Skip to content
Part 4 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Haj murjanatu daya daga cikin manya manyan gidajenta ta zabama mujaheeda inda zata zauna tare da mijinta,bayan da mujaheeda ta tabbatar Mata da gidan yayi Mata ya dace da tsarinta.Duk da gidan lafiya lau yake baida wata matsala haka tasa akara gyara Shi tace tana bukatar amaida Shi sabo.

Ta bangare daya Kuma tuni duk kayan dakin mujaheeda sun sauka daga Dubai Bana tsammanin hatta cokali an sayama mujaheeda daga Nigeria komai daga waje aka sayo.
Hatta kayan da zata sa na biki daga waje akayo order su.mujaheeda Kam ta samu dukkan gata don idan gata Yana yawa hakika yakamata yayima mujaheeda yawa.shirye shirya ake sosai na auren Shi Kansa gidansu gani kawai Alh Mustapha labaran yayi anata gyara babu KO Neman shawararsa hakan yasa shima baisa Kansa aciki ba,don yafi kowa sanin halin Matarsa na kushe da gwasala musamman idan batasa Ka acikin lamarinta ba.

Shi Kam Taufiq ya rasa abinda yasa ya Sami Kansa da rage zumudi da kaguwa akan auran Nasa KO don fitintunun da suke ta biyo baya ne oho,sai dai duk wani shiri shima ta bangarensa angama.

Taufiq yayi sallama ya shiga dakin mahaifiyarsa Haj saratu inda take zaune tare da babbar yarsa Haj Bilkisu ,Haj saratu ta dago cike da walwala ta dubeshi tace ” yauwa Taufiq Ka karaso” ya lalubi kujera ya zauna Yana Dan murmushi yace ” Eh umma ” sannan ya dubi Haj Bilkisu yace ” Ashe kina gidan” tace “eh Ka tasoni ” yace ” ni kuwa?

Haj saratu tace ” Ka tasota mana,lefe ta kawo tace angama hada komai Kuma ya kamata akai tunda bikin nan Bai wuce Saura sati biyu ba” ya gyada Kai yace “to shine sai an kirani,” ya dubi Haj Bilkisu yace “to Ai yaya keya kamata kisa Rana ki kwashi Wanda zaki kwasa kuje Ku Kai musu” Haj Bilkisu tace “to Amma dai ai a sanar da can gidan su mujaheedan cewa zaa kawo lefe” Taufiq yace ” badamuwa idan kinsa lokaci sai ki gaya min ni kima Saina sanar dasu zaku zo”.Haj saratu tace “eh hakan zaayi,ke kina ganin yaushe zaa Kai musu kayan” ta tambaya tana kallon Haj Bilkisu.

Haj Bilkisu ta jinjina Kai tace ” AI umma ina ganin me zai hana akai musu gobe idan yaso sai Taufiq ya sanar dasu zamu zo gobe,tunda an Riga angama komai ai babu amfanin cigaba da ajiyarsu” Haj saratu ta juya ta dubi Taufiq tace”To kaji

Ya gyada Kai yace ” eh, badamuwa Zan sanar dasu insha’Allah,goben sai akai kawai” ” To Allah ya kaimu” cewar Haj saratu.

Haj Bilkisu ta gyara zamanta tana duban Taufiq tace ” AI gaskiya kayi kokarin hada lefen nan ,don koina zaa Kai su to babu yadda zaayi a kushe kayi matukar kokari , Allah dai yasama auren albarka” gaba daya suka hada Baki da Amin.

Haj Bilkisu tace ” To yanzu shikenan ba’anan gidan zaku zauna ba,agaskiya fitinar mahaifiyar mujaheeda yayi yawa,duk kyan da wajen can yayi sun raina ” Taufiq ya cije baki alamar har yanzu ransa Bai masa dadi ba akan hukuncin Haj murjanatu.yace ” babu yadda zanyi yaya tunda Abba ya Bani umarnin na amince,Amma insha’Allah sauri zanyi na kammal gidana mu koma can don Bana Jin Zan laminci wulakanci akan zamana agidanta,don matukar ina kaunar rayuwar yanci dole nabar musu gidansu,” Haj Bilkisu tace ” kwarai kuwa kayi tunani me kyau ai kawai kayi kokari Ka kammala gininka,don Bana Jin wannan matar zata sa maka Ido ba tare da tayi kokarin juyaka ba matukar kana Zama agidanta karshema gori ya biyo baya ” Taufiq yace ” Saima kinga irin katon gidan data bamu,

Don mujaheeda ta kirani dole sai naje Naga gidan idan yayi min na gaya Mata Bassi nazo ba matukar yayi Mata shikenan,Amma yadda ta matsa yasa naje,gidan yayi girma da yawa Amma tunda na fahimci yayi Mata Kuma saboda ita mahaifiyarta take son mu zauna agidan yasa nace yayi don Bana son ma wata doguwar magana.”

