Skip to content
This entry is part 20 of 21 in the series Nauyin Baki

Murya a karye yana rawa, Sadiya ta ce, “Amma Mama ina yiwa Yaya Sadeeq kallon Yayana na uwa ɗaya uba ɗaya ne, Mama ba zan iya mishi wani kallo ba kuma bayan haka, Yaya Sadeeq ya haramta a gareni…”

Mama saurin dakatar da Sadiya tayi ta hanyar cewa, “Sadiya dan kina mishi kallon Yayan da kuke kaman ciki ɗaya, ba yana nufin a zahiri haka bane ko kuwa har a wajan Allah haka bane, sannan ɗan adam ba zai haramta abinda Allah ya halatta ba, dan haka ki iya bakinki, mai babban suna yana son ki, kuma kema kina son shi kawai sai dai idan baki fahimta bane…”

“Mama wallahi ni Haidar nake so, in dai irin wannan soyayyar ne to ba na son Yaya Sadeeq, ban taɓa mishi irin soyayyar ba kuma bazan taɓa ba da yardar Allah, soyayyar da nake mishi na kasancewarshi Yaya ne kawai a gareni cikin Umma ɗaya”, Sadiya ta ƙarishe maganar idanuwanta na zub da ƙwallan da suka jima da taruwa a ciki.

Mama kwantar da murya ta yi, tare da cewa, “Sadiya bana son ki kuma faɗar irin wannar magana a gaban kowa, ciki kuma har da ni da Yayanki Umar, Sadiya kina son mai babban suna kawai kin yi yarinya ne ba za ki iya fahimta ba.”

“Amma na fahimci ina son Haidar Mama, meyasa yaranta bata hana ni fahimtar haka ba? Mama bana son kowa sai Haidar, har abada ba zan yi wa Yaya Sadeeq irin wannan soyayyar ba.”

“Bana son damuwa Sadiya, bana son jan magana, kin san waye mai babban suna, kin san yadda ya zame miki a rayuwa, mutuwarshi za ki zaɓa saboda son zuciyarki? Ba ki ganin ƙoƙarinshi na yunƙurin sallama rayuwarshi saboda farincikinki ba? Ke ba za ki iya sadaukar mishi da taki zuciyar ba? Kin fi kowa sanin jarumta da dauriya irin ta mai babban suna, tunda har ya kwanta ciwo kuma irin haka, abinda bai taɓa yi ba a rayuwarshi tun sani na da shi, to lallai wannan ba ƙaramar soyayya yake miki ba.”

Cikin muryan kukan da ke son ƙwacewa Sadiya ta ce, “Mama, Yaya Sadeeq shi ne duniyata, abinda ya zame mini a rayuwa ya sa nake bashi matsayi fiye da Yaya Umar, nake jin shi tamkar uba a gare ni, kuma hakan ya sa ba zan taɓa yi mishi kallon wani soyayya bayan ta son Yaya da ƙanwa ciki guda ba, Mama ina son Yaya Sadeeq fiye da kai na, zan iya ba shi rayuwata idan aka ce sai na mutu zai rayu, amma ba zan iya bai wa irin wannar soyayya ƙofa a tsakaninmu ba, Haidar nake so Mama, shi kaɗai zan iya kallo a matsayin miji, da shi kawai zan iya zaman aure, Mama wallahi ba na jin komai makamancin wanda nake ji a kan Haidar game da Yaya Sadeeq, Mama dan Allah a bar wannar magana.”

Mama sake baki tayi tana kallon Sadiya zuciyarta na suya, ranta ke ƙoƙarin ɓacuwa amma ta yi ƙoƙarin dannewa matsayinta na uwa, dole ta yi rarrashi, domin tabbas Sadiya na son Haidar, amma yadda Sadeeq zai iya sadaukar mata da rayuwarshi, ya kamata ta iya sadaukar masa da zuciyarta da soyayyarta muddin ita ɗin ƴar halak ce.

Miƙewa tsaye Mama tayi, murya a saisaice ba amo ta ce, “Ki tashi maza yanzu ki je wajan Abbanku yana jiranki zai fice, idan kin je zai tambayeki ne a kan mai babban suna, kamar yadda tun farko ban hango ko tsammaci matsala daga gare ki ba, ina fatan tabbatar haka har yanzu, domin na fahimceki kuma na miki uzurin duk abinda ke faruwa, saboda na taɓa kasancewa a irin halin da kike ciki, amma da nayi abinda ya kamata makamancin wanda nake so ki yi, ga shi ina hamdala da godiya ga Allah da ya bani ikon yin haka tun lokaci bai ƙure mini ba, kuma ina alfahari da hakan, dan haka kema ina miki fatan ki yi abinda ya kamata domin za ki yi alfahari zuwa gaba, ina tsammanin jin labari mai daɗi daga wajan Abbanku a kan kin ce masa kin yarda”, iya haka Mama ta faɗa ta fice, duk da a sigar lallashi ta ƙarishe maganar, sam-sam bata yi wa Sadiya tsawa ba, balle faɗa ko wani abun.

