Skip to content
Part 5 of 11 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

Da murmushi kyakkyawar dattijuwar ta tarbe ta rungume ta tsam tayi a k’irjinta cike da k’auna, kana ganinta kaga balarabiya pure blood ta d’an manyanta amma hutu da kyan jiki ya b’oye tsufan. In ka ganta zaka rantse Yayar su Nadeefah ce, ga tsananin kyau nan na gano inda suka d’auko kyau duk da dai Lelen ta so zarta ta ma a kyan ko dan sun d’auko features na Abbu kad’an ne?

“Ummu who told this spoilt girl cewa mun zo?” aka fad’a daga bayan su. A tare suka waigo wani namiji ne ya na matuk’ar kama da Sadeeq Nadeefah ta na mai tale baki a shagwab’e tace ” ba ni bane spoilt “. Ware ido yayi yace ” sai wa toh?”.

Juya idonta tayi tace ” wanda ya tsargu”, ai ko ya taho a tunzure hakan ya sa ta daka tsalle tana mai sanya ihu kamar an yankata. Da sauri d’ayan da yake fitowa daga kitchen hannun shi d’auke da plate yace ” kar ka tab’ata Malam, daga zuwanta zaka ci zalinta”

Hararar shi yayi a k’ufule yace ” toh ina ruwan ka?, Ummu ki gayawa Ɗalhat ba ruwan shi dani”. Ummu ce tace ” ya isa haka tohm, ke kuma habibti ba na hanaki yi masa rashin kunya ba?”

Kumbura baki tayi tana harararshi tace ” Ummulkhair shine fa yake ce min spoilt and i’m not ” ta k’are da murgud’a baki, cewa tayi ” thats not what i asked you , now say sorry” a hankali tace ” Im sorry brother Ɗayyib.”

Washe baki yayi yana cewa “never mind Lele, i’ve missed you “. Ya k’are yana janyota, k’in zuwa tayi ta ruga ga Ɗalhat tace ” ni wurin Yaya na zan je.” Ai ko da sauri ya biyo su, duk turjewar ta sai da ta saki nan suka sata a tsakiya. Ta tsokani wannan wancan ya tsokaneta, ganin bata ita sukeyi ba ya sa Ummu kwasan k’afarta ta koma kitchen inda take girkin dare.

Ɗayyib da Ɗalhat twins ne daga su sai Lele, Ɗayyib yana da matuk’ar tsokana ga son girma while Ɗalhat yake da sanyi ga shi bai son kwarafniya ko kad’an. Ɗayyib da Lele suna yawan yin fad’an sako musamman in an dad’e ba a had’u ba, da yawa Ɗalhat ke shigan mata fad’an in bata nan kuma sai fad’an sakon ya koma kan shi though bai wani cika biye masa ba. Nevertheless, suna matuk’ar so da k’aunar Lele ko kad’an basu son su ganta a damuwa ko yaya ne akwai shak’uwa da fahimtar juna mai girma a tsakaninsu ba k’arami ba.

Suna wurin har aka kira Magrib, tashi sukayi su suka nufi masjid ita kuma ta nufi room d’inta dake upstairs wanka tayi ta bud’e closet d’in ta. Tsirarun kaya ne a ciki tab’e baki tayi dole ma ta lallashi ko Ɗayyib ne suje ta d’ebo kayanta, wata free gown ta nemo da hijab jin ana shirin tada sallah a masallaci.

Tana kan dadduma aka bud’e d’akin Ummu ce sanye da hijab ta shigo, cewa tayi ” in kin idar ki sauka akwai sak’on Hajjah a dining ku kai mata ke da ko Ɗayyib, ku gaisheta kafin gobe mu shiga”. Gyad’a kai tayi ba tare da ta tanka ba ta cigaba da abunda takeyi, sai da ta kai ak’alla 15mins kafin ta idar da hijab d’in ta fito tana saukowa Ɗalhat na shigowa. Murmushi tayi tace ” yawwa bro, Ummu tace mukaiwa Hajjah.”