Haj saratu ta saki tsaki ahankali tace “shikenan dai anyi Mata abinda take so,sam bana Jin wani kwanciyar hankali matukar ba auren nan Naga an daura ba,gaskiya Taufiq ina tausaya maka don banjin kayi dacen suruka sai dai babu yadda zaayi basa Bai tsallake kaddararsa.”

Haj Bilkisu ta aje numfashi ahankali tace ” umma sai dai addua tunda Shi Taufiq yaji ya gani Kuma Yana kaunar yarta hakanan zai cigaba da hakuri,Amma sangarta da ràshin tarbiyyar mujaheeda waye Bai sani ba,Shi Taufiq dinma AI yafi kowa sani ,kuma wace shawarace baa bashi ba Kan Kada ya Kai Kansa Amma soyayya ta makantar da Shi,AI aikin Gama ya Riga ya gama Allah dai yasa ayi a sa’a kawai.”

Haj saratu ce ta amsa da da “Ameen” ,Shi kam Taufiq shuru kawai yayi ya maida Kansa kasa,duk abinda Haj Bilkisu ta fada hakane,sai dai Shi Kansa yanzu Yana Jin tamkar yayi kuskure wajen zabar abokiyar rayuwa.

A ranar Taufiq ya Kira mujaheeda ya sanar da ita batun kawo kayan lefen gobe, suna Gama wayar ta dubi Haj murjanatu da itama gama wayarta kenan da manajan daya daga cikin kamfanoninta.

“Mummy Taufiq yace Na sanar dake gobe zaa kawo lefena,”

Haj murjanatu ta Tabe Baki tace ” Allah ya kaimu, Allah yasa su kawo abin arziki” mujaheeda ta dubeta sosai tace “shima aiya sani,babu yadda za’ayi ya kawo min kayan lefe na banza don yafi kowa sanin banasa kayan banza” tayi murmushi sosai tace.”

Yanzu kikayi magana kamar yata,haka nake so ki dinga daukar kanki yadda kike ,ki dinga gane matsayinki” mujaheeda tayi murmushi tace ” mummy kenan ,nafasan abinda nake yi duk wani abu da zai kaskantar da darajata ke kinsan Bana so,kullum ina son Naga na wuce na tsara ,don haka Bana tsammanin Zan dankwafar da Kaina a’inda darajata zata Sami nakasu” Haj murjanatu ta dawo ta zauna kusa da mujaheeda ta janyota ta kwantar Kan jikinta cike da matsananciyar kauna.

Tace

“Mujaheeda duk duniya ban hada son ki da komai ba,shiyasa nake son Naga na share Miki duk wasu matsaloli da zasu kwanta ahanyar rayuwarki, musamman matsalar zaman aure,saboda idan mace batayi sa’ar gidan aure ba Ina tabbatar Miki ba zata taba jindadin rayuwa ba ,zata kasance tamkar wacce ta rako Mata duniya za Kuma ta rasa duk wani farinciki na rayuwa” ta Kara kwantar da kanta akan jikinta ta cigaba da cewa.”

Shi yasa kikaga ina tsauwalawa akan Taufiq saboda nasan babu yadda za’ayi ya iya da bukatunki Amma tunda zuciyarki tayi nisa akan sonsa yasa na amince ki aureshi Zan Kuma cigaba da wadataki da duk abinda kike so KO dashi ya gaza saboda na Sani na Kuma fahimci kina matukar sonsa don Shi kadaine mutumin da na tabbatar kina yi masa so na hakika Wanda zaki iya fsdawa wani mawuyacin Hali akansa Shi yasa nake ji Miki tsoron Kada wata Rana Taufiq yayi Miki halin su na Maza.”

Mujaheeda tayi gaggawar tashi ta zauna tana kallon mahaifiyarta da wani irin Ido me cike da tsoro tace, ” yanzu mummy kina tunanin akwai wata Rana da Taufiq zaiyi min halinsu na Maza,kina ganin wata rana Taufiq zai iya kallon wata mace yace Yana sonta?”

Haj murjanatu ta jinjina Kai tace ” Abinda yafi komai sauki kenan wajen namiji”

Nan da nan idanun mujaheeda ya cika da hawaye tace ” Amma mummy kinsan duk duniya babu abinda na tsana sama da kishiya Ko ,na rantse Dana zauna da kishiya gara n mutu…

A gaggauce Haj murjanatu ta rufe bakinta jikinta na rawa tace ” Kada ki Kara furta wannan mummunar Kalmar,ina tabbatar Miki da cewa matukar ina Raye babu ke babu Zama da kishiya Taufiq din banza ya isa ya Miki kishiya waye Shi AI ba irinku akema kishiya ba,ki kwantar da hankalinka, kada ki Kara ma wannan tunanin kinsan Bana son damuwarki.”

