Skip to content

Nima Matarsa Ce 2

Hakkin mallaka nawa ne,ban yarda a juya mun labari ta ko wace siga ba, a guji karanta Shi a YouTube ba tare da izinin marubuciyar ba

Taufiq ya tsaida motarsa acikin harabar gidan,ya Dan Jima acikin mota kafin ya iya bude kofar motar ya fito ,gaba daya jikinsa babu karfi,a hankali ya taka zuwa cikin gidan Wanda gidane na rufin asiri don duk Wanda ya mallaki gidan ba za’a kirashi da talaka ba.shin wane kaskanci haj.murjanatu take kallo acikin wannan zuriar?

Kai tsaye falon mahaifinsa Alh. Yusuf lamido ya wuce sanin Yana gida awannan lokacin,cikin sallama ya shiga falon tare suka amsa sallamar da mahaifiyarsa haj.saratu wacce take aikin damama Alh Yusuf lamido fura.”Ka dawo ?” Cewar haj saratu ya amsa Yana kokarin zaunawa akasan falon “na dawo umma”,daganan cikin girmamawa ya gaidasu,ya cigaba da Zama ba tare daya Kara cewa komai ba bayan gaisuwar.jefi jefi mahaifan nasa suna kallonsa duk sun gama nazarin damuwar da yake ciki hakan yasa bayan Haj saratu ta gama dama furar ta ba Alh Yusuf lamido ta koma ta nemi waje ta zauna tana cigaba da kallon dan nata.

Zatayi magana kenan Alh Yusuf lamido ya rigata, “Taufiq yayane? Akwai damuwa ne?”Haj saratu tace “abinda nake son na tambaye Shi kenan don fuskarka ta nuna kana cikin damuwa menene?”

Taufiq yadan muskuta gami da gyara zamansa sannan yace, “Hakane ina da damuwa wacce bata wuce ta mahaifiyar mujaheeda.” Haj saratu ta saki numfashi ahankali tace “Kai jamaa aikin kenan me Kuma tayi,ta Kara gindaya wani sharadinne?” Alh Yusuf lamido ya aje furarsa a gefe gami da cire gilashin fuskarsa Kamala da nagartarsa ta Kara fitowa ya dubi Taufiq yace “meya faru tsakaninku?”

Sannu ahankali Taufiq ya gama gaya musu duk yadda sukayi da Haj murjanatu ya Kara da cewa”Gaskiya Abba lamarin nan ya fara bani tsoro na Fara hangoma Kaina daukar dala babu gammo,ta yaya za’ayi ace Haj murjanatu zata dinga Dora min abubuwa masu wahala Masu kama da kora da hali na riga na yardarma Kaina cewa ta gama Raina matsayina tana kallona amatsayin Wanda be isa ba tana kallona amatsayin Wanda kamar zatayi masa alfarma Amma wannan Karon Bana Jin Zan yarda da wannan sharadin nata ni gaba dayama auran ya Fara fita araina,ta ina ta yaya Zan auri yarta Kuma na koma gidanta da zama?

