Skip to content
Part 9 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Cikin sauri-sauri ta ciro Ayatul Kursiyun nan ta ce su taimaka mata a kafa tun daga bakin ƙofar Alhaji har zuwa ɗakinsa. Sai da ta tabbatar ta kafe masa, sannan ta yi sallama da su a gurguje.

A gajiye ta dawo gidan, sai dai idanun Anti Zuwaira kamar wacce ta yi kuka ta gaji. Har za ta wuce sai kuma ta dawo da baya,

“Anti lafiyarki kuwa? Me ke faruwa ne?”

Zuwaira ta kauda da kai kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce, “Lafiya lau. Za a ɗaura mini aure sati mai zuwa.”

Wannan kalmar ta yi matuƙar tayarwa Munaya hankali. Tsoronta kada ta sake auren wani ta kashe shi.

“Anti da wurwuri haka? Na zaci ma lokaci ya zo da za ki karɓo Islam ki dawo da ita gidan nan? Gaskiya Anti aure ba naki bane a yanzu.”

Ta yi matuƙar shan mur! Ita kanta bataso ta yi auren yanzu ba, sai dai wannan umarnin shugaba ne. Ya ce wannan ne hukuncin da za ayi mata akan ganganci da ta yi, har aka ga ƙyallen nan. Sannan yanzu ɗakin Alhaji cike yake da kariya, da tsaro, wanda shi kansa duk hatsabibancinsa ya gagare shi shiga. Dole ta auri wani, ta basu jinin su tsotse, babu abin da ya dame shi da zancen da duniya za ta yi akanta.

Tana nan zaune a ɗakinta, zuciyarta ta dinga azalzalarta akan ta je asibitin likitan nan domin ta tabbatar da abin da take zargi. Washegari, bayan ta tafi Makaranta take ba su Hajara labarin asibitin nan. Suka tabbatar mata idan an tashi, za su je tare.

Bayan an tashi Makarantar Munaya ta rufe fuskarta da face mask. Kai tsaye asibitin suka nufa, kasancewar Hajjo ta daɗe da sanin asibitin. Aka tabbatar masu da dokto bai iso ba, dan haka suka zauna zaman jiransa. Sai da suka tabbatar sun faki idanu, sannan suka afka ɓangaren da Munaya ta nuna masu. Cikin matuƙar sa’a ashe a buɗe yake. Basu san ma da mutum a ciki ba. A hankali suke takawa har suka shiga ciki. Munaya ta lallaɓa ta kwaye farin zanin gado ɗaya da aka lulluɓe wani abu a ciki. Take hantar cikinsu ya kaɗa. Ƙafafunsu ya dinga rawa. Gawa ce kwance a lulluɓe akan gadon. An sanya auduga a cikin hancin. Munaya bata taɓa zaton abin da za ta buɗe ta tarar kenan ba. Ƙafafunta suna rawa, garin sauri ta zubar da wasu allurai da aka ajiye a saman wurin. A lokacin wacce take can ciki ta juyo a razane ta ce,
“Waye?”

Habawa. Jikinsu babu inda baya ɓari. Amina ta fi kowa ruɗewa kasancewar tunda take a duniya bata taɓa ganin irin abubuwan nan ba, sai a t.v. A lokacin kuma takun tafiyar Dokton ya cika wurin, da alamun shima wurin zai shiga. A take hawayen firgici ya shiga kwaranya, sun tabbata yau kashinsu ya bushe.
“Ke da waye?”

Ya tambayi Nas ɗin da ya samu a cikin wurin. Ta ce, “Rankashidade motsi na ji da yake nuna alamun akwai mutum a cikin wurin nan.”

Ya ware idanu, “What! Mutum fa kika ce? Tayaya za ki yi sakacin shigowa wurin nan ba tare da kin rufe ba? Bincika ko ina mu gani.”

