Washegari ma da wuri Taufiq ya fice, domin Yana da abubuwan yi da yawa a office, ko karyawa bai tsaya yi ba.
Ba wata Kuma cikakkiyar sallama da yayi da Mujaheeda domin sanda zai tafi tana wanka sallahu kawai ya barma masu aikinta su gaya Mata ya wuce office.
Hakan ko bakaramin bata ran mujaheeda yayi ba don aganinta ya wulakanta ta ta yaya zai gayama masu aiki su gaya Mata abinda Shi kadai ya kamata ya gayá Mata.
Wai me yake nufi ne? Ta tambayi kanta gami da sakin Dan karamin tsaki, me yayi zafi ne da yake kokarin. . .