Skip to content
Part 11 of 11 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

Cikin gida Hajjah ta shiga da ita tana mai jin kamar itama kukan zata yi, amma ta samu sukuni yanzu da ta ganta cikin k’oshin lafiya. Suna shiga Abba ya isa ga Musab dake k’ok’arin shiga motar shi don ya wuce gida, gefenshi Farhan ne da Burhaan da ya d’aure fuska tamau ko sallamar da yayi masa bai amsa ba Farhan ne ya amsa har da masa godiya.

Kallonsu yayi da kyau yace ” mun gode fa bawan Allah, Allah ya saka da alkhairi aina ka sameta? ” murmushi yayi yana cewa ” Babu komai ai Alhaji, a nan gaban sabon wuse Allah dai ya sake tsarewa amma ta auna arziki” cewa yayi ” Ameen dai, we really appreciate your efforts and da buk’atar mu ganka da kyau I can see yanzu kana sauri ga dare kuma”.

Cewa yayi ” haba dai, ai yiwa kaine “. Gyad’a kai yayi cikeda yabawa da d’abiun shi yace ” tabbas yiwa kai ne amma dai zamu ganka we need to appreciate you more, let me have your digits here”. Ya k’arashe yana mik’a mai wayarsa, amsa yayi ya rubuta masa number yace ” name?” ya buk’ata.

A hankali yace ” Arc. Musab Siraj Bawa”. Murmushi yayi yana cewa ” Masha Allah, Allah yayi maka albarka mun fa gode”. Shima Farhan hannu ya sake mik’a masa yana cewa ” mun gode Arc. Allah ya tsare hanya”. Ameen yace ya shiga cikin motarshi, sai da ya bar gidan kafin Abba ya kalli Islaam k’wafa yayi bai ce masa uffan ba ya nufi cikin gidan Farhan ma goya masa baya yayi suka k’yaleshi tsaye kamar tsinkakken silifas, kamar ya wuce gida sai ya tuna rikicin Abba hakan yasa ya biyo bayansu yana b’ata fuska.

A zaune ya taddasu sun zagaye Hajjah dake rungume da Lelen, bai zauna ba ya dai coge a jikin garu jin Abba na cewa. ” A samu tayi wanka, ta sha ko tea ne ta kwanta ta huta kar a matsa mata da wata magana har sai ta dawo jikinta”. Toh Suliem ta furta tana k’ok’arin kamata da niyyar kaita ciki don cika umarnin Abba, sai cewa tayi ” Abba na san yanzu ba lokacin da ya kamata ayi magana bane amma ina son in shaida maka da cewa Ya Islaam baida laifi ko kad’an, duk wani k’ok’ari yayi don yaga mun dawo tare amma ni nak’i baida zab’i sai na k’yale ni so in akwai wanda za ai wa hunkuci toh ni ce ba shi ba”.

Kallonta yayi cikeda jin haushin kalaman da ta fad’i, yayinda takaicinta ya kamashi ainun. Kamar ya shak’eta a wurin yake ji, he hates playing victim that’s why yakeda bak’in tambari. Ko yana da gaskiya bai tsayawa explaining kanshi balle yayi seeking for justice, in aka ce yayi abu zama yake akan haka ya shanye duk wani fad’a da tsangwama da zai biyo baya.

One thing about him is bai k’arya and ya tsane mai yi, wannan maganar da tayi ganinshi yayi a babbar laifi and it makes him hates her more. Abba ne yace ” ban tambayeki waye mai laifi ko mara laifi ba, cewa nayi kije kiyi wanka ki kwanta”.

Kanta a k’asa tace ” kayi hak’uri….” Ya katseta da wata tsawar da ta tsoratata yana cewa ” kika sake wata magana a nan sai na sab’a miki Nadeefah!!” ai da sauri suka wuce ciki ita da Suliem kamar zasu kifa, kallon mutanen parlorn yayi ya ci gaba da cewa ” zaku iya tafiya ku kwanta”. Ya k’arashe da mik’ewa tsaye, Umma ma mik’ewa tayi haka kusan kowa dake parlorn.

Gaban Hajjah ya k’arasa yana cewa ” zamu shige mu kwanta kema ki je ki kwanta Allah ya k’ara kiyayewa”. Cewa tayi ” Ameen ya rabbi Abdoulaye Allah yayi maku albarka “. Ameen yace yana nufar k’ofa bai ko amsa sai da safen da ake yi masa, Farhan ne ya ajiye wayarta a kan handbag d’inta dake gefen Hajjah shima ya nufi k’ofa haka sauran kowa ya nufi gida bayan sun wa Hajjah sallama.

