Skip to content
Part 23 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Tsana da kiyayyar da Ande Dije ke yima muhseena da mahaifiyarta ya Kara kamari tunda muhseena ta daina daukar Mata talla ta koma islamiyya, ko kallon arziki bata yi Mata ko gaisheta tayi daker take amsawa.

Ga uwa uba takaicin shigowar Kabir cikin rayuwar muhseena domin taga yadda suka Fara fin karfin abubuwa da dama, rayuwarsu ta Fara canjawa, domin dai ko bayan da Kabir ya koma Kano kullum Yana hanyar turoma muhseena sakon kudi ta asusun bankin wani abokinsa salisu Wanda shine ke kawo Mata sakon kudin ya Kuma duba masa lafiyarta kamar yadda ya dora ma salisun kulawa da muhseena.

Bugu da Kari kullum idan Kabir bai Kira muhseena ba ya kirata sau hudu a rana, irin Kuma hidimar da yake Mata Ko tace ya daina ko ya rage bai sauraronta illama yayi Mata fadan ta daina cewa haka domin ya riga ya dorama Kansa nauyin Kula da ita.

Domin dai tun Fara zuwa gidansu muhseena, Kabir ya gamsu da cewa suna bukatar taimako ya Kuma daukar ma Kansa taimaka musu da abinda Allah ya hore masa, balle yanzu da ya dauki soyayyar muhseena ya Dora aransa Yana matukar Sonta Yana jinta ajikinsa.tunda ya koma Kano bakin aikinsa baida tunani Saina muhseena sosai ya rage walwala a office domin kowa yasan halinsa na wasa da dariya baida daure fuska baida fushi ko da ko me akayi masa.

Amma tun dawowarsa daga Durmi duk ya canja ko magana bai damu da yayi ba, hatta mutanen office dinsu sun Lura da hakan.

Yana son muhseena Yana Jin tausayinta , burinsa ya aureta ya inganta rayuwarta, baya Jin akwai abinda bazai iya yima muhseena ba domin Samun kwanciyar hankalinta.

Tunda Kabir ya shigo rayuwarsu hatta abinci baya yanke musu ko babu dadi zasu dafa su ci. Hajara hannunta ya dawo dai dai Kuma Kabir dinne ya cigaba da daukar nauyin kudin maganinta.

Sosai abubuwa su kayi musu sauki.harga mallam Umar ya sami sassaucin abubuwa da dama.amma ga Ande Dije abin baiyi Mata dadi ba , tafi son tayi ta ganin Hajara cikin ràshin kwanciyar hankali da sukuni sai kace wacce tayi Mata wani mugun abu.

Muhseena na Kan waya ita da Kabir ne ya kusa awa daya da Kira Amma har zuwa yanzu bai katse ba.hajara ta shigo dakin shine shigowarta na biyu muhseena na waya ta dauki ashana ta fita.

Kwarai itama muhseena yadda Kabir ya kamu da sonta haka itama ta kamu da sonsa, bata taba soyayya ba sai akansa don haka gaba daya ta bude zuciyarta ta saka Shi a ciki.cikin matukar so da kauna suka gama wayar gami da sallama.

Muhseena tayi kasa da wayar tana dan murmushi, dai dai lokacin Hajara ta Kara shigowa dakin.ta dubeta sosai tace ” Allah yayi angama wayar” tadan yi murmushi tace ” eh Inna”. Hajara ta nemi gefen katifar kusa da muhseena ta zauna tana dan dubanta , kafin tayi magana muhseena tace ” Inna Kabir yace jibi zai zo”. Hajara ta numfasa tace ‘ najidadin hakan,’ sannan ta Kara gyara zamanta ta cigaba da cewa ” saboda ina son muyi magana da Shi sosai, Bana son sai kin Gama zura kanki kin Saba da Kabir sannan azo arabaku.”

Da sauri cikin faduwar gaba muhseena ta dubi màhaifiyarta tace ” Inna me yasa kikace haka.”

Hajara damuwa da bayyana sosai a fuskarta ta aje numfashi a hankali tace “akwai matsaloli sosai muhseena ba Kuma na son hakan ya Kara taba rayuwarki kin sha wahalar jure Jin mugayen kalamai Akan rayuwarki da har yanzu baki gama sanin komai akanta ba.”

Jikin muhseena ya kara matukar sanyi, tayi shuru gabanta na faduwa tana kallon mahaifiyarta cikin fargaba.

Hajara tayi dibarar goge hawayenta da ya ke kokarin fito Mata ta cigaba da cewa ” ko kadan Bana son ki shiga mugun yanayin dana shiga a baya nasan zafin rabuwa da masoyin daka shaku da Shi, hakan yasa Bana son ki shiga yanayin da na shiga domin zai yi matukar nakasa Tunaninki.”

Muhseena ta numfasa cikin Karin fargaba tace “Inna me yasa kike tunanin Kabir zai iya fasa aurena” ta girgiza Kai tace ” ba Kabir bane nake fargabar zai fasa aurenki, mahaifansa ne nake fargabar zasu Hana Shi aurenki” “Saboda me Inna”. Muhseena ta tambaya a gajarce.

Hajara tayi shuru ba tare data amsa Mata ba, muhseena tace ” saboda dalilin da kika kasa gaya min gaskiyarsa har yau, haka zalika saboda dalilin surutan da mutanen gari su keyi Wanda har yanzu kika kasa gaya min gaskiyar”.

