Skip to content
Part 24 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Ya shiga duba hotunan daya bayan daya, har ya Gama kallo sannan ya dago Kansa Yana kallon Taufiq sosai, yace ” Amma banjidadi faruwar abinda ya faru ba, babu wanda ya zugaka ya kuma tilasta maka ganin laifin hotunan illa shaidan.”

Ya kara matsowa kusa dashi yana kokarin mika masa wayar yasa hannu ya karba a sanyaye.sannan Alh Mustapha labaran yace “Ta Yaya ko amanarka mujaheeda zata ci , ta rasa da wanda zata ci amanarka sai Alh Jibrin, mutumin da ya haifeta, kuma amintaccen mahaifiyarta ne, shi kansa ba zai iya cin amanar Haj ba. Kuma nayi mamakin da ka kasa gane duk wanda ya turo maka wadannan hotunan yayi ne don kawai ya shiga tsakaninka da matarka.”

Ya nisa ya cigaba da cewa “ban so faruwar hakan ba banso kayima mujaheeda magana ba ba tare da sanin ainihin gaskiya ba, Kuma Ka sani babu abinda mace ta tsana a duniya sama da mijinta ya zargeta akan abinda bata aikata ba kuma zargi a aure babu inda yake kai auran sai tafarkin rabuwa, ko kuma a daina ganin mutuncin juna.”

Taufiq ya yi kasa da kansa zuciyarsa ta fara nadamar faruwar komai, amma ya kasa cewa uffan.

Alh Mustapha labaran yace “don haka ina son kaje Ka zauna Ka natsu kayi ma duk hotunan nan kyakkyawan kallo da fahimta ananne zaka gane basu dauke da abinda kake zargi.” Taufiq ya gyada kai yace ” to Alh nagode.”

Alh Mustapha labaran ya kara kallonsa yace ” zuwa yanzu dai ina son ka tafi kabar asibitin saboda yadda Haj ta fusata ko ni bazan iya shawo kanta ba idan yaso idan ta sakko komai ya lafa zan sanar da kai da kaina kazo mu zauna duka ayi magana.”

Shi kansa Taufiq din zai fi bukatar ya sami lokacin kansa da zai zauna yayi nazari yadda ya kamata zamansa a asibitin kuwa zai iya sawa ya sami sabani da Haj murjanatu domin yadda yake da saurin fushin nan Bai Jin duk ràshin gaskiyar sa zai yarda ta ci masa kashi aka, don haka ya amince da abinda Alh Mustapha ya fada. Yayi masa sallama sannan ya juya ya tafi Shi Kuma ya Kada Kansa ya koma cikin dakin.

Har yanzu mujaheeda na rungume a jikin Haj murjanatu, da alama Kuma mujaheedan ta Gama gaya Mata duk abinda ya faru tsakaninta da Taufiq, idan yayi laakari da yadda ta Kara fusata matuka.

Alh Mustapha labaran ya dubeta yace ” don Allah ki kwantar da hankalinki ki Sami natsuwa Haj a asibiti fa Muke ki Bari mana ta Sami sauki koma me zaayi sai ayi.”

Haj murjanatu ta dubeshi da jajayen idanu tace ” wannan Karon Taufiq zai gane ya tabo ni, har ya isa ya jefi yata da Kalmar zina ni ban haifi maxinaciya ba Kuma zai yi nadamar fadin hakan” Alh Mustapha labaran ya girgiza Kai yace ” yaushe yace mata mazinaciya? Aah kadafa ki maida maganar wata iri” ta Watso masa Ido tace ” meye bambancin kana zargin matarka da zina , ai abinda yake nufi kenan Kuma ma don wukakanci da Alh jibrin kai kai gsskiya Taufiq ya ci mana mutunci ya zaluncemu.”

Àlh Mustapha labaran ya daga mata hannu yace ” naji amma don Allah ki bar maganar nan don babu amfanin yinta anan ki bari mu koma gida tukuna.”

Ya dubi mujaheeda yace ” ke Kuma ki daina wannan kukan ki yi shuru don baida amfani, Kuma ba wai warkewa kikayi ba hakan zai iya sawa ciwon ya kara tashi kin dai fi kowa sanin dalilin tashin ciwonki saboda haka ya zama dole ki kiyaye.”

Haj murjanatu tasa hannu tana goge Mata hawaye tana cewa ” ki daina zubar da hawayenki Akan Wanda bai cancanta ba , Taufiq dai dole ya sake ki don ni ban shirya rasaki ba.”

Gaban mujaheeda yayi mummunan faduwa duk da tana cikin fushi da Taufiq bata Jin zata iya rabuwa dashi domin har yanzu tana son sa fiye da tunanin me tunani.”

Subhanallah haba Haj ta yaya kike irin wannan maganar ki kashema mujaheeda aure a wane dalilin” ta ce ” adalilin kashe min ya da yake son yi da Kuma zargin banza da wofi da yake yi akanta.”

