Tsana da kiyayyar da Ande Dije ke yima muhseena da mahaifiyarta ya Kara kamari tunda muhseena ta daina daukar Mata talla ta koma islamiyya, ko kallon arziki bata yi Mata ko gaisheta tayi daker take amsawa.
Ga uwa uba takaicin shigowar Kabir cikin rayuwar muhseena domin taga yadda suka Fara fin karfin abubuwa da dama, rayuwarsu ta Fara canjawa, domin dai ko bayan da Kabir ya koma Kano kullum Yana hanyar turoma muhseena sakon kudi ta asusun bankin wani abokinsa salisu Wanda shine ke kawo Mata sakon kudin ya Kuma duba masa lafiyarta kamar yadda ya dora ma salisun kulawa. . .
Sidkxknd na melabari da warhaka yan da safiya na