Wani irin kuka ne ya kufcewa Sadiya tana jin Mama ta kulle ƙofa, cikin kuka ta ce, “Why? Meyasa? Meyasa haka Yaya Sadeeq? Meyasa za ka bijiro da abinda bazan taɓa iya aikata maka shi ba? Kullum fatana na yi abinda zan saka maka, na faranta maka ka yi alfahari da ni, amma meyasa da irin wannar magana za ka ɓullo? Ka fi kowa sanin wa zuciyar Sadiya ke so da ƙauna, ka fi kowa sanin Haidar shi ne farincikinki na, meyasa Yaya Sadeeq? Meyasa har za ka zaɓi ka cutu ka kusa mutuwa saboda ni? Bayan ina faɗa maka kai ne duniyata kamar wanda muka fito ciki ɗaya haka na ɗaukeka, idan ka mutu ya kakeso na yi da rayuwata? Wa zai dube ni ya rarrasheni ya bi mini kadu na? Wa zai tsaya mini a komai? Yaya Sadeeq kallon uba nake maka, ba zan iya sauya hakan ba kuma, irin wannar magana ya haramta tsakaninmu, ka yafe mini Yaya Sadeeq, ki yafe mini Mama, Umma ku yafe mini, yanzu Abba zan tunkara na sanar da shi bana son ɗan shi? Ya zan yi da rayuwata? Wayyo Allah na ni Halimatu Sadiya, Allah ga ni gare ka, ka fidda ni, Allah kada ka jarabceni da auren Yaya Sadeeq domin ba zan taɓa iya mishi kallon miji ba, zan cutu zai cutu kuma zan kwashi haƙƙinshi na kwashi zunubi.

Mama na ficewa a ɗakin ta samu waje a palourn ta zauna, tare da faɗin, “Da yardar Allah dai mu ma za muyi surka, daga mai babban suna kuma sai Umar shi ma ya kawo mana ta shi matar.”

Khausar dariya tayi tare da cewa, “Amman kuwa aka bai wa small Mum matsayin surka to tabbas an yi da ita, an mata ƴan ubanci.”

“Ba wani ƴan ubanci fa, ni matar mai babban suna ai ko wace ce to surka take a wajena, kuma ɗiyata.”

“Gwanda-gwanda dai har da matsayin ɗiyar, idan ba haka ba ai har na fara tausayin small Mum, dan ma dai tana da Abba da Umma ga su Khalid, kuma nima dai partynta nake, Allah dai ya tabbatar mana da alkairi, Allah ya kuma kawo wa su uncle U ma mataye na gari.”

“Amin Ya Allahu”, Mama ta amsa tana murmushi cike da fatan ganin sauran surakunan nasu.

Khausar miƙewa tayi tare da cewa, “Bari na kawo muku abin karyawanku Mama.”

Amsawa Mama ta yi, Khausar ta wuce kitchen, it kuma ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiya ganin har yanzu Sadiyar bata fito ba, da sallama ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, Sadiya da ke rungume da pillow tana shan kukanta da sauri ta haɗiye kukan tana jin sallaman Mama.

Mama tana tsaye daga bakin ƙofar ta ce, “Amma dai kamar cewa nayi ki tashi ki je Abbanku na jiranki zai fita ko Sadiya?”

Miƙewa tsaye Sadiya tayi ba tare da ta amsa wa Mama ba, toilet ta wuce ta wanko fiskarta, sannan ta fito kanta a ƙasa ta rarumi hijabinta ta nufo ƙofa.

Mama tana tsaye tana kallon Sadiya har ta sanya hijabi, daga idanuwanta kuma ta gane kukan da ta sha, hakan ya sa ta ce, “koma ki kuma sanya wa idanuwanki tozali, kar ki kuskura Abbanku ya tsammaci tilasta miki na yi, domin ni ban tilasta miki ba, kawai dai Sadiya ina hango miki alkairi a auren mai babban suna ne, Sadiya ni na haifeki, duk wani mai sonki bayana zai biyo, ba zan so miki abinda zai cutar da ke ba.”

Wasu ƙwallan ne suka cikowa Sadiya a idanuwa, amma ta yi ƙoƙarin shanyesu, ta juya ta sanya kwalli kamar yadda Mama ta ce, ai kuwa ta sake yin kyau rass da ita abinta, a nitse ta ƙaraso bakin ƙofar har inda Mama ke tsaye kanta a ƙasa.