KO ta yaya zan watsar da darajata na amshi gidanta na zauna da yarta aciki meye matsayina idan nayi hakan,” ya karasa magana da sauti me cike da tsantsar damuwa.
Alh Yusuf lamido yayi shuru idanunsa na kafe akasan kafet din falon,ayayinda Haj saratu ta numfasa itama duk damuwa ta baibaye fuskarta tace ” Ni Kam na rasa wace irin macece Haj murjanatu,wacce ta dauki rayuwar duniya tamkar ba zaa mutu ba babu komai agabanta face arziki bata ganin kowa da daraja idan ba mai arziki ba, fitinarta tayi yawa sai kace akanta aka fara aurar da ya,duk wulakance wulakancemta ta gama don dole ta yarda da auren saboda yarta na so Amma Kuma duk da haka ba zaa samu kwanciyar hankali da maslaha ba komai ita zata tsara Aina aka taba wannan,gaskiya Taufiq ina tausaya maka don ban hango maka farinciki acikin wannan al’amarin ba”,Alh Yusuf lamido yayi saurin dakatar da ita yace “Kada kiyi masa mugun baki insha’Allah zai Sami farinciki acikin auransa” ya dawo da kallonsa Kan Taufiq yace “Taufiq Ka kwantar da hankalinka duk wani bawa baya tsallake kaddararsa idan har mujaheeda Allah ya zaba maka amatsayin Mata babu Wanda ya isa ya hana hakan kasancewa,Kuma ni duk abinda Haj murjanatu takeyi baya damuna saboda bana kallonta marigayi Alh sulaiman kadai nake kallo mahaifin mujaheeda Wanda bazan taba manta halaccinsa gareni ba nayi aiki dashi Bai min mugunta ba duk abinda na Samu na Samu ne asanadiyyar Shi har Allah ya dauki ransa bamu taba batawa ba Bai taba fadan aibuna ba ban taba fadan aibunsa ba mutum ne me mutunci da sanin darajar Dan Adam hakan yasa nake son mujaheeda ta kasance surukata don na Kula da ita kamar yadda uba yake kulawa da yarsa” ya aje numfashi ahankali Yana cigaba da kallon Taufiq yace” Akwai halin mutum da bazaka iya canjashi ba to irin halin Haj murjanatu kenan tana da baudaddan Hali nasanta nasan halinta bata da kirki Shi Kansa marigayi Alh sulaiman baiji dadinta ba macece me izza kudi na zugata don haka yasa duk abinda takeyi baya Bani mamaki kaima Kuma ina son Ka cirema kanka damuwarta tunda kana son yarta Ka kauda kanka akanta da halinta” Haj saratu ta dubeshi tace “Amma Alh Baka ganin zakewarta yayi yawa gaba dayafa ayadda na fahimceta so take taja akalar rayuwar auren yaran nan don Bana Jin ko auran akayi zata bar Taufiq ya Zama namiji agidansa Wanda Kuma Kai kanka kasan akwai matsala,Kuma yanzu awannan sharadin data gindaya kana ga akwai hanyar bullewa yaron nan ya gyara bangaransa ya kashe kudi yayima wajen hidima, bugu da Kari idan tayi hakuri ta bari ta Fara Zama anan din inace Gini yake yi ahankali zai Gama kwana nawa ne idan Allah yasa ya gama ginin zasu tashi su koma gidansu meye abin gaggawa,meye aibu don sun Fara Zama anan KO ko rainin arzikin data Saba ne yasa zata CE haka” Alh Yusuf lamido yace “Na fahimceki kema ina son ki fahimceni ,itafa Haj murjanatu tunda bata son auren nan duk hanyar da zata bata lamarin Shi zata bi don haka biye Mata bashi da amfani” ya dawo da kallonsa Kan Taufiq ya Kira sunansa ya amsa sannan yace”kayi hakuri Ka karbi gidan da zata Baku Ku zauna,Ka cigaba da gininka ranar da Allah yasa Ka gama saika tattara Ka dawo gidanka bikin nan ya kusa kowa yasani Bana son asami wata matsala me kama da an fasa Ka kyaleta ta karata ina CE dai idan aka daura auren shikenan duk wani iko ya dawo hannuna” Taufiq ya girgiza Kai yace “Abba bana Jin KO Anyi auren nan Zan mallaki yancina da cikakken maigida Bana Jin zata barmi na tsara rayuwar gidana yadda nake so dagaske Abba ina Jin kamar nace na fasa auren nan” ya daga masa hannu yace ” Kada Ka Kara fadan haka yar Alh sulaiman tafi karfin haka awajenmu kamar yadda na gaya maka ne Ka yarda da bukatar ta wahalarta adaura auren kama cirema kanka damuwa Ka fita batunta.”

Taufiq ya aje numfashi ahankali cikin ràshin sanin madafar dafawa yace “shikenan Abba babu damuwa zanyi abinda kace.” Haj saratu cikin ràshin gamsuwa da hukuncin tace ” yanzu shikenan duk wahalar daya sha wajen gyaran wajen nan ya tashi abanza tsakani da Allah babu adalci awannan maganar na rasa abinda Haj murjanatu ta dauki kanta ” Alh Yusuf lamido ya dau furarsa ya cigaba dasha Yana cewa ” gyaran waje Bai tashi abanza ba ga kaninsa nan Ibrahim duk ranar daya tashi aue shiga kawai zaiyi babu wata damuwa” Shi Kansa Taufiq Bai dauka humncin da mahaifin nasa zai yanke kenan ba asanyaye ya tashi ya fita duk jikinsa babu laka.

Bookmark
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

<< Nima Matarsa Ce 1Nima Matarsa Ce 3 >>

Drop a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.