Dukkan godiya su tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga annabi Muhammad (SAW).
Sun tozartar da zumuncin da ubangiji yace ayi sun zamo ababen kallo da tuhuma,sun maida waɗancan ruhin tamkar babu su a doron ƙasa duk da cewa suna kusans, hantara da kyama da cusgunawa,dukdan akan ƙaddarar da babu mai ɗora ma kansa ƙaddara kasancewarsu talakawa,shine dalili mafi ƙarfin yanke girman kusancin.
Duk dai a littafin Na Cancanta, labari ne da ita kanta jarumar ke bada shi a yanayin tsarin rubutun,An ƙirƙireshi ne indan labarin yayi kama da naka/ki a yi haƙuri bisa rashin sani ne fata Allah yasa mu anfana ya zama gyara ga wasu fannukan na kuskurenmu.
Farkon Labari
Sumayyah Abdullah Khalil sunana ni hafaffaffiyar garin gwarzo ce,da ta ke karamar hukuma ce dake qarqashin jahar Kano da sana’a ta maida mahaifina cikin birnin Kano bayan haihuwata da muke yanzu zaune a cikin birnin kanon unguwar Gandun Albasa mahaifina Malam Abdallah Khalil da mahaifiyata Hauwa’u nice diyar fari a gurinsu sai kannena Ahmad shine mai bina daganan Rumaisa,Khadija,Sadiq,Khalil da a yanzu shine karaminmu,mahaifina karamin karfi gareshi yadika yake saidawa ficis a kasuwar kantin kwari a gefen kasuwa da runfarsu take wani lokacin kuma zagayawa yake cikin kasuwar,tun tasowata dana soma fahimtar yanayin yadda rayuwarmu take na fara janye jiki ga duk wanda ya fimu karfi,haka burina na zama ma’aikaciyar jarida duk na ajiyesa gefe,burina yau ace na kammala secondary da nake yanzu SS1a government Girls Gadun Albasa na cikin garin Kano badan komai ba saidan hidimomi su fara sauki daga kaina,Mamarmu macace mai zurfin ciki koda garinmu mu kaje sam baza kaji ta fadawa ‘yan uwanta babu ba haka zamu yi kwanakinmu mu dawo dukda kasancewar danginta ba masu kudi bane haka suke kokarin hadomu da kayan abinci dana sawa idan mu kaje,a gurin mahaifiyata na koyi boye sirrina zai wuya maganganuna masu muhimmanci na fadawa wasu musamman rayuwar da muke ciki a gidanmu,danginsu Abba kuwa babu laifi duk masu kudine sai dai suda Abban sam babu taimako idan mukaje gidajensu koda munje Gwarzo ko gidajen wadanda suke anan cikin Kanon babu kyauta tsakaninmu sai jifanmu da maganganu marasa dadi,nasani tun ina karama Abbanmu mai zuciyar neman nakanshi ne sai dai har yau Allah bai kaddara zaiyi arziki mai yawa ba,dukda kasancewar yayi karatu aikin ne garesa yayi wuyar samu,bazance Abba baida sa’ar rayuwa ba,tunda yanada lafiyar fita ya samo na kansa harma ya ishi iyalansa mu shida dashi da Mama suka kasance na takwas kawai abinda na sawa raina arziki ne Allah bai kaddara zai tara ba,irin yanayin da muka tsinci kanmu na hantarar dangi yasa muke zaune guri guda babu mai sha’awar zuwa dangi da gani har kannena,dukda kasancewar mu din talakawane amma sam ba muda kwadayi irin na wasu daga cikin talakawa kamarmu,kai idan bakazo gidanmu ka gani ba dan kaganmu waje tunaninka bazai baka mu talakawa bane sosai dukda bawai kaya bane masu tsada jikinmu amma kullum zaka ganmu kayan jikinmu wanke goge,da ya kasance aikin Mama tun ina yarinya har na girma na dora da yiwa kannena,haka batun abinci babu maiwa Mama korafin abinci a gidanmu musamman idan munyi baki koda munajin yunwar har sai sun tafi,dukda saimuyi watanni ba muga bakinba domin dai da masu kudi akafi harka a yanzu mukam idan anzo kudin mota ma bazaka samu ba,masu kudi kuwa sam indai ba haihuwa ba Mama tayi ba bamai zuwa gurinmu shima haihuwar baza’azo suna dawuri ba da duk dangin Abba ke hakan to mai za suci daga garemu,dan sanin kowane irin rayuwar da talaka yake cikin dangi bama sai an fada ba,Mama idan tayi maganar ba’a zuwa gurinta mamarsu ta kan ce,
“Hauwa’u idan anzo nauyi za’a dora muku,kinsan ‘yan uwanki suma ba karfi garesu ba wata da kyar zata hada kudin zuwa,kuma tana zuwa daga gareki keda Abdullahi zatace tana jiran nadawowa.”
