Skip to content
Part 25 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Kamar a mafarki, Fareeda ta ji muryar Sayyid da Shahid sun yanka wani rikitaccen kuka mai cike da ƙara da taratsi. A firgici tayi wani irin juyi ta dirgo ƙasa daga kan kujera, da sassarfa ta fice don gane ma idanunta abinda yake faruwa.

Ƙanƙance idanunta tayi da wani irin bala’in ɓacin rai tana kallon Fatima da ta riƙe hannayen Shahid da hannunta ɗaya, ɗayan hannun kuma babu tausayi babu jinƙai ko tunanin ƙaramin yaro ne a gaban Fareeda ta sake ɗaga hannu ta tsinka ma yaron mari.

Da Shahid da aka tsinkawa mari, da Sayyid yake tsaye gefe ɗaya ya ƙanƙame hannayensa a ƙirji yana makyarkyata cikin tsoro da firgici, a tare suka sake ƙwalla ihun kuka.

Ita kuwa Fareeda kawar da kanta tayi da sauri ta lumshe idanu, nan take suka cicciko da hawaye. Wani irin zafi ya lulluɓeta lokaci ɗaya, har wani ƙaiƙayi take ji a kumatunta kamar ita aka tsinkawa mari.

Da wani irin fusata da ɓacin rai matsananci ta buɗe idanunta da suka canza launi lokaci ɗaya, ta ɗaga ƙafa a fusace za ta ƙarasa gurin Fatimar sai taja ta tsaya cak, tunawa da tayi da wata magana ta Malam bahaushe da yake cewa.

“Ka so naka, duniya ta ƙi shi. ka ƙi naka, sai duniya ta so shi.”

Fatima da take kallon yanayin Fareeda ta ƙasan idanunta ganin ta ja ta tsaya sai ta sake ɗaga hannunta na dama fuska cike da murmushin mugunta ta sake fallawa yaron mari, sannan ta saki hannayensa haɗe da ture shi ya faɗi ƙasa yana rusa kuka.

“Don Uwarka waccan da take tsaye zan nuna maka kai ƙaramin mare kunya ne. Idan ita gantalalliya ce ta kasa baka tarbiya mai kyau ni zan koya maka.”

Da gama faɗin haka sai taja ta tsaya ta riƙe ƙugunta, jira take Fareeda ta zaburo ta naɗa mata nata marukan kamar yadda tayi ga ɗanta.

Sai taga ko da Fareeda ta ƙarasa gurin ɗanta ta ɗaga jikinta na rawa ta rungumeshi a ƙirjinta. Ta ƙarasa kusa da Sayyid ta kama hannunsa suka nufi ɓangarenta, har lokacin jikinta bai daina rawa ba.

Tana jin sa’adda Fatima taja mata wani dogon tsaki haɗe da cewa,

“Sakarya kawai.”

Daƙyar ta iya ƙarasawa cikin falonta. Nan kan kafet ta zauna ta rungume ƴaƴan a jikinta ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka, zuciyartaa in banda tuƙuƙi da suya babu abinda take yi.

Fatima ba fin ƙarfinta tayi ba, amma ko kaɗan ba ta son zubar da mutuncinta ta hanyar biye mata su dinga kace-nace kamar wasu dabbobi. Balle irin yadda Fatima ta dinga marin yaron kowa zai san da gayya tayi, ta yi ne domin ta tanka mata. Ita kuwa in Allah ya yarda baza ta ƙara biye mata suyi cacar baki ba, ba ita ce sa’ar yin ta ba, Mukhtar ne, don haka zai dawo gidan shi zaiyi wannan shari’ar, ita kam baza ta iya ba. Tana lallaɓa lafiyarta asa ta cikin wani mummunan hali na tashin hankali da ko kusa ba ta fatan shigarsa.

Acan ɓangaren Fatima kuwa tana shiga ɗakinta wayarta ta ɗauko, ta nemi gurin zama akan kujera ta lalubo lambar Mukhtar ta danna mishi kira.

Yana ɗagawa daga can ɓangaren sai ta sakar mishi kukan kissa. A rikice ya fara tambayarta menene? me yake faruwa? Wa ya taɓa mishi ita?

Sai da ƙyar ta iya sassautawa da kukan ta fara Magana.

“Haskenah! A tunanina ko ban aure ka ba ƴaƴan Fareeda ƴaƴana ne?”

“Haka ne! Me yake faruwa?”

Ya tambayeta cikin zaƙuwa.

