Mujaheeda na kwance asaman doguwar kujera cikin kwalliya ta alfarma Kai Ka dauka wani waje zata,sai tashin kamshi take na musamman, karfe takwas da minti daya ne na dare,tana rike da wayarta iPhone 14 Ga iPhone 13 can asaman tebur gefenta Ga daya wayarta nan Samsung s22 ultra.
Hadimanta guda biyu lami da lauratu suna ta aikin Kai kawo akan bukatunta duk sun cika gabanta da abubuwan ciye ciye masu saukin ci marasa nauyi Wanda suka dace aci da daddare.Babu Wanda take kallo acikinsu idonta na Kan waya tana aikin danne danne babu abinda ya dameta.Har. . .