Hakkin mallaka nawa ne,ban yarda a juya mun labari ta ko wace siga ba, a guji karanta Shi a YouTube ba tare da izinin marubuciyar ba
Taufiq ya tsaida motarsa acikin harabar gidan,ya Dan Jima acikin mota kafin ya iya bude kofar motar ya fito ,gaba daya jikinsa babu karfi,a hankali ya taka zuwa cikin gidan Wanda gidane na rufin asiri don duk Wanda ya mallaki gidan ba za'a kirashi da talaka ba.shin wane kaskanci haj.murjanatu take kallo acikin wannan zuriar?
Kai tsaye falon mahaifinsa Alh. Yusuf lamido ya wuce. . .