Skip to content
Part 18 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Don kuwa ya fahimci ta fara yin nisan da ba zata ji kiran kowa ba a wannan tafiyar, bai daɗe a wurin ba ya tashi, tunda dama ba a tanaji dining don zama ba. A babban falonsa ya nufa, bayan ya gama amsa calls ɗin da suka shigo wayarsa ne ya kira number Deena tare da faɗa mata ta same shi a falonsa yana son magana da ita.

Deena bata yi mamakin kiran Alhaji Lawan ba tunda ba yau ne karon farko ba, sai dai zulluminta na kan abin da zai yi mata magana akan shi ne, wanda tana da yaƙinin maganar aurenta ne, duk da tana ji a jikinta ba zai goyin a raba ta da mijinta ba saboda shi ya yi tsayuwar daka har Allah ya sa ta auren shi, “Toh amma kuma ai wannan matsalar da banbanci”, ta faɗa a ranta, toh ko ma dai menene Allah na nan, ta miƙa lamarinta kaf a wurinsa.

A kafaɗa ta saɓa Raihan ta fito, a step suka yi clash da mamanta lokacin da take hawowa sama, ko kallon Deena bata yi ba, bare kuma ɗanta, wanda a can baya in zasu haɗu sau goma a cikin gidan, toh sai ta yi ma Raihan wasa, don tana masifar son yaron, hakan ne kuwa ya ƙara sanya ma Deena tsoro a ranta, saboda ta tsani mahaifiyarta ta ɗauke mata kai, gudun kada Allah ya yi fushi da ita, saboda “Yardar Allah tana tare da yardar Iyaye, kamar yadda fushin Allah ma yana tare da fushin iyaye” kamar yadda Farin Jakada Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa.

Idanunta cike da ƙwalla ta ƙarasa sauka ƙasa, kai tsaye babban Falon Alhaji Lawan ta nufa bayan ta miƙa Raihan wurin Nanny ɗinsa, cikin muryarta mai cike da rauni ta yi sallama, yayin da shi ma ya amsa mata cikin murya mai cike da tausayinta. Shi kam yana son Deena, da ace shi ya haife ta toh sai ya yi da gaske wurin fifita acikin ƴaƴansa, saboda tana da haƙuri, uwa uba kuma ga biyayya, toh amma ko a yanzu ba wanda zai ce ba ƴar shi bace.

Gefensa ta zauna a ƙasan carpet, inda shi kuma yake a kan kujera, kanta na sunkuye a ƙasa ta ce “Daddy ga ni”, sai da Alhaji Lawan ya ɗan sauke ajiyar zuciya kafin ya ce “Okay”, ɗan shiru falon mai cike da ni’ima ya yi, daga bisani yake tambayar ta Raihan, shaida mashi ta yi yana wurin Nanny ɗinsa, ya kuma cewa “Okay.”

Mai kaza aljihu baya jimurin ass! Kawai sai tsarguwa ta sa Deena fara zargin ko shi ma fushi yake? Don kuwa ya juya mata baya toh bata san ina zata je ta samu mafaka ba, saboda shi ne wanda take sa ran zai tsaya mata.

Bata ida shiga ruɗani ba sai da ya ambaci sunanta “Deena”, gabanta na faɗuwa ta ɗan ɗago kanta “Na’am daddy”, lokaci ɗaya kuma tana sauraron me zai ce, “Ɗago kanki ki dube ni, magana nake son yi dake mai muhimmanci”, kamar yadda ya buƙata haka ta yi, duk da firgici ba zai bari ta iya haɗa idanu da shi ba, cewa ya yi “Na lura da akwai ƴar damuwa a tsakaninki da mamanki, kuma da na yi bincike sai take faɗa mani akan aurenki ne ko?”, Kai Deena ta ɗaga alamar “Eh”, sai da ya jinjina kai sannan ya ce “Toh ke meye ra’ayinki?”, Idan har batun ra’ayi ne ai a bayyane komai ya ke, don ba zata iya rabuwa da mijinta ta daɗin rai ba, shiru ta yi, wanda shi ne amsar tambayarshi.

Ya fahimci ma’anar shirunta, amma don ya ƙara tabbatarwa ne ya ce “Idan na fahimce ki za ki iya rayuwa da mijinki a kowane yanayi ya samu kansa ko.?”