Cewa yayi ” ki dai jira Ɗayyib ya shigo ni Abbu zan d’auko a gidan Baba Tijjani”, ok ta furta ta koma ta zauna a kan kujera. Bata jima da zama ba Ɗayyib d’in ya shigo yana waya, cikeda tsokana ta d’auko buffet basket d’in da Ummu ta jera kyawawan warmers a ciki ta dire a gaban shi. Kallon basket d’in yayi cikin son k’arin bayani cewa tayi ” Hajjah za’a kai wa inji Ummu “, tab’e baki yayi ya cigaba da wayar da yakeyi.

Sai da ya kammala kafin ya tashi yana cewa ” ai sai ki taso mu tafi ko?”, cikeda daure dariyarta ta biyo shi da basket d’in a ranta tana mamakin da bai yi k’orafi ba saboda shi d’in gwani ne in dai ta wannan fannin ne. Da yake daga gidan zuwa gidan Hajjah babu nisa don ko gida biyu ne tsakani daga gidan Sen. Bunami( Bilyamin) wanda suke kira da Baba Senator, sai na Baba Modu sai gidan Hajjahn hakan yasa a k’afa suka taka. Suna tafe yana mata tsiya tana ramawa har suka k’arasa, a parlor suka tarda ta tana Iftar.

Shigowar su ya sanya ta ware idanu tace ” ‘yar gari kin barni nan ina damuwa tun d’azu baki dawo ba  ashe ke kina can gidan iyayenki har kiran ki nayi baki d’aga ba “. Fari tayi tace ” ya san ranki”, cewa tayi ” fari k’al ai zasu tafi ne ina kyakkyawan zamana”. Zama tayi a gabanta tace ” k’afata k’afarsu don bin su zanyi.”

“In kin tafi kar ki dawo don Allah ” ta k’arashe tana harararta, maida kanta tayi ga Ɗayyib tana tambayarshi hanya. Tura mata warmern tayi ta amsa cikeda farinciki tana sanya ma Ummu Sameeha albarka, duk da ba gari d’aya suke ba amma duk zuwanta garin har ta koma kullum da kwanonta daga gidan hakan yana d’aya daga d’umbin alkhairanta da suka janyo mata farin jini a dangin duk da kasancewarta bak’uwa.

Sun jima suna fira da Hajjah don basu baro gidan ba sai around 9, shiga d’aki Lele tayi sai gata da trolley da kit shak’e da kaya kamar mai shirin barin gari. Ita dai Hajjah bata tanka ta ba don tasan yanda aka fita da kayan haka zaa dawo dasu, da k’yar Ɗayyib ya tayata jan akwatin suna tafe ya na mata k’orafi ita dai bata tanka ba tunda ta samu ma ya d’auka.

A parlor suka tarda Abbun ya dawo ga su Burhaan da sauran mazan family sun cika parlorn kamar zasu tsageta, wurin Abbu ta nufa da murmushi tana danne zuciyarta dake mata kamar zata buga ta tashi daga aiki.

Gaisawa sukayi yana zaunar da ita gefenshi, gaishe da mazan tayi duk suka amsa cikin kulawa da sakin fuska banda mutumin nata da sai jifanta yake da muggan kallon da ya sanya ta tsargu har sai da tayi excusing kanta ta nufi sama jakar ta kuwa nan ta sake shi a corridor.

Wurin Ummu ta nufa ta shaida mata dawowarta tana ta narkewa kamar wata sabuwar haihuwa, biye mata tayi sai da taga ta fara lumshe idanu alamun bacci ya sanya tace mata ” bibtie je ki kwanta” tashi tayi ta sumbaci cheeks d’inta a hankali ta firta good night kafin ta wuce d’akinta. Wanka ta sakeyi ta zura nightie tayi kwanciyarta, ko ta kan wayar ta da ake ta kirantabbata bi ba don ta gaji da kujiba-kujiba ba kad’an ba.

