Skip to content
Part 3 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Mujaheeda na kwance asaman doguwar kujera cikin kwalliya ta alfarma Kai Ka dauka wani waje zata,sai tashin kamshi take na musamman, karfe takwas da minti daya ne na dare,tana rike da wayarta iPhone 14 Ga iPhone 13 can asaman tebur gefenta Ga daya wayarta nan Samsung s22 ultra.

Hadimanta guda biyu lami da lauratu suna ta aikin Kai kawo akan bukatunta duk sun cika gabanta da abubuwan ciye ciye masu saukin ci marasa nauyi Wanda suka dace aci da daddare.Babu Wanda take kallo acikinsu idonta na Kan waya tana aikin danne danne babu abinda ya dameta.Har zuwa lokacin da Alh Mustapha labaran ya shigo falon cikin sallama duk su lami sukayi masa sannu da zuwa gami da ficewa daga falon , sannan Mujaheeda ta waiwayo ta dubeshi ahankali tace “sannu da zuwa daddy”,ya dan dubeta yace ” mujaheeda kina lafiya”,ta amsa “lafiya lau”.Dai dai lokacin Haj murjanatu ta shigo falon itama cikin shiga ta kasaita Kai da kallonta kasan kudi suna hsukatata,ta dubi yarta tace “Sun tura miki datar”ta gyada Kai tace “sun tura ” ta fada atakaice,Haj murjanatu ta saki tsaki tace “Don shirme kuna sane da lokacin da ya kamata kusa data Amma wai har sai an tuna musu na rantse idan sukayi wasa Zan canja inda zaa dinga Sanya Miki data ba tare da sun dinga bata Miki Rai ba” mujaheeda ta shagwabe fuska tace “Gaskiya mummy gara kiyi hakan kawai.”

Alh Mustapha labaran ya aje boyayyiyar ajiyar zuciyarsa gami da gyara zamansa zuciyarsa cike da Jin zafin yadda Haj murjanatu take lalata rayuwar yarta da kanta,ta shagwabata ta fifitata ta dauki son duniya ta Dora Mata ,duk da bashi ya haifeta ba hakika ransa Bai masa dadi ,yadda ta gurbata rayuwar yarta.ya dawo da kallonsa Kan manya manyan wayoyin da mujaheeda take rikewa Wanda duk wata datar da ake Dora musu yà ishi Haj murjanatu ta dauki hidimar marayu masu yawa.

“Ka dawo?” Muryar Haj murjanatu ta katsema Alh Mustapha labaran tunaninsa,ya juyo Yana kallonta sannan yace “eh nadawo”,ta nemi kujera ta zauna tana dubansa tace ” An Sami fito da Kayan”ya gyada Kai yace “eh ,masu shima har sun zo sun dauka ,sun Kuma tura sauran kudin”ta gyada Kai tace ” Hakan yayi kaga an warware dasu ,hankali ya kwanta” yace ” sosai kuwa.”

Mujaheeda ta dubi Haj murjanatu tace “mummy Taufiq ya turo text” ta dubeta sosai tace “Kan maganar da mukayi KO me?” Ta Dan gyara kwanciyar ta tace “eh”, nan da nan ta hade rai tace “yafi karfin ya Kira waya,KO ya dawo ya Fada da bakinsa shine zai turo sako saboda tsabar ràshin muhimmancin maganar agunsa”. mujaheeda tace ” mummy don Allah ki daina fadin irin maganganun nan akan Taufiq zuciyata fa bata min dadi ” ta saki tsaki tace ” saboda ke dinne ma nake daga masa kafa don babu yadda zanyi Amma har kullum bazan fasa gaya Miki ba Taufiq Bai dace da ke ba asalima nayi Imani KO bukatarki daya bazai iya dauka ya biya ba tun daga abinda kike ci zuwa kayan da kike Sawa da man da kike shafawa balle aje batun bukatunki na yau da kullum,babu abinda zai iya tsinana Miki.”

Alh Mustapha labaran ya muskuta cike da ràshin jindadin maganganun da Haj murjanatu take yi yace ” wai Haj me yasa kike kallon yaron nan amatsayin Wanda be isa ya auri mujaheeda ba,bayan dimbin tarbiyya da nagarta da yake dashi ta KO wace fuska mujaheeda tayi Saar Miji baida wata makusa ,illa ke da kike kokarin dole sai kin dauka kushe kin Dora akansa,”

Tayi saurin dubansa tace ” zaka Fara ko Alh?” Ya girgiza Kai yace “Ba batun Zan Fara bane akalla ya kamata ki Fara dawowa hayyacinki ki fahimci ba kudi bane kadai jindadin rayuwa ba Kuma me arziki bane kadai me daraja da mutunci aah ina tabbatar Miki wani talakan yafi wani me kudin arziki da daraja da mutunci ba komai kudi yake saya ba ba komai kudi yake badawa ba ,haka zalika ba koina kudi yake kawo kwanciyar hankali da jindadi ba,kallon da kikema talaka ba dai dai bane”

Haj murjanatu ta Tabe Baki tace ” shikenan don kana son na daidaita tsakanin talaka da me kudi sai na rungumi talaka ya Zama abokin rayuwar yata bayan kafi kowa sanin yadda yarinyata ta taso da irin rayuwar da take ciki da irin gatan Dana bata ,kasan Kuma ban hada kowa da ita ba”, ya Kara gyara zamansa yace ” Tunaninki da hasashenki bazan taba hanaki ba don da Zan iya hanaki da tuni nayi hakan shekara da shekaru don haka na barki da Tunaninki. Amma kisani Taufiq da kikema kallon talaka be isa ya auri mujaheeda ba ba dai dai bane, saboda Taufiq baya sahun talaka mutumin da yake da babban aiki ahannunsa ,yake da ilimi yake da abin hawa yake iya daukar hidimar wasu yake iya kyauta ya Kuma fi karfin bukatunsa to ya wuce adinga jifansa da Kalmar talauci,Kuma Samun namiji irinsa yanzu sai an tona kamata yayi ma Kima Allah godiya da yasa shine zai auri mujaheeda don babu Wanda zai iya da Halinki da nata sai Shi.”