Motar Burhaan Safwaan yabi zuwa gida don wacce ya tuk’o a zuwa Abba da kanshi ya tuk’a abinshi zuwa gida, kusan a tare suka shiga gidan su da Umma part d’inshi suka shige suma suka wuce nasu.

Suna shiga zama yayi yana amsa kiran Baba Tijjani da bai k’asar, shaida masa yayi da ta dawo da kuma hukuncin da ya yanke na kar a tada maganar a yanzu sai ta dawo hayyacinta. Ya goyawa shawarar shi baya, inda ya bashi tabbacin dawowarshi a sati mai kamawa sallama sukayi da juna ya ajiye wayar yana sauke numfashi.

Zama tayi a gefenshi tana cewa ” Abun dai babu dad’i wallahi, anya ba hak’ura za muyi ba Zauj?”. D’ago kanshi yana mata kallon tsaf irin kar ta kawo wargin nan yace ” dame zaa hak’ura?”. Murmushi tayi ganin kallon da yayi mata tace ” da had’in mana tunda kaga sun kasa fahimtar juna sun kasa jure tafiya tare daga Abuja zuwa Kaduna ina ga in aka had’a su gida d’aya?”.

Cewa yayi ” babu abinda zai hana had’in nan na fad’a yafi sau ba adadi, in ma ke kike zugashi toh tun wuri ki janye cos i won’t it lightly with you guys. In akayi auren su kashe juna karshen k’iyayya”. Daga haka ya wuce zuwa bedroom d’inshi dake nuni da ya gama magana, da mamaki ta bishi da idanu wai ita yake cewa tana zuga Islaam ita da ba wanda ya kaita murna da had’in nan. Amma kuma idan zai kawo matsala barinshi yafi yinshi alkhairi, but yanzu kam nata idanu da adduar Allah ya kad’e fitina amma ba za a k’ara jin yawunta a kan maganar ba.

Koda tayi wanka sai da ta jero salloli daga Asr zuwa Isha’i ta bisu da shafa’i da wutri, tean kawai ta iya sha shima ba da yawa ba ta kwanta a tsakiyan Zulfaa da Suliem bata jima ba bacci ya saceta.

Washegari bata fita koina ba bacci ta kwanta tayi, sai to 1 Dr. da Abba ya turo ya dubata da kyau kafin ya wuce. Sai lokacin ta samu zarafin amsa kiran Ummu da tayi ta mata fad’a akan k’in d’aga kiranta, ita dai hak’uri ta bada don ta fahimci labarin bai isar musu ba kenan sai ma wani hirar da ta kamo.

Suna gama wayar sai ga kiran Nana da ta kira ta jajanta akan abinda ya faru jiyan, da yake su Suliem sun kirata a tunaninsu ko gidansu ta wuce don fara mata gyaran. Hakan ne yasa ta sani, godiya tayi mata inda ta shaida mata da nan da kwana biyu zasu fara in shaa Allah sallama sukayi ta ajiye wayar tana sauke numfashi cikeda gajiya.

Hajjah dai kallonta takeyi cike da tausayi, duk da bata tanka ba don bata son ta cika tofa magana kan Burhaan amma jikinta yana bata kamar shine jarabawar Nadeefah ko dai ya zama alkhairi gareta ko akasin haka. Da tana da dama da ta hana wannan lamari amma kuma idan akwai rabo a tsakanin su fa? Tana da hanyar hana wannan yiwuwa? Hakan ne yasa take bin komai saffa-saffa ta gefe take binsu da adduar tabbatar alkhairi tsakaninsu.

Da yamma duk wanda ya dawo daga aiki sai ya shigo ya dubata, da yake sanda suka shigo da safe tana bacci. Abba da Daddy har da kayan dubiya haka Farhan da Safwaan, sai dai babu ko inuwar Islaam har tsawon kwanakin da tayi a gida.

Kwananta 3 da dawowa sai ga Musab wai ya dawo dubata, har parlor ya shiga suka gaisa da hajjah tayi ta surfa masa godiyar da sai da ta sanya shi jin kunya yana ta cewa babu komai. Tashi tayi ta nufi ciki sake gaisawa sukayi da juna inda take tambayarshi madam, dariya yayi yana cewa ” babu wata madam fa, ranar ma Mama ce ke ta kira ta ga dare yayi ga yanayin hanyar” murmushi tayi tace ” ayyah, ai ranar na shiga fargaba ainun Allah dai ya sake tsarewa”. Ameen ya furta yana k’ureta da idanu ashe ranar kallon tsoro ya mata, ko don itama a tsorace take? A k’asan ranshi ya furta ” she’s a damsel”.

