Skip to content
Part 21 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Amsa Umman Deena ta bata da “Maganar ba ta cikin waya bace Hajiya”, cike da fargabar shu’umancin Umman Deena ta ce “Toh maganar ta ina ce Hadiza?”

Amsa ta bata “Yanzu ina Kebbi, jibi idan na dawo zamu zan zo har gida mu yi magana”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Toh Allah ya dawo da ku lafiya”, ta ce “Amiiiin”, ba tare da sun yi sallama ba sai dai Hajiyarsu Deeni ta ji ta katse kiran.

Jiki a sanyaye ta sauke hannunta daga kunne, lokaci ɗaya kuma ta ce “Wata sabuwar”, dukkansu sun ji abin da suka tattauna a wayar, amma tsabar ruɗu Deeni bai san lokacin da ya tambaye ta ba “Me ya faru?” cewa ta yi “Ni ma ban gane ina ta dosa ba, ta dai ce a dakata da zuwa gyaran gida, na kuma tambaye ta dalili ta ce maganar ba ta waya ba ce sai ta dawo daga Kebbi”, bakin Deeni na kyarma ya ce “Ko dai ƴar ta zata karɓe?”, Cike da son kwantar mashi da hankali Hajiyar ta ce “Bana tunaninin haka, ƙila akwai wani shiri da take son yi.”

Asma’u da ke gefen Hajiyar ta ce “Wane shiri ne wanda kusan kwana hamsin ba a gama shi ba? Kawai dai tsiyarta ce ta motsa, kuma kanta zata ƙare Insha Allahu”, Hajiyarsu Deeni da ta daina shakkar halin Umman Deena ta ce “Wallahi kuwa Asma’u”, shi kuwa cewa ya yi “A bari ta dawo ɗin kawai”, Hajiyarsu ta ce “Haka za a yi, Allah ya sa mu ji Alkhairi”, ya ce “Amiiin.”

Sosai Deeni ya shiga ruɗani, take ya fara tuna halin ƙuncin da Deena ta ke ciki a ƴan kwanakinan, wanda yake ji a jikinsa yana da alaƙa da maganar da Ummanta ta ce sai ta dawo, “Toh wace magana ce?”, Bashi da amsa, mafarin ya tashi da nufin komawa ɗaki, saboda ruɗu kasa kai kansa ya yi, sai da Asma’u ta raka shi.

Bayan ta dawo ne murya ƙasa-ƙasa ta ce “Hajja, jikina na ba ni raba auren nan zata yi, kin ga dama ba so take ba”, Hajiyarsu ta san yadda Deeni ke masifar son Deena ba zai iya ɗaukar wannan baƙincikin ba, ko da lafiyarsa lau, cewa ta yi “Allah ya fi ta, kuma ko da ta karɓe ƴarta Allah zai ba shi wadda ta fi ta.”

Shi kuwa number Deena ya kira, cikin hanzari ta ɗaga kiran bakinta na faɗin “Sorry Yaya, ina ta son kiran in ji ka koma lafiya”, kamar zai yi kuka ya ce “A’a ke dai kin fara mantawa da ni”, a marairaice ta ce “Yaya indai na manta da kai ai zan iya mantawa da kaina”, ya ce “Ko?”, Ta ce “Eh”, shiru ya yi ba tare da magana ba, cewa ta yi “Yaya ka yi shiru”, ya ce “Ina cikin firgici”, yana jin lokacin da ta firgice itama ta ce “Firgicin me?”, Ya ce “Nima ban sani ba Deena”, kamar zata yi kuka ta ce “Kai Yaya, ka faɗa Mani”, ya ce “Ai ba zan iya faɗar abin da ban sani ba Deena, kawai Allah ya bamu mafita”, ta ce Haka ne, amma dan Allah ka da ka sa ma ranka damuwa”, ya ce “Insha Allahu.”

Domin ta basar da maganar ne ta ce “Ranar Saturday ne su Asma’u zasu je gyaran gida ko?”, Ya ce “Nope”, ta ce “An chanja ne?”, Ya ce “Yes”, ta ce “Why, and yaushe ne aka sake fidda rana”, ya ce “Only God knows Deena”

Ba ta matsa sai ta ji ba, tunda itama ta san tambayar da ta yi mashi bata da wani amfani, idan ma ba neman ma kanta ɓacin rai ba, kuma ta wani ɓangaren hakan ma ya mata daɗi, saboda kusanto da maganar komawar ta ce zata bayyana abin da mahaifiyarta ke shirin aikatawa.

Hirar duk ba wani armashi, mafarin suka yi sallama. Deeni kuwa saƙe-saƙen zuci mai cike da tashin hankali ya shiga yi, da ya ga ba mafita sai ta komawa wurin Allah bai san lokacin da ya sauko daga kan gado ba, da lalube ya isa banɗaki ya yi alwala ya fito, bai wani ɓata lokaci ba ya kabbara sallah domin samun nutsuwar zuciyarsa.