Jin maganar Gwaggo da Mama taji gaskiyace yasa ta hakura da batun son ‘yan uwanta suzo gurinta,batun gidan da muke na haya ne ina tausayin Abba da yadda yake biyan kudin hayar da sai Mama ta hada da nata kudin da take sana’ar cikin gida gishiri,ashana,maggi,Omo da sauransu dukda kasancewar cinikin kayan jefi jefi akeyi dan yawanci unguwar tamu mazajensu ajiyemusu kayan abinci suke komai sunadashi idan ba abun ya kare ba kafin a siyo anan ale cinikin,wasu kuma da su siya gurinka gwara su tafi bakin titi su siyo.
Batun kawa sam ni ba maison tara kawaye bace dan kawata daya ce wadda muka shaku ba laifi Halima Farouk tun daga JS 1 muke tare da yanzu muke SS1 Halimace kawai tun farkon haduwarmu na fahimci tamkar rayuwarmu zata zo daya wannan yasa kawancenmu dorewa,kasancewar itama Haliman bawai ‘yar masu kudi bace,bawai ziyartar Haliman nake ba dan da tazara tsakaninmu,sai dalilin auren da kanwar Abbanmu Aunty Asma’u tayi unguwarsu Halima take ganina shima nakan dade banje gidan Aunty Asma’un ba dan mijin da Aunty Asma’un ta aura mai kudi ne itama kuma Aunt Asma’un tana auren ta fara business har kasar waje take zuwa hakan yasa naja baya da zuwa gidanta danni banison shigewa wanda muke da tazara dashi ta arziki dan na girmama tawa rayuwar,kuma Aunty Asma’un zan iya kirgawa tun aurenta a Kano baifi zuwa biyu tayi gidanmu ba shiyasa nima naja baya da zuwa gidanta dan dama itama baso take aje gidantaba hakan yasa bana sha’awar zuwa,dan tun daga Gwarzo zatayi waya azo a tayata zama idan mijinta bayanan muda muke a guri guda sam bazaka ji ta kirani ba saboda kada na shafawa rayuwarsu talauci nafi yakinin dalilin da take hakan kenan.
Batun tarbiyyarmu iyayenmu suna tsaye kanmu ni da kannnena hakan yasa komai namu yakanzo da sauki dan ko su Khadija da Rumaisa idan angansu waje saidai makaranta ko aike, basa kulafucin zuwa makwabta kwadayi,kai koda an aikesu sunje ruwan gidanma basa sha,idan ko zamu tafi makaranta tare muke tafiya sai sun fara zuwa tasu nake wucewa tamu.
Yau ma kamar kullum mun fito tare nida su Khadija da tun fitowarmu take kunkunai na dube ta.
“Wai ke mai aka miki ne Khadija.”
Ta ‘dan bata fuska
“Yaya yau ma babu,kudin tara,ga makarantarmu da nisa kuma ba kudin Napep,gashi mun makara”tayi maganar tana duba agogon hannnunta.
Na sake duban ta.
“Haba Khadija cikinmu mu hudu wa aka bawa kudin taran,kuma ai munci abinci ko,kuma da zaki maganar kudin Napep ko tafiyar kasa da makara baga Sadiq ba shi da yake karamin yaro baiyi magana ba,Dan Allah ki canza.”