“Wai kawai don na ji su Sayyid suna wasa a tsakar gida na fita ina tsokanarsu nan take Fareeda ta fito a fusace ta janye ƴaƴanta. Ta saka su sukai ta min rashin kunya suna zagina, kalaman tozarci ta dinga faɗa musu da turanci tana nuno ni su kuma suna kwaikwayonta haɗe da min daƙuwa. Na tausaya maka Haske, wallahi idan baka yi da gaske ba, Fareeda sai ta lalata maka tarbiyar waɗannan ƴaƴan da kake alfahari da su, ba don komai za tayi hakan ba sai don baƙin kishi irin nata, idan za ka ji shawarata, ka ɗauki mataki da gaggawa tun kafin lokaci ya ƙure maka.”

Ta sake fashewa da kuka sannan ta katse wayar, daga bisani ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya yadda ko ya kira bazai same ta ba.

Nan kan kujera ta miƙe ƙafafu tana ƙyalƙyala dariya ita kaɗai kamar sabuwar kamu.

Daƙyar da suɗin goshi ta samu ƴaƴan suka yi barci. Daƙyar ta rarrashi kanta ta tsayar da kukanta, ta fara rarrashin su biyun da suka urunce da kuka kamar duk su biyun aka mara.

Bayan tsawon lokaci suka yi shiru, lamo sukai kwance a jikinta suna sauke ajiyar zuciya. Jikinsu ya ɗauki zafi sosai, da ta kalli fuskar Shahid sai wasu zafafan ƙwalla su sake taruwa mata saboda yadda shatin yatsun Fatima suka fito ruɗu ruɗu.

Kan kujera ta lallaɓa ta kwantar da su, ciki ta shige ta haɗa musu ruwan wanka. Ko da ta fito sai ta tarar duk sunyi barci. Kamar za ta tashe su, sai kuma taga yadda jikinsu yayi ɗumin nan ga ajiyar zuciyan da suke ta saukewa duk da suna barci gara ta bari idan sun tashi sai tayi musu wankan.

Ɗaya bayan ɗaya ta ɗaukesu zuwa cikin ɗaki ta kwantar da su kan gado. Falon ta koma ta zauna, tagumi ta buga da hannu bibiyu, zuciyarta cike da tunanin inda ta taɓa kuskure ma Fatima a mu’amalar ƙawance da suka gudanar na tsawon shekaru.

“Ashe ƙauna da yarda suna juyewa su zama matsananciyar ƙiyayya da jin haushi? Tun bayan da Mukhtar ya auro Fatima cikin gidannan babu abinda take kallo a cikin idanunta sai matsananciyar tsanarta da jin haushinta. Ga shi yanzu abin har ya fara gangarowa kan ƴaƴanta.

Ko dai akwai wani mummunan abu da ta taɓa yi ma Fatiman a baya ne da take burin ɗaukar fansa a yanzu?

Tayi imani da Allah, ta san aure tsakanin Fatima da Mukhtar ko kaɗan babu haramci a ciki. Kalmar ana barin halas ko don kunya bai taɓa samun matsuguni a zuciyarta ba balle har ta ƙullaci Fatimar.

A tunaninta ko basuyi zaman daɗi ba, za suyi zama ne irinna kowa tasa ta fisshe shi. Amma na miye duk wannan tsana da ƙiyayyar da take nuna mata?”

Tun daga bakin ƙofar falonta take jin yadda Mukhtar yake ƙwallah mata wani irin mahaukacin kira. A gigice ta miƙe tsaye tana zare idanu, ya buɗe ƙofar ya shigo fuskarsa na bayyana wani irin ɓacin rai da fusata da ta daɗe bata gani a tare da shi ba.

“Mmmmme ya faru? Menene?”

Ta tambaye shi cikin rawar murya.

“Fareeda, me nayi miki da zafi da za ki dinga nuna min irin wannan matsananciyar tsanar? Kin nesanta kanki da ni, ƴaƴan nawa da nake gani ina jin daɗin samunsu daga gare ki su ma so kike ki nesanta su da ni ta hanyar lalata min tarbiyarsu?”

Idanunta a warwaje, fuskarta cike da mamaki da tsoro, a ƙwaƙwalwarta take ta jujjuya maganganunsa don gano inda ya dosa amma sam bata gane ba.

Da sassarfa ta taka ta haɗe tazarar da ke tsakaninsu, ta miƙa hannuwa za ta riƙo nasa da sauri ya janye hannayensa kamar wacce ta nufe shi da bakin wuta. Ta buɗe baki za tayi magana yayi saurin dakatar da ita da wani irin gigitaccen tsawa.