San da ta bud’e ido da aka kira sallah da box d’in ta ta fara cin karo ta ‘yar dim light d’in d’akin, ajiyar zuciya ta sauke don ko waye ba k’aramin taimaka mata yayi ba, hamma tayi ta wuce toilet. Ko da ta idar da sallah kamar kullum azhkar tayi da tilawa kafin ta d’auko wayarta. Data ta kunna ta d’an dad’e tana replying messages kafin ta kashe datar, lokacin haske ya fito.

Parlorn Abbu ta nufa yana kishingid’e CNN news yake kallo hannunshi da casbaha, rusunawa tayi ta gaida shi cikeda girmama. Ya amsa mata cike da kulawa kana ta matsa gaban shi ta fara sabon nata wato shagwab’a, da sallama Ummu ta shigo d’akin hannunta da tray da tea cups da kettle.

Mik’ewa tayi ta tarbeta sai da ta ajiye kayan kafin ta gaishe ta, amsawa tayi cikin jin dad’I kafin tace ” me ake zantawa ne ‘ya da uba?”. Cikin kanurin ta mai sirki da turanci, don har yanzu ba wani iya yaren tayi sosai ba duk da dad’ewarta sabili da rashin zama cikinsu hakan ne ma ya sanya yaranta ba wani sosai suka iya ba har ma sun fi iya larabci. Don ma Abbu ya kanyi musu though ba sosai ba don yafi yin turanci ga kuma societyn da suka taso a ciki sai daga baya ne ma saboda yawan zama da Hajjah Lele da ElSadeeq suka iya yaren fiye da twins shi ko Hausa a school ne suke jin shi ba laifi kam ko a family ma sukan surka saboda dai ba a can garin suka taso ba and Hausa is the dominant language a north.

Amsa mata yayi da ” sirrin su ne.” Dariya tayi mai fad’i har kyakkyawar wushiryarta ya bayyana, hakan ne ma ya sanya lob’awar cheeks d’in ta tace ” ai ni d’in ce sirrinsu su biyun, so no secrets” ta k’arashe with a wink. Dariya suka yi ita kuma Lele ta tashi don ta san halin soyayyar iyayenta da har yanzu tak’i tsufa, a kullum adduarta bai wuce her matrimony ya zama tamkar ta iyayenta or more ( Ameen Nadee).

Kitchen ta wuce breakfast ta fara had’a musu dai-dai da available cefanen da suke da shi, tayi nisa a aikinta as usual kunnenta mak’ale da iPod kafin Ummu ta shigo. Before 8 sun kammala sun gyara koina, Karima maid d’in Ummu ta gyara parlor da sauran wurare d’akin ta ta wuce. Wanka tayi da normal routine d’in ta kafin ta fito ko mai bata shafa ba ta baje a gado da towel d’in jikinta quilt ta ja har kanta bayan ta k’ure split nan bacci ya kwasheta.

Sanda ta farka har 11 tayi hamma tayi baccin bai isheta ba, tsaki tayi ta sauka daga gadon. Gyara shi ta fara yi tsaf tayi vacuuming room d’in tsaf, kallon koina tayi ganin yayi mata yanda take so ta sakar masa turare kafin ta koma toilet. Dukda ta wanke sai da ta sake kafin ta watsa ruwa sai da baccin ya saketa da kyau sannan ta fito sai da ta gama mutssike-mutssikenta sannan ta nufi box d’in ta.  Yau native tayi shaawa hakan yasa ta zaro Kampala blue mai bak’i d’inkin straight gown ( her favorite ).

Zura shi tayi tana kallon kanta, murmushi tayi haka nan tayi shaawar d’aura d’ankwali. Normal Zahra Buhari tayi a kanta bayan ta  lank’wasa gashinta dake shek’in hair colorn da ta fesa.

