Skip to content
Part 22 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Shin tsawon wani lokaci Mujaheeda ta dauka tana cin amanarsa , kenan duk zargin da yake MMata gaskiya ne. Taufiq yasa hannunsa biyu ya dafe Kansa da yake azabar sarawa.

Ya maida kansa ya kwantar Kan tebur ya rasa Abinda ke yi masa dadi, komai ya tsaya masa cak.shi Kansa baisan iya lokacin daya dauka Yana cikin mawuyacin hali ba, daga karshe ya tattara komai ya aje yabar office din.

Cikin matukar damuwa da tashin hankali Taufiq ya isa gida dai dai karfe shida da rabi.ya zubama harabar gidan idanu babu motar mujaheeda alamar bata dawo ba, yasa hannu ya daki sitiyarin motar Yana girgiza Kai.

Ya kusan minti goma zaune acikin motar kafin ya iya fitowa , Yana kokarin rufe kofar motar, hancin motar mujaheeda ya shigo cikin gidan kallo daya yayi ma motar ya dauke Kansa.

Sam Sam baya son ganin fuskarta, kafin ta Gama parking din motar tuni har ya shige cikin gidan. 

Zaune Maheeda ta tadda Taufiq Akan kujera ya zuba tagumi hannu biyu.ta aje key din motar ta akan tebur gami da aje gelen ta, tana kallonsa ” yaya Taufiq mun dawo kusan tare kenan” cewar Mujaheeda,

Bai tanka ba, bata damu ba ta cigaba da cewa “kaji wani irin sanyi da yamman nan, ai akwai aikin da ya kamata na tsaya na karasa nace ina gida zan taho kaina har ciwo yake min,”

Taufiq baice uffan ba, tadan kara kallonsa tace ” ruwa Zan Samu yanzu Mai zafin gaske nayi wanka ko na rage Jin sanyin.”

“Ke don Allah Kada ki dameni da shegen surutunki na tsiya” Taufiq ya fada da karfi cikin fusata, Wanda hakan yasa Mujaheeda saurin dawowa hayyacinta tana kallonsa a kidime cike da mamakin irin wannan tsawa daya katsa mata.

Tace ” yaya Taufiq lafiya zakayi min irin wannan tsawar meye yayi zafi?”. Ya dubeta da jajayen idanunsa yace ” komai ma yayi zafi, wai mujaheeda me kika dauki kanki ne? Sannan me kika dauki aurena da ke kanki”. Duk duniya idan akwai abinda mujaheeda ta tsana to fada ne da tsawa da daga murya, don haka tuni idanunta suka Fara kokarin tara hawaye. Tace ” meya faru kake min irin wannan tambayar cikin wulakanci gadara da iko, me nayi maka?”. Ya saki tsaki ya Mike Yana kallonta afusace ” dole nayi miki wannan tambayar idan akayi laakari da muguwar hanyar da kikasa kanki ciki, shin akanki mace ta taba yin aiki, meye Tunaninki da kike ganin zaki ci amanata Allah ya rufa miki asiri.”

Nan ne ta tsaida idanunta akansa cikin bakinciki domin ta Fara tunanin inda maganganun sa suka dosa, tace ” cin amana nice nake cin amanar taka, to da nayi me?” Yace ” da kike kokarin maida ni sakarai, wancan Karon har fushi kikayi da ni duk da na baki hakuri na maida laifin akaina , yadda kika nuna yasa na yarda da cewa shaidanne kawai ke son yin wasa da hankalina, sai Kuma yau Naga abinda ban taba tsammani ba, saboda haka idan da bani da shaida yanzu ina da shaidar irin cin amanar da kike min”

Mujaheeda ta kasa magana ta sa hannu ta dafe kirjinta da yake bugawa, duk sanyin da take ji ta neme Shi ta rasa.dako Taufiq ya Matso kusa da ita Yana falle Mata hotuna tana gani daya bayan daya sai ji tayi zufa na kwarara asaman goshinta.

Cikin rawar harshe tace ” waye ya tura maka wadannan hotunan da Banda masaniya akansu,” ya daka Mata harara yace ” Baki da masaniya akansu, to wacece a hoton” muryarta na rawa tace ” nice, Amma bansan sanda aka dauka ba, domin duk abinda ya faru acikin hoton babu cin amana aciki, mafi yawancun hotunan an daukesu ne alokacin da Muke aiki ni da Alh jibrin” ya Kara zuba Mata harara gami da daka Mata tsawa ya Nuno Mata wani hoton Wanda tasa hannu ta taba kirjin Alh jibrin yace ” wannan Kuma Kuna me aka dauke Shi , nace kuna me?”. A gigice tace ” ya shigo office ne kafet ya tadiye Shi shine zai Fado Kaina nayi sauri nasa hannuna nayi masa Katanga daga fada min.”

“Karya kike yi, nace karya kike yi” ya fada da karfi cikin matukar fusata.

Da sauri mujaheeda ta runtse idanunta tasa hannu ta dafe gefen kirjinta wajen zuciyarta da taji tana Mata mugun zafi tamkar zata keto kirjinta ta fito.