Shiru tayi kanta a k’asa hakanan taji ta uncomfortable, ba kuma komai yaja ba face Hazel eyes d’inshi masu wani kallo mai saukar da kasala ga jiki da ruhi.

Sallamar su ne ya katse musu yanayin da suke ciki, PT Adnan ne da Burhaan da ya tursasa wa zuwa bayan ya gama masifar abinda ya aikata. Bai tanka masa ba ya dai biyo shi zuwa gidan hajjahn don ya gujewa mitarsa.

D’an turus Adnan yayi sai kuma ya washe baki yana cewa ” a’a Amaryarmu kice kin warware ma, da fatan dai bamuyi latti ba”. Murmushi tayi tana cewa ” aa bakuyi ba amma kun kusa yi” zama yayi yana mai cewa ” ayi mana afuwa kawunanmu bisa wuyoyinmu”. Waigawa yayi gefenshi da Musab yake zaune yace ” My boss how far”. Gaisawa sukayi kamar kafin ya waiga ga Islaam dake tsaye a tsakiyar parlorn yace ” Ango ka tsaya daga baya, ko sai anzo an d’aukeka ne “.

Tab’e baki yayi yana k’arasowa inda suke, kamar almara ya nemi waje a gefen kujerar Nadeefah ya zauna yana cewa ” Ya jikin naki”. She was shocked by what he just did! Yau Burhaan ne yake mata magana da tone mai taushi? Lallai ma. Cewa tayi ” Alhamdulillahi amm this is Musab wanda ya dawo dani gida”.

“Ahhh Boss mun gode fa Allah ya saka” Adnan ya fad’i don ya san in zaa mutu abokin nashi ba zai ce uffan ba, sai kuma ga mamakinsu biyun suka tsinkayeshi yana cewa ” ooh Masha Allah an gode ai”. Murmushi yayi kawai yana cewa ” haba ai it’s nothing much” cewa tayi ” it is more than that, you rescued me a tsakiyar daji baka sanni ba baka tab’a ganina ba ai no words in the world is enough to express our outmost gratitude”.

Adnan yace ” indeed we are truly grateful for that, Allah ya saka da khair” tace ” Ameen ya rabbi, well Musab meet PT Burhaan Abdullah Yerwa my fiancé”. Jin maganar yayi ta doke shi a tsakiyar k’irji, he’s not expecting that saboda rai da zuciyarshi suna da k’uduri mai girma a kanta. Runtse idanu yayi ya bud’e idanu a kansu yace ” Masha Allah, you two will make a perfect couple may Allah bless the union”. Adnan ne kawai yace Ameen while ita ta furta a k’asan ranta, shi ko gogan is busy studying him. In ya cinka dai-dai the guy is in love with her amma kuma ya makaro inda da ne da sai ya san yanda akayi ya aureta, but now ba zai tab’a yarda ta zauna da wanda yake sonta ba.

Tunda ta sa aka tursasashi auren wacce bai so wato ita, to the price she’ll pay is life-long punishment ta hanyar zama da wanda bai sonta. And akwai buk’atar ya saita ta zuwa hayyacinta, don ya lura da cewa she’s not in her right senses. Tashi tayi tana cewa ” bari in kira Hajjah ku gaisa”.

Adnan da sauri yace ” please do so Allah ya sa akwai danderu” dariya kawai tay, sai da ta fara biyawa kitchen tayiwa Yana magana akan ta kawo musu abun motsa baki kamar yadda aka cika gaban Musab. Dukda bai tab’a komai ba sai ruwa, kafin ta shige wurin Hajjahn. Sallama tayi ta sameta zaune akan rug ta mik’e k’afafunta, shaida mata zuwansu tayi kafin ta m’ike suka jero izuwa parlorn tare.

Suna shigowa yana mik’ewa tsaye don ji yayi parlorn is suffocating him, iskar d’aci take masa yace ” toh Nadeefah mai turare Hajjah  mu zamu tafi, dama daga office nake shine nace bari in tsaya mu gaisa”. Bata zauna ba tayi murmushi tana cewa ” amma ko na gode da ziyara, a gaida Mama” Hajjah tace ” mun gode sosai Allah yayi albarka” ameen ya furta kafin ya juya kansu Burhaan.

