Skip to content
Part 26 of 26 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Cike da kumfar baki Umman Deena ta nuna ta da yatsa, lokaci ɗaya kuma tana faɗin “Kitattara kayanki ki bar mani gida don Ubanki, in dai a kan Deeni ne kamar yadda na faɗa yafe ki, kin ga na daina ganinki bare baƙincikinki ya kashe ni, wanda kuma ya zalinci wani ni da ke Allah ya isar mashi.”

Mutuwar zaune Deena ta yi, don bata yi zaton abin ya yi girman gaske haka ba, duk da raba ta da Deeni fitina ce a gare ta da bata misaltuwa. Idanunta a rumtse ta riƙa naɗar maganganun mahaifiyarta masu ɗauke da guba, domin harshen uwa cike yake da samatsi, saboda duk abin da ta furta ma ɗanta toh da wahala idan bai tabbata ba, Alkhairi ne abin ko sharri, shi ya sa hankalin Deena yake tashi idan mahaifiyarta ta yi fushi.

A yanayin da Deena ta shiga ya ci ace ta tausaya mata, amma sai da ta gama zage ta tas, sannan ta fice ta bar mata ɗakin a buɗe.

Da ace mutuwa zata zo ta ɗauki Deena a wannan lokacin, toh da ta yi farinciki, domin ita kaɗai ce hutu a gare ta. Raihan ma da take matuƙar tausayi ta san Babansa ba zai bari ya yi kukan rashin Uwa ba. A hankali ta janye hannunta dake dafe da kumci, Jiki ba ƙwari ta ɗauki Raihan da ke ta tsala kuka ta ba shi abincinsa a baki, “Allah ka ɗauki raina in huta”, ta faɗa cikin ranta, lokaci ɗaya kuma idanunta na cigaba da zubar da hawaye.

A bangaren Deeni kuwa, tuni tashin hankali ya kashe mashi jiki, ganin kuma za a iya gane mashi ya sa shi tashi da nufin fita, “Ina zaka je?”, Hajiyarsu ta dakatar da shi, saboda lokacin komawarsa ɗaki bai yi ba, amsa ya bata “Ɗaki zan koma da zama”, sosai ta gane ɗanta na cikin ruɗani, kuma komawarsa ɗaki ce kaɗai ya fi buƙata domin faɗaɗa tunanin yadda zai ji da wannan ƙaddara.

Cewa ta yi “Toh”, tare da bin sa da idanu lokacin da ya nufi ƙofa, “Ka kula mana, ko ka kira Lalu ya zo ya fidda ka”, ta faɗa tare da ƴar zabura, sakamakon karkacewar da ya yi har ya kai ma ƙofa karo, “Toh, zan iya fita”, ya faɗa cike da ɗacin rai, don duk lokacin da irin haka ta faru ko da farinciki yake yana jin ƙuna, bare kuma da yake cikin baƙinciki. Ita kuwa da a ce zata iya tashi, toh ita zata kai shi har ɗakinsu, toh ciwon ƙafa ya sanya ta a gaba, “Allah ya shiga lamarinka”, ta faɗa a bayyane lokacin da ya saita sandarsa ya fice ɗakin.

Jiri da kuma magagin rashin gani suna ɗibarsa ya kai kansa ɗakinsu da ƙyar. Yana jinsa kusa da gado ya saki sandar a ƙasa. Wayar ma bai san lokacin da ya wurga ta saman gadon ba, jiki a mace ya laluba gami da kwanciya kan kafaɗarsa a makure, a wannan yanayin da yake ciki ko da idanunsa lafiya lau suke ba zai iya buɗe su ba, bare kuma yana cikin halin makanta. “Me kuma zai sake faruwa da ni ne?” Ya yi ma kansa tambayar da ya san mutuwa ce amsarta, don zai iya rayuwa ba idanu, amma ba zai iya rayuwa ba Deena ba. Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro, inda suka dire kan fillon da ya aje kansa, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya furta, hannunsa da ke shimfiɗe a jikinsa ya rumtse gam, don ji yake kamar ya kurma ihu. Tabbas Deeni na cikin tashin hankalin da a yanzu suruka ce ta sanya shi. Hango kansa yadda zai iya rayuwa ba tare da Deena ba ya riƙa yi, anya kuwa zai iya?

Zuciya ce ta ingiza shi kiran Deena don jin wane hali ita kuma take ciki, daga kwancen ya riƙa laluben wayar a gabansa da bayansa, sai dai bai ji ta ba, yunƙurawa ya yi da nufin tashi zaune, aikuwa ya harba wayar da ƙafarsa har ta faɗa ƙasan gadon ta tarwatse, bai ba kansa wahalar sauka ba, don bai san ta ina zai fara tattara ta ba, komawa ya yi ya kwanta tare da cigaba da kai kukansa wurin Ubangiji, domin a wurinsa dukkan mafita take.