Mindil ta yafa a kan nan ta fito tsaf, kamar mai shirin zuwa gasar kyau barimar hanci na gold ta sanyawa piercing d’in ta da ba kullum take sawa stud ba. Sa mai da tayi yau kam ya k’ara mata kyau ainun.

Wayarta ta d’auka selfies ta saki masu kyau da short videos har ma mirror portraits jaka da takalmi that matches her outfit ta sanya ta nufi parlor. Daga yanayin dining d’in ta gane an yi breakfast, zama tayi ta tattab’a abincin for like 30 mins kafin ta nufi d’akin Ummu da ke aiki a system d’in gabanta.

Hakan yasa bata zauna ba ta shaida mata da tafiyarta office, addua tayi mata sosai kafin ta juya ta wuce zuwa waje. Motarta da aka wanke mata tas ta nufa, zama tayi ta rero adduointa kafin ta ja motar gidan Hajjah ta wuce sai da ta gama shagwab’arta kamar ‘yar goye kafin ta wuce zuwa office.

Yau aikin ba laifi da sauk’i, da yamma ne ma zata yi ma wata amarya bridal makeup a wurin sun ma tayi gyaran jikinta har da henna ita da friends d’in ta. Ayyukan dake gabanta ta tattab’a kafin ta shiga ciki, as usual in tana free ta kan rage musu aiki yau ma hakan tayi. Tana yi suna hira da staffs d’in yanda kasan k’awayenta.

Bayan jumaa ne tayi bak’in friends d’inta da Burhaan yake kira da tarkace. Y’ay’an manya ne kuma y’an kaud’i da iyayi, sai dai ba cima zaune bane dukan su suna da business d’insu wasu kuma suna managing family business ko kuma aikin gomnati kana ganinsu kaga wayayyun mata.

Su biyar suka fara zuwa;  Ayush Maleek, Nana Saraki, Sophia Kabo da Nadeefahr ke kira bestie, Deeyah Habeeb sai Hafsat Jalal saboda maaikatan ciki ana office, order tayi kafin suka fara shiriritar hirar su na bikin Nana Saraki da zaayi nan da 2 months. Asoebin bikin suke magana akai wai wanda aka zab’a bai yi musu ba, Nanan tace su zab’i wanda suka ga ya musu.

Suna zaune aka kawo abinda tayi order, sai da aka canja ankon kafin suka fara cin abincin. Sai wurin 3 kafin sauran 6 suka iso, suma sun yaba da ankon da aka zab’a sai after 4 suka wuce gida bayan sun lek’a su Suleim da suka san su sanadiyyar Lelen.

Tana dawowa daga rakasu direct studio ta nufa, don amaryan ta riga ta iso hak’uri ta basu kafin professionally ta fara zana mata kwalliyan cikeda natsuwa. Ya d’auke su more than an hour kafin aka gama tayi kyau tsaf shiryawa tayi a dinner dress d’inta mai mugun kyau ta d’aura mata d’ankwali ta saita mata net veil d’in ta kafin ta sallamesu, anan aka d’auketa zuwa wurin dinner.

Fitowa tayi zuwa gida don a kwanakin nan daurewa kawai takeyi, tana jin yanayi mara dad’i a tattare da ita. Tana gyara parking mai gadi ya iso yana shaida mata da tayi bak’o tun d’azu a mamakance ta ware idanunta tace ” ni kuma?, me yasa bai tafi ba?”.

Amsawa yayi da ” eh ai hajiya ta ga zuwan shi ita tace ya jira ki nikuma tace in kin shigo in shaida miki sanda zata fita”. Ok tace masa ta nufi parlorn da niyyar ganin waye wannan bak’on.

Da sallama ta shiga k’amshin turaren shi yana mai amsa mata sallamar kafin kwakkyawan gayen ya waigo da murmushi a fuskar shi ya amsa mata, k’irjinta ya buga don bata yi expecting ganinshi ba don haka a d’arare ta zauna.

