yi haƙuri in yi mata kwana uku saboda gidan ba kowa ba lallai ta iya kwana ita kadai ba.
Za a samo mata mai aiki kafin kwanakin su cika.”

Sai na ji ya yi shiru ni ma na ci-gaba da tsayuwa har sai da na ji ya kare wayar na shiga na kwanta.

Washegari zan shiga makarantar don haka tashi na yi na shiga kitchen akwai kayan abinci don haka na yi mana abin karyawa mai sauki don ba lokaci da zan yi dogon girki na wuce na yi wanka na shirya sai na iske shi har lokacin yana kwance na zauna gefen shi ina tunanin ta yadda zan tashe shi.

Na miƙa hannu na dan ja yan yatsun ƙafarsa ya buɗe ido “Me ya sa kika tashe ni? Na dubi agogo sai na langaɓe wuya “Makaranta ya Safwan.” “Kina amarcin ma sai kin je makarantar? Na yi shiru “Mu yi zaman mu kawai.” Ya ce yana tsare ni da idanuwansa na girgiza kai ina bata rai ya miƙe, na zauna har ya kammala shirin shi muka fita ya sauke ni da aka tashi turowa ya yi aka mayar da ni gida.

Abinci mai sauki na yi na ci na yi barci sai yamma na shiga kitchen na shirya mishi lafiyayyen girki ana yin sallar magrib sai ga shi tare muka ci na ji daɗi sosai yadda na ga ya ci da kyau, sai dai muna gamawa ya ce zai koma gidan Aunty Farha zan iya kwana ni kaɗai?

Jarumta mai yawa na sa wurin amsa mishi da E don magana ta gaskiya ina jin tsoron yadda zan kwana ni kaɗai sai mai gadi a get.

Har inda ya adana motarsa na yi mishi rakiya sai da motar ta fita gidan na koma ciki.

Ban wani zauna ba ina yin ishai na hau gado cikin haske na kwanta ban kashe haske ba na yi addu’o’i na rufe idona.

Na dan fara barcin ya Safwan ya kira ni tambaya ta ya yi na kwanta na ce E ba wata damuwa na ce babu ya yi min sai da safe ya kashe wayar.

Haka ma da asuba ina cikin sallah ya kira ni sai da na idar na kira shi na gaishe shi ya tambaye ni yadda na kwana na ce lafiya muka aje wayar ba zan shiga Sch ba don haka da na gama barci na na nemi abin kari sai gyara gidan na yi wanka na shirya cikin wata riga mai roba ce don haka ta kama ni na sanya hularta ina nufin fita na ji karar wayata na ɗauka lambar mai gadi ce da muka yi musaya jiya ya ce ina da baƙi na ce ya yi musu rakiya gani nan fitowa.

Ina buɗe ƙofar Mami na gani fara’a ta ƙwace min na shiga mata sannu da zuwa bayan ta wata mata ce na yi musu iso Mami ce ta zauna a kujera ita matar kasa ta zauna na shiga gaida Mami matar ta gaishe Ni.

Na mike don kawo musu dan abin maraba da nake da shi a kusa Mami kamar ta san nufi na ta ce “Koma ki zauna Bilkisu ba sai kin kawo komai ba.”

Ta shiga yaba kyan da wurin ya yi ta kuma gabatar min da matar a matsayin mai aikin da aka samo min sai kuma da muka tashi zagaya gidan ni da ita ta ce ba ta so wannan matar ba amma zama na ni kaɗai dole ta amince ta amsar min ita. Da ta gama ganin wurin muka dawo na ce matar ta zo in nuna mata inda za ta zauna tana ta godiya na tambaye ta sunan ta ta ce Hajjo ta zo ne daga wani kauye da ke jihar Kano.

Na bar ta na koma wurin Mami ta ce tafiya zan yi Bilkisu. Na ce “Ba ki ci komai ba Mami.”

Ta ce idan na dawo na ci.

Ta gyara zaman mayafinta ta kama hanyar fita

<< Mutum Da Kaddararsa 44Mutum Da Kaddararsa 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×