Skip to content
Part 1 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

“Wayyiiiihuhuhuuuuu… jama’a ku saurara, kowacce ƴar abu kaza-kazan uba ta tsaya cak a inda take! an sace jakar uwar amarya cike taf da maƙudan kuɗaɗe…”

Na jiyo wata murya mai tsananin taratsi da hargagi daga can cikin ɗakin uwar bikin tana faɗin haka, a daidai lokacin da na ɗaga cinyar kaza na nufi bakina da nufin yi mata wani yaga na wulaƙanci, irinna an daɗe ba’a gamu ba.

Ƙirjina ne ya yanke ya faɗi rugugum! na ɗaga idanu a tsorace na kalli Fatima, akayi arashi naga ita ɗinma ni take kallo.

Amma ita saɓanin ni da na ƙame da cinyar kaza a hannu baki buɗe, ita tauna take yi, hankalinta kwance kamar tsumma a randa, ga faskeken rabin ƙirjin kaza nan a hannunta ta kusa cinyewa.

Muƙut na haɗiyi wani kakkauran miyau da na ji yana barazanar yaga min maƙogwaro, ɗauke kai nayi daga kan Fatima na waiga gefe kusa da ni, sai naga jakata tana ajiye inda na barta.

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, jikina a sanyaye kamar wacce aka naɗawa na jaki na aje naman hannuna cikin soyayyiyar shinkafar da aka shaƙo min cikin faranti. Lumshe idanu nayi, na girgiza kai, na fara maganar zuci.

‘Yau babu sa’a, daga zama da niyyar ɓarje gumi sai ace anyi sata? Sawuna a likkafa gara in tattara tsumman rayuwata in san inda dare yayi min tun kafin wata tsautsayin ta rutsa da ni in shiga uku.’

Hannu nasa na ɗauki jakata na maƙala a kafaɗa, na kalli Fatima da maɗaukakin mamaki a fuskata, ganin har lokacin cin naman take yi a nutse, bisa ga dukkan alamu hankalinta a kwance yake, har wani ƙara balance tayi a cikin kujera don taji daɗin loda abinci, kamar bata ji satar da aka ce anyi daga can cikin ɗaki ba.

Wani kakkausan kallo na watsa mata, na yunƙura zan miƙe tsaye daga zaunen da nake sai naji caraf ta dafe hannuna.

“Ferry?”

Ta kira sunana da mamaki a muryarta.

“Ina za ki? baki ci komai ba fa, ko naman ma baki ci ba, kuma kinsan dai bamu daɗe da zuwa ba ko Jiddah bamu gani munyi mata Allah ya sanya alkhairi ba balle har mu fara tunanin tafiya.”

Tayi maganar da murya ƙasa-ƙasa yadda babu mai jin abinda ta ce in dai ba a kusa da mu sosai ake ba.

Kafin in ce uffan wata kakkauran mata mai ƙiba ta fito daga cikin ɗakin uwar amarya gudu-gudu sauri-sauri, ta nufi babban ƙofar falon da ake shiga da fita ta rufe, ta ƙara da murza key ta datse ƙofar ɓam.

Ta zare makullin, ba tare da kunyar kowa ba ta janyo wawakeken wuyan rigarta yayi ƙasa-ƙasa har ana hangen tudun ƙirjinta ta jefa ɗan makullin a cikin rigar mama.

Ta juyo tana kallon cincirindon matan da suke zaune rukuni-rukuni a makeken falon, fuskarta ɗauke da wani mummunan murmushin da ya fi kama da na rainin wayau, sai wani irin numfarfashi take saukewa kamar wacce tayi tseren gudu.

Ta fara magana da garjejen muryarta mai kama da na magidanci.

“Sas-sannunku fa, kuyi haƙuri don Allah, kar ku tashi hankulanku!! Abu ne kamar wasa ƙaramar magana tana neman zama babba! Kunji anyi shelar anyi sata ko?

To wallahi ta tabbata da gaske anyi satar, Kamar ɓatan dabo Ƙasa ko sama mun nemi jakar Hajiya Mariya yanzunnan akan gado mun rasa, abu kamar layar zana ƙad-da-bus jaka ta ɓace ɓat!

Ba zarginku muke ba fa, Don Allah ku kwantar da hankalinku kamar tsumma a randa. Yanayi ne na rayuwar duniyar da ta canza, kun san mutane ba gaskiya… inji bahaushe yakan faɗi kai dai ga mutum, sanin zuciyarsa sai Allah…”

“Aunty Kubura menene haka? me nake gani haka? me nake ji haka? ya kike ta wani lallaminsu kina basu hakuri? Sata ne dai an riga anyi kuma na tabbata kwarankwatsa dubu a cikinsu ne akwai ɓarauniyar nan. Duk inda jakar nan take na tabbata bata bar cikin falon nan ba don ƙasa da minti bakwai da suka gabata jakar tana kan gado a ajiye.