Ya nemi wuri ya zauna, ita kuma ta dinga bincike. Tana gab da kaiwa in da suke ɓoye duk sun yi zuba Dokto Jafar ya ce,

“Zo ki ga wani abu. Ki ajiye shirmen nan naki babu kowa a cikin wurin nan. Ki zo mu haɗa wannan allurar, an jima an umarceni da in yi wa Alhaji Mohd Hashim Allurar nan, kasancewar duk hanyar da za su bi, sun bi amma bai mutu ba. An ce yanzu yana iya magana. Da alama sun farka sun gane musulunci tana da maganin kowane irin cuta.”

“Rankashidaɗe jikina yana bani akwai mutum a cikin wurin nan. Amma ka bincika ka gani.”

Ya ɗan waiwaya, ya kuma kafe gadon da su Munaya suka ɓoye a wurin.

“Bana jin akwai mahaukacin da zai iya shigowa nan. Ki yi sauri ki zo mu haɗa yanzu zan wuce gidan Alhajin domin aiwatar da allurar nan.

A hankali suka fito suna sanɗa kasancewar duk sun mayar da hankali wurin haɗa maganin. Suna ficewa yana ɗago kansa. Inuwar mutum kawai ya gani, hakan yasa ya tashi da sauri ya bi bayansu. Bai ga kowa ba, sai ‘yan mata su uku, suna zaune kusa da Office ɗinsa, kamar hankalinsu ma ya yi nisa a wurin hirar da suke yi. Ya kafesu da ido, sannan ya juya ya koma. Ita dai Munaya zuciyarta tafarfasa kawai take yi. Ta yi alƙawarin in dai tana raye, ba zata taɓa barin wani ya cutar da mahaifin Zayyad ba.

Basu tsaya ɓata lokaci ba, su Hajara suka fara zuwa ofishin ‘yan sanda suka kai report akan lallai mai asibitin Sa’i Hospital yana da ɗakunan da yake kashe marasa lafiya yana cusa su a ciki. Da dabara suka shigo da ɗan sanda suka nuna masa ɗakin. Dan haka suka koma suka shiryo sosai, sannan, suka zo a cikin motarsu.

Hankalin Dakta Jafar idan ya yi dubu, to ya tashi. A lokacin da suka gama yi masa bayanin suna son yin bincike a cikin asibitinsa sai ya, shiga matsanancin tashin hankali. Bakinsa yana karkarwa ya ce,

“Rankashidaɗe ta ya ya haka kawai za ku ce zaku duba asibitina kamar wani ɓarawo?”

A take suka warware masa takardar samun umarnin duba ko ina. Munaya da Hajara da Amina suka tsaya daga wani gefe ba tare da kowa yasan cewa su suka haɗa wannan wutar ba.
A lokacin da suka nuna masa ɗakin da suke son fara shiga, ya dinga keta zufa. Ga shi sun sako shi a gaba. Hakan ya ja hankalin mutane da dama, dan haka wasu suka shigo su ganewa idanunsu. Daga cikinsu akwai su Munaya. Da ƙyar ya buɗe ƙofar. Sai dai abin mamaki. Babu komai a ciki sai tarkace. Hajjo ta dubi su Munaya a firgice. Haka zalika ‘yan sandan suka dubi su Munaya, sai kuma suka basar tare da ci gaba da bincika ko ina. Babu wata shaida da ta nuna masu akwai matsala a cikin asibitin. Dan haka suka juya. Munaya suka zauna a mota duk suka yi shiru. Hajara ta hango likitan nan ta cikin madubi, ya fita a motarsa. Cikin tashin hankali ta dubi su Munaya ta ce,

“Mun shiga uku. Likitan nan fa gidan Alhaji zai je.”

Munaya ta jijjiga kanta ta ce,
“Hajjo ina tsoro. Ina tsoron mu je taimakon Alhaji a sake samun matsala irin wanda aka samu yau. Ƙarshe ya jawo mini tsana a gidan, bayan a yanzu babu wacce suke so sama da ni. A dai nemo shawara.”