Cikin sakwannin da basu wuce biyu ba mujaheeda ta yanke jiki ta Fadi. Hakanne ya dawo da Taufiq hayyacinsa da sauri ya zube kasa Yana jijjigata gami da Kiran sunanta. Nan da nan ya gigice musamman da ya ji duk jikinta babu inda yake motsi, baisan lokacin daya dau makullin mota ya jefa a aljihunsa ba sannan ya tattageta cak ya dagata ya fita da ita yana tsuma. Asibitin data Saba zuwa ya wuce da ita.

Bai Sami sukunin Kiran kowa ba har saida aka karbi Mujaheeda aka bata gado likitoci suka shiga aiki akanta, sannan ya sami numfasawar da ya daga waya ya Kira Haj Murjanatu, sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta dauka, cikin tashin hankali ya gayá mata suna asibitin da Mujaheeda ke ganin likita ciwonta ya tashi.

Tashin hankali Haj murjanatu ta rude ta shiga tambayar sa “me kayi ma yata ? Me kayi ma Mujaheeda?” Yayi shuru Yana Jin yadda take huci awayar.

Ta cigaba da cewa” na rantse maka matukar wani abu ya sami yata sai munyi shara’a da Kai, sai Naga Wanda ya tsaya maka, sai kayi mamakin yadda Zan maida Kai abin kwatance”. Da sauri ya kashe wayar domin Jin yadda Haj murjanatu ta koma tamkar wata zararriya.

Daganan ya Kira mahaifinsa ya sanar da Shi, hakama mahaifiyarsa duk sun damu.sannan ya Kira Alh Mustapha labaran ya sanar dashi.

Cikin kankanin lokaci Haj murjanatu ta iso asibitin Dama tun kafin ta iso ta Kira Dr Balarabe ta sanar dashi Mujaheeda tana asibitin anan ya tabbatar Mata Yana daya daga cikin likitocin da suke kanta. Ko ta kan Taufiq bata bi ba tukuna tana tsaye bakin kofar da Mujaheeda take ciki, sai dai ta Kai gauro ta Kai Mari , jefi jefi Kuma tana sakar ma Taufiq harara Wanda shima ya ke tsaye a kusa da kofar dakin ko gaisuwarsa bata amsa ba.

Fitowar likitocin yayi dai dai da isowar Alh Mustapha labaran,Dr Balarabe ne ya tsaya wajen Haj murjanatu Yana yi Mata bayani, Alh Mustapha labaran ya dube Shi yace ” yanzu an Sami allurar da akayi Matan” Dr Balarabe yace ” itace ta bada wahala allurar daker aka Samo ta nera dubu sittin yanzu zaa biya sannan akalla sai anyi Mata allurar sau shida kafin ta dawo yadda ake bukata.”

Haj murjanatu tace da sauri ” ko nawa CE za’a biya ni kawai bukatata yata ta Sami lafiya” Dr Balarabe yace ” insha’Allah Zata Sami sauki babu damuwa, yanzu nan da minti talatin zata dawo hayyacinta insha’Allah “. Ya karasa maganar Yana wucewa zuwa office dinsa.

Gaba daya Haj murjanatu da Àlh Mustapha labaran suka shige cikin dakin domin ganin mujaheeda. Shima Taufiq din da sauri ya bi bayansu amma Yana shigowa Haj murjanatu ta juyo a fusace cikin daga murya tace ” fita Ka Bani waje, bana bukatar ganinka kusa da yata ” Alh Mustapha labaran ya dubeta cikin mamaki yace” wace irin magana ce wannan bakya bukatar ganinsa kusa da mujaheeda don me? Mijinta ne fa.”

‘Mijin ta din me, mutumin da yake kokarin kashe min ya” Alh Mustapha labaran yace ” ya kike irin wannan maganar ta yaya Taufiq zai kashe mujaheeda amatsayin sa na mijinta, ko kuwa ciwon mujaheeda bazai iya tashi hakanan ba daga Allah har sai Taufiq ya Zama sila”. Zata yi magana kenan Alh Yusuf lamido da Haj saratu suka shigo dakin da yake tun kafin zuwansu Taufiq ya gayá musu dakin da Mujaheeda take.

Nan da nan Alh Mustapha labaran ya shiga kokarin boye maganar da suke yi ta hanyar yi musu sannu da zuwa, amma ina Haj murjanatu fada ta cigaba da shi” ina da yakinin shine dalilin tashin ciwon mujaheeda domin tunda ta aure Shi kullum cikin bata mata rai yake, saboda tsabar mugunta yafi kowa sanin Mujaheeda bata bukatar bacin rai amma tunda ta fara aikin nan kullum idan bai bata Mata rai ba baya sukuni”. Haj saratu tace ” haba Haj ya kike irin wannan maganar , Kuma a irin wannan lokacin da bai kamata ba.”

