Skip to content
Part 11 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

“Zaman har na nawa ne da zakayi maganar Islamiyya ko kuma zaman ta kenan,nufinka ba zata koma garinsu ba,Samir kana sane dai da cewa Abbanku ba san zaman yarinyar nan yake a gidan nan ba,karka ‘dorawa kanka nauyi tun kafin ka aje iyalanka,kamin magana tun kwanaki kan Islamiyya kuma ban goyi baya kasata ba shine kawai magana”
Muryar Ummi nake jiyo  wa daga falo har zuwa ‘dakina da alamun fa’da da nafi tsammanin saboda ‘daga muryar da tayi nake jiyowa amma ba na jiyo zancensu,bansan mai Yaya Samir ya fa’damata ba naji ta ‘dora da cewa
“To taji mana,ai ba zaginta nayi ba,kawai gaskiya na fa’dama shi Abban naku baka fishi kusanci da ita ba amma yayi biris da lamuranta ko kulata ba yayi akan wanne dalili kai kuma zaka shiga so kake ka qarawa kanka laifi a gurin sa kana gani turka turkar da akayi kafin ya yarda yarinyar nan tazo haba Samir ka riqa tunani mai kyau”
Kaina ne naji ya saramin jin maganganun Ummi da ma Abba baiso zuwana cikin ahalinsa ba ko da yake ba wai abin musu bane dan yanayin da nake gani a gurinsa ya   da’de da fahimtar dani gaskiyar lamari,tunani nake mai nene makomata anan gaba a gidannan, zaman nawa kansa mene anfaninsa,tabbas na fahimci akwai wata qaddarar da take sargafe dani da zamana a cikin wannan ahalin,ban sake jin hayaniyar Ummi ba hakan yasa ni jin da’di ya kuma bani da mar cigaba da tunanina.

Da yammacin ranar na fito a kasalance nake tafiya harabar gidan na nufa dan yau bana sha’awar zaman ko da falon a tsaye na hangosa ya jingina da bishiyar dake harabar gidan da gani tunani yake dan shi bai hango ni ba hakan ya bani damar kallonsa sosai Yaya Samir yanayinsa yana burgeni sam bai da kwaranniya daka gansa zaka fahimta mutumin kirki ne sosai,gurin da yake na qaraso ina murmushi tare da sallama sallamartawa nafi yaqinin ta maidosa tunaninsa yayi firgigit ya dawo daga tunaninsa amsamin sallamar yayi hakan yasa ni gaishesa ya amsamin da murmushi fuskarsa ya kuma yi gyaran murya ya fara magana.

“Sumayya bansan ta ina zan fara baki hakuri ba saboda nasan zaman haquri kikeyi gidan nan daga zuwanki tabbas inaso ki koma garinku a yanzu,sai dai kuma duka zaman da ba’afi sati biyu da kwanaki ba na ce zaki tafi inaga bai kamata ba,dan Allah ki qara haquri”
Shiru nayi na mintina da sai da kyar na iya lalubo amsar da zan basa dan gaskiya nafi buqatar komawa gida da irin wannan zaman da baida wani anfani sam,zama cikin mutanan da basu san zumunci ba
“Bakomai Yaya Samir nima ban gaji da zama ba.”

Ya ce”Sumayyah kenan na sani ba wanda zaizo gidannan yace bai gaji da zama ba,muddin ba yanada abin hannunsa ba,gashi batun islamiyyarki ya rushe,dan Allah kimin afuwa ba laifina bane”
Shiru nayi na maida kaina qasa ina tuno maganganun ‘dazu da kunnuwana su ka ji na dai daure na ce”Bakomai Yaya Samir tunda ba wai zama na kenan ba idan na koma gida zan cigaba da zuwa.”

Ya ce”Haka ne Allah ya kaimu lafiya,ya qara miki hakuri da juriya.”

Na amsa da.

“Amin”

Na cigaba da cewa ina mai duqar da kai.

“Yaya Samir dan Allah ka kiramin Halima mu gaisa.”

Ya ce,

“Halima wacece haka Kuma?”

Na ‘dago na kallesa na ce,

“Ka manta Halima da Batul qawayena daka tarar dasu gidanmu ranar da zamu taho nan.”

Ya ce

“Oh sorry na tuna kina da number ‘dinsu ne ni ba nida ita.”

Nayi saurin ce wa”Eh Yaya Samir akwai na haddaceta.”

Ya ce”ok to”

Da ganan ya miqomin wayar yana mai ‘dorawa da ce wa.

“Saka number ‘din ki kira.”

Wayar na amsa na kira da bugun farko Halima ta ‘daga sallamata da taji yasa naji ‘yar qarar da ta saki tare da ta na ce wa
“Nayi tsammanin kece,dama shiyasa na ‘daga ba wani ‘bata lokaci.”

Na yi murmushi na ce,

“Shine ko amsa sallama babu.”

Naji muryar Haliman tana”ke rabu dani wanni sallama zan amsa,kullum cikin tsammanin kiranki nake yi baki Kira ni ba tunanina ko kin manta da ni.”

Na girgiza kai kamar tana ganina

“Ya zanyi na manta dake Halima idan na manta dake ban cancanta da zama qawar qwarai ba kamarke,Yanzu dai ya kike ya Batul da Mama.”

Haliman ta ce,

“kawar kwarai ai ke ce Sumayyah nayi rashinki daga ni har Batul,nima ina lafiya haka ma Batul da Mama dan jiya i yanzu muna tare da Batul,gidanmu ta yini dan har gidanku na barta zata biya ta gaida Mama sannan ta wuce gida.”

Naji da’din jin yadda qawayen nawa basu manta dani ba dukda bana nan sun tuna da mahaifiyata na ce,

“Naji da’di sosai Halima Allah ya bar zumunci.”

Ta ce “Amin yawwa baki tanbayeni su Yaya Baffa da Yaya Hakeem ba,da Yaya Yazid kullum suna tanbayarki ke har Faisal ma”
Na ce”yi haquri Halimatu,suna raina fa”

Haliman ta ce,

“Ba wani nan,yanzu yaushe Zaki dawo?”
Na ce”sai sanda Yaya Samir yasa rana”
Halima ta ce”Dan Allah karki da’de,munyi rashinki sosai Sumayyah,,kuma ga karatu ma,kinsan mun kusa komawa hutu.”

Na ce “Haka ne Halima,ai ba zan da’de sosai ba duka ma yau kwana na nawa anan ‘din”
Haka dai muka cigaba da fira da Halima Yaya Samir kuma bai ce na basa wayar ba sai da muka gaji mukayi sallama na basa wayar sai da ya amshi wayar ya kalleni,

“Da gaske kike Haliman qawarki ce?”

Na ‘daga kai na kallesa na Kuma maida kaina qasa dan bana jurar ha’da ido da mutane sosai ba ma Yaya Samir ka’dai ba na ce,

“Eh qawata ce.”

Ya ce, “Kai amma abin ya birgeni kuna ta hira kamar yayarki ko qanwarki,banyi tsammanin akwai qawa kamar wannan ba a yanzu”
Nayi murmushi na ce”Yaya Samir Halima tana da alkhairi sosai kullum fata na na kwatanta abinda ta yimin saboda nasan ba zan iya biyanta ba.”

Ya ce, “hakane insha Allah nima zan taya ki kwatanta hakan indai zaki tayani” haka muka cigaba da fira da hirar duk ta Halima ce sai ko Batul da Yaya Samir ya buqaci na sanar da shi alkhairin Haliman da Batul a gare ni.

<< Na Cancanta 10Na Cancanta 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.