Lalu na shigowa ɗakin ya hangi wayar Deeni a tarwatse “Subhanallah”, ya faɗa, lokaci ɗaya kuma ya dubi Deeni da ya ba shi baya, cike da tausayinsa ya duƙa ya tattara wayar sannan ya haɗa ta ya kunna, “Yaya ga wayar”, ya faɗa tare da saƙa ma Deeni ita a hannu, daga kwancen Deeni ya ɗan jinjina kai, don ba zai iya buɗe baki ba, bare ya yi mashi godiya.

Lalu bai daɗe cikin ɗakin ba ya fice cike da tausayin ɗan’uwansa. Hakan ya ba Deeni damar ta shi zaune, ɗaukar fillon ya yi haɗe da jingina sa a kan gadon, ɗan kwantar da bayansa ya yi kan fillon sannan ya danna ma number Deena kira, sau biyu tana tsinkewa bata ɗaga ba, sai a kira na uku ne ta ɗaga kiran, tambayar farko da ya fara yi mata ita ce “Kuka kika yi ko?”, ba musu ta amsa mashi da “Eh”, saboda dakushewar da muryarta ta yi.

Idanunsa a lumshe ya ce “Mommah ce zata raba mu ko?”, ta ku ma cewa “Uhmm”, ɗan shiru ya yi, kafin daga bisani ya ce “Deena, ban san ya rayuwata zata kasance idan babu ke ba, ina ji a jikina mutuwa zan yi”, yana rufe baki wasu hawayen da bai iya tsaida su suka gangaro mashi a kumci. Fashewa ta yi itama da kuka, bai kuma lallashe ta ba, don shi ne kaɗai a bin da ya rage musu, cewa ta yi “Ni ce zan mutu Yaya, ban san me na yi ma Mommah ba, bata ƙauna ta, ta raba ni da kai, kuma ta dake ni, wai na bar mata gidanta.”

Yadda kukanta ya rinjayi nashi ne ya sa shi haɗiye nasa da ƙyar, lallashinta ya riƙa yi ta hanyar faɗin “Ki yi haƙuri kin ji Dear, Mommah tana ƙaunar ki, shi ya sa ta zaɓi rabamu, don ba zata so ki sha wahala ba.”

“Haba Yaya! Akwai wahalar da takai raba ni da kai?”, kai ya girgiza kamar tana a gabansa “Babu Deena”, domin ya san yadda take tsananin ƙaunarsa, sai dai duk da haka ya faɗa mata hukuncin da suka yanke, cewar ba zasu sake jayayya da mahaifiyarta ba, zasu yi duk abin da take so domin zaman lafiyar dukkansu.

“Yaya mutuwa zan yi”, daga can ta faɗa cike da razani, don bata yi zaton Deeni zai iya faɗa mata kalmar rabuwa da ita ba, cewa ya yi “Deena ni ne zan mutu in huta, ke kuma zaki rayu ki kula mani da ɗana”, yana rufe baki ya fashe da kukan tausayin kansu.

Toh shi da wane zai ji? Rashin idon da ya ja aka guje shi, ko kuma rashin matarsa? Kuka suka sha sosai, aka rasa wanda zai lallashi wani a cikinsu.

Idan muka koma wurin Rahila kuwa zuciyarta ta kasa sukuni, babban fatanta shi ne mahaifiyar Deena ta ƙwace ƴarta, hakan zai bata damar kutsa kai cikin zuciyar Deeni cikin sauƙi. A ƙasan ranta ta san wannan fatan da take mugunta ce, sai dai ta kasa hana kanta, saboda so da ya rufe mata ido, duk da ita ɗin ba muguwa bace, a wani bangaren na tunaninta ma bata ƙi Deeni ya haɗa su ba, toh ta san hakan ba mai yiyuwa ba ne.

“Allah ka cika mani burkina, ka sa Deeni ya zama mijin aurena, ba don halina ba ya Allah”, ta faɗa, lokaci ɗaya kuma idanunta na akan system ɗinta da ke kan table. Knocking ta ji an yi alamun ana son shigowa office ɗin, idanunta a kan ƙofa ta ce “Yes.”