Baki Khadija ta turo
“To shikenan amma Yaya ciyayya muke da kawayena kullum suke kawo abin da zamu ci da zamu ci idan anyi break ni babu abinda nake kawowa,sai suga kamar wayau ne.”
Na dubeta sosai
“Khadija ciyayyya fa,ai kema kinsan wayon ne kike,ke da ko kudin tara a sati baifi ki samu sau ‘daya ba zakiyi ciyayya da mutane,dan Allah ki daina Kinga koni banayi.”
Tace
“Maiyasa Yaya?”
“Kawai bana san gori shiyasa,kinsan idan kanacin na wani ba acin naka watarana sai anyi ma gori.”
Da wannan hirar da muke da Khadija muka karasa special primary dinsu suka shiga su biyu ita da Sadik sai ni da Rumaisa muka wuce tamu da Rumaisa take aji ‘daya a Secondary Rumaisa bata da surutu gata da hakuri halayyarta da Khadija ta banbanta Khadija yarinyace mai son gayu sosai da son ace ita ajin farko take a komaima,kyau dai Allah ya bata dan kaf cikinmu bamai nunawa Khadija kyau,sai dai dukda hakan Khadija bata jure wulakanci,kuma ita bamai son gori bace.
Har muka karaso makarantarmu da har an fara taron makara Rumaisa batayi magana ba.
“Rumaisa Abdallah”naji Sajida kawar Rumaisan ta fada da mukaci karo dasu gurin makarar suma an taresu Rumaisa da bata kula da ita ba sai lokaci gurinta ta karasa,bulalar makarar akayi mana,muka wuce ajijuwanmu,sallama nayi na shiga da a bencinmu ni kadaice nazo,zamana ba wuya Halima ta shigo itama tana aikamin sakon hararar harta zauna.
Na fara tanbayarta
“Haba Halima mai yayi zafi ido zaici wuta mai nayi Miki.”
“Bansani ba ‘yar rainin wayau,tunda na hango ki nake kwala miki kira kikayi banza dani”Haliman ta karasa fadar hakan tana ajiye jakarta gefen tawa.
“Yi hakuri Halima Kena kinsan ban jiki bane,amma ya za’ayi nayi miki shiru,daga wajen ina kika kirani.”
“Kofar makaranta mun sauka a Napep.”
Nace
“Yi hakuri Sady banjiba hankalinmu yayi gurin taron makarar da akeyi.”
“Kice dai baki jiba dan Rumaisa ko taji nasan bazata fadamiki ba,yarinya mai nauyin magana.”
Nayi murmushi da dariyata jin Halima ke korafin nauyin bakin Rumaisa da ita dinma hakan take.
“Ai halinku ‘daya da Rumaisan.”
Ta dubi kanta
“Allah ya kyauta,ni ai ba sunanmu guda ba kece kika koyamata halinki Kika mata wayau.”
Sallamar Batul Ahmad da take itama ‘yar bencinmu ta katse firarmu data shigo wadda ita kawancenmu baikai kawancen da nake da Halima ba Batul na zama malaminmu na physics ya shigo mikewa mukayi muka gaishesa daganan muka fara lesson da ba laifi ana gane karatun Malam Hamid da yake bautar kasa ta kawo shi makarantarmu,sai dai bahaushene ‘dan aalin garin Katsina ne.
Bayan Watanni
Haka rayuwarmu ta cigaba da kasancewar cikin godiyar Allah dan sai nace yanzu al’amura sun sake rinca’bewa fiye da da,dan yanzu Abba saiyaje kasuwa ya yini baiyi cinikin dari ba,wannan abun idan na tuno yakan sani hawaye tare da tuno makomarmu a haka.
Sallamar Halima da naji yasani sauke tagumin da nayi da hannu biyu na kirkiri murmushi na dorawa fuskata,ganin Haliman da nayi da nake zaune tsakar gida ina tsare gida Mama ta fita makwabta barka,yara suna ‘daki suna kallo kasancewar akwai nepa garin,sallamar na amsawa Halima ta zauna gefena akan tabarmar da nake kai gefena ta aje kula.
