Ya miƙo takardar da aka rasa mai amsa, Sha’awa ta fashe da kuka ta fita da gudu. Na yi ma Dr sallama ba tare da na yi mishi complain na tawa damuwar ba na bi bayan ta bayan na ce Hajjo ta taso mu tafi don bai kamata a yi wannan tonon sililin gaban likita ba haɗi kuma da kaina ya ƙulle.
Sai da muka shiga mota Sha’awa na ta razgar kuka Hajjo dai ba baka sai kunne kai na ƙasa.
Muna sauka ɗakina na wuce sai da na tabbatar sun zauna na fito na shiga wurin Hajjon har lokacin kuka Sha’awa take tana faɗin “Mun shiga uku Innarmu, wannan wane irin abu ne?
Na shiga cikin sanyin jiki na ce Sha’awa ta fita ta mike ta fita ina daga tsayen na ce “Hajjo me nake ji likita ya faɗi? Ta yi shiru “Garin yaya hakan ta faru? “Ki yi haƙuri Haj, sharrin shaiɗan ne.” Na dube ta cike da takaici wai sharrin shaiɗan ne, to ina take zuwa har ta samo abokin shashanci?
“A yi haƙuri a rufa min asiri yadda Allah ya rufa miki.”
Wani takaicin ta ya ƙara rufe ni “Kin san ba ki iya riƙe kanki ai da ba ki fito ba kin yi zaman ki a gida kin yi aure ? Sharrin shaiɗan ne na tuba a yi min rai.”
Wani tuƙuƙin baƙin ciki ke ƙulle ni idan ta ce sharrin shaiɗan ne in ji kamar in zazzage mata abin da ke cin raina darajar shekarunta na juya na koma daki ina yanke shawarar yadda zan yi da su zan bar su har mai gidan ya dawo ya sallame su da abin da zai ba su sai in sallame su daga ita ba mutumniyar kirki ba ce. Ciki Hajjo to ina ta samo shi? Da girman ta ita da za ta yi ma ya’yanta faɗa.
Na ja tsaki na janyo wayata Zainab na kira na ba ta labarin abin da Hajjo ta yi ta ce “To me za ki jira ki kori shegu kawai daga ba mutunen arziki ba ne.
Washegari bar musu gidan na yi zuwa gidan Ummu hani da kullum ke min ƙorafin ban son zuwa gidanta.
Mun ƙule a daki muna ta hira ta ce “Kullum ki ce ba ki da lafiya ni na ga kyau ma kika ƙara.”
Na jinjina kai “Haka dai kika ce, amma komai ban iya ci. Ke ce dai kina ta fargabar kishiyar da za a yi miki, ga shi nan sai ƙiba kike yi.”
Ta yi yar dariya “Na sha fargaba kam, amma da Allah ya tashi duba na Innar dai da nake wulaƙantawa ita ta zame min garkuwa, amaryar ta zo da shirin ta na kama miji ta kuma samu nasarar ɗauke hankalin Habibi, amma nasihar Inna a kaina ta sa dole yake juyowa kaina ga shi Alhamdulillahi na samu ciki Bilkisu.”
Na ce “Da gaske? Ta ce “Wallahi amma ƙarami ne ƙwarai.”
Na taya ta murna muka yi ta hirar mu na ce ta zo ta raka ni wurin Juwairiya mu gaisa, ta ce in dai je, na yi na yi ta ƙi na ce to ta raka ni ƙofar part ɗin ta mike muka tafi sai da na kwankwasa ta juya Juwairiyar ta zo ta buɗe.
“Oyoyo Momin Mashkur.”
Na yi murmushi ta ba ni hanya na shiga kafin in zauna sai da ta kawo min abin taɓawa muka taɓa hira Hassan da ban san yana ciki ba ya fito na ce ina wuni ya ce lafiya ƙalau ya yara? Na ce lafiya lau. Tana murmushi ta ce min “Ina zuwa Momin Mashkur.”
Na miƙe na ce tafiya ma zan yi na riga shi ficewa na koma wurin Ummu Hani ban daɗe ba sai ga ta ta ɗan zauna ba ta jima ba ta yi min sallama tare da cewa in gaida Khadijah.
Sai La’asar na yi ma Ummu Hani sallama na koma gida don ko gidan Mami ban biya ba.
Ya Safwan saukar dare ya yi washegari ya wuni gida bai fita ba sai dare ya tafi gidan aunty Farha ya kwana na kira shi da safe na ce zan je Hospital Antenatal na kusa kammalawa ya kira ni ya ce in jira shi zai zo ya mayar da ni yana kusa da wurin sai da ya gaisa da Dr suka ɗan yi maganar su ya zo muka tafi.
Mun shiga gida dukkan mu muka yi mamakin ganin motar Aunty Farha a harabar gidan, na kuma ji raina ya ɓaci, yau ba zan ba ta fuska ba ta zauna na ta gidan in zauna nawa sau ɗaya na taɓa zuwa gidanta tun da ta tare.
Ta zo rannan yau ma ta dawo to me ta zo yi?
Muka sauka muka shiga ciki a falo da muka shiga ba ta, gabana na ji ya buga na kama addu’ar Allah ya sa ba wani sharrin ya kawo ta ba wurin su Hajjo na nufa in tambaye su har ya Safwan ya wuce sai kuma na ga ya biyo ni da dosar wurin muryar Aunty Farhan na fara ji cikin masifa tana faɗin “Ku tattara ku bar gidan nan yan iska kin kwaso shegiyar yar ki kin kawo me kike nufi?
Hajjo cikin na ta bala’in ta ce “Ba inda za ni, zama daram kin kuma yi kyan kai da kika hasaso na kawo Sha’awa ne don ta auri mijinki. Kika kuma matsa sai mun tafi wallahi sai na tona duk tuggun da kika ƙulla ma Haj.
Jin furucin Hajjo na ƙwace jikina daga riƙon da ya Safwan ya yi min tun yunƙurin farko da na yi zan faɗa ɗakin.
Na faɗa sai dai gani na suka yi a kan su.
Na ce “Wa kika kawo Hajjo ta auri mai gidan? Hajjo ta yi wiƙi-wiƙi suka kama kallon kallo, kayan su na fara kwasa ina watsa musu waje na ce “Ku zo ku fita daga ku ɗin matsiyata ne da ba ku san arziki ba.”
Ganin za ta ɓare da su su kaɗai ya sa Hajjo cewa “Ai ba ni kaɗai ba ce Haj, ki gafarce ni.” Ya Safwan da ke tsaye naɗe da hannaye ya ce “Wane tuggu kuka ƙulla ke da Farha?
Ta haɗa hannaye “Wallahi ita ta kira ni Alh, ta ce in riƙa ɗauko mata duk motsin Maman Mashkur. Ta sai min waya ni na daukar mata hoton matar da ta zo wurin ta aka nuna maka kan ta kawo magani.”
Farha ta yi kukan kura ta kama wuyan Hajjo ya Safwan ya isa ya damƙi Farha da kyar ya raba ta da maƙogoron Hajjo ya wurgar da ita wuri ɗaya, ta tashi har na ji mamaki don ban sha za ta iya tashi ba don faduwar da ta yi.
Ta kara kai mata wawura ya tare ta ya rike ta tam