“To wannan ba ita bace mafita babu maganar saki, Zama dai zaayi ayima hanci tufka amma har yaushe akayi auran da zaace zaa rabu.”

Cikin fusata tace ” to rabuwar aure da mutum irin Taufiq har wani abin damuwa ne, shiyasa tun farko ban so auran nan ba don nasan babu abinda zata samu a auran talaka sai bakinciki da kuntatawa amma saboda kwanciyar hankalinta na yarda ta aure Shi don gudun damuwarta Amma Shi ya kasa gane alfarmar da akayi masa na auran mujaheeda to zai sani, idan ma baya hayyacinsa ne zai dawo hayyacin nasa.”

Cikin kosawa da maganar Àlh Mustapha labaran yace ” duk naji a dai bar maganar zuwa ta samu lafiya”. Ta saki tsaki gami da Kara rungume mujaheeda ji take tamkar ta cire duk wata damuwarta ta dawo da ita kanta, tana son yarta matukar so akanta zata iya yin komai.

Tun fitar Taufiq daga asibitin Yana zaune cikin motarsa ya kasa tuka motar idonsa na kafe Kan hotunan mujaheeda da Alh jibrin ya natsu ya tattara hankalinsa Kan hoton sosai yake son ya gane gaskiyar lamarin.

Kwayar idon mujaheeda acikin dukkan hotunan babu Wanda ya nuna son Alh jibrin aciki, haka zalika duk yanayin zaman daukar hoton baiyi Kama da Zama na soyayya ba.

Hatta hoton da mujaheeda ta taba jikin Àlh jibrin ya tsaya yayi masa kallon tsaf yanayin fuskarta da yanayin data nuna a tsorace take alamar abin da batayi tsammani ba yana gaf da faruwa, hakan yasa ya fara gasgata maganarta na cewa kafet ne ya tadiye shi ya kusa fadowa kanta cikin ràshin sani .

Nan da nan zuciyarsa ta fara gaya masa anya baiyi garaje ba , Anya baiyi saurin yanke hukunci ba. 

Ya Fara ji aransa tamkar yayi kuskuren Kara zargin matarsa, wai meke faruwa ne? Zaman kwanciyar hankali da jindadi yasa ran yi da mujaheeda shin meyasa sabanin hakan ke kasancewa?. Kiran mahaifinsa daya shigo wayarsa ya katse masa komai da sauri ya dauka daga yanayin maganar Àlh Yusuf lamido Kadai Taufiq ya gamsu da cewa baya bukatar wata doguwar gaisuwa ko magana , ce masa kawai yayi Yana nemansa yanzun nan, Taufiq ya tabbatar masa gashi nan zuwa.

Daker ya iya tada motar, cikin matukar damuwa ya yima gidansu tsinke tare da adduar Allah yasa ba wata damuwar bace.

******

Bayan isarsa gidan zaune ya tadda Alh Yusuf lamido acikin falonsa , rike da karamin kur’ani Yana karantawa 

Hakan yasa Taufiq ya dade da Zama a falon har Haj saratu itama ta shigo , bai Gama karatun ba sai daga bisani sannan ya rufe kur’anin ya Mika Shi inda yake ajewa.

Sannan ne ya dawo da kallonsa ga Taufiq gami da gyara zaman gilas din dake idonsa.

“Gani Abba” cewar Taufiq, Alh Yusuf lamido yace ” surukarka ta Kira mahaifiyarka da kakkausan lafazi tayi magangsnun data Saba yi marasa dadi Wanda basai na gaya maka ba, Amma dai duk da haka na fahimtar da mahaifiyarka cewa Dan kuka Shi ke jama uwarsa jifa, don haka duk irin maganganun da ta gaya mata Kaine ka ja Mata.”

Kasa kawai yayi da Kansa, ayayinda Haj saratu ta dube Shi sosai tace ” Taufiq ina ce mun gama wannan maganar me kuma ya dawo da ita?”

Alh Yusuf lamido ya Kara cewa ” kana Jin tambayar da tayi maka “. Taufiq ya numfasa yace ” na gamsu da duk abinda kika gaya min hakan ne yasa Muka Sami daidaito a tsakaninmu komai ya wuce , to bayan hakane sai Kuma aka turo min wasu hotuna”. Sannu ahankali ya gayá musu komai sannan ya fito da hotunan ya Mika ma mahaifiyarsa wayar bayan ta Gama kallo ne ta Mikama Alh Yusuf lamido shima ya amsa Yana kallo.

Alh Yusuf lamido ya dade Yana kallon hotunan Yana nazari kafin daga bisani ya Mika masa wayarsa, Yana yi masa wani sakaran kallo sannan yace ” idan baka iya kama barawo ba to lalle barawo zai kamaka , an gaya maka aure wasa ne, don me zaka dinga zargin matarka wai kai dakatama dama yarinyar nan baka sonta ka aureta?”