A can Kebbi kuwa bayan Umman Deena ta gama waya da su Hajiyarsu Deeni ne take labarta Hajiya Hauwa, wadda ita ce uwargidan ga Alhaji Muhammad, wato Yayan Alhaji Lawan da suka zo ganinsa irin hukuncin da ta yanke a kan auren Deena.

Ɗan jum kaɗan Hajiya Hauwa ta yi, daga bisani ta ce “Gaskiya zama da makaho akwai wahala, musamman ga yarinya ƙarama kamar Deena”, Umman Deena na son ta ji an goyi bayanta dangane da wannan al’amari, ranta sal ta ce “Toh kin gani dan Allah, shi ya sa gwara kowa ya nemi daidai da shi”, Hajiya Hauwa ta ce “Haka ne, amma wani hanzari ba gudu ba Hajiya Hadiza”, Umman Deena ta ce “Na me kenan?”, Ta ce “Sai in ga kada ayi gaugawar raba auren nan, a ba shi dama ya ƙara neman lafiya”, Umman Deena yadda bata ƙaunar cigaba da surukuta da Deeni ko sabbin idanu zai sake ba zata yarda ba, bare kuma babu tabbacin zai samu lafiyar ma, cewa ta yi “Hajiya ba na ƙi taki ba, amma a raba auren kawai shi ne kwanciyar hankalina.”

Duk yadda Hajiya Hauwa za ta so Deena bai kai ga mahaifiyarta ba, amma ta zaɓi ta raba mata aure, su da nasu bai wuce addu’a ba, cewa ta yi “Allah ya zaɓa mafi Alkhairi”, ta ce “Amiiiin”

Sabuwar hira suka buɗe ta gyaran zamantakewar aure, inda a nan take Umman Deena ta tura kuɗaɗe a kan wasu kayan da zata siya, Hajiya Hauwa ta ce “Baccin dai ga yadda aka tsara a auren Deena, da sai ki sai mata wasu masu kyau, tunda wanka zata koma”, baki Umman Deena ta ɗan taɓe “Gaba da yawa ai”, Hajiya Hauwa ta ce “Hakane.”

A ɓangaren Dr. Safiyya kuwa tuni sun gama tsare-tsarensu na fidda Deeni ƙasar India, mafarin asubar fari ta kira Deeni tare shaida mashi zasu zo anjima.

Tunanin me zai kawo ta ne ya ɗan rage mashi fargabar da ya kwana da ita a rai ne, shaida ma Lalu ya yi cewar Dr. Safiyya zata zo, Lalu da a kusan ya ji komai ya ce “Allah ya kawo su lafiya”, Deeni ya ce “Amiiiin.”

Jin alamun Lalu na shirin fita ne ya tambaye shi “Ina zaka je?”, Ya ce “Ɗakin Hajjah”, sai da Deeni ya ɗan rausaya kai kafin ya ce “Ƙarfe nawa yanzu?”

Power wayar Lalu ya danna ta kawo haske, sannan ya kalli Deeni ya ce “Ƙarfe bakwai yanzu”, cewa ya yi “Okay, muje toh”, miƙewa Deeni ya yi, Lalu ya kama hannunsa suka fice, kai tsaye ɗakin Hajiyarsu suka isa, kan kujera Deeni ya zauna da taimakon Lalu, rashin jin muryarta ya sa Deeni tunanin ko bata cikin ɗakin, mafarin ya tambayi Lalu “Ina Hajiyar?”, kusan a tare shi da Asma’u da ta shigo yanzu suka haɗa baki wurin faɗin “Sallah ta ke”, Kai ya jinjina “Okay”, lokaci ɗaya kuma ya amsa gaisuwar Asma’u.

Shi kuwa Lalu bai isa ta gaida shi ba, don haka bai kalle ta ba ma, bare ya sa rai. Deeni kuwa a ransa ya ce “Duk za ku bari”, saboda shi ma sun yi wannan ƴar tsamar da Asiya, tana yin aure basu ƙara ba.

Hajiyarsu tana gama addu’ionta ta ce “Kun shigo?”, Lalu ya amsa “Eh Hajjah, barka da Safiya”, ta ce “Barka dai, an tashi lafiya”, Bayan Lalu ya amsa ne shi ma Deeni ya gaishe ta, cike da tausayinsa ta amsa, don rutsum bata yi barci ba, saboda ta kasa gane inda maganar Hajiya Hadiza ta dosa, fatanta kawai shi ne Allah ya sa su ji Alkhairi.

