Skip to content
Part 11 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Washegari ma da wuri Taufiq ya fice, domin Yana da abubuwan yi da yawa a office, ko karyawa bai tsaya yi ba.

Ba wata Kuma cikakkiyar sallama da yayi da Mujaheeda domin sanda zai tafi tana wanka sallahu kawai ya barma masu aikinta su gaya Mata ya wuce office.

Hakan ko bakaramin bata ran mujaheeda yayi ba don aganinta ya wulakanta ta ta yaya zai gayama masu aiki su gaya Mata abinda Shi kadai ya kamata ya gayá Mata.

Wai me yake nufi ne? Ta tambayi kanta gami da sakin Dan karamin tsaki, me yayi zafi ne da yake kokarin maida karamar magana ta Zama babba gaskiya ba zata juri wannan abin ba ,don kanta bazai iya dauka ba.

Ta shirya tsaf ta wuce gidansu ba tare data nemi izini wajen mijinta ba , don Tasha alwashin ba zata Kira wayarsa ba .
Isarta gida ta nunama Haj murjanatu cewa a kamfanin sarrafa auduga take son tayi aiki saboda abubuwansu sunfi burgeta.

Haj murjanatu tace.” to shikenan babu damuwa , ranar litinin zamu je zan gabatar da ke za kuma ki dare jujerarki , Shi Kuma Wanda yake matsayin manajan wato Alh jibrin zai koma mataimakinki , nasan Kuma zakiji dadin aiki dashi domin Yana da hankali Yana da kirki kwarai , ya taimakeni Akan kamfanin nan sosai , baida damuwa” mujaheeda tace ” to mummy Allah ya kaimu”.

Haj murjanatu tadan zuba Mata Ido tana karantar damuwar dake kwance Akan fuskar yarta , sannan tace ” mujaheeda meke faruwa ne ?” Ta waigo tana kallonta tace ” me kika gani?”, Tace ” damuwa nagani a tattare dake ,akwai wani abu da yake damunki ne, Bana son ki boye min komai domin duk duniya kinsan dai idan akwai Wanda ya kamata ki gayama damuwarki to baya na ne.”

Mujaheeda tadan numfasa gami da lankwashe Yan yatsunta har saida sukayi Kara , tace ” mummy, kullum fargabata da tunanina Bai wuce ace yau na tsinci Kaina cikin irin rayuwar aurenku da kuka gudanarwa tsakaninki da daddy ba , saboda rayuwace da babu dadi , babu fahimtar juna atsakaninku , babu wata jituwa , to sai gashi nima tamkar nasa kafata acikin takalminki, shin mummy me ke Sanya ràshin jituwa atsakaninku da daddy ki gaya min KO don na kare Kaina daga fadawa irin rayuwar da kuke yi.”

Haj murjanatu ta Mike ta tashi nan da nan fuskarta ta canja damuwa suka baibaye fuskarta, cikin sautin da yake nuni da bakinciki da bacin rai tace ” bazan iya gaya Miki abinda ya ke Haddasa mana ràshin jituwa ba da Alh Amma kisani abin Mai girma ne Abu ne Kuma da bazan taba mantawa dashi ba har na koma ga Allah shiyasa Ko na manta na saki jiki dashi da zaran na tuna nakan ji haushi da tsanarsa fiye da kullum ina ganin dalilin da yasa kenan farincikinmu tare baya nisa “.

Mujaheeda ta gyada Kai tace ” bazan matsa Miki ki gaya min komai ba ,saboda tunda na mallaki hankalin Kaina nake son na Sani Amma kinki sanar dani, don haka KO yanzu. Bazan matsa Miki ba , duk ranar da kike ganin ta dace ki gaya min to Zan tsaya na saurareki da kunnan basira.”

Haj murjanatu ta koma ta zauna tace ” Zan gaya Miki alokacin daya dace.”

“Me zaki gaya Mata alokacin daya dace ” muryar Alh Mustapha labaran ta tambaya lokaci daya Yana shigowa falon.

Gaba daya suka dube Shi , rai ahade Haj murjanatu tace ” abinda ke tsakaninmu Wanda yake Haddasa mana ràshin jituwa alokuta da dama.”