Nan da nan Haj murjanatu ta hayayyako tace ” meye halin nawa da na mujaheedan? Ko kaima zaka jefeta da Kalmar ràshin tarbiyyar ne kamar yadda wasu ke fada,tunda Naga tamkar Taufiq yafi mujaheeda muhimmanci awajenka”, ya girgiza Kai yace ” Uba Ai Bai taba jifan yarsa da Kalmar ràshin tarbiyya sai dai yakamata ki Kula kiyi tunani KO don. Sabuwar rayuwar da mujaheeda zata shiga ayanzu ki tallafeta ki fahimtar da ita meye ma Kalmar Auren Dan nayi Imani bata sani ba.”

Haj murjanatu ta hadiye yawun takaici tana kallonsa ranta abace batace uffan ba ta dubi mujaheeda wacce tayi shuru ta Dora hannunta asaman kuncinta,babu abinda ta tsana sama da ràshin zaman lafiya da hadin Kan da mahaifiyarta ba tayi da daddy in dai zasu zauna tare to minti biyar yayi yawa zaa Fara fada,sau tari tana yawan tambayar kanta wai Dama haka zaman aure yake babu komai cikinsa sai fada da tashin hankali.

“Wace amsa ya bayar” Haj murjanatu ta tambayi mujaheeda tana cigaba da kallonta , mujaheeda tadan numfasa sannan tace” yace bazai iya Zama acikin nan gidan ba, Amma zai iya Zama a daya daga cikin gidajenki, Amma shima da sharadin idan ya gama gininsa zai koma gidansa da Zama.”

Haj murjanatu ta saki tsaki tace ” oho dai ,ba dai zaki zauna a gidan gado ba”
Alh Mustapha labaran yayi Mata wani irin kallo yace ” yanzu kina nufin inda zai zauna da matarsa ma sai kin zaba masa Haj.”

“To da me kake tsammani nabar yata ta zauna a gidan gado inda zaa hanata sakat to ban raini yata don daga karshe taje ta wahala agidan wani Kato ba.”

Numfashi kawai ya aje ba tare daya Kara cewa komai ba ya Mike ya shige daki,a zahiri Yana tausayin Taufiq auransa da mujaheeda ba karamin kalubale bane a gareshi,hakika don baa kawo cikas akan aure ne Amma da Shi da Kansa zai gayama Taufiq ya rabu da mujaheeda don bata dace dashi ba.

Kwarai da gaske Yana ganin darajar mahaifin Taufiq Yana ganin kimarsa Kuma Yana ganin mutuncin Taufiq Yana jinsa aransa kamar Shi ya haifeshi,

Bai son duk wani abu dazai taba kwanciyar hankali Taufiq Wanda yayi Imani auren mujaheeda shine babban ràshin kwanciyar hankalin da zai fuskanta a rayuwarsa.

*****
Washe gari Alh Mustapha labaran da Kansa ya tafi gidan Alh Yusuf lamido,ya Kira Taufiq duk suka hadu a falon Alh Yusuf lamido.

Sun Dade suna tattaunawa Kan maganar data kawo Alh Mustapha labaran inda ya cigaba da cewa,

“Duk wani abu da Haj tasan zatayi, Wanda ya sabama hankali bata Bari nasani asalima bata son sani cikin duk wani lamari datasan Zan iya Mata gyara aciki,shiyasa da zatayi wannan KO kadan ban sani ba,don Allah ku Kara hakuri akan halinta

Tunda aikin Gama ya Riga ya gama auren nan yazo kuyi hakuri akarasa ahaka daga sanda ya aureta babu wani sharadi KO wani iko da dole zaa bi nata.” Taufiq ya numfasa cike da damuwa yace ,”Ni kam Alh Bana tunanin Ko auren nan akayi zata barmu mu sami natsuwa.”

Alh Mustapha labaran yace “kaine zaka dage Ka Zama namiji agidanka KO kadan Kada Ka bata damar da zata shiga cikin lamarin gidanka,” ya karasa magana Yana yi masa kallon tausayi don ya fishi sanin dala ba gammon daya dakkoma Kansa don auren mujaheeda Alh Mustapha labaran yasan shine kuskure na karshe da zaiyi a rayuwarsa Amma ta yaya zai fahimtar dashi?

Alh Yusuf lamido ya dubi Alh Mustapha labaran yace ” babu komai Alh nagode kwarai da yadda kake nuna damuwa akan lamarin yaran nan ,ina Kuma Kara tabbatar maka da cewa Ko da wasa duk wani abu da haj zata nuna KO ta bullo dashi bazai taba Sawa mu janye daga maganar auren nan ba,Kada kadamu.”

Alh Mustapha labaran yajindadin maganganunsa shima yayi masa godiya kafin sukayi sallama ya tafi.zuciyarsa cike da tunanin irin sa’ar da mujaheeda tayi na shigowa cikin wannan kyakkyawar zuriar wacce Yana Mata fata gami da adduar Allah yasa sanadiyyar gyaruwar tarbiyyarta ne.

DAGA TASKAR YAR GIDAN IMAM.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 2Nima Matarsa Ce 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×