Gaida shi ta fara cikin k’aramar murya, shiko ya amsa da murmushin da har yanzu bai d’auke daga kan fuskar shi ba. A hankali yace ” na san zaki yi mamakin gani na a nan though it ain’t nothing to be surprised of, as I’ve talked to Farhaan and I’m pretty sure he have talked to you”.

Ajiyar zuciya ta sauke tace ” yes” gyad’a yayi yana cewa ” Good, so how about it?”. Rufe idanunta tayi Khaleel Randagi is a nice guy, ya na da certain features na mazan da kowacce mace take fatan samu ga aji ga hankali. Yet, zuciyarta baa nan take ba. Babu wani namiji da take so take fatan samu kamar Ya Islaam, don haka tace ” I’m sorry Ya Khaleel it is not like I don’t like you or so it’s just that akwai wanda nayi wa alk’awari”.

Shiru ya ratsa tsakanin su tsawon 15 mins, ita k’irjinta bugawa yake na k’aryan da tayi shi ko na jimamin amsar da ta bashi. Sai can ya katse shirun ta hanyar cewa ” Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi a tsakaninku and you can congratulate him for me as he’s lucky to have a gem like you…….”. Kasa k’arasawa yayi don zafin da yake ji haka nan bai yarda da ita ba, jikin shi ya bashi cewa son shi ne ba tayi ba wani abu ba though she covered it.

Ruwa ya d’auka cikin kayan da aka jera mai a gabanshi yace ” cire soyayyarki will be hard for me, amma I’ll try kema ki tayani da addu’a shall in case kin canja ra’ayi then ina jiranki whether today, next week or even next years if you just need me then I’ll be there for you,,,,,na barki lafiya”. Ya k’arashe ya na mik’a mata package d’in da ya shigo dashi, har zata k’i amsa yace ” ba da wata manufa na kawo ba ko kin manta cewa I’m your brother ne?”, murmushi tayi for the for st time da ta shigo ta furta Thanks.

Mik’ewa yayi zuwa waje, rako shi tayi har inda yayi packing motarshi. Isarsu wurin yayi dai-dai da shigowar su Burhaan da ElSadeeq a cikin mota, a kusa dasu sukayi packing. Fitowa sukayi ElSadeeq yake mai tsiyan ” Randagi idonka kenan?”. Dariya yayi yace ” toh sarkin sharri sak’o na kawo ma k’anwata ko an hana ne?”, k’yalk’yalewa da dariya yayi yana cewa ” ba a hana ba, in ma tayi wari ma ji”.

“Ba ma zata yi ba”. Ya bashi amsa, barka da zuwa tayi musu shi kuma tayi masa a sauka lafiya. Bata jira amsar kowannensu ba ta wuce ciki, suma basu dad’e ba su kayi sallama da juna shi ya ja motarshi ya wuce su kuma suka nufo parlorn inda ElSadeeq yake cewa ” shege Randagi Lele yake so”. Tab’e baki yayi yana cewa ” da girmanka kana sa baki a love life d’in k’anwarka baka gudun raini” ya k’arashe da tsaki k’asa-k’asa. Dariya yayi kurum ya na son yaga matar Burhaan a duniya don yaga k’arshen dakon girman da yakeyi kullum bai sake maganar ba har suka wuce d’akin  ElSadeeq d’in.

Khaleel Randagi friends d’in su ne tun suna yara, tare suka yi school tundaga nursery har suka gama primary. Inda kuma suka tafi California a can sukayi high school and college. Daga nan suka rabu kowa ya kama profession d’in da yake so, alak’ar Khaleel tafi kusanci da Farhaan saboda course d’aya suka karanta wato ‘business management” yanzu haka shi ne CEO na Randagi Inc.

Sai after Magrib Ummu ta dawo daga gaisuwar jumaan da ta tafi gidan Hajjah, har lokacin twins suna can yawon su da Safwaan da Zaheer. Sanda ta dawo Lele ta gama dinner ta adana shi a dining, har d’aki ta tardo ta a zaune ta na latsa waya. Barka da dawowa tayi mata ta amsa cikeda kulawa, kafin ta dubeta da kyau tace.