Hajara ta dubeta sosai tace ” wace gaskiya kike son sani bayan wacce kika riga kika Sani,”

Ta Kara kallonta sosai tace ” Baki da wani uba da ya wuce mallam, duk surutun Mai surutu bai isa ya canja hakan ba.”

“To idan hakane Mai yasa kike fargabar mahaifan Kabir zasu Hana auren mu” Hajara tace “saboda irin maganganun da mutane ke yi Wanda kema ya ke son juya Miki tunani kullum, balle mahaifansa da suke cikin garin Durmi suka San komai, Bana son kisa kafarki acikin takalmina.”

Gaba dayansu su kayi shuru na wani lokaci, sannan Hajara ta cigaba da cewa ” Shi yasa nake son idan ya zo muyi magana da shi ya turo iyayensa, ke Kuma kisama kanki dangana akan duk hukuncin da ya biyo baya.” Muhseena ta gyada kanta tace “Insha’Allah.”

Daganan ta yi tagumi komai ya tsaya Mata tunani ya addabi ruhinta kullum mahaifiyarta na nuna Mata tayi hakuri don ba lalle bane ta auri Kabir , ita Kuma zuciyarta ta kasa yakice Kabir ta kasa sassauta ma kanta soyayyarsa balle nisanta dashi, duk da kullum cikin fargaba take da damuwa gami da tunanin inda zatasa kanta idan har hakan ya kasance.

******

Da kuka Mujaheeda ta farfado, da sauri Haj murjanatu ta sa hannu ta rungume ta, tana Kiran sunanta . Jin muryar mahaifiyarta yasa tayi sauri ta Karasa Bude idanunta gami da sa daya hannunta da ba’a daura masa ruwa ba ta rungume Haj murjanatu tana Kiran” mummy.”

Àlh Mustapha labaran ya Matso shima sosai kusa da yarsa Yana kallonta Yana Kiran sunanta.

Taufiq dake jingine jikin kofar dakin ya turo kofar ya shigo a rude ya dauka wani abu ne ya sameta don yadda ya ji Àlh Mustapha labaran Yana Kiran sunan mujaheeda.

Idon mujaheeda dore kan Taufiq , nan da nan ta saki Haj murjanatu cikin fushi tace ” me kake yi anan yaya Taufiq, ba so kake Ka kasheni da bakinciki ba me yasa zaka zo inda nake bayan abinda kake so kenan.”

Haj murjanatu ta riketa sosai tace “don Allah ki kwantar da hankalinki , daker aka Samo lafiyarki Bana son ki Kara fadawa halin da kika fito Kan Wanda Bai damu da ke ba Bai damu da mutuwa ko rayuwarki ba.”

Alh Mustapha labaran ya dubi Taufiq cikin mamaki yace ” Taufiq meke faruwa ne, wace magana mujaheeda take yi, ko kana nufin kace duk zargin da Haj keyi akan ka gaskiya ne.”

Kafin yayi magana Haj murjanatu tace cikin matukar fusata da tsana ” duk abinda na fada akansa ba zargi bane gaskiya ne, Kuma kamar yadda na fada ne sai na dauki kwakkwaran mataki akanka sai kayi mamakin irin fansar da zan daukar ma yata,don ban hada komai da yata ba a duniyar nan.”

Mujaheeda tace Ido a runtse ” don Allah daddy kacema yaya Taufiq ya fita , dagaske nana son ganinsa.” Alh Mustapha labaran yaja hannun Taufiq suka fita daga dakin.

Tsaye sukayi a waje Alh Mustapha labaran Yana kallon Taufiq sosai idanunsa cike da neman Karin bayani.

Yace ” Taufiq meke faruwa tsakaninka da matarka, na yarda da hankalinka da kuma son da kake ma mujaheeda hakan yasa nake tunanin ba zaka taba yin abinda zai cutar da mujaheeda, sabanin yanzu da na shiga shakka tun daga yadda mujaheeda ta nuna bayan shigowarka, shin meke faruwa.”

Taufiq yayi kasa da kansa yana jin tamkar yayi kuskure, daga yadda idanun mujaheeda suka nuna babu komai acikinsu face gaskiya. Shin ko dai yayi kuskure ne kamar yadda yayi da wajen zarginta, shin wadannan hotunan da aka turo masa sun isa su sa shi zargin matarsa?

“Kai nake sauraro Taufiq” cewar Àlh Mustapha labaran cikin kaguwa da son sanin amsar tambayarsa.

Taufiq ya dago ya dube Shi yace ” Alh maganar tana da nauyi”, Alh Mustapha labaran yace ” komai nauyinta ya zama dole ka fada.”

Taufiq ya numfasa yace ” ina cikin zargin mujaheeda ne adalilin wasu hotuna da aka turo min hakan yasa nake zargin tana cin amanata ne.”

Alh Mustapha labaran ya saki salati cikin ràshin jindadin maganar ya zuba masa Ido yace ” what?( Mene)” ya gyada Kai yace ” hakane Alh, bayan ganin hotunan ne na yi mata magana shine dalilin tashin ciwon ta.”

Alh Mustapha labaran ya mika masa hannu yace” Bani hotunan na gani.”

A sanyaye ya ciro wayarsa a aljihunsa ya danna ya fito da hotunan ya mika masa wayar yace ” gasu Àlh.”

Ya Mika hannu ya karbi wayar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 22Nima Matarsa Ce 24 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×