Duk suka yi shiru. Daga bisani suka yanke shawarar zuwa gidan Alhaji Mohd Hashim. Sun ci nasarar shigowa gidan, sai dai dole kafin isarsu sai da suka biya ta wani kanti suka sauya shiga. Abin mamaki, ba gidan ya fara zuwa ba, wannan ke nuna masu da gidan ya fara shigowa da babu makawa sai sun makara. Munaya ta ce ƙawayenta su jirata za ta haura sama ta duba jikin Alhaji. Da ita da Suhaima da Hajiya suka haura. Yana kishingiɗe idanunsa biyu.

“Sannu Daddy. Ya jikin?”

Munaya ta buƙata cikin wata marainiyar murya.

“Da sauƙi sosai ɗiyata. Allah ya yi maki albarka.”

Farin ciki ya tsirga mata, ta dubi Hajiya ta ce,
“Mommy wai haka jikin ya yi kyau? Kai masha Allah. Ƙawayena da muka zo da su, sun taimaka mini ƙwarai akan ciwon Daddy. Ɗayar mahaifinta yana bayar da maganin Islamic. Allah ya ƙara maka lafiya.”

Dukkansu sun ji daɗin jajircewar Munaya da ƙawayenta. Sallamar Daktan yasa duk suka dube shi. Ruma ke biye da shi, alamun ita ta yi masa jagora. Ya nemi a ɗan fita zai yiwa Alhaji Allura. Hajiya ta ce babu komai kawai ya yi masa tunda duk ‘ya’yansa ne. Ya karkace ya zuƙo ruwan allura.

“Mu ga allurar nan? Nasan allurai sosai. Kuma lokaci ya zo da ya kamata a daina yiwa Daddy allura sosai.”

Ya dubeta a rikice. Ya kasa ganeta, amma kuma muryarta tana yi masa kama da wacce ya sani. Ya so ta buɗe fuskarta dan ya ga wa ce ce take shirin rusa masa aiki. Dama ɗazu ya shiga, tashin hankali, a sakamakon asirinsa da ya kusa tonuwa. Shugaba ya taimake shi ya turo aka kwashe gawawwakin, da yanzu gidajen tv da jaridu sun sami abincin ci akansa.

“A’a wannan allurar zai taimaka masa wajen samun barci.”

Daddy ya musƙuta ya ce,

“Dakta ya kamata daga yau a sallameka. Na sami sauƙi, ina iya barci ba tare da wani taimako ba. Gaskiyar ɗiyata ce abar alluran nan dan nasha su har na ji babu daɗi.”

Munaya ta miƙe ta ce,

“Mu ga allurar.”

Da sauri ya fizge ya mayar cikin jaka, jikinsa babu ta in da baya ɓari. A ƙoƙarinsa na neman ƙarfin hali ya ɗorawa kansa abin ya faskara. Dole ya ɗan yi shiru tukun, kafin daga baya ya ce,

“A lokacin da muke taimakonsa me ya sa ba ki zo kin duba irin taimakon da muke bashi ba? Alhaji na barka lafiya. Allah ya ƙara sauƙi.”

Duk suka kafe shi da idanu har ya fice jikinsa yana kyarma.

A gajiye Hajara ta ajiyeta a gida ta shiga. Tana son watsa ruwa kafin ta je wurin Anti Zuwaira ta ji me a ke ciki da zancen aurenta. Bayan ta, watsa ruwa ta haɗo baƙin tea ta fito ta nufi ƙofar ɗakin Anti Zuwaira.
“Dakta nima asirina saura ƙiris ya tonu. Naje gidan Alhajin da nufin in dubo ƙyallen nan, domin shugaba ya ce in je in duba. Ina doso ƙofar ɗakin Alhajin Wallahi na, gagara shiga. Karatun Qur’ani kawai nake ji. Dole na juya, saboda na shigo da kayan aiki ne, naso in kashe shi kawai kai tsaye idan ya so daga baya sai a tsotsi jinin. Dole na koma da baya na ce masu na yi mantuwa zan dawo. Abun duniya ya isheni Wallahi. Kwanaki biyun nan sai laifi nake yiwa Shugaba. Yanzu kuma ya tabbatar mini da wani mutum ya ƙona ƙyallen, bayan ya yi wa Magen Shugaba mummunan lahanin da har yau bai warke ba. Na rasa waye yake ɓata mini aiki.”