Mama jawo Sadiya jikinta ta yi ta rungumeta, ta dinga bubbuga bayanta alamar rarrashi da ƙarfafa guiwa, ta ce, “Halimatu Sadiya yarinyar kirki ƴar albarka, in sha Allahu za ki ji daɗin wannan aure, za kuma ki yi alfahari da hakan, watarana ko da kuwa bama raye za ki bi mu da addu’a tare da gode mana, Allahu ya miki albarka autata, Allah ya dubi rayuwarki da ta zuri’arki, duk wani mugun abun na ji ko na gani Allahu ya kareku da shi.”

Sadiya lafewa ta yi a jikin Mama, amma ta kasa amsa wa, saboda zuciyarta da ta ɗanyace kuma ta raunata, ji take idan ta buɗe baki to kukan ne za ta kuma yi, hakan ya sa sai ajiyar zuciya kawai take jerawa.

Mama shafa kanta tayi tare da janyeta a jikinta, tana murmushi ta ce, “Allahumma ya miki albarka Sadiya, ki je ko, kuma ki tabbata kin sanar da Abbanku kin yarda, kada ki bani kunya Sadiya”, Mama ta ƙarishe faɗa tare da matsawa a ƙofar ta bai wa Sadiya hanya ta wuce, ita dai jinjina kai kawai ta yi ta fice kai a ƙasa, bata ko kalli cikin palourn ba balle ta yi wa Khausar ko sauran yaran magana.

Mama sai da ta tabbatar Sadiya ta fice a palourn, sannan ta sauƙe gauron numfashi tare da ficewa ta ja ƙofar ɗakin, palourn ta ƙarasa ta zauna, wanke hannu ta yi da ruwan wanke hannu sannan ta soma cin ɗumamen tare da cewa, “Allah yayi albarka Khausar.”

“Amin Mama”, Khausar ta amsa tana murmushi, cike da ƙaunar Mama, sai ta rasa tsakanin su Umma da Mama wa ya fi wani kara, sosai Mama take da kara da kuma kirki, kamar yadda Sadiya ke faɗin ta fi ƙaunar Sadeeq a kan Umar, to haka idan Mama na tare da Sadeeq da Umar, za ka ga tsantsar ƙaunar Mama ga Sadeeq, za ka ɗauka ma shi ne asalin ɗan ta.

Daga haka Mama ta cigaba da karyawanta, suna hira sama-sama da Khausar, su Najla da Nayla kuma an nitsu an mayar da hankali ga cartoons.

Sadiya a sanyaye take tafiya kanta a ƙasa, idanuwanta na kawo ƙwalla amma tana mayar da su dan dole, a haka har ta ƙarisa ƙofar gidan Abba, wadda take jin yau nauyin shigarsa take, sosai take kunyar Abba da Umma, yanzu sai ta dubi idon Abba ta ce mishi bata son ɗan shi? Ko kuwa Umma za ta kalla kuma bayan ta nuna bata son ɗan su? Sun yi halarci gare su musamman wa ita da Yaya Umar, idan ta yi haka bata kyauta ba, amma kuma Haidar fa? Shi ta kyauta mishi? Yana sonta yana ƙaunarta ita shaida ce, idan ya rasa ta shi kuma bata san wanne hali zai shiga ba, domin ba ta ta kanta ta shi take yi, dan ta sani a rubuce yake, wannan wajibi ne za ta yi matuƙar cutuwa, kuma ba za ta iya damƙa kanta da soyayyarta ga wanin Haidar ba, ko da kuwa shi Yaya Sadeeq ɗin ne, tukunna ma idan ta aikata haka me Haidar zai ɗauketa? Mayaudariya? Maƙaryaciya? Macuciya? Ko kuma maciyiyar amana? Ya za a yi ta jure irin waɗannan kalamai ko sunaye daga Haidar, idan Haidar ya mata wannan kallon ba za ta taɓa yafe wa wanda ya zama sila ba, a ko da yaushe Haidar na jaddada mata irin soyayyar da yake mata da irin kishinta da yake yi, amma yake faɗa mata ya yarda da ita, daga gare ta baya taɓa tunanin samun wani damuwa ko abinda bai kamata ba, a yanzu kuma yarda da maganar Yaya Sadeeq, tamkar ta sa almakashi ne ta kekketa yardar da ke tsakaninta da Haidar, yarda abu ne mai matuƙar, wuya, muhimmaci da buƙata a ko wacce iriyar zamantakewa, ba ta fatan a rayuwarta ta ƙeta yardar da ko ƙawa ce ta mata balle Haidar nata, Al-Sad nata, natsuwar ruhinta kuma farincikinta, ta kasance kullum ita ke tunatar da shi kada ya barta kada ya yaudareta, shi kuma ya yi alƙawarin ba zai yi ko ɗaya ba, yanzu ita idan ta bar shi me tayi kenan? “Ya Malikul Mulki ga baiwarka Halimatu”, ta faɗa a fili daidai ta kai hannunta kan ƙaramin ƙofar gidan ta tura ta shiga da bismilla da sallam, domin duk wannan zancen zucin a tsaye a bakin ƙofa ta yi su, kuma yau ji take gidan ya zame mata tamkar sabo.