Ya tsaya tsakiyar falon Yana yi Mata wani irin kallo Mai nuna alamun kinfi kowa iya ruko a duniya yace ” tunda ke Abu baya wucewa agunki ba duk wañnan tsawon shekarun ace kin kasa mantawa tunda nake a duniya ban taba ganin mutum me ruko da Mita da ràshin mantuwa da yafiya ba irinki, sannan meye na tunanin zaki gaya ma mujaheeda wannan sirrin Wanda kinsan babu abinda zai Kara Mata sai damuwa , Amma idan kin zabi hakan kina iya gaya Mata komai.”

Haj murjanatu tayi shuru zuciyarta na tafasa ranta Yana Kara baci , ji take kamar yanzu abin ya faru, wani irin tsanarsa ta cigaba da shiga cikin zuciyarta.

Ayayinda Kan mujaheeda ya daure ta Kara fadawa fagen tunani, shin meke tsakanin mummy da daddy tsawon lokaci sun kasa shawo Kan matsalarsu.

Ta dubi Àlh Mustapha labaran da shima ya hade rai gami da neman kujera ya zauna a kokarinsa na son kauda maganar ya dubi mujaheeda Yana kokarin kirkiro fara’a yace ” yaushe kika zo gidan” itama tayi kokarin maida damuwarta tace ” nadan Dade kadan” ya dubeta yace ‘ to yakamata ki shirya ki koma gidan mijinki , Kuma tahowa gida aduk lokacibekkv kike so baida amfani gidan mijinki shine fadarki ciki yakamata ki zauna kiyi Mulki ki Kula da mijinki da bukatunshi”.
Haj murjanatu ta kauda Kai, mujaheeda tace cikin murmushi” to daddy.” Haj murjanatu tace,” ranar litinin mujaheeda zata zamo manajan kamfanin sarrafa auduga.”

Yayi saurin kallonta yace” aiki zatayi mujaheeda.”

Ta gyada Kai tace “eh.” Cikin mamaki mujaheeda ta dubi Àlh Mustapha labaran tace ” wai Dama Baka sani daddy “. Ya tsaida idonsa Akan nata yace ” ta yaya zanyi na Sani mujaheeda bayan bani da mutunci ko kimar da zaa iya sanar da ni.”

Haj murjanatu ta tabe Baki ba tare data CE uffan ba , mujaheeda ta juya tana kallonta tabbas da akwai yadda zatayi ta gyara tsakanin mahaifanta da tayi,

“Mujaheeda ki gaya min , shin da izinin mijinki zakiyi aiki ko kuwa ra’ ayin mahaifiyarki ne?”

Ta girgiza Kai tace ” aah daddy yaya Taufiq ya amince da Kansa ya barni.”

Ya jinjina Kai yace “To Alhamdulillah, najidadi Allah yasa hakan shine mafi alheri , Allah Kuma ya Baki ikon yin dai dai” ta amsa da ” Ameen.”
Daganan ya cigaba da fahimtar da ita kalubale dake cikin aikin mace da yadda dole zata kare mutuncinta a matsayin ta na matar aure, sosai mujaheeda tajidadin nasihohin Àlh Mustapha labaran domin duk abinda ya gaya Mata gaskiya ne.sai kusan karfe shida na yamma mujaheeda ta koma gida.
Kusan tare suka shiga get din gidan da Taufiq, ta rigashi tsaida mota ta fito tadan dube Shi sannan ta shige cikin gida.
Shuru Taufiq yayi acikin mota ya kasa fitowa maimakon hakama sai Kansa ya kifa ajikin sitiyarin motar, Yana maida ajiyar zuciya sai kace Wanda ya shiga gasar gudu.

Wai Anya kuwa mujaheeda ba kunnan Kashi gareta ba , ta yaya mace zata dinga fita ba tare da izinin mijinta ba, ya Lura Sam Sam mujaheeda bata San asa Mata Ido ba.anya bai hango kofar bullewa ba.

Gaba daya ji yake Yana neman ya Fara nadamar aurenta, kwata kwata yaji baya ko sha’awar shiga gidan.

