Sun ci nasarar sauya tunanin kowa a daren. Dan, haka Umma ta fasa tafiya a gobe. Iyayen suna ta walwalarsu kasancewar basu san komai da yake faruwa ba.
Washegari da sassafe suka nufi wurin aikin mahaifin Amina. Kasancewar ta sanar da shi ta waya, sun same shi a can. Bayan koro masa jawabi ya yi shiru yana nazari.
“Zayyad ba aljani bane, bai kuma mutu ba. Sannan dole akwai wani ɓoyayyen al’amari a cikin abubuwan da suke faruwa. Sannan shi ma Alhaji Mohd Hashim akwai wani ɓoyayyen abu a wurinsa. Ba sani na yi ba, hasashena ne kawai ya bani hakan. Amma zan baku magunguna ku kaiwa Alhaji Mohd Hashim. Idan har bai taɓa cutar da kowa ba, bai da haƙƙin kowa akansa, ina tabbatar maku babu wata barazana da za ta sake tunkaro shi. Idan kuwa akwai matsala a cikin rayuwarsa, abubuwa masu firgitarwa za su ci gaba da samunsa, idan ba ayi da gaske ba kuma, za, su ci nasara akansa wurin kashe dukkan zuri’arsa.
Kowa a wurin ya yi shiru. Daga bisani suka yi masa godiya suka wuce. Kai tsaye gidan Alhaji Mohammed Hashim suka nufa. Bayan zaman jiran sakkowar Alhaji, da tun jiya yake fama da matsanancn zazzaɓi. Mamakin Munaya ya ƙaru da ta duba taga dukka abubuwan da ta kafe a wuraren duk babu an cire. A gigice ta ce,
“Waye ya cire su Ayatul Kursiyu ɗin da na kakkafe? Me ya sa kuma aka cire?”
Da sauri Hajiya ta ɗaga kanta sama. Dukkansu babu wanda ya kula cewa an cire. Sai wannan ya kalli wannan, waccen ya kalli wannan. Munaya ta dafe goshinta sannan ta dubi Alhaji ido cikin ido ta ce,
“Daddy mun je karɓo maka magani ne, aka ce mu tambayeka babu wani abu da ko yake ɓoye da ka taɓa aikata shi a wasu shekaru baya?”
Sai da ta yi masa tambayar kuma, ta ɗan ji kunya da nauyinsa. Hajiya ta kalle shi, shima ya kalleta,
“A’a babu abin da na taɓa aikatawa.”
Munaya ta yi ajiyar zuciya.
“Ga wannan maganin kayi amfani da shi. Kuma ka ci gaba da addu’a.”
Ya karɓa yana mata godiya da sa albarka. Hajiya ta kafe shi da idanu, daga bisani ta ce,
“Anjima zamu zo gidan Zuwaira mu yi mata murnar bikinta. Allah ya basu zaman lafiya.”
Gaba ɗaya suka amsa da “Ameen.”
Basu wani jima ba, suka fice daga gidan, suka dawo min ci gaba da shirye-shirye. Hajara har yanzu bata dawo daidai ba, ko motsi akayi sai ta firgita. Wannan wani lamari ne da ba zata taɓa mance shi ba. Gawawwakin mutane ta gani da idanunta. Sannan ta ga ana ɗibar namarsu ana ci. Abubuwan babu kyan gani. Ko rufe idanu ta yi sai ta gansu.
Suna ɗaki suka ji ana ihu ga Hajiya da su Suhaima. Da sauri suka fito domin, su tarbe su. Hajiya, ta kafe hoton ɗanta da idanu. Har kullum abin da yasa take matuƙar son Zuwaira kenan. Bata taɓa mance alkhairin ɗanta ba. Ko da ya mutu amma har yanzu tasan akwai soyayyarsa a zuciyarta. Ta dinga kallon ko ina tana tunawa da shi. Ta tuna lokacin da bai da lafiya yana kwance a doguwar kujerar. Ta tuna lokacin da Zuwaira ta kawo masa magana fir ya ƙi ya sha, ƙarshe ta kirata ta zo ta matsa masa ya sha. Bai sha ɗin ba, amma ya ɗora hannunta a bisa goshinsa ya ce,
“Hajiyata ke ce babbar maganina. Yi mini addu’a zan warke fiye da magani.”