Amsawar Deena ta yi daidai da shigowar Hajiya Hadiza a falon, kuma ta ji tambayar haɗe da amsar, cikin tsananin fusata ta ce “Ai kuwa kina tare da wahala”, Alhaji Lawan ya san zamanta a falon ba ƙaramar ɓarna zai haifar ba, cewa ya yi ta fita, ba musu ta fice falon a fusace, don itama ba zata iya zama ta kwashi kayan takaici ba.

Wannan abu ba ƙaramin ɗimauta Deena ya yi ba, a ranta ta ke faɗin “Me ya sa mahaifiyata ba zata fahimce ni ba? Me ya sa ta zaɓi farincikinta a kan nawa ba tare da lura da ni ɗin mai rauni ba ce?”, Wani irin kuka mai ƙarfi ne ya sarƙe ta, wanda ya sa Alhaji Lawan ƙara maido dukkan nutsuwar shi a wurinta.

Cike da takaicin halin matarshi ya girgiza, ita dai babban rauninta shi ne babu mai hana ta abin da ta yi niyya, ko da kuwa zai zama illah ga wani, madamar ita dai bukatarta ta biya toh shikenan. Sunan Deena ya ambata cikin lallashi, bayan ta ɗan nutsu ne ya ɗora da faɗin “Ina son ki fahimci wani abu dangane da mahaifiyarki a kan wannan issue, bana tunanin zata raba ki da mijinki kawai don jin daɗinta, tunda haka kawai ba mahaifiyar da zata so mutuwar auren ƴarta”, a ran Deena ta ce “Toh saboda me za a raba ni da mijina?”, Tamkar Alhaji Lawan ya ji tambayar da ta yi a ƙasan ranta ya bata amsa da “Mun yi magana da ita tun ba yau ba, abin da take guje maki shi ne wahala da ƙuruciyarki. Ɗawainiya da makaho, musamman sabuwar makanta ba abu bane mai sauƙi, don komai sai an yi mashi, sannan ga ƙaramin goyo kina da shi, da wanne zaki ji.?”

Duk wannan Deena bata ɗauke shi aiki ba, sai ma jihadi da neman lada a wurin Ubangiji, domin Deeni mai jiɓintar lamarinsa yake nema, ba wai rabuwa da shi ba, toh amma ta san da wahala a fahimce ta, mafarin yana bata damar magana cikin kuka ta ce “Daddy zan iya zama da shi a haka, kuma akwai masu aikin da ke taya ni aiki, an ce za a ƙaro wata ma”, ko babu mai aiki Alhaji Lawan ya san zata iya, toh amma tunda mahaifiyarta bata san wannan ba, dole ya ɗan kawar da kai domin guje ma Deena samun matsala tsakaninta da mahaifiyarta.

Cewa ya yi “Deena yau da gobe sai Allah fa, a yanzu ne kike ganin zaki iya, sai nauyi ya fara haye maki za ki fahimci aikin ba na wasa bane, don haka ki yi nazari sosai”, Indai a kan Deeni ne ba wani nazarin da Deena zata iya, sai dai kawai zata bi abin da Allah ya ƙaddara mata ne kawai.

Shawara sosai ya bata akan kada son da take yi ma mijinta ya haifar mata da matsala a tsakaninta da mahaifiyarta, don kuwa zata iya chanja miji, amma ba zata iya chanja uwa ba, sannan duk yadda take ganin kirkin Deeni, toh a matsayinsa na namiji zai iya bata mamakin da zai goge mata hadda, don haka idan har mahaifiyarta ta nace a kan ba zata koma gidan Deeni ba, toh ta ɗauki dangana, a dalilin wannan biyayyar Allah zai kawo mata mafita ta inda bata taɓa zato ba a rayuwarta.

Sosai Deena ta kasa kunne tana sauraron sa, bata yi magana ba sai da ya tambaye ta “Kin ji shawarata a gare ki ko?”, Kai ta ɗaga “Eh Daddy” ya ce “Yauwa, kuma ina son ki sani ban maki tilas a kan sai kin bi shawarar nan ba, idan kina da wata hanyar bayan wadda na faɗa maki, toh za ki iya bi, amma ki sani uwa ba wasa ba ce, ki samu ku rabu lafiya da ita.”

Ta inda baki ya fi karkata, aka ce ta nan yawu ke fita, sosai Deena ta fahimci kamar shi ma yana team ɗin mahaifiyarta, gashi kuma a wurinshi ne take ganin samun mafaka, toh amma tunda shi ma ra’ayinsu ɗaya, dole itama ta bi, ko da hakan zai zama ajalinta.