Mujaheeda ta maida kanta ta kwantar Kan jikin mahaifiyarta tana maida numfashi ahankali, ayayinda Haj murjanatu ta cigaba da shafa bayanta tana kwantar Mata hankali da duk wasu maganganu da zasu kwantar Mata da hankali.ita kanta tasan kishin mujaheeda yayi yawa hakan Yana daya daga cikin dalilan da yasa take ganin Taufiq Bai dace da yarta ba don beyi kama da namijin da zaa yarda dashi ba Amma ya Zama dole yanzu tasan duk hanyar da zata bi wajen ganin ta cika duk wani burin murjanatu.

Ita Kam mujaheeda KO yaya maganar kishi ta ratso takan ji tamkar ranta zai fita ta rasa irin kishinta akan Taufiq Wanda bata iya boyewa,shin ta yayama mummy zatayi tunanin Taufiq zai iya Mata kishiya? Bayan ta gamsu da irin son da yake Mata ta Kuma tabbatar babu wata mace da zai so bayan ita.

*****
Tun safe ake shirye shiryen zuwan masu kawo lefe.hadiman gidan ba Zama anyi girki Kala Kala na alfarma.

Haj murjanatu ta gayyato kawayenta su biyu Haj Nana da Haj Binta Mata masu ji da Kansu da kudi sai kanwar Alh Mustapha labaran Haj madina wacce ita kadai ta rage masa anan garin jigawan take aure.

Karfe daya da kwata Haj Bilkisu da kannanta biyu Harira da Haulat sai kanwar mahaifinsu Haj laraba suka isa gidan Alh Mustapha labaran.

Duk a falon kasa suka zauna bayan an cika gabansu da Kayan abinci sun Dan ci dai dai misali.

Sannan aka dawo Kan lefen akwati masu tsada seti daya masu guda shida KO wanne cike yake da Kaya .kawayen Haj murjanatu sune suka tashi suka Fara Bude kayan suna dagawa.

Suna Tabe baki,ganin hakan yasa Haj madina ta tashi itama tana duba kayan cike da fara’a tana yabawa tana fadin Kai Amma anyi kokari wai.

Zuwa lokacin Haj murjanatu ta gama zuwa wuya ta yima Haj madina wani irin kallo sannan tace ” haba madina yaya sai wani koda Kaya kike Wanda ke kanki kinsan ba suyi ba.”

Haj Nana tace tana kallon kayan ” to nima dai abinda na gani kenan duk kayan kanana ne ba masu tsada bane,nasan dai mujaheeda bata Saba sa irin wadannan kayan ba.”

Nan da nan Haj Bilkisu ta harzuka ta dubi Haulat ta dubi Haj laraba tace ” Inna Ku tashi mu tafi kafin ayi batacciya don kinsan Bani da hakurin dazan juri Jin irin wadannan maganganun na wulakanci” Haj murjanatu tace ” don Baki da hakuri sai akasa fadin gaskiya,Shi ai Taufiq din ya fi kowa sanin inda ya zo Neman auren ,yasan irin kayan da ya ta ke Sawa to don me zai kwaso wannan kayan akawo” a harzuke Haj Bilkisu tace.”

To gidan Karuna masu karyar arziki ,idan bakwa so ai sai Ku fada mu kwashe kayanmu mu tafi,alabasshi sai ki saya Mata kayan da wani Bai taba sa irinsa ba aduniya”

Haj laraba ta Mike ta dubi Haj Bilkisu tace ” Kada ki sake magana idan kika Kara cewa uffan sai na bàta Miki Rai” ta dubi su Harira tace ” Ku tashi mu tafi”

Haj madina tayi saurin tahowa kusa da Haj laraba tana bata hakuri ” don Allah Haj kuyi hakuri Kada wannan ya kawo wata matsala don Allah kuyi hakuri.”

Haj murjanatu ta saki tsaki tace ” ke madina Bana son munafinci me akayi da har kike Basu hakuri.”

Haj Bilkisu ta saki tsaki ta wuce ta fice ayayinda su Haj laraba suka bita dukkan su cikin matsanancin bakinciki musamman yadda suka bsrsu suna jagwalgwala maganar gami da cigaba da kushe kayan lefen.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 3Nima Matarsa Ce 5 >>

5 thoughts on “Nima Matarsa Ce 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×