“Bintie, Khaleel yazo wurin ki d’azu I’m not trying to be inquisitive but me ya kawo shi?”. Saukar da kan ta tayi k’asa bata iya k’arya ba but baza ta iya sanar mata abunda ya kawo shi, a hankali cikin inda-inda tace ” Ya Khaleel wai Nana yake so,,,,,,shi ne na gaya masa an sa mata rana bikinta is in two months time”.

Kallon ban yarda dake ba tayi mata don yanda yaron yake gaisheta yau ya sha bamban da yanda ya saba, har ta fara taya ta murnar samun shi ga kuma maganar da Abbu yayi mata d’azu akan Lelen. A hankali itama tace ” Allah sarki, Allah ya sanya alkhairi “, daga haka suka cigaba da wata maganar tasu.

Yau ma da wuri tayi kwanciyarta dukda dai ba tayi wani baccin kirki ba sai tunane-tunane, ganin basu zasu fisshe ta bane ya sanya ta tashi ta d’auro alwala. Ta jima tana kai kukanta ga Allah sai bayan asubah baccin ya kwashe ta a nan k’asa, sanda Ummu ta shigo ne ta tada ta ta koma bed. Gyara mata lullub’i tayi kafin koma zuwa parlor.

Sai 8 ta tashi ba don baccin ya ishe ta ba, sai don alarm d’in ta da ya tada ta. Bud’e idanu tayi ta kafin ta maida su ta lumshe, bata da k’arfi ko kad’an and she can’t say why. Addua tayi ta sauka daga gadon, kamar kullum gyaran shi ta fara first sannan room d’in nata. Kafin ta nufi toilet facial scrub na honey da  ta shafa kafin ta shiga ruwan da ta had’a mai d’auke da sinadarai har da wani rose powder( yana saukar da gajiya sosai ana dafa rose petals da ruwan zafi da kayan tea a sha for for relaxation of mind and body, it’s has an antioxidant, serves as a moisturizer, helps in digestion and it contains vitamin C it helps in weight management, menstrual cramps and more).

Ta dad’e a ciki sai da taji tayi relaxing kafin ta wanke face d’inta ta fito, gashinta tayi spraying da rose and clove hair spray kafin tayi drying tare da rolling kafin tayi packing d’in shi in messy bun. Ta d’ade gaban mirror tana shafe-shafen ta kafin ta shirya cikin lace black mai touches na cream da nude d’inkin A line da yai matuk’ar amsarta, costumes ta sanya kafin ta d’aura d’ankwali murmushi tayi ma kanta tana mai tasbihi ga gwanin iya halitta da ya halicci kyakkyawan surarta.

Dai-dai lokacin Ummu ta shigo da niyyar tashin ta ganin time d’in meeting ya kusa 10 ake farawa ba African time yanzu kuma 9 har da minti 10. Ganin ta tsaf ya sanya tayi murmushi ta na cewa “Masha Allah bintie”, murmushi ta maida mata tana gaishe ta. Amsawa tayi kafin ta shaida mata da jiran ta da ake yi, tashi tayi ta nemo veil nude color da wasu wedge shoes suma nude sai k’aramar jaka na Zara shima nude turare ta k’ara kafin ta fito.

Tana saukowa daga stairs duk suka bita da idanu Ɗayyib yace ” omo, Lele wannan had’uwa haka?, kar ki sa mazan family gwara kai fa”. Turo baki tayi tana mai k’in kallon shi shiko Ɗalhat wayar shi ya ciro ya fara d’aukarta har da videos, ba dai ta tanka ba har sai da ta k’araso.  Abbu ta fara gaisarwa ya amsa da sakin fuska har da tsokanarta shi ma, tura baki tayi a shagwab’e tana diddira k’afafunta a k’asa. Gefen Ummu ta koma ta sake gaisheta kafin ta gaisar da yayyen nata cike da girmamawa da wata bayyananniyar shak’uwa da soyayya a tsakanin su.