Faɗa mata Deeni ya yi cewar yau Dr. Safiyya zata zo, ta ce “Allah ya kawo su lafiya”, ya ce “Amiin”, tambayar shi ta yi “Ta faɗi lokaci?”, Ya ce “Eh, around ten ne”, ta ce “Okay.”

Rufe bakinsa ke da wuya wayarsa ta shiga ruri, Asma’u dake gefensa a hannun kujera ya ba ta duba mashi, ɗan leƙawa ta yi kafin ta ce “Dr. Rahila ce”, kai ya ɗan rausaya “Okay”, ɗaga kiran ya yi da sallama, bayan sun gaisa ne take shaida mashi cewar zasu zo tunda weekend ne, sosai ya nuna mata jin daɗin sa tare da faɗin “Allah ya kawo ku lafiya”, ta ce “Amiiin.”

Bayan ya aje wayar ne ya shaida musu cewar Rahila da ƴan gidansu ma zasu zo, Hajiyarsu ta ce “Lallai yau muna da baƙi”, sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce “Wallahi kuwa”, saboda bai so zuwansu a yau da yake cikin mood marar daɗi ba.

Ta ɓangaren Lalu kuwa murna fal da cikinsa, saboda tsananin ƙaunar da yake ma Rahila.

Gidansu a koda yaushe tsaf yake saboda suna da Almajirai masu yi musu shara da wanke-wanke, kuma ko ba Almajirai Asma’u na iya ƙoƙarinta, saboda juju ɗin da ke cike da kanta masu tsafta ne har ta wucewar misali.

Breakfast suka yi, sannan Lalu ya fita don yo musu cefane, yana dawowa ya tarar da Salma a tsakar gidan, gabanta ya ajiye cefanen lokaci ɗaya kuma bakinsa na faɗin “Kin zo a kan gaɓa”, don ya san aikin ya yi ma Asma’u yawa, cewa ta yi “Aikuwa ba, an ce baƙi zaku yi”, ya ce “Eh”, ɗan duƙawa ya yi tare da rage murya “Dr. Rahila ce, don Allah a yi girkin ya yi daɗi Aunty Salame”, da dariya ya ƙarashe maganar, itama tana dariyar ta ce “Baka da case, hala itama ta shiga layi?”, Saboda ta san halinshi na son ƴan mata, amma fa sai masu class, ba masu kambusharanci ba.

“Kamar kin sani, so nake a garin nan in bayyana mata matsayinta a raina, don idan har zata amince, toh tsaf zan aure ta”, ba ta son sare ma ƙanenta guiwa, mafarin ta ce “Toh Allah ya tabbatar, amma yadda ta ga hoton Rahila, da kuma labarin daular da ke gidansu ta san ta fi ƙarfin Lalu.

Ɗakinsu ya wuce, ita kuma ta ɗauki cefanen ta shiga ɗakin Hajiyarsu don ta gani. Cefane ne mai kyau, Nana ne da ƴan cikin rago, sai kuma kaji manya guda uku, tambaya Salma ta yi “Nan duka nawa?”, Hajiyarsu ta ce “Allah kaɗai ya sani, Lalu ne bawan Allah, wannan duk da kuɗinshi fa”, Salma ta ce “Allah Sarki”, wannan ne ya sa suke son ƴan ‘uwansu, don basa baƙincikin kashe kuɗi a yi hidimar fita kunya ko nawa ne kuwa, sai da Lalu ya sha yabo kafin Salma ta ɗauko cefanen ta fito.

Kiciɓus suka yi da shi a tsakar gida, cike da son yaba ma ƙoƙarinsa ta ce “Cefane ya yi kyau Uncle Lalu”, ya ce “Ai sai da na je wurin mai kyau”, tambayar shi ta yi “Nan na nawa ne”, kai ya girgiza yana ƴar dariya “Abar kaza cikin gashinta kawai”, ta ce “Ko?”, Ya ce “Eh, kin san dai cefane ya yi tashin gwauron zabi”, ta ce “Kai dai bari, Allah ya sa mu dace”, ya ce “Amiiiin.”

Gyaran ta shiga yi, yayinda Asma’u kuma ta yi Kitchen ta kama wani aikin, cikin ɗan lokaci suka ci ƙarfin aikin.

Dr. Safiyya gab da azuhur suka zo ita da wani handsome ɗin matashi, wanda da alama shi ma Dr ne, cike da girmamawa aka tarbe su a gidan, bayan sun gama gaisawa ne kai tsaye Dr. Safiyya ta bayyana musu abin da ke tafe da su cewar Deeni zai fita India nan da two weeks masu zuwa domin duba lafiyarsa.

Tamkar almara suka ji maganar, Hajiyarsu Deeni kuwa bata san lokacin da ta fashe da kukan daɗi ba, don itama burinta kenan, toh sanin basu da ƙarfin fita waje ne shi ya sa ta bar maganar a ranta.