Haj saratu tace cikin damuwa ” ni dai na fara damuwa da lamarin nan, tun da akayi auren nan babu wani kwanciyar hankali sai kace ba auren soyayya ba , na rasa inda matsalar take” Alh Yusuf lamido ya nuna Taufiq yace ” matsala tana wajen danki, matukar ba zaisa hakuri acikin zaman aurensa ba ba kuma zai daina saurin fushi da saurin yanke hukunci ba to fa bazai taba zama lafiya agidan sa ba.”

Kasan illar da zargi yakema aure kuwa, Kuma Kai zaka bada shaidar kamewar mujaheeda ba sai ka Jira wani ya baka ba, Kuma Shi Wanda ya turo maka hotunan kasan shine?”

Ya girgiza kai alamar a’ah, ya girgiza kai yace “kaji shashanci, ko wannan ya isheka shaida, idan har gaskiya yake fada me yasa zai boye kansa, ya bayyana kansa mana ya gayá maka, to duk wanda ya turo maka burinsa ya rabaka da matarka kuma ina ganin burin nasa ya kusa cika.”

Da sauri Taufiq ya dago ya dubi mahaifinsa kamar yadda Haj saratu ta dube Shi tace ” burinsa ya kusa cika Kuma” yace “kwarai kuwa, domin mujaheeda yata ce farincikinta da kwanciyar hankalinta shine kan gaba ko tana da lafiya bazan lamunci wannan wulakancin ba balle bata da lafiya ko tausayi baka da shi don haka gara tun wuri idan baka sonta ne ko kuma zargin da kake mata yayi kamari yadda bazai iya barin ranka ba to gara ka sallameta Allah ya hadata da wanda ke Sonta tsakani da Allah.”

Nanne Taufiq yace agaggauce ” Abba ina son matata bana jin kuma akwai abinda zata yi min da zan iya rabuwa da ita” ya girgiza kai yace “to idan hakane me yasa kake kokarin bata dangantakarku Ko kana tsammanin mujaheeda zata taba mantawa da wannan batancin haba Taufiq Ka dinga sama kanka hakuri da juriya kaifa namiji ne akwai gwagwarmaya sosai agabanka ya kamata kayi tunani ka tsaya Ka zama namiji wanda zaa dinga kwatance dashi na alheri bana sharri ba.”

Haj saratu tace ” gaskiya ne Taufiq yakamata ace zuwa yanzu babu wannan maganar ka rungumi matarka Ku zauna lafiya wannan cece kuce duk abarshi kafi kowa sanin Haj murjanatu da irin yadda take daukar zafi idan har abu ya hado da mujaheeda don haka ya zama dole matukar kana son cigaba da zama da mujaheeda ka koyi yadda ake hakuri da sadaukarwa.” 

Alh Yusuf lamido yace ” kadama ya koya ranar daya rasata ai ya gane muhimmancin abinda ya rasa.”

Cikin damuwa da nadama Taufiq yace ” nasan nayi kuskure don Allah Abba kuyi hakuri insha’Allah hakan ba zai Kara faruwa ba” Alh Yusuf lamido yace ” bamu zaka ba hakuri ba kaje kaba wacce ka batama hakuri.”

Haj saratu tace ” babu komai Allah ya daidaita tsakaninsu ya Kuma bata lafiya, wannan Kuma ya Zama na karshe duk abinda wani zai turo maka baka da hujjar zargin matarka har sai kagani da idonka don Sharia sabanin hankali ce” yace ” insha’Allah Zan kiyaye” Shi dai Alh Yusuf lamido Bai Kara tankawa ba illama rai da ya Kara hadawa ya dau wayarsa ya fita harkarsu.

Hakan yasa Taufiq yayi sallama dasu jikinsa babu laka ya tafi.

Kullum Taufiq sai yaje asibiti Amma babu wani sassauci tun daga Kan mujaheeda har mahaifiyarta domin dai mujaheeda ko magana taki masa, balle Haj murjanatu da kullum fada. Ke tsakaninta da Shi. Hatta su Alh Yusuf lamido idan suka je dubata babu wani sakin fuskar da suke Samu daga gareta asalima ko kallon kirki bata yi musu.

A cikin haka ne aka sallameta kai tsaye gida Haj murjanatu ta wuce da yarta ba tarema da Taufiq din yasan an sallameta ba. Sai da ya je asibitin ya tadda an sallameta ta.

To meye tunanin Haj murjanatu na tafiya da mujaheeda gidà ba ta maidata gidan mijinta ba? Ya Ciro waya ya Kira Alh Mustapha labaran bayan sun gaisa ne ya gayá masa ya zo asibiti ya tadda an sallami mujaheeda Amma kuma ba gidansa aka kaita ba.

Alh Mustapha labaran yace ” Kada Ka damu Haj ta wuce da ita gida koma menene kada kazo gidan har saina kiraka”. Gaban Taufiq ya Fadi asanyaye yace ” to shikenan.”

Yayi kasa da wayar cikin matukar damuwa da tunani yana son matarsa babu kuma Wanda ya isa ya raba shi da ita.

<< Nima Matarsa Ce 23Nima Matarsa Ce 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.