Basu b’ata lokaci ba suka karya kumallo ganin lokaci yana gabatowa, suna fitowa motoci suka shige Ummu da Abbu motar su daban sai ita da ElSadeeq sai su twins suma. A jere suka taho da motocin su har izuwa d’akin taro na Yerwa Conference hall. Babban hall ne da yake a farkon shigowa unguwar sukan bada hayan shi in domin seminars, conferences, business workshops har waliman aure ko suna ko saukar alk’urani da sauransu. Yana da parking space da zai iya cin motoci hamsin or more, ba hall d’aya bane halls sun kai shida a wurin ga outdoor suna da shi ga kuma tight security. Ba kowani meeting suke yi a nan ba, sai in akwai gararumin lamarin da za’a tattauna ko kuma in ‘yan familyn sun zo da yawa. Amma most meetings a nan gidan Hajjah ake yi.

Sanda suka iso wurin ya fara cika daga motocin da suke parke zaka tabbatar da hakan, samun wuri sukayi suka parka a wurin da ya dace kafin su doshi hall d’in. A cike yake da iyaye da ‘ya’ya har ma da jikoki kowa da nashi wurin zaman, sai da suka fara zuwa wurin iyayen suka kwashi gaisuwa kafin kowa ya nufi na shi wurin.

Cikin yaran matan wurin dake sanye da lafayun su ta nufa wainda duk sun girme mata, dukan su sunyi aure da ‘ya’yayen su su uku ne a matan kawai basu yi ba amma ba a tab’a ware su ba a ciki suke. Su Zulfaa basu k’araso ba don haka ta shige cikin su Aunty Najwaa tana musu tsiya. Basu ma dad’e ba suka iso, nan suka had’e ana ta hira inda ake jiran isowar manyan gidan.

To 10 su Hajjah suka shigo sanye da tsadaddun lafaya, kana ganin su kaga cikakkun kanurai da zanen su da nad’in da sukayiwa lafayan su zaka shaida hakan ga kuma kalar su black mai matuk’ar kyau da d’aukar idanu. Su uku ne tsoffafi ne kana gani kasan sun girmi duk wanda yake wurin, wato sune iyayen gidan gabad’aya su kad’ai suka rage a manyan gidan. Hajjah Meram / Budu ce a tsakiya sai Yamara ( Hafsat) matar Baba Bunami a hannun dama, sai Ya Madari ( Hauwa) matar Baba Modu.

Suna shigowa aka mik’e cikeda girmamawa suna takawa a hankali kafin su k’arasa Lele ta nufi wajen zaman su sai da ta fara gyara musu suka zauna kafin ta gaishe su, Yamara ce ta amsa da d’an fad’an da halinta ne tace ” ke dai Nadeefah kin daina ziyara ko? Ga gida ga gida ” da harshen kanuri tayi maganar. Duk’ar da kai tayi don ita fa tsoron fad’anta ne yake hanata zuwa gidan Yamaran.

Kafin ta bada amsa Ya Madari tace ” Ya ai ko Lele tana k’ok’arin ziyara sai dai in ayyuka sun tare ta” ajiyar zuciya ta sauke cikin kanurin itama tace ” Eh Ya, aiki ne yai yawa jiya na so zuwa sai na koma gida na tarda Ummu bata nan kuma ta bar min girki” ok ta furta kawai. Hajjah dai bata tanka musu ba don ta san Lelen bata zuwa wurin Yamaran sai in da dalili, wurin zamanta ta koma ta zauna. ( dama haka takeyi duk taro ita ke musu rakiya sai sun zauna kafin ta dawo ta zauna, iyayen suna jin dad’in hakan sosai hakan ne ma yake k’ara musu son ta).

