A yamutse ta tambaye shi “Takardar miye?”, amsa ya bata a taƙaice “Abin da kike so ne”, sosai kanta ya kulle, don har yanzu bata fahimce shi ba, “Kamar ya abin da nake so ne Alhaji? Ka yi mani bayani mana”, ta faɗa a tsiwace.
“Takardar Saki ce, don haka ki buɗa ki karanta”, ras gabanta ya faɗi, har ta suɓutar da takardar a jikinta ba tare da ta sani ba hankalinta a tashe ta jefo mashi tambaya “Kana nufin ka sake ni?”, domin abin da zuciya ta ruwaita mata kenan.
Bai bata amsa ba, sai ma ya tsaya yana karantar firgicin da ya bayyana a cikin muryarta da kuma fuskarta, wanda ke nuna ba zata iya jurar mutuwar nata auren ba, amma saboda isa da mulkikin mallaka zata kashe na ƴarta, hannunta mai kyarma ya bi da kallo lokacin da ta ɗauki takardar a kan cinyarta kafin ya ce “Ki buɗa ki karanta mana, ba kin iya karatu ba.?”
Ai buɗawa tare da karantawa ma dole, ko da kuwa bai ce ba, wani yawun tashin hankali ta haɗiye kafin ta warware takardar, gabanta na dukan uku-uku ta fara karanta “Ni Deeni, na rabu da matata Deena saki ɗaya, amma ba don son raina ba, sai don bin umarnin mahaifiyarts, wadda ta matsa in bar mata ƴarta saboda na kamu da lalurar makanta..”
Yadda numfashinta ke fita da sauri-sauri ne ya sa Alhaji Lawan faɗin “Kin ɗauka sakin ki na yi ko?”, kasa magana ta yi, sai dai ta ɗaga mashi kai ba tare da ta sani ba “Uhmm”, girgiza na shi kan ya yi “Na san dama za a raina! Toh kamar irin haka ne kika jefa ƴarki a bala’i, don haka sai ki san yadda zaki fidda ta.”
“Ni ba bala’in da na jefa ƴata, don haka ka daina ma faɗar haka”, ya ce “Ko ban faɗa ba, duniya zata faɗa, don haka gwara tun yanzu ki fara ji a bakina”, cike da gadara ta ce “Wai Alhaji me ya sa ba zaka fahimce ni bane?”, ya ce “An ƙi a fahimce ki, kuma idan kika dame ni kema zaki fita da takarda biyu a yanzu, taki da ta ƴarki”, a hasale ta ce “Ni zaka saka?”, nuna mata ya yi ya fi ta gadara ta hanyar faɗin “Ko kin fi ƙarfin sakin ne?”, ta ce “Ban fi ƙarfi ba, tunda ba gidan ubana ne ba, kuma na iya jure mutuwar miji ma? Bare kuma saki?”, ya ce “In dai ni ne zaki gani, sai na nuna maki nima ƙwallon shege ne.”
Aikuwa tana jin haka ta yi shiru, don ta fahimci da gaske yake, kuma idan ya sake ta ina zata je ma?, dolenta ta juya akalar faɗan wurinsu Deeni, don bata yi zaton takardar Deena zata zo haka da sauƙi ba. Tabarmar kunya ta shiga naɗewa da hauka ta hanyar faɗin “Gwara ma da basu wahalar da shari’a ba, don ba zan lamunci a bautar mani da ƴa ba.” Ta ƙarashe maganar tana kallon takardar.
Baki kawai Alhaji Lawan ya taɓe tare da faɗin “An faɗa maki su ƙananan mutane ne kamar ki? Ai basu da lokacin ɓatawa ga mutum irin ki, kuma wlh you must face the consequences of your bad action, ban maki baki ba Hadiza, amma daga yau zaki fara regret”, yana rufe baki ya miƙe ya bar mata ɗakin, ƙasan ransa yana jin ɗacin kunyatar da shi ta yi a idon jama’a, don ta nuna ma duniya bai isa a kanta ba, don haka ya ɗaukar ma ransa wahalar ɗaukar ma Deena fansa tun daga yau.
Da idanu ta raka shi tana faɗin “Ki ji mani ɗaukar ɗaukakkiya! Wato kai ka tura ƴaƴanka Abuja da ƙasashen waje, shi ne ni zaka hana ni neman ma ƴata ƴancinta, toh fushinka na banza ne”, ko kusa bata yadda laifi ta yi ba, bare ta fara tunanin sauko da kanta.