Daman tun safe akwai fushi da ɓacin ran jin maganar ita ke amfani da magani don kar ya samu damar kusantarta. Don haka yanzu da ya samu damar da zai wanke ta wani irin tsiya na bala’i yake zazzaga mata kamar bai taɓa sanin wacece ita ko kuma daga ina ta fito ba. Daga ƙarshe ya ɓuge da maimaita mata abinda Fatima ta ce ita da yaran sunyi mata ya kuma kora mata kashaidin kar ta kuskura ya sake jin makamancin irin wannan shirme da dabbancin, idan ba haka ba zai ɗauki mummunan matakin da bata taɓa tsammani ba.

Fareeda ta kasa kuka, sai wani irin ajiyar zuciya take saukewa cikin zafin rai. Tun tana tsaye tana saurarenshi, bata san sa’adda ta sulale zuwa ƙasa ba, mamaki da ɓacin rai haɗe da baƙin ciki ke neman sumar da ita. Bata san sa’adda ya fice ba, kawai buɗe idanu tayi taga baya falon.

Minti uku ta ƙara durƙushe a gurin tana nishi kamar mai naƙuda. Sai kuma ta miƙe a zabure ta nufi cikin ɗakinta, har lokacin su Sayyid suna kwance suna barci.

Tun a tsakar ɗakin ta fara cire kayan jikinta tana hurgi da su, har ta zama daga ita sai rigar mama da ɗan kamfai. Durowar kayanta ta buɗe ta fara janyo kayan cikin sauri tana ɗaɗɗagawa har ta ciro wasu sakakkun riga da wando ƙananu, wandon iya gwuiwa, rigar kuma da kaɗan ta ɗara cibiyarta.

A gurguje ta saka kayan a jikinta, ta fice daga ɗakin gudu-gudu kanta babu ko ɗankwali, daman shekaran jiya ta tsefe kan, yalwataccen gashinta ya kwanta a saman kafaɗunta.

Silifas ɗin da take sakawa a cikin ɗaki tana tafiya saboda sanyin tiles shi ta zura a kafafunta ta fice daga apartment ɗin gaba ɗaya. Kai tsaye ɓangaren Fatima ta nufa da sassarfa, idanunta sun kaɗe sunyi jajur.

Wani babban sa’a da ta ci shi ne tana murɗa hannun ƙofar ya buɗe, aikuwa ta afka cikin falon a guje kuma a haukace.

Mukhtar na kwance kan doguwar kujera, Fatima ta sa gwuiyawunta a ƙasa tana mishi tausa kawai Fareeda ta afko cikin falon babu ko sallama.

Ko kafin suyi wani yunƙuri na magana ko na miƙewa tuni Fareeda ta isa ga Fatima ta damƙi wuyarta ta miƙar da ita tsaye, da wani irin ƙarfi kamar ba ita kaɗai ba ta wujijjiga Fatiman sannan ta haɗa ta da bango, ta shaƙe ta da hannu ɗaya hannu dayan kuma ta fara gaura mata mari, tana marinta tana cewa,

“Ni za ki gwadawa makirci?”

Ko kafin Mukhtar ya samu nasarar ɓanɓare Hannayen Fareeda a wuyan Fatima ta yi mata maruka sun kai sha biyar.

Fatima kamar wacce aka riƙe ma hannaye ta kasa wani kataɓus na ramawa ko kuma yunƙurin ƙwacewa, ihu kawai take ƙwallawa tana faɗin Haskenah ka ceceni, ta haukacee za ta kashe ni.

A haukace Fareeda ta damƙi damtsen hannun Mukhtar na dama ta kai bakinta ta gantsara mishi wani matsiyacin cizo kamar za ta gutsure fatar gurin. Saboda azaba Mukhtar bai san sa’adda ya ƙwallah ihu ba.

Ita dai Fatima tunda ta samu tsira ko ta kan Mukhtar bata bi ba da rarrafe ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa.

Da ƙyar da gumin goshi ya samu nasarar ɓamɓare hannunsa a bakinta bayan yayi mata wani mugun damƙa a gashinta, yadda Fatima ta shige da rarrafe haka ya bi bayanta yana yi yana waigen ko Fareeda ta biyo bayansa…

Ina da mare lafiya, jiya a asibiti na kwana sai da yammannan na dawo gida. Sannan ina da biki wannan satin.

<< Rabon A Yi 24Rabon A Yi 26 >>

2 thoughts on “Rabon A Yi 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×