Wanda ta tsani gani ne a hospital ɗin wato Dr. Salim, don ya manne mata, shi a nashi rawar kan ta amince mashi su yi aure, bayan muguwar shaidar son matan da aka yi mashi, don kusan ƴan matan hospital ɗin ba wadda bai ce yana so ba, sai dai son da yake ma Rahila na gaske ne, fatansa kawai ta amince mashi su yi aure, ita kuma ko ba son Deeni a ranta ba zata iya soyayya da Salim ba, bare har ta kai su ga aure, bare kuma a makance take, bata iya jin zata so wani idan ba Deeni ba.

“Ɗan wahala”, ta faɗa a ranta, a zahiri kuma amsa sallamar da ya yi mata ta yi, shi kuwa idanunsa ƙyam a kanta ya ce “Barka da safiya ranki ya daɗe”, ba tare da ɗauke idanunta a kan system ɗin ba ta ce “Barka dai”, da hannu ta yi masa alamun ya zauna.

Ƙunshin da jan lallen da ta yi ma yatsunta ne ya tafi da shi, a slow ya zauna kan kujerar tare da ƙare ma yatsun kallo, kasa haƙuri ya yi har sai da ya ce “Madam wannan lalle ɗan Madina ne ko Sudan.?”

Rumtse yatsunta ta yi haɗe da sauke ajiyar zuciya, dubansa ta yi kafin ta ce “Abin da ya kawo ka office ɗina kenan?”, yadda ta fusata ne ya sa shi langaɓar da kai “No Ranki ya daɗe, kawai ƙunshin ne ya yi kyau”, ta ce “Toh Nagode, ka faɗi abin da ya kawo ka, don ina da aiki”, ta zaɓi yi mashi haka don ta gaggauta ficewa ya bata wuri.

Ko kusa bai ji daɗi ba, amma sai ya danne ma ransa tunda son ta yake. Kai tsaye maganar Patient ɗin da za a yi ma aiki da yammacin yau ne, wanda har sun iso, kuma ita ce ja gaba wurin aiki.

“Okay, ba damuwa, zan fito yanzu”, ta faɗa a takaice, rufe bakinta kenan kiran Lalu ya shigo wayarta, da hanzari ta ɗaga kiran, inda suka cigaba da gaisawa, ƴar hirar da suka fara ce ta mantar da ita wani Salim da ke zaune a gabanta. Shi kuwa kishi kamar ya kashe shi, fuu! Ya tashi gami da ficewa office ɗin. Baki ta taɓe, inda suka cigaba da hirarsu da Lalu a wayar, suna gamawa ta rufe system ɗin, sannan ta fice itama, cikin ranta tana jin wani sanyi, duk da ba da Deeni ta yi magana ba.

Da alamun burin Rahila na dab da cika, don kuwa yadda su Deeni suka ɗaukar ma ransu haƙura da Deena haka aka yi, sai dai ba kai tsaye ba, tunda ta inda aka hau, ta nan ake sauka. Walliyyan Deeni da suka haɗa da Alhaji Bala, da Alhaji Musa, waɗanda yan’uwa ne a wurin mahaifansa, sai kuma Khamis da yake matsayin Babban Yaya. Har gida suka taras da Alhaji Lawan a kan wannan batu, inda ya sauke su a garden ɗinsa, don Umman Deena ma bata san sun zo ba har sai sun tattauna a matsayinsu na maza kafin su zo ta kanta.

“Ban so kuka sa ka ni a zancen nan ba, domin tuni mahaifiyar Deena ta cire ni a ciki, a raggon tunanin ta shi ne don ba ni na haife Deena ba, shi ya sa nake insisting a kan ta barta da mijinta”, ran Alhaji Lawan ba daɗi ya faɗa musu haka, lokacin da suka zayyana mashi abin da ke tafe da su, gaba ɗanyansu sai da kowa ya girgiza kai, don sun jiye masa ba daɗi, Alhaji Bala da ke kusa da Alhaji Lawan ya ce “Wani raggon tunanin sai mata, idan ɗanta ne wannan ƙaddarar ta sama zata so ayi musu haka?”, Alhaji Musa ya ce “Kai dai bari”, Alhaji Lawan ya ce “Ita ai bata yi wannan tunanin ba.”