Sallama yayi musu sannan ya fita binshi tayi a baya ta barsu suna gaisawa da Hajjah, har mota ta rakashi tana sake masa godiya sai da ya ja motar kafin ta koma. A tsaye ta samusu da alamu wucewa zasuyi, Adnan yace ” yawwa toh muma bari mu rankaya zuwa gida ” tace ” toh Masha Allah, nagode sosai, a gaida Uom Naim ” zataji kawai yace yana nufar k’ofa, bata ko kalli side d’inda yake ba ta wuce ciki gefen da Hajjah take zaune.

A bakin motocinsu suka tsaya suna fuskantar juna cewa yayi ” ka fara ja yarinyar nan tana shirin rainaka, in haka ta faru kuma I’m sorry to say but ba zata dinga ganin girmanka ba ko da a gidanka ne”. Tab’e baki yayi yana cewa ” raini kalma ce wacce ba zata tab’a wanzuwa a tsakaninmu ba, can’t you see that she’s scared of me?”. Kallon shi yakeyi yana imagining halayen abokin na shi, mutum har mutum amma hali a bau’de yanzu wani riba zai ci idan matar da zai aura is scared of him tun a yanzu?.

Yace ” hear yourself well, scared you said which is way different from respect. Yarinyar nan bata da matsala, in ka bita ta lalama ina mai tabbatar maka da your home will be one of the perfect home she’ll be your NISFU DEEN but in kace yanda kake mualamarta a yanzu haka zakayi a gidan aurenku then what you never expected will happen and in a way that you will be regretting….”

“I won’t regret anything Malam,,,, she’s the one that’ll yanzu zaka wuce ne ko in tafi in barka a nan ” ya karashe furkarshi a cunkushe, cewa yayi ” kaga tafiyata in zauna in mata mene, salan ka huce haushin kishin Musabu a kaina?” Ya fad’a motarshi yana dariyar shak’iyanci, girgiza kai yayi ya shige tashi yaja zuwa gida.

Washe gari 10am ta bar gida zuwa office, zuwan bazata tayi musu but she’s impressed with abinda ta gani. Kowa aikinshi yakeyi kamar yadda ya saba in tana nan, kai har ma da wanda basu saba yi ba saboda bata nan balle ta d’auke wasu musamman. Yau d’in ma bata yi aiki ba iyaka gyaran Nana da sai da ta dawo farko don wanda akai matan bai mata yadda take so ba.

A nan office d’inta dake d’auke da luxury room ta shigar da ita, ruwa mai zafi da aka zuba sinadarai masu gyara fata kafin ta sa ta shiga ciki wani mixture tayi scrubing mata a face sai ta fita ta bar mata toilet d’in. For like 30 mins ta dawo da yaranta, face d’in aka fara wankewa sawa tayi ta fito daga bath d’in.

Fita sukayi ta fito tana d’aura wani shawl black sabo fil, zama tayi a inda ta nuna mata kafin ta fita. Dawowa sukayi aka fara main business, dilka ne original mai k’amshi had’i na musamman suka shafeta da shi suka mik’a mata ta shafa a cikin jikinta meanwhile ta had’a rushi ta zuba turare a ciki zama tayi a kujeran tsuguno ta lullub’a mata wani shawl mai girma don turaren ya shiga jikinta da kyau shima ta d’auki time sosai. Haka dai suka wuni daga wannan sai wannan, zuwa yamma har ta fara canjawa alamun gyaran zai amshi jikinta 5 drivernta yazo ta wuce gida itama ta ja motarta zuwa gida.

Kwananta biyu da komawa bakin aiki Baba Tijjani ya dawo, ko hutawa bai yi ba yayiwa gidan Hajjah tsinke lokacin ma tana office. Kiranta yayi a waya ita da Burhaan da sauran manyan familyn, a tsorace ta taso ta bar PAn ta da Nana ta wuto gidan.

Kusan tare suka iso da shi, bai kalleta ba ya wuce gaba bin shi a baya tayi tana jin bugun zuciyarta yana d’ad’uwa just by seeing him ga kuma na abinda zasu tarar a ciki. Shi da Abba ne a zaune, sai Daddy Adam da Baba senator da yake yana gari sai Hajjah da Yamara ita Ya Madari taje Yerwa an yi rasuwa. Zama tayi a k’asa gabansu Hajjah tana gaishesu, da kulawa suka amsa shima gaishesu yayi suka amsa.