Tana kukan baƙincikin hukuncin da a take ta yanke ta dube shi tare da faɗin “Daddy, na yarda zan yi yadda mahaifiyata take so”, kai ya girgiza yana mai matuƙar tausayinta “A’a Deena, kada ki yi abin da zai cutar da ke, sannan idan kika ce ba zaki iya rabuwa da mijinki ba, zan tsaya maki da yardar Allah, kawai bana son ki sake samun matsala da mahaifiyarki, don kin ga yadda ta fusata sosai.”

Cewa ta yi “Duk da haka Daddy, na yarda zan bi abin da take so”, ya ce “Lallai?”, Ta ce “Na amince”, idanunsa a lumshe ya ce “Allah ya ba ki mafita ta Alkhairi”, cikin ransa kuma yana jin kamar ya yi kuka shi ma, yarinya ƙarama, amma matsaloli sun haye mata, wanda kuma tsarin Allah ne ya jarbci wanda ya so, abin da kawai ya ke so ga bawan da ya jarabta shi ne haƙuri mai cike da tsoron Allah, madamar bawa ya yi wannan, toh zai samu mafita mai yawa a wurin Allah.

Umarni ya ba Deena a kan ta je su yi magana da mahaifiyarta, miƙewa ta yi, jiri ba ɗibarta ta haura sama. Knocking ƙofar ɗakin ta yi, daga can cikin ɗakin Naman ta ce “Waye?”, Cikin dakusasshiyar murya Deena ta amsa “Ni ce”, sake tambaya ta yi “Ya aka yi ne?”, sai da Deena ta haɗiye wani irin baƙinciki kafin ta ce “Shigowa zan yi.”

Shiru Maman ta yi, sai da Deena ta kusan yin minti goma a tsaye sannan ta buɗe mata, a tsorace Deena ta bi bayanta suka ƙarasa cikin ɗakin, a ƙasan carpet Deena ta zauna, yayinda ita kuma sai da ta gama duba kaya a wardrobe ɗinta sannan ta zo gefen gado ta zauna. Wannan ɗauke kai na yau kaɗai ya jigata zuciyar Deena, kuma ba zata iya ɗaukar sa ba ko da tana tare da Deeni.

Shiru bedroom ɗin ya yi, babu sautin komai daga na AC, sai kuma famfo dake ɗan zuba a banɗaki.

Deena na tunanin ta ina zata fara magana, mamanta ta tsinke mata shi ta hanyar faɗin “Idan baki da abin faɗa ki tashi ki fice mani daga ɗaki”, sosai maganar ta daki zuciyar Deena, idanunta dake lumshe ta buɗe a hankali tare da duban mahaifiyarta da ta yi tagumi tana jiran tsammanin abin da Deena zata faɗa.

Alhaji Lawan ya mata faɗan saurin kukan da take, ya kuma cunkusa mata dakiya a ranta a gaban mahaifiyarta da sauran jama’a, idan ya so bayan ta keɓe ita kaɗai ta ci kukanta.

Cike da dakiya ta ce “Momma, don Allah ki yi haƙuri”, katse mata numfashi ta yi “Haƙurin me, ai ki je ki bi ra’ayinki, ni ma zan bi nawa”, kai Deena ta girgiza “Ba haka bane Mommah, duk hukuncin da kika yanke na yarda da shi ɗari bisa ɗari”, baki Maman Deena ta taɓe haɗe da guntun murumushi “Hu’um”, lokaci ɗaya kuma ta biyo bayan shi da faɗin “Ni ban maki tilas ba, idan ra’ayinki shi ne daidai ga hanya nan ki bi.”

Kamar ya za’a riƙa faɗa ma Deena ba a yi mata dole ba, alhali duk fushi da ɗauke kan da ake mata na don an ga tana son mijinta ne, idan har ba haka bane a daina fushi da ita mana, a takaice ta ce “Mommah, na yarda da duk abin da kike so, na san ba zai taɓa zama illah a gare ni ba Insha Allahu.”

Wannan magana ta zo ma Hajiya Hadiza da mamaki, don a yadda take yi ma Deena kallon sakarya, bata taɓa zaton zata furta haka ba, take ta watsar da duk wasu makaman yaƙinta, ta kuma ce “Kin tabbatar da duk hukuncin da na yanke a kan aurenki ba zai zama illah a gare ki ba?”, Kai Deena ta ɗaga “Eh Mommah.”