Khamis dai “Allah ya kyauta” kaɗai ya iya cewa, saboda lamarin Umman Deena na sosa mashi rai, don inda shi ne surukinta da tuni gayyar ma ta watse, don bai zai iya tolerating wannan wulaƙncin nata ba. Sosai Alhaji Lawan ya nuna musu ya zare hannunsa a cikin wannan magana, amma zai kira musu ƙanen mahaifin Deena su ji ta bakinsa. Sun ji daɗin haka, wayarsa ya fiddo aljihu ya kira number, bugu biyu ya ɗaga da Sallama, bayan sun gaisa ne Alhaji Lawan ya ce “Yauwa Barrister, maganar Deena ne, ban sani ba ko kun yi wata magana da mahaifiyarta akan lamarin aurenta?”, daga cikin wayar Barrister ya ce “Eh Alhaji, jiya Hajiya Hadiza ta kira ni tana faɗa mani zata raba Deena da mijinta, da muka nemi ba’asi sai ta ce saboda yanzu baya gani. Na so nuna mata illar hakan, tunda ba shi ya ce ya fasa ba, sai ta ce ai ba shawara take nema a wurinmu ba, kawai ta kira ta faɗa mana ne, don kada mu ji labari a wurin jam’ar gari.”

Handsfree wayar take, don haka ba wanda bai ji me Barrister ya faɗa ba, girgiza kai kawai suka riƙa yi suna suna sauraron yadda Barrister ke ta sababi, daga ƙarshe Alhaji Musa ya karɓi wayar suka cigaba da magana, inda ya ce “Toh zamu yi abin da take so, zamu bata ƴarta kawai”, Barrister ya ce “Wannan shi ne dai-dai, don Hadiza ba zata bari ku zauna lafiya ba”, Alhaji Musa ya ce “An gama fa Barrister, godiya muke.”

Miƙa ma Alhaji Lawan wayar ya yi suka ƙarasa magana, a nan Barrister ya ba shi haƙuri kan abin da Hajiya Hadiza ta yi mashi. Sallama suka yi, Inda Alhaji Lawan ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin “Kun ji me waliyyanta ya ce ko?”, suka amsa “Eh”, ya ce “Toh duk hukuncin da kuka yanke mai kyau ne”, Alhaji Bala ya ce “Ai hukuncin ɗaya ne, zamu sakar mata ƴarta yanzu, ko ba haka ba?”, ya ƙarashe maganar yana kallon Alhaji Musa da kuma Khamis da suke jere, Alhaji Musa ya ce “Ƙwarai kuwa”, Khamis dai ya gaza cewa komai, saboda mutuwar aure bata da daɗi, sai ya tuna lokacin da saki A’isha, da irin damuwar da shi da ita suka shiga, duk da irin kulawar da yake samu a wurin Maryam, amma hakan bai hana shi kuka da hawayensa ba, bare kuma yadda ya san yadda Deeni ke ƙaunar Deena, haƙiƙa yana tausayinsa, shi ya sa ya kasa cewa komai.

Wayar Hajiyarsu Deeni aka kira tare da shaida mata abin da Walliyyan Deena suka ce, aikuwa ta ce “Kafin ku baro gidan ku bada takardar Deena, shi kuma Allah na tare da shi, na san ba zai wulaƙanta mani shi ba.”

Yadda tace haka aka yi, cikin mota Khamis ya je ya ɗauko jotter da pen bisa ga Umurnin Alhaji Bala, miƙa ma Alhaji Balan ya yi “Ga shi Alhaji.”

“Ai kai zaka rubuta sakin”, Ras gaban Khamis ya faɗi, a marairaice ya ce “Ba zan iya ba Alhaji”, wani kallo ya watsa mashi “Au ka zaɓi a cigaba da tozarta ɗan uwanka don ya makance ko?”, kai Khamis ya girgiza, “Ba haka bane Alhaji”, Alhaji Bala ya ce “Toh rubuta mata saki ɗaya ka bani takardar nan.”

Jagwab Khamis ya zauna a kan kujera, hannunsa na kyarma ya rubuta takarda mai ɗauke da saki ɗaya, miƙa musu ya yi, bayan Alhaji Musa ya gama karantawa ne Alhaji Lawan ya ce “Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi”, suka ce “Amiiiiin.”

Su kansu tunda aka rubuta takardar suke jin gidan ba daɗi, ƴar magana kaɗan suka ƙara, daga bisani suka tafi. Cikin gida Alhaji Lawan ya koma, a falo ya taras da Umman Deena ita da Aunty Hafsat suna hira, ba tare da kalli inda suke ba ya ce “Ki same ni a ɗaki.”

Sosai Aunty Hafsat ta sha jinin jikinta, don ko ɗazu ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar ta, duban Umman Deena ta yi “Wai ko dai mun yi ma Alhaji laifi ne?”, baki Umman Deena ta ɗan taɓe “Ke rabu da shi, bari in je in ji”, tashi ta yi ta bi bayansa a babban falonsa.

Gefensa ta zauna a kan kujera two seater, fuska a kicincine ta ce “Ga ni”, sauke mata g

irman kanta ya yi ta hanyar miƙa mata takarda “Karɓi.”

 

 

 

 

 

 

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 25

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×