Don haka wallahi tallahi yau in za a kwana a yini sai sun fito da jakar nan sannan ko wacce za ta fita daga nan! Caje ne daga sama har ƙasa sai munyi in ta kama daga nan har caji ofis sai mun je!”

Idanu warwaje nake kallon wata figaggiyar matashiyar mata da ta fito daga cikin ɗaki tana faɗin haka cikin fushi da masifa, bakinta har yana kumfa da tartsatsin miyau.

A tsorace na sake mayar da idanu kan Fatima da har lokacin hannunta ke damƙe da nawa, da rawar murya mai cike da tsoro nayi ƙasa ƙasa da murya na raɗa mata.

“Fatee na shiga uku na lalace! Wallahi Mukhtar bai barni ba na fito gidan bikinnan, yau idan suka riƙe mu anan ina zan saka kaina?…!”

Kafin Fatima ta ce wani abu ɗaya daga cikin hamshaƙan matan da suke zaune a can wani ɓangare na falon ta miƙe tsaye a fusace ta kalli tsigaggiyar nan ta fara maida mata martanin maganganunta cikin fushi

“Wai wane irin zancen banza kuke yi haka? ku kalle mu dakyau ku gani, kusan duk cikar mu babu wata wulaƙantacciya mai wulaƙantacciyar sutura balle har ku maƙala mana satar ƴan kuɗin da kila ma ba wasu masu yawa bane.”

A ɗarare na kalli kayan jikina, inda Allah ya taimakeni zanina na ƙasan akwati ne a jikina, Chiganvy Gold, atamfar da daƙyar da jiɓin goshi na mallaketa, tsabar na so siyanta bazan iya ƙayyade kwanaki nawa nayi ina ƙwangen kuɗin cefane da na karyawa kafin na tara kuɗin siyanta ba. Naira dubu goma sha uku cif haka na caskewa Hajiyar Barrister kafin na samu nasarar mallakar atamfar, na ƙara asusun dubu huɗu cif na ba Yayana Musty don yayi min ɗinkin kece raini!

Ajiyar zuciya mai nauyi na sauke na mayar da hankali kan matar nan inda naji ta ci gaba da cewa;

“Mun ci, mun sha, mun rufa mun tada kai balle har ayi tunanin za mu gani mu ɗauka.
To Satar me za ayi? ina ƙudan yake balle romonsa? in dai da gaske ne ma anyi satar to kuwa na tabbata ko rantsuwa nayi babu kaffata ƴar iskar ɓarauniyar baza ta wuce a cikin ku ƴan’uwanta na jiki-jiki da kuka maƙale kuna zaune a cikin uwarɗakinta ba…”

Maganar da tayi sai ya zama kamar mabuɗin bakin ko wace mace da take zaune a falon, nan take aka fara cece-kuce da ƙananan maganganu, aka fara zage-zage da wannan figaggiyar kamar za aba hammata iska.

Tana masifa ana maida mata martani, ko wacce mace na ƙoƙarin kore gaskiyar zancen anyi satar balle har a maƙalawa ɗaya daga cikinmu mazauna falon.

Aminiyata Fatee ta gallah min harara, ta fusge hannunta daga cikin nawa, cikin fushi da ƙarfin hali ta fara min magana da faɗa-faɗa.

“Ke dallah banza ki nutsu ki kwantar da hankalinki, to miye don ba’a barki ba kika fito? kanki farau satar fita? da wannan mutsu-mutsu da zare-zaren idon da kike yi ai sai ki zama abar zargi a cikin mat…”

Wani mahaukacin ƙaƙƙarfar ihu mai cike da amo da amsa kuwwa da aka ƙwallah daga cikin ɗakin uwar bikin yasa kusan duk mazauna falon muka miƙe tsaye a tsorace, tsit kake ji ! duk hayaniyar mata ya tsaya cak kamar ɗaukewar ruwan sama.

Hankalinmu bai ƙara mugun tashi da ɗugunzuma ba sai da wannan ƙatuwar da aka kira da Aunty Kubura ta fara jero sallallami tana tafa hannaye, fuskarta bayyane da matsanancin tashin hankali, da saurin murya mai ɗauke da damuwa ta ci gaba da magana,

“Shi ke nan! Ta faru ta ƙare anyiwa mai dami ɗaya sata. Abinda muke ta gudu da alamun shi ne ya faru. Mugayen aljanun da suka yi dafifi a jikin Aunty Adama ƙanwar Hajiya Mariya sun tashi.

