Khausar ta ɗago tana kallon Sadiya tare da cewa, "Small Mum anya kin tuna daidai kuwa, ko ɓata miki rai Yaya Sadeeq ɗin yayi? Haka ya sa kika mance."
Sake cunna baki Sadiya tayi tare da fara magana idanuwanta na cikowa da ƙwalla, don ta taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi a zuciya, cewa tayi, "Aunty yanzu Yaya Sadeeq yana kyauta mini?"
Da mamaki Khausar ke kallon Sadiya, lokaci guda kuma tana ƙara zuba mata ido, dan ta fahimci abinda suke tunani a kai da kyau, cewa tayi, "Me ya miki small Mum?", cikin sigar tausasawa tayi maganar da kuma. . .
