"Zaman har na nawa ne da zakayi maganar Islamiyya ko kuma zaman ta kenan,nufinka ba zata koma garinsu ba,Samir kana sane dai da cewa Abbanku ba san zaman yarinyar nan yake a gidan nan ba,karka 'dorawa kanka nauyi tun kafin ka aje iyalanka,kamin magana tun kwanaki kan Islamiyya kuma ban goyi baya kasata ba shine kawai magana"Muryar Ummi nake jiyo wa daga falo har zuwa 'dakina da alamun fa'da da nafi tsammanin saboda 'daga muryar da tayi nake jiyowa amma ba na jiyo zancensu,bansan mai Yaya Samir ya fa'damata ba naji. . .