Wallahi duk wacce tasan ta ɗauki jakar nan ina bata shawara ta fito salin-alin sawunta a likkafa tun kafin a fito da ita a tozarce a wulaƙance.

Don wallahi aljanunta ƴan fallasa ne, kuma duka suke yi, idan suka zuciya babu ruwansu da mai gaskiya da mare gaskiya, kan mai uwa da wabi suke yi da wacce taji da wacce bata gani ba su naɗi fata”

Kayan cikina ne suka tattaru suka cure guri ɗaya, lokaci ɗaya jikina ya ɗauki rawa kamar ana kaɗa min ganga, hanjin cikina sai mazari suke yi kamar ana tsakiyar hunturu. A ƙanƙanin lokaci idanuna suka cicciko da hawaye, bayan wasu daƙiƙu sai ga hawayen sun zubo shar…

Na kalli Fatima ita ma ta kalle ni, a wannan gaɓar ƙuru-ƙuru na hangi matsanancin tausayina a idanunta, domin ta san Mugun tsoro ne da ni.

Na tsani aljanu, na tsani tashin aljanu a gabana, tun ina ƴar ƙanƙanuwar yarinya duk idan naji labarin wata wacce na sani tana da aljanu ni da ita haihata-haihata.

Ko a cikin dangi ne nakan guje ta faufau balle kuma a cikin ƙawaye ko kuma ƴan ajinmu, a islamiyarmu na canza aji fiye da sau goma saboda tsoron tashin aljanu.

Kafin wata a cikinmu tayi wani yunƙuri don motsawa ko cewa wani abu sai muka fara jin buge-buge daga cikin ɗakin kamar ana watsi da kayayyaki, ko kuma ana mugun dambatuwa.

Can kuma sai muka ji an sake yanka ƙaƙƙarfar ihu a karo na biyu, aka buɗe ƙofar ɗakin buf sai ga wata gajeriyar mace mai kama da wada wacce da alama ita ce Aunty Adaman ta fito falon a guje daga cikin ɗakin.

Daga ita sai shimi a jikinta, ƴan uwanta har da uwar bikin suna biye da ita da gudu suna yunƙurin riƙeta, fuskokinsu cike da maɗaukakin damuwa suna cewa;

“A tara jama’a… ku tare mana ita. Taimako jama’a ku riƙeta kar ta futa waje, yunƙurin guduwa da ita suke yi ako wane lokaci.”

Abin mamaki da tsoro Aunty Adama tana zuwa kusa da ƙafafuna ta zube ƙasa yaraf kamar an taɗiyeta, takai wa ƙafafuna wani mugun damƙa da wawaso da yasa nayi taga-taga kamar zan faɗi amma na tsaya daƙyar bayan na damƙi ƙugun Fatima da take kusa da ni, Aunty Adama kuwa ta riƙe ni ƙafafuna tamau.

Tsananin tsoro da firgici yasa na ƙame a tsaye kamar wata mutum-mutumi, na kasa ƙwaƙƙwaran motsawa na kasa numfashi mai ƙarfi, gani nake da nayi wani ƙwaƙƙwaran yunƙuri za ta zare min rai.

Sama-sama nake jiyo ringing ɗin waya a cikin jakata da ke kafaɗa tana rera waƙar

“Fareeda gimbiya… fareedah kin zama sarauniyar mata…”

Waƙar da idan na ji ta na tabbatar mijina Mukhtar ne yake kira na…

‘Na shiga uku!!!’

Na ayyana hakan a zuciyata wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle min kamar an buɗe famfo.

A Fusge kamar daga can nesa naji muryar wata mata tana cewa;

“Baiwar Allah ki nutsu, ki kwantar da hankalinki. Da alama aljanunta suna son ki ne…”

Ƙaƙƙarfar kukan da na buɗe baki na fashe da shi yasa mai maganar ta kasa aje numfashin maganarta daidai.

‘So dai? aljanun ne suke so na? A duniya in rasa suwa za su so ni sai aljanu? ni kam yau wace irin mummunan rana ce a gare ni?

‘Fareeda kar ki tafi gidan bikinnan, in dai ni mijinki ne kuma na isa da ke ban baki izinin ki tafi gidan bikinnan b…’

‘Haba Baby haba haba don Allah? me yasa kake irin haka ne wai? Jiddah ce fa za tayi aure ba wata ƙawata can nesa ba. Fisabilillahi duk yadda muke da Jiddah ace bikinta ya zo bazan samu halarta ba? haba ai duniya ma sai ta zage ni, ka tuna yadda tayi uwa tayi makarɓiya a bikinmu…

Ni na sata dole tayi? na dai faɗa miki kar ki fita ko ina, gobe zan dawo. Idan kuwa kika fita wallahi tallahi duk abinda nayi miki ke kika jawo wa kanki. Domin a wannan karon zan ɗauki mummunan mataki a kanki. Ƙit ya katse wayar ba tare da ya sake sauraren abinda zan ce ba.