Godiya sosai suka yi musu, Dr. Safiyya ta ce “Ai Deeni ya wuce haka ma Hajiya, don taimakon Deeni taimakon kai ne”, Hajiyarsu ta ce “Duk da haka dai, Allah ya saka maku da mafificin Alkhairi”, suka ce “Amiiin”

Dr. Bashir da suka zo tare ne za’a yi tafiyar tare da shi, don shi a can ma za’a baro shi zai tsaya karatu, sai kuma mutum ɗaya da ake so a danginsa, Asma’u na ji ta daka tsalle “Hajja don Allah a tafi da ni, kin san ina son zuwa India”, wani kallo Lalu ya yi mata tare da faɗin “Ke kauce! Duk a rasa wanda za a je da shi sai ke”, Hajiyarsu ta ce “Faɗa mata dai Lalu”, su Dr. Safiyya kuwa sai dariya suke mata, don sun fahimci wauta ce kawai irin ta Asma’u.

Dr. Bashir ne ya sa baki a maganar “Da gaske kina son India?”, sai da ta haɗiye haushin da ta ji kafin ta ba shi amsa da “Eh wlh”, kamar da wasa ya ce “Zaki je Insha Allah”, cike jin daɗi ta ce “Allah ya sa”, idanun Dr. Bashir ƙyam cikin nata ya ce “Amiiin, amma wannan tafiyar namiji ake so ba mace ba”, don ta maida ma Lalu martanin abin da ya yi mata ta ce “Yo ni abin da zan yi wani namijin ko kuɗi aka ba shi ai ba zai iya ba”, da hararar gefen da Lalu yake ta ƙarashe maganar, kafa ɗakin ba wanda bai yi dariya ba, don duk sun gane inda ta dosa, Lalu na dariya ya ce “Ke dai kika sani.”

Ficewa ta yi daga ɗakin, inda suka cigaba da magana, nan aka buƙaci passport ɗinsu, tuni da ma suna da shi, Salma ta ce “Lalu yaushe ka mallaki Passport?”, ya ce “Tunin duniya Madam, saboda ko Allah zai jefo wata dama”, tana dariya ta ce “Gashi kuma Allah ya jefo.”

Maganar serious aka koma, inda aka shirya zasu je su yo visa, don duk rintsi ba a son su wuce four weeks basu tafi ba.

Tabbas Deeni ya tabbatar da babu mai yi sai Allah, shi ne gatan kowane bawansa, don haka ko ya ɗaura maka lalura da Rahamarsa ne kuma zai baka mafita.

Bayan ya gama gode ma Allah a fili da kuma ɓoye ne ya maida dubansa na zunci a inda yake jiyo muryar Dr. Safiyya, cike da respect ya sunkuyar da kai tare da faɗin “Thank you so much Maa, Allah ya saka da mafificin Alkhairi, Nagode”, cike da tausayinsa ta ce “Ai ba komai Deeni, Allah dai ya baka lfy”, ya ce “Amiiiin Maa”.

Sun sha godiya sosai a wurin ahalin gidan, daga bisani suka fara shirin tafiya, Hajiyarsu Deeni ta ce “Gashi kuma ba a gama abinci ba”, Dr. Safiyya ta ce “A’a, wata rana zamu ci Insha Allah.”

Dr. Bashir kuwa sai wurga idanu yake yana son sake ganin Asma’u amma bai ganta ba, jiki ba wani karsashi ya riga su fitowa daga gidan, cikin ikon Allah kuwa suka yi arangama da ita a waje, wata irin ajiyar zuciya ya sauke ta jin daɗi, bakinsa na murmushi ya ce “Madu”, cike da rashin fahimta ta ce “Madu?”, Lokaci ɗaya kuma tana ɗan jujjuya idanunta alamun nazari, amsa ya bata “Madubala uwar kyau mana”, wani irin kayataccen murmushi ta yi haɗe da ƴar dariya”, cewa ya yi “Ba ni contact ɗinki, zamu yi batun tafiya India”, ba kowa ne namiji Asma’u ke iya ba number ba, amma cikin sauƙin kai ta karɓi phone ɗinshi ta sanya mashi number.

Jin motsin su Dr. Safiyya ya sa shi saurin karɓar wayar “Thanks, and zamu yi magana”, ta ce “Okay”, tare da shigewa ciki, da idanu ya raka ta, lokacin kuma su Dr. Safiyya sun fito tare da rakiyar Deeni da Lalu.

Suna cikin ƙara maganar tafiyar kenan wata Jeep baƙa ta shigo layin, ko Deeni da baya gani, sai da ya jikinsa ya basuko su waye, Dr. Safiyya kuwa cewa ta yi “Wa nake gani kamar Rahila.?”

 

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 20Mutuwar Tsaye 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×