Naɗe takardar ta yi kana ta fice itama, cikin shirin tafiya ta iske Aunty Hafsat “Ya na ga kin yafa gyale?”, ta faɗa lokacin da ta ƙarasa tsakiyar falon, Aunty Hafsat ta ce “Tafiya zan yi”, saboda ta tsorata da mugun kallon da Alhaji Lawan ya watsa mata lokacin da ya fito, Umman Deena ta lura da a tsorace take, mafarin bata matsa ba a kan ta bari sai anjima, kai kaɗai ta rausaya gami da miƙa mata takarda “Ki taya ni murna, an kawo takardar sakin Deena.”
Kasa karɓar takardar Aunty Hafsat ta yi, sai ma ta fara Sallallami gami ta tafa hannu, “Saki fa?”, Umman Deena ta ce “Ai na faɗa maki dama ba zata koma ba, kin ga cikin sauƙi sun kawo mata takardar har gida”, ajiyar zuciya Aunty Hafsat ta sauke kafin ta ce “Allah ya sa haka ya fi alkhairi”, Umman Deena ta ce “Amiin”, miƙa mata takardar ta sake yi “Ki karba ki duba”, ƙememe Aunty Hafsat ta ƙi karɓa, sai ma ta ce “Haba in duba me? Ai Alkhairi ake rububin gani ba sharri ba, Ni jikina duk ya mutu”, Umman Deena ta ce “Ko?”, langaɓar da kai Aunty Hafsat ta yi “Kin san mutuwar aure yadda take, bata da daɗi”, Umman Deena ta ce “Amma ban da irin auren Deena”, Aunty Hafsat da ta gama karantar Umman Deena ta ce “Ke dai Allah ya kyauta”
Jakarta ta saɓa, bata bari sun yi doguwar magana ba “Ni fa tafiya zan yi, ki gaisar mani da Deena idan ta fito.”
Umman Deena ta ce “Na lura dai kamar ana tsunkulinki a gidan nan”, tabbas bata yi ƙarya ba, ƙagare Aunty Hafsat take ta bar gidan, don ko shakka babu sai ta shiga zargi a wurin Alhaji Lawan a kan tunzura Umman Deena. Har bakin ƙofa Umman Deena ta raka Aunty Hafsat, bayan ta dawo ne ta wuce ɗakin Deena, zaune ta same ta a kan stool ɗin gadonta tana danna waya.
Tamkar azara’ulu haka Deena ta ke kallon mahaifiyarta, don ta gama bata tsoro, dakatawa ta yi da danna wayar tana jiran da wace ta zo?
Umman Deena bata damu da yaƙunewar da Deena ta yi ba ta ɗora mata wani bala’in ta hanyar faɗin “Toh daudawa uwar aure, ga takardar sakinki an kawo, ko ki yi haƙuri ki bi ni, ko kuma ki mutu, amma ki sani baki ba Deeni har abada.”
Wata irin faɗuwa gaban Deena ya yi, amma sai ta daure, don ta ɗaukar ma ranta Ummanta ba zata sake ganin gazawarta ba, bare har ta wulaƙanta ta “Allah ka ba ni ikon ɗaukar wannan ƙaddara”, ta faɗa a ranta, a zahiri kuma sai dai ta riƙa kallon Ummanta da ke faɗin “Ni dai ban cutar da ke ba, don haka ya rage naku da ke duk wanda ke ganin na cutar da ke.”
Umman Deena ta yi zaton Deena zata gigice, amma sai ta ga saɓanin haka, mafarin jiki ba ƙwari ta fice ɗakin, inda ta bar Deena da tambayar kanta “Shin da gaske ne yaya ya sake ni? Ko mafarki nake.?”
Deeni ya fi ta buƙatar ace mafarki ne ba gaske ba, don tun da su Alhaji Bala suka koma ya rasa ina zai sa ransa ya huta da wannan masifa, don ma ya yi ta maza wurin nuna musu ba komai bane, hakan ya ma Alhaji Bala daɗi, mafarin ya ce “Allah ya zaɓa maka mafi Alkhairi, amma ina mai tabbatar maka da rabuwa da yarinyar nan shi ne mafita, don uwarta ba zata bari ku zauna lafiya ba”, Hajiyarsu da ke jin bp ɗinta na shirin tashi ta ce “Kai dai bari Alhaji, Allah ya bashi mafita ta Alkhairi”, suka amsa da “Amiiiiin.”