Tana murmushi ta ɗora hannunta a bisa kansa ta karanto addu’o’i ta tofa masa. Ya miƙe zaune yana murmushi,
“Na ji sauƙi bani labarin mutanan da kika gani a bisa tituna.”
Hajiya ta yi dariya sosai ta ce,
“Na ga mutane har da masu jajayen kunnuwa.”
Ta tuna ana gobe zai bar duniyar, yadda ya dinga zama kusa da ita. Ta tuna yadda ya tara ƙannansa yana yi masu nasiha.
Hawaye suka gangaro mata, ta goge hawayen ta duƙar da kai. Munaya ce kaɗai ta kula da halin da ta shiga, sai kuwa ‘ya’yanta.
Ana can ana taro har ƙarfe taran dare. A lokacin Hajiya Nafisa suka yi wa kowa sallama suka nufi gida. Ƙarfe goma saura Munaya tana tsakiyar wurin amarya ta ji gabanta ya yi mummunar faɗuwa. Ta daure dai, kasancewar tasan sun kaiwa Alhaji magani. Da ta sake tunawa ta watsar da abubuwan hannunta ta jawo su Hajara ta ce ta ɗauko mota. Haka suka fita a daren zuwa gidan Alhaji Mohd Hashim.
Abin mamaki da al’ajabi gidan babu wuta, sai duhun da ko hannunka baka isa ka gani ba. Duk suka dubi juna ta cikin hasken motarsu. Lallai akwai matsala a cikin gidan.
Sun fito suna neman mai gadi, sai ganin wani shirgegen abu ya faɗo suka yi, hakan yasa duk suka yi tsalle gefe. Hajara ta haska shi da hasken wayarta. Mai gadin gidan ne aka kashe shi, aka kwashe kayan cikinsa.
Anan fa jikinsu ya kama karkarwa. Sun tabbatar idan ba a kashe iyayen Zayyad ba, to ana gab.
A wannan karon Amina ta fi su ƙarfin hali, kasancewar addini ya ratsata fiye da su. A take ta karanto wasu addu’o’i ta shafa a jikinta. Sannan ta dube su. “Ku zo mu je ciki.”
Duk, suka zaro idanu.
“Ke kinyi addu’a kike so mu mu shiga hakan nan? Kalli irin kisan da akayi wa mai gadi.”
Amina da kanta tofa masu addu’a. Sannan kowacce ta ƙara da dukkan addu’o’in da ta iya. Suka riƙe hannun juna. Cikin sanɗa suka cusa kai.
Wurin fa akwai duhu na gaske. Wannan aiki kuma ya fi ƙarfin su Munaya. Alamun kuka kawai suke ji, da haka ba sa jin komai.
Amina ta buɗe wayarta. Ta buɗe Alqur’aninta. Cikin Suratul Rahman take rera ƙira’arta. Munaya bata da buƙatar kallon allon waya, domin yana haddace a kanta. Dan haka suka dinga yin karatun cike da tarin natsuwa. Tsoro da firgici duk suka kama kansu. Ayar Allah ake magana. Ji suka yi tim! Abu ya faɗo. Munaya ta ji ruwan hawaye a fuskarta. Tana tsoron ta buɗe idanunta ta ga gawar Alhaji Mohd Hashim. Idan ta bari aka cutar da shi, bata kyautawa Zayyad ba. Yasan za ta iya ne shiyasa ya ce ta je ta kai masu taimako.
Cikin ikon Allah suna buɗe idanu suka ga haske ya mamaye ko ina na gidan. Da sauri suka ƙarasa ware idanun. Babu kowa haka zalika basu ga abin da ya faɗo ɗin ba.