Kallonsu Baba yayi yana cewa “ba lallai ya zama abu da yake buk’atar sai an zauna ba gareku but garemu da buk’atar hakan, tunda magana ake na ran d’aya daga cikin y’ay’ayenmu mafi soyuwa garemu. Amma ba wata magana bace mai tsayi infact tambaya ce guda, meya faru daga Abuja zuwa Kaduna ?”.

Duk dakewarshi sai da tambayar ta razana shi, bai yi tunanin maganar zata yi girman da har zaa tara mata mutane har haka ba. Shi fa ganin ma ba a tada ta ba ya sa shi tunanin ko an barta ne, sai dai kasancewarshi gwani bai nuna girgizarshi a fili ba hasalima d’ukar da kan shi yayi kamar ba dashi ake maganar ba.

“Ba daku ake magana ba?!” Abba ya buk’ata yana d’an d’aga murya, hannu Baba ya d’aga masa don yana son abi komai a sannu. Dukda yafi Abban zafi da masifa, amma ya fishi fahimta da bi da mutum ta yadda yazo masa yana cewa ” ka bisu a hankali zasuyi magana tabbas”.

Yawu ta had’iye tana cewa ” Ammm…..” katseta yayi da cewa ” kul kika yi magana a nan Lele, don na tabbatar ba GASKIYAR LAMARI ( Aunty Nazeefah Nashe) zaki fad’i ba “.

Baba yace ” Haba Abdu ka bari tayi magana mana” cewa yayi ” Yaya ina da dalilin fad’in haka saboda in da gaskiya zata fad’i me yasa shi bai yi magana ba sai ita?”. Yace ” shima zai yi maganar amma now let’s hear from her ina jinki Lele”. Ta duk’ar da kai daga kallon tuhumar da Hajjah take mata tace ” duk abinda ya faru ranar laifi nane, saboda har ga Allah banyi niyyar biyoshi ba bani da yadda na iyane yasa na shiga motar shine da muka bar gida nace ya saukeni zan dawo da kaina. Kuma bai so saukenin ba amma na tursasa masa, har threatening nashi nayi akan in bai saukeni ba zan dira haka ne ma ya sa ya ajiyeni “.

Duk ido suka zuba mata har dashi cikeda mamaki baba yace ” meyasa?”. A tsorace ta kalleshi tace ” da flight naso bi, don ni ban son tafiya dashi ” Abba ya karb’e da cewa ” yana miki wani abune da baki so?”. Girgiza kai tayi tana mai jin inama tana da hali ta fad’i amma ba zata iya ba, shiko kallonta yakeyi a ranshi yana adduar kar ta fad’i maganar da can lead to fasa aurensu cewa tayi ” ko d’aya ni ce ma nake masa, amma bayan abinda ya faru nayi alk’awarin na daina bazan kuma ba in shaa Allah “.

Kallon tsaf Abba ya tsaya yana mata he doesn’t believe her, kai ta ina ma zai yarda da ita bayan yafi kowa sanin waye Burhaan his own instinct is telling him that something is fishy but he can’t point a finger to it. Yace ” me ya kaiki sabon wuse?”. Da sauri ta d’ago tana kallonshi don ita bama ta san inda ya ajiyeta ba, tafi tunanin Jere ne ganin akwai d’an daji a wuri. Yoh ita bama ta san sabon wusen ba sai yau tace ” amm motar da muka hau ne daga Kaduna road ta lalace a hanya, shine sai akayi juye. Da yake wacce aka juye mawa ta cika sai nace ni bari in koma gida sai the following day in bi flight shine sai ga Musab ya d’aukoni………(nan ta basu labarin abinda ya faru har k’arshe)”.

Yanzu kam Yamara ce tace ” meyasa toh kika hau motar wanda baki sani ba, Idan shi mugu ne fa? Ita wayarki me ya faru da ba zaki kira ba?”. Miyau ta had’iye ta sake yanko wani k’aryar ” Yayan k’awatace na sanshi, kuma na bar wayata a motar Ya Islaam shiyasa ban kira gida ba”.