Ta dubeta sosai tace ” koma dai menene bazan fasa fada ba wannan karon duk abinda ya ami yata bazan taba yarda ba sai munyi shara’a da Taufiq”. Anan ne Taufiq ya Kai matuka gurin hasala a fusace ya bude baki zaiyi magana Alh Yusuf lamido yayi saurin daga masa hannu yace,

“Kada kayi magana.” Hakan yasa ya hadiye abinda yayi nufin fada ya juya ya fice daga dakin cikin matukar takaici.

Alh Yusuf lamido yace ” don Allah ayi hakuri abar maganar har Allah yaba Mujaheeda lafiya Muji komai daga bakinta, idan har Taufiq ne ya janyo faruwar wannan al’amarin ni Kaina zan hukunta shi, amma yanzu dai Samun lafiyarta shine abin nema.” Haj Murjanatu zatayi magana kenan Alh Mustapha labaran ya dubeta yace ” na hadaki da girman Allah ki yi hakuri ki bar maganar nan.”

Ta jinjina Kai cike da fushi ta zauna kusa da yarta tana shafa ta, hawaye ya fara fita mata ahankali take fadin ” Allah ya baki lafiya, wannan ciwo yana wahalar da ke inda zan bada duk abinda na mallaka ki warke daga wannan cutar hakika dana bayar, bani da wata damuwa aduniya sama da wannan ciwon naki, bana son bacin ranki bana son damuwarki saboda sune sanadin tashin ciwonki. Amma kin sami miji mara Imani Wanda Bai damu da ke ba ke kadai kike sonsa.”

Irin wannan maganganun Haj saratu ba zata iya jurar su ba kuma bata son su raba abin fada a asibiti hakan yasa ta dubi Mujaheeda da har yanzu tana kwance kamar matacciya tace ” Allah ya baki lafiya” tana Gama fadan hakan ta juya ta fita tana cema Alh Yusuf lamido ” ina wajen mota Alh” kafin ya sami karfin guiwar tsayar da ita tuni harta fita.

Shine yadan tsaya ya kara dubata sannan yayi musu sallama ya fita ba tare da Haj Murjanatu ta ko kalleshi ba balle ta amsa sallamar da yayi Mata. Alh Mustapha labaran ne ya bi bayansa , suna fita ya shiga bashi hakuri yace ” kasan halin ta bata raina abin magana ga zargi na banza da wofi.” Àlh Yusuf lamido yace ” babu komai kada kadamu, Allah dai ya bata lafiya” yace “amin, Allah ya kiyaye hanya an gode” daga nan sukayi sallama ya koma cikin dakin, shi kuma ya nufi wajen motarsa.

Tsaye bakin motar ya tadda Taufiq da Haj saratu da alama magana suke yi, yayi masa kallon tsaf tacee” Kai Taufiq ya akayi ciwon Mujaheeda ya tashi meya faru ko kuwa dai hakanan ciwon ya tashi.”

Taufiq yayi shuru yana jinjina maganar da zai fada, Alh Yusuf lamido ya daka masa tsawa yace ” dakai nake magana ko baka jina ne?”.

Haj saratu tace ” haba Alh meye na wannan tsawar, Kabi komai a hankali mana” ya dubeta rai a bace yace ” Anki abi ahankalin, Dama ai nasan kece ke daure masa wajen zama yàke yin abinda yake so, kina kallonsa tamkar wani ma’asumi da baya laifi, Kuma wannan kuskure ne.”

Haj saratu zatayi magana yace ” Kada kice min komai ki bari wanda na tambaye shi ya bani amsa” ta hadiye maganarta rai abace ta juya ba tare da tace uffan ba. 

Àlh Yusuf lamido ya Kara kallon Taufiq cike da zargi yace ‘me kayi mata Taufiq.” Yadan gyara tsaiwarsa yace ” Abba mun Sami sabani ne da ita”. Ya aje numfashi cike da damuwa yace ” wai Kai don Allah meke damunka , shin Baka shirya zaman auren ba kayi, Kai Nama fahimci baka San meye auren ba, shin Baka son yarinyar nan Ka aure ta, kafi kowa sanin lalurarta amma ba zaka tayata samo lafiyarta ba.”

Ya kafe Shi da Ido yace ” me tayi maka?” Haj saratu tace ” tun farko tambayar da ya kamata kayi masa kenan” ya dubeshi yace ” to nayi masa yanzu.”

Taufiq yace ” Abba Zan zo gidan Zan gaya Maka komai.” Ya Bude mota ya shiga sannan ya ce, “Ina jiranka.” Haj saratu ta shiga motar tana ma danta kallon tausayi.

Da gudu ya ja motar tabbatar yana cikin fushi.

Taufiq ya runtse idonsa yana kokarin maida hawayen dake kokarin fito masa, Anya yayi Saar aure kuwa? Tunda yayi auren nan bai Sami natsuwa ba balle kwanciyar hankali, Yana son matarsa Amma dalilai da yawa na son maida soyayyar kiyayya, shin yaya zaiyi? 

Anya mahaifinsa zai fahimce shi kuwa, sannan ya zaiyi da Haj Murjanatu da take kokarin daura masa jakar tsaba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 21Nima Matarsa Ce 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×