Ya dade acikin motar kafin ya iya fitowa ya taka ahankali kamar Mai koyon tafiya ya shiga cikin gidan.

Ya tadda har mujaheeda ta kintsa ta canja Kaya tana zaune akujerar falo , Kan Dan karamin tebur din dake gabanta an cika Mata Shi da Kayan ciye ciye harda su cakulet.hannunta na rike da waya tana sana’ar dannawa kamar yadda ya Zama al’ adar rayuwarta.

Tadan dago ta dubeshi ta danne fushinta domin dai ta Fara gajiya, tace ” sannu da zuwa”, ba tare daya dubeta ba yace ” yauwa”.
Har zai wuce daki Saiya tsaya ya dawo ya zauna Yana fuskantarta yace ” daga ina kike?” Ta dan muskuta tace ” daga gida nake, naje na kaima mummy files dinta na Kuma gaya Mata kamfanin Dana zaba zanyi aiki dashi.”

Cikin fusata da daga murya yace ” da izinin wa kika fita?”

Ta gigita da Jin tsawar daya daka Mata , cike da mamaki tace ” yaya Taufiq ni kakema irin wannan tsawar kamar karya.”

Ya daga Mata hannu yace ” tambayarki kawai nayi da izinin wa kika fita ,wai ke kinsan abinda kikeyi kuwa me kika dauki rayuwar aure ne, shin ma wai ni meye matsayina agunki? Da kuke kokarin maidani wani sakarai.”

Kuka ta fashe dashi da karfi tana fadin ” yau ni na shiga uku, na rantse wannan ba yaya Taufiq bane canja min Shi akayi.”

Taufiq yace cikin daga murya “babu Wanda ya canjani illa ke , ya kike son nayi kowane magudanci baida buri agidansa daya wuce ya Sami kwanciyar hankali da natsuwa acikin iyalinsa , kwata kwata mujaheeda yaushe mukayi auren da zamu kasa mallakar farincikinmu kullum muna cikin damuwa akan me? Ki fita bada izinina ba , ki tilasta min yin abinda raina baya so , Baki San abinda Zan ci ko Zan sha ba dawainiyata tana wajen Yan aiki , bana fita da farinciki bana shigowa da farinciki gidan nan , Akan me?”

Kuka mujaheeda take yi da karfi sai kace wata karamar yarinya , hakan bausa Taufiq ya sakko ba illama haushi daya ke Kara kamashi.

Ya cigaba da fada ” ni dama nasan mahaifiyarki ta kirkiro da maganar yin aikinki ne don kawai ta kawo baraka atsakaninmu Kuma ta samu hankalinta ya kwanta , Amma lalle na gaji bazan iya dauka ba.”

Cikin fusata da hawaye tace ” Kada Ka karasa mahaifiyata acikin maganarka, ni dai kamin Ka wulakantani yadda kake so nagode, na rantse da nasan haka zaka rikide min kamar hawainiya daban aurena ba, don kawai zanyi aiki shine zaka koma min haka, shin ko dai dagaske ne hassada da bakinciki kake yi min don baka son cigaba na.”

Ya saki tsaki gami da mikewa tsaye Yana kallonta Rai a matukar bace yace ” nine zanyi Miki hassada don zakiyi aiki, hmmm to kije kiyi aiki me yin aikin naki zai rageni dashi KO zai kare NI, Amma ina son ki sani bazan taba kwanciya Ku takani ba KO ku wulakantani ba, Zan rike kimata da darajata ta mijinki Kuma ya Zama dole ki bini ” .yana Gama fadan haka ya tashi ya fada daki.

Mujaheeda ta Kara rushewa da kuka shin menene haka?. Bakinciki yakara kamata data tuna duk masu aikinta suna Jin wannan tijara da Taufiq yayi Mata .ya ci Mata mutunci tunda take aduniya babu Wanda ya taba tsayawa akanta yayi Mata fada irin wannan.
Shin ina matsalar take?, Tambayar da mujaheeda take fanan yima kanta kenan.

<< Nima Matarsa Ce 10Nima Matarsa Ce 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.