Bayan sun gama jajanta ma Deeni ne Hajiyar ta nemi attention ɗinsu don yi maganar Asma’u, inda ta dubi Alhaji Musa “Toh hausawa suka ce, mutuwar wani, tashin wani”, duk suka rausaya kai, ta ce “Asma’u ce ta samu mijin aure”, Alhaji Bala ya ce “Alhamdulillah”, don burinshi kenan auren Asma’u ya tashi, bai ƙi ba dama ya haɗa ta da ƴaƴanshi uku ya aurar a rana ɗaya ba.
Cigaba ta yi da faɗin “Toh amma shi da sauri yake so, don bai ƙi ba nan da kwana goma an gama komai, idan su Deeni zasu tafi India, sai ya tafi da ita”, Khamis ne ya tari numfashinta “Da shi mai son Asma’un za a tafi?”, ta ce “Eh”, yadda haɗuwar Asma’u da Bashir ta samo asali ta basu labari, da kuma ɗanƙaramin binciken da suka yi a kanshi ya gamsar da su, sai dai duk da haka a matsayinsu na walliyyan Asma’u ta basu damar ƙara bincike.
Khamis ya ce “Ai Alhaji Alhassan babban mutum ne mai nagarta, kuma na san Bashir, baya da matsala, sai dai ƙarin bincike ba laifi ne ba”, Alhaji Bala ya ce “Gaskiya ne, zamu ƙara bincike sosai a kansa, tunda shi aure sai da faɗaɗa bincike”, suka ce”Gaskiya ne”, sun yi magana sosai, daga bisani Alhaji Musa ya ɗauki Alhaji Bala suka tafi.
Khamis kuwa so yake ya ga Deeni privately ya ba shi magana, mafarin ya tsaya nan har aka yi Magrib.
“Deeni, na san kana cikin tashin hankali ko?”, Khamis ya faɗa tare da dafa kafaɗar Deeni, yayin da suke zaune a gefen gadon ɗakinsu Deena.
Deeni ya ce “Ji nake kamar zan mutu, ka taya ni da addu’a, ina cikin jarabawa, ba idanu, kuma ba ƴar jagora, ya kake ganin rayuwar zata kasance?”, cikin muryar kuka ya ƙarashe maganar, cike da lallashi Khamis ya ce “Da sannu Allah zai baka mafita, ka yi haƙuri ka ji”
Shiru suka yi, Khamis na jin kamar ya yi kuka, don tuni Deeni kukan ma yake, wayar Deeni ce ta shiga ruri, ya san Deena ce, mafarin da Khamis ya miƙa mashi wayar ya ƙi karɓa, Khamis ya ce “Why?”, ya ce “Ban san me zan ce mata ba ai, kuma kuka zata yi mani”, Khamis ya ce “No, ka ɗaga, idan ta yi kukan ka bata haƙuri, tana son ka, mamanta ta ja mata”
Bayan Deena ta sake kira ne ya ɗaga, maganar farko da ta fara yi ita ce “Yaya dama zaka iya sakina? Toh ka sani idan na mutu hada kai aka kashe ni”, bata bari ya yi magana ba ta katse kiran.
Sosai maganarta ta soki Deeni, cema Khamis ya yi “Ka ji fa”, Khamis ya ji komai, cewa ya yi “Rabu da ita, zata fahimce ka nan gaba, yanzu duk a ruɗe take.”, Ai shi ma a ruɗen yake, don ba kowace maganar Khamis ce yake fahimta ba.
A wawannan dare sai da su duka suka gwammace mutuwa ta ɗauke su, don kwana suka yi kuka suna sanar da Ubangiji. Hajiyarsu kuwa kwana Asma’u ta yi a kanta, don bp ɗinta ya tashi, tana kukan tausayin Deeni ta ce “Allah ya saka maka Deeni”, don mutuwar auren nan babbar cutarwa ce a gare shi, ko da lafiyarsa lau.
Kamar yadda gidansu Deeni basu yi bacci ba, haka itama Umman Deena ta yi kwanan zaune, a zatonta zata yi farinciki da mutuwar auren Deena, sai ta ga saɓanin haka, don wani baƙinciki marar misaltuwa ne ya mamaye mata zuciya. Ga shi Alhaji Lawan bai kwana a gidan ba, duk da ranar girkinta ne, kuma ta kira waya bai ɗauka ba. Haka ta yi ta juyi a kan gado. Faɗin ɗacin da ta ji a ranta baya misaltuwa, don Alhaji Lawan bai taɓa yin fushi da ita irin haka ba, asali ma basa faɗa, don ta iya zama da miji daidai gwargwado. Wannan kawai ramuwar gayya ce yake mata, akan ƴar da take mashi gorin ba shi ya haife ta ba.