Daidaituwar su a wajen zaman su ne ya sanya kowa ya natsu aka fara gabatar da abunda ya tara su a wurin. Bud’e taro Baba Adam yayi da addua sannan Baba Tijjani ya tashi a matsayin shi na babban dukan zurian ya fara yi wa kowa barka da isowa. Komawa yayi ya zauna Daddy senator ne ya tashi ya fara bayani akan mak’asudin zama wanda mostly akan business d’in su ne wanda kowa yana da alhakin sanin riba da fad’uwa, sai kuma maganar foundation d’in da suka gina kowa zai bada contribution saboda empowerment program d’in da za’a fara nan da wasu satuttuka sai most important kuma auren da za’a sa wa rana.

Tattauna na business d’in aka fara tattaunawa, gold store suka bud’e 2 years back baa tab’a bibiyar ta ba sai a wannan watan da suka samu riba na ban mamaki a cikin shekarun don haka as usual kowa zai ga kason shi dai-dai da share’n shi. Sai kuma na mai iron and steel sai construction companyn su. Sai maganar foundation kuma aka yanke yanda kowa zai sanya na shi da niyyar a satin gaba za a kad’d’amar da ita, a take a wurin aka fara sa donations inda Hajjah tace mai zai hana a d’iba a family account nan Baba Tijjani yace ” ai akwai maganar orphanage wanda kin san daga nan ake kaiwa” . haka ne ta amsa.

Sai da maganar kud’in ya kammalu ne aka fara babbar maganar wato aure, nan samarin suka sake natsuwa don jin me za a tattauna. Gyaran murya Abba yayi ya dube su dukan su kafin ya fara magana ” kamar yadda aka saba a tsarin wannan gida maganar aure a hannun Yaya Tijjani yake a matsayin shi na uba kuma jagora garemu, toh a wannan karon ma bata canja zani ba domin dai maganar aure har biyu ta isa ga hannun Yaya sannan wani abun birgewar shi ne duk na gida ne kana akwai wata hob’basa da muka yi wa ‘ya’yanmu bayan dogon nazari yanzu bikin uku za a sanya in shaa Allah zakuji komai daga bakin Yaya”.

Nan jiki yayi sanyi don jin ance an zama uku duk da dai guda biyun ma ba kowa ke da masaniya ba. A take Baba ya mik’e ya taho gaban podium ya d’an washe fuska sai kuma ya d’an had’e alamar babu wasa, dama shi Baba Tijjani da wuya ka ga murmushin shi. Gyaran murya yayi yace ” A shekaran jiya ne neman aure har biyu ya iso mini wato na Bakura da kuma Farhan inda dukan su na yaba da zab’in su haka za ‘yanuwana duka mun yi farincikin zab’in nasu, a take kuma Abdullah ya kawo wani hanzari bamu k’i amsa ba amma an ba da shawarar a kwana d’aya domin bincike…….”

Nisawa yayi yace ” toh Alhamdulillah sakamakon ya iso mana jiya inda a take muka zartar da hukunci don mun tabbatar da cewa su d’in zasuyi mana biyayya”. Dakatawa yayi kafin ya kalli gefen mazan inda duk sunyi k’uri da idanu wurin kallon shi, kana ya waiga kan matan suma sunyi shiru musamman Lele da ta tabbatar itace cikon ta ukun amma kuma bata san da waye ba.

Maganar da ya fad’a ce ta sanya sandarewar numfashi ga d’aukacin jamaar dake wurin don kowa jin zancen yayi tamkar dirar aradu, su ko iyayen ko alamun hakan ya razana su sai ma alamun farinciki da ya bayyana a fuskokin su. Wayar dake hannunshi ne tayi saurin sab’ulewa sakamakon karkarwa da hannunshi ya fara yayinda zufa ya wanke mai fuska despite the way split ya saukar da rab’a a hall d’in jajayen idanunshi ya d’ago ya na kallon Baban don ji yake tamfar shi d’aya aka tsana a familyn gabad’aya…

<< Nisfu Deeniy 4Nisfu Deeniy 6 >>

3 thoughts on “Nisfu Deeniy 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×