Ta numfasa. Muryarsa da ta ji, yasa ta gane, ashe suna tare ne ma ba waya take yi ba.

“Nima ɗazu wasu ‘yan mata sun so su jiƙa mini aiki. Har yanzu jikina rawa yake yi, duk da na tsira. Ina zargin yarinyar da ta so tona mini asiri ita ce ta warware dukkan shirinmu domin ɗazu ma cewa ta yi sai na bata allurar ta gani.”

Zuwaira ta lumshe idanu tare da hura iska. Ta ce

“Anya? Shugaba fa namiji yake gani ba mace ba. Tayaya za a yi wacce kake zargi ta iya aikata wannan babbar aikin? Dole sai dai idan akwai namiji a bisa kanta. Wallahi daga macen har namiji, muddin na kama ɗaya sai na hallakasu da hannuna. Na, kai shekaru da dama ina jiran abubuwa masu yawa, amma saboda wasu can komai ya ruguje.”

Munaya ta ja da baya ta koma ɗakinta tare da faɗawa kan gado.

“Anti Zuwaira ni ce nan matsalarki. Idan mahaifiyarki tasan ƙazantar da kike toyawa anan garin Kaduna, sai ta tsine maki.”

Idanu take lumshewa alamun barci yana shirin ɗauketa. Sai dai tunanin Zayyad da abubuwan da suka faru sun taru sun yi mata yawa. Tana so ko yayane ta samu ta sarara amma abun ya faskara.
Har ƙarfe ɗayan dare tana juye-juye. Sai yanzu ta tuna da wayar da Hajara ta siya mata.
Da sauri ta jawo wayar, har ta kusa mutuwa alamun babu caji. Abin mamaki kiran waya ta gani daga wata lamba a ƙalla ya kai sau hamsin. Ta, ware idanu cike da tsoron waye yasan wannan layin? Daga Hajara har Amina duk tana da lambobinsu. Bata ƙware a harkar waya ba, dan haka tana shirin mayarwa ta sake ganin waya tana haske. Gabanta ya faɗi da ƙarfi. Hannunta yana karkarwa ta ɗauka ta ɗora a kunne.
“Na kiraki mu yi hira ne, duk da ban kasance daga cikin masu iya hirar ba.”

Sanyi ya ziyarceta ta ƙudundune, ta sake manne wayar a kunnenta,

“Kai waye? Me na yi maka?”

Murmushi ya fidda mai sauti.
“Me ya hanaki barci?”

Kamar ta ce tunaninsa sai kuma ta basar. Shima ya shaƙi iska ya ce,

“Ban taɓa jin son wata ‘ya mace ba.” Sai kuma ya yi shiru. Zuwa can ya ce,

“Ki tashi ki yi alwala ki yi nafilfili. Ki yi addu’a. Sannan kiyi takatsantsar da Yayarki domin za ta iya kashe kowa akan muradin ranta. Idan nace kowa ina nufin har mahaifiyarta.”

Munaya ta zaro idanu. Ta ya ya za ta iya kashe uwar da ta haifeta? Kafin ta yi magana ya kashe wayarsa. Ta dinga kiran lambar bata shiga. Zuciyarta ta dinga in gizata akan ta je ta ga me Anti Zuwaira take aikatawa yanzu? Tunda ta fahimci lokacin barci shi ne lokacin da ta, zaɓa ta aikata ta’asarta.

‘Yar mutan Bornonku ce.

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 8Na Kamu Da Kaunar Matacce 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×