Nan baba yace ” meyasa kika aikata hakan kin san ko me kika aikata ” Abba yace ” ko d’aya bata da laifi Yaya ga mai laifi nan, inda bai sauketa ba da duk haka bata faru ba” sai yanzu Daddy yayi magana ” exactly my take, ko k’arfin shi tafi da ba zai tursasata sai ta zauna ba in yaso yayi locking motar tayita haukar da taga dama har zuwa kaduna”. Daddy senator yayi murmushi yace ” don rashin kyautawa dukansu ne basu kyauta ba, amma ita da take maganar ba tason su kasance guri guda kun manta aure ake shirin d’aurawa in less than 2 months?, in an musu auren ya zasuyi?”.

Baba yace ” su kwad’a juna su cinye damuwarsu ce,,,,,,,,amma a yanzu na kuma jin makamancin haka ya faru sai na d’auki matakin da dukanku ba zaku so shi ba don na lura so kuke ku watsa mana k’asa a idanu toh baku isa ba, ba ma ku ba babu wani d’a a familyn nan da ya isa”. Abba ma yace ” ai ni so nayi k’arshen sati a d’aura musu aure k’arshen rashin son zama guri d’aya, kuma shi ya bad’a k’ofa fa ni ban ma yarda ba Allah yasa ba shi ya sauketan a Kaduna road d’in ba take rufa mai asiri”.

Yamara tace ” zai aika nima fa ban yarda da ita ba, tunda aka fara maganar yayi shiru sai itace suda tana magana zai-zai ita ga y’ar jarida” Hajjah tace ” ai in ma ta kareshi ba laifi bane ai mijinta ne ba na kowa ba.”

Nan suka rufe su da fad’a ta inda suke shiga ba tanan suke fita ba wannan na ajiyewa wancan zai d’auka musamman ma su Baba Abba da Yamara.

Saida suka gama kuma aka d’aura da nasiha mai ratsa jiki kafin aka sallamesu. Wucewa ciki tayi shima yayi waje bayan yace musu a tashi lafiya, tunda ya zauna bayan gaisuwa sai wannan ne kad’ai maganar da yayi a parlorn.

Yana fita tab’e baki yayi yana cewa ” shegiya, sai k’arya da karya harshe ita ga gwana dama ta fad’a musu gaskiya ta ceci kanta don wannan maganar da tayi bashi zai hanani abinda nayi niiyya ba, ni dama auren aka d’aura yanzu in fara tun yanzu so that kafin bikinsu Sadeeq sun sa na saketa don kansu”. Shiga motar yayi yana barin gidan cikeda k’unar rai.

Zama tayi a bakin gado tana lissafi a cikin ranta, ji take kamar auren ya fara fita a ranta. Amma ta san fasa shi kamar zare bugun numfashinta ne yadda bata fatan mutuwarta kusa, haka bata fatan duk abinda zai jawo fasuwar aurenta a nan kusa tama san ba abune da zai iya yiwuwa ba. Zama Hajjah tayi a gefenta tana cewa ” na fahimci cewa akwai abinda kike b’oyewa, kuma abune mai kyau idan kika koyi sirri a mu’amalarki dashi saidai kar ki shafa ma kanki kashin kaza a dangi don ki rufa masa asiri. Kar ki zama kyandir ki kashe kanki ki rayashi”.

Kallon Hajjah tayi tana cewa ” Hajjah ban b’oye komai ba duk abinda na fad’i gaskiyane, kin san shi ba gwanin yin magana bane shiyasa bai tanka ni ba ya bari na fita”. Tace ” kuma daman neman yanda zai rabu dake yakeyi ba?, a tunaninki wai zan yarda kece kika fita a motar don baki son zama kusa da shi ? Ke da baki da burinda ya wuce ganinshia kowani dak’ik’a?”. Runtse idanu tayi tana cewa ” tabbas ina son zama dashi, amma ina tsoron haka a yanzu” dafata tayi tana cewa ” kenan baki shirya rayuwar aure dashi ba kenan, indai har kin fara tsoronsa.”

Daga haka ta nufi k’ofar fita jin ana shirin kiran magrib, rik’e k’ofar tayi tana cewa ” d’amara zaki d’aura don baa karaya da wuri, kuma sa’a bata ga raggo”. Daga haka tayi ficewarta ta barta zaune cikin nannauyan tunanin da ta tafi akanshi, why is she so obsessed with him ne dame ya fi sauran maza? Amsar dai bata dashi ta kuma nema ta rasa, abu d’aya ne that’s she’s certain of shine she loves him unconditionally kuma she won’t rest har sai ta same shi that’s why she’s patiently waiting for the next two months don tabbatar da cikar mafarkinta.

<< Nisfu Deeniy 10

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×