“Halima mene ne wannan.”
Na nuna kular gefen nawa
Halima tayi murmushi
“Abinda kikeso na kawo miki”
Na dubeta da zaro ido
“Dan Allah fa Alala ko faten doya?”
Tayi dariya
“Faten doya ne,ina komawa gida naga shi muka yi shine nace Mama ta zuba Faisal ya kawo miki,to Mama ta aikesa kasuwa,kawai shine na taho ina fitowa naci Karo da yaya Baffa ya dawo cin abinci shine ya kawoni.”
Ba karamin dadi naji ba dan yau babu abinda muka girka tun safe sai ruwa da nakesha da cikina ya fara kullewa da muka dawo makaranta ma bamu tarar an girka komai ba, Halima na kalla inajin a raina Halima ta kara matsayi a gurina dukda dama tana dashi hawayen da bansan sun zubo ba sai duminsu naji nayi saurin gogewa na dubi Halima
“Halima nagode”
Haliman ta girgiza kai
“Godiya babu tsakaninmu,kuma kukan mai kike,na sani,baki taba kokarin fadamin abinda ya shafi rayuwarki ba amma ni ina kokarin fahimta,Sumayyah idan kina farin ciki nasani,haka idan kina sabanin haka,mainene na hawayen.”
Nayi murmushi
“Babu komai”
“Kya ji dashi dai,ina Mama”cewar Halima
“Ta shiga makwabta,barka yanzu zata shigo”
“Aiko dai sauri nake ki gaidata,tayi maganar tana mikewa
Na dubeta “badai tafiya zakiyi ba,bazaki jira tazo ku gaisa ba”
“tare da Yaya Baffa muke shiya kawoni a adaidaitarsa,kar yayi ta jirana,ko gida bai shiga ba nace ya kawoni ba zama zanyi ba.”
Hijabin Rumaisa dake kan igiya nasa na rakata har gurin adaidaita Yaya Baffa
“Ina yini yaya Baffa”
Ya amsamin da cewa
“Lafiya lau,ya karatu?”
“Alhamdulillah Yaya”
Daganan Halima ta shiga adaidaitar ya ja suka tafi bayan mun yi Sallama.
Yaya Baffa ba mutum ne mai surutu ba iyakacin ka dashi gaisuwa ce,Koda gidansu naje
cikin gidan na dawo inda na tashi na koma na zauna ina jiran Mama ta dawo a kasafta faten dan ba iya yunwar kowa ke jinta musamman Mama da take goyon Khalil a lokacin nasani duk ta fimu ji,bansan a wanne mataki zan aje Halima a cikin zuciyata ba tana bani kulawa da tausayina fiye da ‘yan uwanmu da suke watsar damu saboda mu din ba wasu bane idan anzo gurinmu mai za’a samu dan ko a yanzu kafin kaga mai kudi yana mu’amala da talaka zaka shekara da shekaru kana bincike kafin ka samu,amma Halima tana tare dani tun kafin tasan wacece ni kuma har ta sani hakan bai canza ba,dukda Haliman talakawanne amma a hakan take kokarin kyautatamin ,kafin na fadamata matsalata take fahimta idan tanada maganin hakan tana kokarin yimin,hawaye na goge tunowa da Aunty Asma’u da kaf layinsu Halima da unguwarsu baki ‘daya ba gida irin nata amma da biyar bata ta’ba tunanin kawo mana na nuna kyautatawarta garemu ba,sai Halima da kaf layin gidansu ne na kasa dake zagaye da langa langa,yayyenta maza guda uku ke yin komai na gidan kasancewar mahaifinsu baida cikakkar lafiya hawan jini da ciwan sugar ke damunshi,amma a haka take kokari duk ranar da taga wata damuwa fuskata take kokarin kawomin abinci data koma gida,saboda zuwan da take gidanmu ta fuskanci rayuwartamu.