A cikin ɗan taƙaitaccen lokaci taƙaddamar da muka kwasa da mijina Mukhtar a ɗazu da safe ya faɗo min arai, da yake ni ɗin mai kunnen ƙashi ce tsautsayi da rabon ayi yasa nayi fatali da hanawarsa, kashedinsa, rantsuwarsa nayi fitowata bayan ƙawata Fatima ta shirya ta biyo min har gida da direbanta.

“Baiwar Allah kiyi haƙuri, kibar kuka, yanzunnan za mu ɓamɓare hannuwanta daga jikin ƙafafunki, ki nutsu, kiyi hakuri babu abinda za tayi miki.”

Ɗaya daga cikin ƴan uwan Aunty Adama ta faɗa min haka, da sassanyar murya mai ɗauke da alamun rarrashi don kwantar min da hankali.

Sannan ta kalli matan suke tsattsaye cirko-cirko a falon ta buɗe murya ta ce;

“Ina Hafizai mahaddata Alƙur’ani? ku marmatso kusa da ni kuyi aikin lada.”

Sai tayi zaman dirshan a gabana tayi basmala da zazzaƙar murya ta fara rero karatu cikin suratul-baƙarah.

Tsoro ne ko kuwa rashin iya karatun ne oho! a cikinmu babu wacce ta tayata karatun, sai zazzaƙar muryarta ne ya ci gaba da ratsa dodon kunnuwanmu cikin wani daddaɗan saut da iya ba ko wace kalma haƙƙinta.

Bata yi mintuna bakwai cikakku tana karatun ba naji hannuwan da sukayi ram da ƙafafuna sunyi sanyi laƙwas, ina motsawa naji zan iya janye ƙafafuna ai a saba’in na matsa can gefe guda ina zazzare idanu kamar wacce tayi ƙarya a gaban sarki, sai kallon Adama nake yi da wani irin kallo mai bayyana tsananin tsana da ƙyama, a zuciyata babu abinda nake ja mata sai Allah ya isa na firgici da tashin hankalin da ta ƙara jefani a ciki, a daidai wannan lokacin na tabbata da za a auna jinina za aga ya hau.

“Alhamdulillahi! Yau an taki sa’a, sun jirge da gaugawa.”

Uwar bikin ta faɗi haka fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki, wani abu a cikin kwalba mai kama da magani ta miƙawa wacce tayi karatun tana faɗin,

“Ungo nan Aliyah, yi sauri ki shafa mata a goshi, idan tayi barci ta tashi za ki ganta garas kamar ba ita ba.”

Ana gama shafa mata suka yi kama-kama suka kaita cikin ɗaki, sannan suka dawo cikin falon.

Umarnin zama suka mana sannan wannan wacce tayi Ruƙya ta fara mana nasiha tana janyo ayoyi da hadithai, a ƙarshe ta dire da haɗamu da girman Allah da na ma’aki kan duk wacce ta ɗauki jakar nan ta dawo da shi cikin mutunci da lalama ba tare da anyi tsiya-tsiya ba.

Hajiya Mariya ta ƙara da cewa;

“Ni wallahi ba kuɗin jakar ne ma yafi damuna ba, akwai muhimman takardun His Excellency a cikin jakar! I’m sorry to say idan ba’a ga jakar nan ba gaskiya daga nan sai dai a kwashe mu zuwa station din gidan gayu…”

Da rarrafe na ƙarasa gabanta saboda tsananin tashin hankali.

“Hajiya… don ya rasulillahi ki rufa min asiri… kin sanni tun ba yau ba wallahi bazan taɓa ganin abin wani in ɗauka ba. Ki min rai ki sallameni in koma gida, bikinnan ba da izinin mijina na taho ba ga shi yayi min saƙo yana hanyar shigowa kaduna. Idan ya dawo ya tarar bani a gida na mutu kawai, na tabbata a zafin rai da rashin hakuri irinna Mukhtar igiyoyin aurena da suke hannunshi tsaf zai tsittsinka su…”

“Kiyi haƙuri Fareeda, a al’amarin sata irin wannan kowa ma abin zargi ne, kinga har ƙannaina ban cire su a cikin ɓarayin ba.”

Tsabar tashin hankali yasa ban ankara da waya take dannawa a hannunta ba sai da naji tana cewa;

“Hello… Inspecter…”

Rabon A Yi 2 >>

4 thoughts on “Rabon A Yi 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×