Washe gari wurin ƙarfe goma ya shigo gidan, ko kusa Umman Deena bata ji motsinsa ba, saboda a waje Driver ya tsaya da motar. Ta fito ɗakinta kenan ta ji motsi a ɗakinsa, murɗa handle ɗin ɗakin ta yi, ta hange shi tsaye a jikin mirror yana chanja links. Shigowa ta yi, amma da ita babu duk ɗaya, don bai kalli inda take ba, bare ya ji me take son cewa.
“Alhaji, lafiya baka kwana gida ba?”, a yamutse ya kalle ta “Lafiya lau”, ta ce “Toh amma yau ranar girkina ne fa”, ya ce “Na sani ai”, bai bari ta ƙara magana ba ya fice daga ɗakin ya bar ta nan cike da ƙunar rai.
Kai tsaye ɗakin Deena ya nufa tare da knocking, tana buɗewa ya yi mata kallon tausayi tare da amsa gaisuwar da ta yi mashi, cikin ɗakin ya ƙarasa haɗe da zama kan stool, inda ita kuma ta zauna gefen gado sakamakon goyon da take ɗauke da shi.
Yadda ta koma kamar one ne ya ƙara mashi tausayinta, don duk wanda ya ganta zai fahimci tana cikin bala’in rayuwa, bai wani ɓata lokaci ba ya shiga yi mata nasiha a kan ta yi haƙuri da wannan jarabawar, sannan shi ba don son ransa hakan ta faru ba, sai don yana son ba mahaifiyarta damar da take ganin ita kaɗai ke da ita, daga ƙarshe ya tabbatar mata da komin daɗewa sai ta yi farinciki, tunda ƙaddarar nan haye mata ta yi.
Deena ta ji daɗi sosai, hakan ma ya sa ta ji ɗan sauƙin uƙubar da ke ranta, musamman da ya yi mata albishir ɗin shige mata gaba, ta yadda dukan ba zai zame mata biyu ba.
Tambayar ta ya yi “Kin yi breakfast?”, saboda alamu sun nuna tana jin yunwa, kai ta girgiza, ya ce “Why?”, ta yi shiru. Faɗa sosai ya yi mata akan kada ta bari yunwa ta kama ta, ta dayaye kawai, da sannu zata yi farinciki mai ɗorewa. Da zai tashi ne ya ce ta biyo shi baya, bai zame ko ina da ita ba sai dining. Karɓar Raihan ya yi kafin ta zauna, abinci ya sa aka akawo mata, inda ya tursasa ta riƙa ci da kyar. Ummanta na fitowa ta taɓe baki, duk da fushi take da shi, amma hakan ya mata daɗi, don rabon Deena da falo tun da azuhur ɗin Jiya, tana da yaƙinin bata ci komai ba.
Kai a ɗage ta zo ta wuce su, yayin da Alhaji Lawan shi ma hankalinsa na kan Deena da ya fahimci ta ɗan tsorata da ganin Ummanta, cikin ransa ya ce “Dole a san abin yi kan lamarin nan”, don ba yadda za a yi ɗiya ta riƙa tsoron uwarta irin haka, kuma tafiyar ta yi kyau.
A bangaren ƴan hasidin iza hasada kuwa, wato Dr. Bello, tunda ya ji labarin Deeni zai fita India ya kasa zaune ya kasa tsaye, domin jikinsa na ba shi Deeni zai warke. Abokin ɓarar gujiyarsa ya kira a waya wato Jabiru yare da shaida mashi Deeni fa ƙasar zai bari, daga can Jabiru ke cewa “Na ji fa, Allah ya tsare”, a wurin Bello bai ƙi ba Deeni ya mutu, don haka ba wani fatan Alkhairin da zai yi mashi.
Daga can Jabiru ya ce mashi “Ka kuwa san surukarsa ta ƙwace ƴarta?”, zaune ya tashi daga kwancen da yake a kan three seater, lokaci ɗaya kuma yana faɗin “Da gaske?”, Jabiru ya ce “Haka nake ji a bakin ƙawarta Hafsat, ka ga uƙuba goma da ishirin nen, ba idanun, kuma ba mata.”
Dariyar mugunta ya Bello ya ɓaɓbake da ita, saboda tsabar ƙiyayyar da ya ke yi ma Deeni sai cewa ya yi “Allah ya ƙara.”