A gurguje suka afka cikin ɗakuna suna nemansu amma babu kowa. Wani ɗaki suka kalla a, tare, daga bisani suka tura kansu ciki. Ƙaton atore ne a ciki aka ɗaɗɗaure su Hajiya da yaran. Shi kuwa Alhaji Mohd Hashim ɗaurin wulakanci akayi masa. Lamarin da ya fusata Zayyad kenan, wanda shigowarsa kenan ya biyo bayan su Munaya. Yasan za ta iya amma hankalinsa ya gaza kwanciya. Babu yadda ba a hana shi zuwa ba, amma ya ji ba zai iya jurewa ba. Da sauri ya juya. Ya yi rantsuwa da Allah sai ya yi masu muguwar ɓarna. Sai ya je har matsafar nasu ya ɗauki fansar wulakanta masa iyaye.
Munaya ta yi namiji ƙoƙari, ko in ce sun yi namijin ƙoƙari. Domin su suka kwance su, suka kwance Alhaji. Sai numfarfashi yake yi. Gaba ɗaya har ya fara fita hayyacinsa. Munaya ta dubi Amina ta ce,..
“Kirawo Baba a waya mu ji ko akwai wani taimako da zai iya yi.”
Hannunta yana rawa ta danna kira. A lokacin har sha ɗaya ta gota. Baban Amina ya tsorata, ya firgita jin ‘yarsa ba tana gidan biki bane, tana wuri mai hatsari. Da kuma ya tuna tarin iliminta sai ya ɗan sami sassauci. Da gaggawa ya fito ya ɗauki mota ya nufi gidan Alhaji Mohd Hashim da taimakon Amina.
Munaya ta fito ta shigo da shi. A yadda ya ga Alhaji Mohd sun riga sun ci nasarar ɗauke kuruwarsa. Ya dube su ya ce,
“Kun yi latti. Sun riga sun ɗauki Kuruwarsa.”
Munaya ta fashe da kuka ta ce,
“Baba tunda ka ce mu bashi maganin, muka bashi muka tafi cike da ƙwarin guiwar babu abin da zai same shi. Yanzu shikenan Daddy mutuwa zai yi kenan?”
Gaba ɗaya suka gigice da kuka. Anan falon suka shimfiɗe shi, mahaifin Amina yana bashi dukkan taimakon da ya zo da shi. Amma babu wani sauƙi. Dole sai sun karɓo wannan kwalbar an fasa shi.
Munaya ta miƙe tsaye, idanunta sun yi kaca-kaca da hawaye,
“Daddy ba za ka mutu ba, sai na dawo maka da rayuwarka da ƙarfin ikon wanda ya haliccemu.”
Ta juya tana kallon su Hajjo.
“Kun yi ƙoƙari kuma na gode. Ku zauna anan ku kula da su Daddy. Ku bar mini wannan aikin. Ni nasan in da zan same su. Idan har ya wuce wannan daren, bana jin Daddy zai sake dawowa duniyar nan. Idan ya wuce yau, gobe iyayena za su tafi da ni, shikenan na ci amanar Zayyad.”
Kawai ta juya. Yau ko Zuwaira ko kuma ita. Hajjo ta dubi su Baban Amina ta ce,
“Baba ina ganin ku tsaya anan, dole zan bi bayanta kasancewar bata iya mota ba. Zan kaita da motata.”
Tana fitowa taga Munaya ta fizgi motar Hajjo da ƙarfin gaske. Sai yanzu ta tuna a cikin motar suka bar key ɗin. Bata taɓa sanin ta iya mota ba, sai yau ɗinnan. Tana tsaye har ta ɓacewa ganinta. Hajjo ta lumshe idanu tana fatan Allah ya tsare Munaya.
Muna fatan Allah ya tsare Munaya da Zayyad daga shiga hatsarin Zuwaira da Hauwa.