Mai gadi da sauran ma’aikatan gidan ne suka mata sannu da shigowa, suna haɗa wa da sunan amarya, don Sadiya ba ta da damuwa akwai ƴar raha da su ranar da ta ga dama.

Sama-sama Sadiya ta amsa musu sannanta shige palourn gidan da sallama, ba kowa a palourn, hakan ya sanya ya sauƙe gauron numfashi tare da samun waje ta zauna tana karantar wasiƙar jaki, gabas da yamma ya rasa ina za ta hi hanya ta ɓulle mata.

ABUBAKAR SADEEQ POV

***

Khalid na gama daidaita sawayen motar, Sadeeq ya fara fitowa cikin kamewa da aji, ƙafafuwanshi ya fara fiddawa waje, tare da lumshe idanuwanshi yana shaƙar daddaɗar iskan gidansu, yayin da a zuciyarshi yake addu’ar Allah ya shiga tsakaninshi da ciwon da zai kuma saka wa ya jima haka a asibiti.

Khalid da Umar kusan a tare suka fito, Khalid ya fara fidda tarkacensu da ke bayan boot, mai gadi da Hammadu direba suka ƙaraso da sauri tare da yi wa sh Khalid sannu da dawowa dan basu kula da Sadeeq ba ma, dan har yanzu ƙafafuwanshi ne a waje bai gama fitowa ba.

Khalid gaba yayi, yayinda Umar ya zagaya gefen da Sadeeq yake ya ce, “Hey mai ciwon soyayya fito mu shige ciki, ka san yanzu barinka kai kaɗai risky ne, kana iya sake sumewa ka ja wa mutane asara, ka san ba iya amarya tsautsayi ke bibiya ba har da ango, wani abu ya same ka kuwa ka ga ba kanta batun soshalewa.”

Sadeeq da bismilla ya ƙarisa ficewa a motar, ba tare da ya kalli Umar ba ya ce, “Na san kai ɗan guguwa ne, but bansan ka wuce haka ba, anyway keep on talking like a parrot, if you mistakenly mess up around Mama or Umma, you’ll explain very well.”

Hammadu direba da mai gadi, suna kallon Sadeeq suka washe baki, maganarsu ta hana Umar bai wa Sadeeq amsa, cike da matuƙar farincikinki da murna suka dinga jera mishi sannu, tare da fatan Allah ya sauwaƙa ya ƙara ƙarfin jiki, Sadeeq ya amsa sannann suka wuce ciki da Umar.

***

Sadiya tana zaune a palourn shiru-shiru ta yi nisa a duniyar tunani, har Khalid ya shigo bata sani ba, ko hayaniyar mai gadi da musa direba basu fargar da ita ba, sai da Khalid ya aje abin hannunshi ya ƙarisa gabanta, ya yi clapping hannayenshi a gaban fiskarta, hakan ya sanya ta dawo dawo hayyacinta, duk da dai ta ɗan tsorata, ta ɗauka ma ko Mama ce, sai da ta yi tozali da fiskar Khalid yana sakar mata murmushi, sannan ta ɗan tura baki tare da cewa. “Yaya Khalid you scared me.”

“Haba jaruma Sady baby, ƙanwar Yaya Sadeeq, amaryar Haidar, autar Umma da Abba”, Khalid ya faɗa yana ƴar dariya.

Sadiya ta buɗe baki da jiyar amsa ma Khalid kenan, sai ga sallaman Umar da Sadeeq, wanda ko mutuwa ta yi ta dawo za ta gane muryoyin nasu, jin muryarsu dukansu biyu lokaci guda wani irin bugawa ƙirjinta ya yi, she have to be happy saboda jin muryar Yaya Sadeeq yana nufin an yi discharge nashi kenan, that’s mean he’s feeling better, amma a yanzu ba ta da sauran kuzarin ɗin da za ta nuna farin cikinta, she can’t.

Sadeeq na stepping ƙafarshi cikin palourn, idanuwansu suka gauraye cikin na juna, domin idanuwanta na a kan ƙofar ta kasa janyewa.

Wani irin kallon kallo suke yiwa juna, kallo mai ma’anoni da yawa, kallon da kowa da abinda yake kitstsimawa a zuciyarshi.

**

Nauyin Baki

Nauyin Baki 19 Nauyin Baki 21

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.