Shiru Hajiya Hadiza ta yi tare da sauke nannanuyar ajiyar zuciya, lokaci ɗaya kuma ta ce “Toh shikenan, hukuncina dai kin san shi, shi ne zaki rabu da Deeni, don kwata-kwata tsarin zama da shi ba na ƙaramar yarinya irinki bane, kin amince?”

Cike tsanar wannan tilasti da aka yi mata ta ce “Na amince”, Mamanta ta ce “Allah ya yi maki albarka”, nan ta shiga nuna ma Deena ita mai ƙaunar ta ce, duk wata fafutuka da take yi a rayuwa don ita take yi, tunda ita kaɗai Allah ya bata, don haka itama ta koya ma kanta son abin da mahaifiyarta ke so.

Sannan ta kara nuna mata auren Deeni yanzu wahala ce a wurinta, duk yadda take ganin zata iya, toh sai a gaba zata gane ta ɗaukar ma kanta dala ne ba gammo, don idan ba’a yi sa’a ba har abinci sai an riƙa kai musu, tunda shi bai da lafiyar da zai fita nema, ta manta da babu maraya sai raggo.

Deena ta fahimci maganarta ta farko a kan don ita take komai, amma batun Deeni sam bata fahimta ba, kuma za’a daɗe kafin ta iya fahimta.

Haƙuri sosai Deena ta ba mahaifiyarta, ta kuma ji daɗi sosai tare da sa mata albarka.

A gidansu Deeni kuwa basu san wainar da Mahaifiyar Deena take toyawa ba, mafarin suka fara shirya yadda Deena zata dawo, kamar kullum idan suka yi breakfast Deeni na zuwa ɗakin mahaifiyarsu a ɗan yi hira, kafin lokacin sallar azuhur ya yi, tambayar shi ta yi “Toh yaushe kake ganin Deena zata dawo?”, Shi idan ta ɓangarenshi ne ta dawo yau ma, toh amma komai na buƙatar shiri, cewa ya yi “Kin ga komai na buƙatar shiri”, ta ce “Hakane, amma kamar wane shiri?”, Ya ce “Na farko dai a faɗa musu, su ma su shirya, sannan kamar gidan yana buƙatar a gyara shi sosai, sannan a ƙaro wata mai aikin, su haɗu su uku, wurin kula da gidan.”

Cewa ta yi “Wannan duk ba wani abu bane, shiri ne dama da dole a yi shi”, anan take faɗa mashi Asma’u da su Yaya Asiya ne zasu je su gyara gidan, ƴar aikin ce ma take ganin ɗaya ta isa, sai idan an ga gazawar Deena ne sai a ƙaro wata, kuma basu tsammanin faruwar hakan ma.

Sosai ya gamsu da maganar Hajiyarsu, bayan ya koma ɗaki ne ya kira number Deena, bai mamakin jin ta da sanyi murya ba, tunda tun jiya ya gane tana cikin damuwa, gaisawa suka yi, daga bisani yake faɗa mata sababin kiran ta hanyar faɗin “Yaushe kika shirya dawowa ɗakinki? Saboda a fidda ranar da su Asiya zasu je a gyara maki gidan.”

Amsar tambayar shi ta ba shi cewar “Shirinka shi ne nawa Yaya”, ya ce “Da gaske?”, Ta ce “Yeah”, ya ji daɗin maganarta, don babu inda ta nuna mashi rashin dawowarta a gidanshi. Faɗa mata ya yi idan son samu ne nan da two weeks ta koma, don haka ta fara shiri.

Natsuwar waya da matarshi ce ta tunatar da shi kiran da Rahila ta yi mashi a jiya bai ɗaga ba, number ta ya lalubo a waya ya kira, aikuwa itama sai da ta ja ajinta sannan ta ɗaga mashi, maganar da ta fara fitowa bakinsa ita ce “Har na yanke tsammanin ba zaki ɗaga ba Dr.”, Daga can ta ce “Ko?”, ya ce “Ƙwarai”, ta ce “Ai ba zan ƙi amsa kiranka ba, Ni ce ma ya zan yi complain, jiya na kira three times amma ba ka ƙi picking”, haƙuri ya bata, tare da faɗa mata yana cikin uzuri a lokacin..

<< Mutuwar Tsaye 17Mutuwar Tsaye 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.